Nine Farkon Fara Zina Da Ita, Nayi Silar Ɓata Mata Tarbiya Har Ta Zama Karuwa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalam Alaikum.. Allah gafarta Mallam, nine nake lalata da wata yarinya inama tunanin nine farkon fara zina da ita, nine silar ɓata mata tarbiya gaba ɗaya. Amma ni yanzu na tuba nabar zina kuma har nayi aure na haihu harda yara. Ita kuma wannan yarinyan har yanzu ina ganinta kan titi tana yawo ta zama karuwa. Idan mun haɗu ko kallonta bana son yi balle ma asan cewa na taɓa kulla wata hulda da ita saboda kariyan mutuncina da kimana. Shin mallan yanzu a hakan meye matsayina gashi ni na tuba amma kuma ita tana kan aikinta na alfasha wanda nine sanadiyyar shigarta shi, shin ni bayan neman Allah gafara ya isa ko sai na nemi gafaranta, 'yan uwanta da kuma kila mijinta idan zata yi aure?

    𝐀MSA❗️

    الحمد لله وحده.

    Dafarko dai muna tayaka murna da Allah yasa kagane wannan danyen aiki daka aikata babban kurene tun mutuwa bata riskeka kaba, Allah yasa tubanka ya dore yakuma karbi tuban, yasa wannan yarinya ta tuba tadena.

    Hakika kaci amanar wannan yarinya kaci amanar musulunci da al'ummar musulmai ka cutar da rayuwarta ka cutar da iyayenta kaci Amanar Allah da manzansa, baya kuma da cin zarafinta amatsayinta na mace wacce musulunci ya girmamata. Zina dai zunubine mai girman gaske wanda ke kwashewa mutum albarkar rayuwa.

    Sannan kasani tundaka ranar daka yaudareta kaci mutuncinta harkai zina da ita wallahi duk wata zina datayi bayan wacce kafara yaudararta to kana da kaso nazunubi acikinta, kasani Allah ba'azzalumi bane ba zai barka hakaba.

    kai yanzu zakaso ace, Uwarkace wannan yarinyar? zakaso ace kanwarkace wani yazamto sanadiyyar zamanta haka? zakaso ace yayarkace takasance haka ko zakaso ace 'yarkace haka? gashi yanzu kaida kanka bakama so kanuna alamarma kasanta, to kasani zina bashice wallahi duk wanda yai da uwar wani za ai datasa uwar, inkai da 'yar wani za ai dataka, idan kai saida kabada kuɗi ko wani abu najan hankali idan Allah yaga dama kai taka 'yar ita zata nema ayi da ita kuma acikin gidanka za ai zinar da ita akyaleka da bakin ciki kamar yanda kasa iyayen wata bakin ciki, kullum baka da sukuni.

    Anan zamu kara fahimtar fasaha da hikima cikin hadisan Annabi sallallahu Alaihi wasallam wanda ya ce duk wanda ya assasa wani abu na alkhairi duk wanda yai aiki ko koyi da wannan alkhairi to asalin wanda ya assasa  alkharin zaita samun ladan duk wanda yai aiki da alkhairin koda shawarace kuwa yabayar wajan wani akin alkhairi har duniya takare haka wanda ya assasa aikin sharri.

     Yanzu kaga wannan baiwar Allah kaine farkon wanda ya assasa mata zina duk wanda yai zina da ita kanada zunubinka na musamman amatsayinka nawanda ya assasa mata zina.

    Amma dangane da neman yafiyar iyayenta ko mijinta duk wannan bai taso ba, saboda Allah bayasan bayyana mummunan Abu haka shari'a batasan abun da zai haifar da fitina atsakanin al'umma wanda bayyana ma iyayenta da neman gafararsu zai iya buɗe wata sabuwar kofar fitina da rikici atsakani, dan haka ka kara zage damtse wajan nema mata gafara wajan Allah da iyayenta, miji kuwa bata samu ba, balle kanemi gafararsa.

    Kadage wajan bin duk wasu hanyoyi nakaga kajawo hankalinta danta daina wannan mugun aiki, zance baka kulata dankare mutuncin kanka baima taso ba anan, dole kabi hanyoyin dakabi wajan yaudararta harka shawo kanta kai zina da ita, sune za ka sake bi wajan jan hankalinta dataji tsoran Allah ta tuba kamar yanda katuba, kanuna mata kaima kayi nadamar abun da ka aikata da ita, kuma kanajin ciwon abun atare dakai, kada ka karaya wajan bin hanyoyin dazaka tabbatar kaci nasara wajan tadena karuwanci ta tuba.

