Raɗa Suna Jiya Da Yau

    English Rendition as “Naming Past and Present”, in Himma Journal of Contemporary Hausa Studies, Vol.3 No. II October, 2011, Department of Nigerian Languages, Umaru Musa Yar’adua University, Katsina, Page 126 – 141.

    Raɗa Suna Jiya Da Yau 

    English Rendition as “Naming in Hausa Past and Present”

    Dr. Bashir Aliyu Sallau
    Department of Nigerian Languages
    Umaru Musa Yar’adua University
    Katsina – Nigeria

    1.0 GABATARWA

    Kowace al’umma a wannan duniya tana da irin tsarin da take bi domin tafiyar da rayuwar mutanenta dangane da yadda ake gudanar da al’amarin aure da haihuwa da mutuwa da sauran al’amuran da suka shafi rayuwar yau da kullum na wannan al’umma. Idan muka ɗauki al’amarin da ya danganci haihuwa za a ga al’ummar Hausawa suna tafiyar da harkokin rayuwa bisa wani tsari da suka gada iyaye da kakanni wanda a wasu wurare ana samun ɗan saɓani wanda bai taka kara ya karye ba a kan yadda ake zaɓar suna da raɗa suna ga abin da aka haifa da kuma dabbar da ake yankawa domin raɗin suna. Haka kuma shigowar baƙi ƙasar Hausa musamman Larabawa da Turawa sun taimaka wajen kawo sauyi a kan yadda ake zaɓar suna da sauran mu’amalolin da suka danganci bikin raɗin suna da dabbar da ake yankawa a lokacin raɗin suna da kuma yadda ya kamata a yi da naman dabbar wanda ya saɓa da yadda ake yi kafin zuwan waɗannan baƙin al’ummomi cikin ƙasar Hausa.

    Haihuwa al’amari ne wanda kowace al’umma a wannan duniya take ba muhimmanci domin kuwa ta wannan hanya ce ake samun ƙaruwar al’umma, wannan dalili ne ya sa Hausawa suke yi mata kirari kamar haka; ‘ba don haihuwa ba da iri ya ƙare’. Idan aka haihu sai kuma a raɗa wa abin da aka haifa suna wanda yakan dace da yanayi ko lokacin da aka haife shi, ko kuma a zaɓa masa sunan wasu shaharrun mutane waɗanda suka gabata domin neman albarkarsu da sauran dalilai. Wannan ya danganta ga al’ada ko addinin kowace al’umma ko zuri’a. Haka kuma, ana yanka dabba don cika wani ɓangare na al’ada da addini.

    2.1 Raɗin Suna da Dabbar Suna a Al’adar Hausawa

    Kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa, idan aka haihu ana raɗa wa abin da aka haifa suna ne ta la’akari da lokaci ko yanayin da aka yi haihuwar.A mafi yawancin lokaci ire-iren waɗannan sunaye kakanni ne suke zaɓar su. Yana da muhimmanci kafin a kawo ire-iren waɗannan sunaye, a yi waiwaye don duba yadda Hausawa suke yin taron raɗa suna ga ‘ya’yansu kafin zuwan addinin Musulunci a ƙasar Hausa.

    A al’adar Kaina-Fara Arnan Birchi waɗanda suke zaune a ƙauyen Goda ta Ƙasar Birchi a Ƙaramar Hukumar Kurfi ta Jihar Katsina, idan mace ta haihu ba ta da damar fita daga ɗakinta, sai bayan kwana arba’in, don kuwa a wurinsu wannan ita ce ranar da ake raɗa wa abin da aka haifa suna. A wannan rana, sai dattawa misalin su goma su taru a gidan da aka yi haihuwar.A lokacin da suka haɗu, sai su sanya a samo kundon kara a tsaga shi biyu, daga nan sai su yi zane iri daban-daban a jikin kowane tsagin na wannan kundon kara kamar irin yadda ake yin tsagen fuska na gargajiya. Idan an gama sai a kira wata tsohuwa daga cikin zuriyarsu, a ba ta waɗannan tsagaggun kundon kara wanda aka yi wa tsage ta kai wa mai jegon don ta zaɓi ɗaya. Bayan ta zaɓa sai ta miƙa wa wannan tsohuwa wanda ta zaɓa, ita kuma tsohuwar, sai ta kawo wa waɗannan dattawa wanda mai jegon ta zaɓa. A lokacin da suka karɓa, sai su duba zanen da yake jikin wanda mai jegon ta zaɓa, ta wannan hanya ce suke gane sunan abin da aka haifa. Daga nan sai su sanar da wannan tsohuwar sunan da aka raɗa wa wanann jariri, ita kuma sai ta sanar da mai jego wadda ta haifi jariri, amma kuma za su gargaɗi tsohuwar ita da mai jegon da kar su kuskura su gaya wa kowa sunan. Su ma dattawan ba za su sanar da kowa ba, sai ranar da za a yi masa aure ne za a sanar da shi da sauran jama’a sunansa.Daga nan sai kakanni su laƙaba masa wani suna na daban wanda za a riƙa kiransa da shi kafin zuwan ranar aurensa (Hira da Sarkin Noma Na-Goda a Gidansa da ke Goda Birchi, a ranar 16/8/1988).

    Su kuma Maguzawan da suke zaune a kudancin ƙasar Katsina mafi yawancinsu ba ruwansu da taron suna bayan kwana uku ko huɗu da haihuwa. Abin da suke yi kawai shi ne, idan mace ta haihu, sai a kawo kaji biyu daga gidan mahaifan mijinta don a yi ƙauri.Daga nan ba a sake yin wani abu sai bayan kwana arba’in. A duk tsawon wannan lokaci ba a yi wa abin da aka haifa suna. A lokacin da aka kwana arba’in, sai a yi wani biki wanda mata ne kawai suke taruwa a wurin wanda ake kira “kantsaki” watau a ci abinci a kuma bayar da gudummuwa ga mai jego. Yadda ake yi shi ne, kowace mace da za ta wurin wannan biki tana tafiya da irin gudummuwar da ta ga ya dace ta ba mai jego.A wurin wannan taron ne ake yanka ɗan akuya a yi abinci a ci, a wannan lokaci ne kafin matan su watse suke tunanin lokacin da aka haifi jaririn, wannan ne zai ba su damar zaɓar irin sunan da suka ga ya dace a raɗa wa wannan jariri. Misali, idan an haife shi a lokacin ana ruwa sosai da damina sai su raɗa masa suna “Anaruwa” da sauransu (Ibrahim, 1982: 131-132).

    Ga Maguzawan da suke a gundumar Kwatarkwashi ta Jihar Zamfara waɗanda ke bautar magiro a garuruwan suna da Toka ba su da wata tsayayyar rana wadda suke raɗa wa ‘ya’yansu suna.A al’adar waɗannan mutane ba a raɗa wa yaro suna,sai lokacin da ake da damar yin sunan ko da kuwa bayan shekaru ne. A wurinsu mutum yana iya haɗa ‘ya’yansa da yawa tun daga ɗaya ko fiye da ɗaya don ya yi masu suna a rana ɗaya. Wannan dalili kansa a wani lokaci, sai a sami mutum har ya yi aure ba a raɗa masa suna ba, sai dai a yi ta kiran sa da sunan kakanni (Hira da Alhaji Joɗi Kwatarkwashi, wadda Farfesa Sa’idu Muhammed Gusau ya yi da shi a cikin shekara ta 1985).

    A lokacin da wannan mutum ya sami damar yi wa ɗansa ko ‘ya’yansa suna, sai ya gayyaci ‘yan uwa da abokan arziki, ya sanar da su ranar da za a yi sunan. A wannan rana akan haɗa yaran unguwa ɗaya don yi masu suna, kafin zuwan ranar suna, sai uban kowane yaro ya tanadi abin da zai yanka, wannan ne ya sa ake ɗaukar lokaci don a shirya. A ranar suna sai jama’ar da aka gayyata su taru a ƙofar gidan da za a yi sunan.Farkon abin da za a fara yi shi ne, sai a ba jama’ar da suka halarta abinci kowa ya ci, a kuma sha giya.Bayan an gama, sai a yanka dabbar suna a feɗe ta a kawo fatar gaban dattawa a ajiye. Daga nan sai babba daga cikin waɗannan dattawa ya kira wanda za a raɗa wa sunan, sai ya zo gabansa ya durƙusa. Daga nan sai wannan dattijo ya ɗauko fatar dabbar sunan ya rufa ta a kan wanda za a yi wa sunan, ya ce, ‘sunanka wane’, bayan ya raɗa masa suna, sai ya ajiye fatar a wani wuri. Haka za a yi wa dukkan waɗanda za a raɗa wa suna a wannan rana, ɗaya bayan ɗaya har sai an yi wa kowa (Hira da Alhaji Joɗi Kwatarkwashi, wadda Farfesa Sa’idu Muhammed Gusau, ya yi da shi a cikin shekara ta 1985).