    Idan Allah yasa kai nasara ta tuba, to tunda kaine kasata wannan hanyar kuma katuba, itama ta tuba, to ihsanin dazakai mata shi ne ka aureta kazauna da ita itama tasamu zurriya, ko kuma katashi haikan kashiga nema mata mijin aure nakirki ya aureta danta samu zurriya dayyiba, dan kasamu ko Allah yakalli tubanka yayafema wancan cin mutunci dakai mata ko Allah zaisa yakalli niyyarka yakarbi tubanku kai da ita baki daya.

    wannan shi ne kadai abun da zakayi idan harda gaske kayi nadamar wanan mugun aikin naka kuma ka gwammace  jin kunyar duniya a kan ta lahira agaban mutanenen duniya baki ɗaya, ta duniya kuwa watakilama iya unguwarkune kawai kuma bata kaiwa wata kana cikinta wannan jin kunyar shi ne Zaman lafiyarka.

    Sannan ku kuma mata irin waɗannan bayanai nayanda ake maida rayuwarku kamar ta dabbobi awulakantaku wulakanci makaskanci ya isheku izinah a kan yanda kuke bada kanku bori yahau yayi sukuwa daka baya yafi kowa kinku daganinku aruyuwarsa.

    'yar uwa yanzu kiduba dai yanda mai tambayarnan yake bayani waifa yama tuba kenan, amma haɗuwa da ita kan hanya bayasan yi, shi namiji inzai zina da mata dubu ba muwarsa bane bawanda ya isa yagane kuma zaisamu wacce zata zauna dashi, ayayinda ke kuma zai lalata miki rayuwa cikin wasu 'yan mintuna biyar zuwa goma dazaki wulakantar dakanki danki faranta masa rai ki kuma fusata mahaliccinki mahaliccinsa ga kuma kaskanci da tozarci dazaki janyowa rayuwarki har ta 'yayanki kinci amanarsu, iya abun da wanann mai tambayar yafadi acikin tambayarsa ya isa wa'azi da kukan zuci a kan yanda kuke saida rayuwarku da mutunciku da darajarku da Allah yaimuku ga wasu maikiyanku makiyan rayuwarku, a kan naira dubu ɗaya ko uku dazai baki kiyi ankon bikin kawarki ko yasaki amotar daya sato kuɗin babansa ko uwarsa ya iyo hayarta, ko yadakko batare da ubansa ya sani ba, ko saboda kuɗin kifin gwangwani da maltina da shinkafa dakayan makulashe dazai dunga saya miki kina zuwa dasu collage kina nuna kewatace alhali mahaukaciyace wacce dabba tafita tunani maikyau.

    Saboda darajar 'ya mace ne fa musulunci yai umarni daki dunga rufe duk jikinki inzaki fita saboda tsadarsa ne aka umarceku da hakan, bawai dan atsananta muku bane, duk wani abu mai tsada ɓõyeshi ake ba'a bayyanashi afili shin bazaku hankaltaba yaku uwayen al'ummar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam! koda kuɗi ɓõyesu ake bakasan kowa yasan nawane alalitarka saidai kadunga dakkowa kaɗan-kaɗan kana hidimarka meyasa saboda suna da daraja, to kuma darajarkuce tasa musulunci ya umarceku da ku kame kanku tahanyar sutura mai kyau, da kin ruduwa da kyalekyalen duniya.

    Mace zinari ce bata tsufa, shiyasa sanda wani yagi sake alokacin ne kuma wani sai ganki ya ce yana sonki, kuma babu mummuna cikin mata saidai inbata gyara kanta bane danme zakibar wani mugu azzalumi makiyinki ya lalalata miki rayuwa da hanakalinki da kimarki da mutuncinki, haka kawai dan wata karamar bukata ta duniya, ya kamata muyi tunani na nutsuwa kugane masu alaka daku danku zauna dasu kuyi rayuwa mai kyau gwargwadon abun da Allah yabasu, ba masu aro mashin roba-roba, ko masu aro mota suna zuwa suna hure muku kunnuwa kuna mantawa da irin darajar da Allah yai muku ba, ko masu shiga rigar addini suna yaudararku dasunan cewa sudin na Allah ne, a'a kawai wani abune ajikinki suke bukatar su ɗanɗana suji yaya kuke su gujeku.

    Da rayuwa cikin kaskancin da fushin mutane da fushin Allah dana masu imani gwara rayuwa cikin mutunci da talauci. Allah yasa mufahimta kuma mu gane.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.