    Bisa la’akari da yadda waɗannan al’ummomi na Hausawa suke raɗa sunaye ga ‘ya’yan da aka haifa masu, za a fahimci akwai bambance-bambance a tsakaninsu ta fuskar lokaci da yanayin raɗin suna da hanyoyin da ake bi wajen raɗa suna.Amma duk da haka, a mafi yawancin sunayen da suke raɗa wa ‘ya’yansu su iri ɗaya ne, sai dai ɗan bambanci kaɗan wanda ba mai yawa ba. Wannan kuwa ya faru ne saboda a lokacin raɗa suna ana la’akari da lokacin da aka haifi yaro, wanda ta wannan hanya ce ake bi don a zaɓa masa sunan da ya dace da shi. Ga wasu daga cikin ire-iren sunayen Hausawa na gargajiya.

    2.1.1 Sunayen da Suka Danganci Yanayin Shekara

    Anaruwa ko Mairuwa – Yaron da aka haifa a lokacin ana yin ruwan sama.

    Damina – Yaron da aka haifa da damina.

    Marka – Yarinyar da aka haifa a lokacin da ake yin ruwan sama sosai a kullum.

    Shaɗari – Yaron da aka haifa a lokacin da ake yin muku-mukun sanyi ba ƙaƙƙautawa.

    Nomau – Yaron da aka haifa a lokacin da ake yin noma.

    Dare – Yaron da aka haifa da tsakiyar dare.

    2.1.2 Sunayen da Suka Danganci Yawan ‘Ya’Ya Wurin Wadda ta Haihu

    Mati ko Tanko ko Namata – Sunaye ne waɗanda ake kiran yaron da aka haifa bayan an haifi mata uku ko fiye da haka kafin a haife shi.

    Dudu ko Kande ko Dela ko Delu – Sunaye ne waɗanda ake raɗa wa yarinyar da aka haifa bayan an haifi maza uku ko fiye da haka kafin a haife ta.

    Auta – Sunan da ake raɗa wa yaro ko yarinya waɗanda bayan an haife su ba a ƙara haihuwar wani ba.

    2.1.3 Sunayen da Sukan Danganci Watannin Jariri a Ciki

    Haka kuma, akwai waɗanda saboda watannin da suka yi a ciki kan sa a zaɓar masu sunaye, misali yaron da ya yi wata bakwai a ciki aka haife shi ana raɗa masa suna Bakwai.

    Shekarau – Ana raɗa wa yaron da ya shekara a ciki ba a haife shi ba wannan suna.

    Shekara – Suna ne da ake raɗa wa yarinyar da ta shekara a ciki ba a haife ta ba.

    2.1.4 Sunayen da Suka Danganci Rayuwar Mahaifa a Lokacin da aka Haihu

    Audi – Suna ne da ake raɗa wa yaro ko yarinya waɗanda mahaifinsu ya rasu kafin a haife su.

    Talle – Ana raɗa wa yaro ko yarinyar da mahaifiyarsu ta rasu a lokacin haihuwarsu.

    2.1.5 Sunayen da Suka Danganci Yanayin Jikin Jariri a Lokacin da aka Haife shi

    Cindo ko Maicindo – Ana raɗa wannan suna ga yaro ko yarinyar da aka haifa da yatsu shida ko a hannu ko a ƙafa ko duka.

    Kumatu – Suna ne da ake raɗa wa yarinyar da aka haifa da kaurin kumatu.

    Waɗannan misalai ne kawai daga cikin ire-iren ɗumbin sunayen da Hausawa suke raɗa wa ‘ya’yansu na gargajiya.Abin kulawa a nan shi ne, ko a wannan lokaci da addinin Musulunci ya mamaye ƙasar Hausa, har yanzu wasu Hausawa na sanya wa ‘ya’yansu ire-iren waɗannan sunaye bayan na Musulunci ko sunan littafi kamar yadda ake kiransu.A yanzu ire-iren waɗannan sunaye ne zaman laƙabi.

    2.2 Dabbar Suna

    A al’adar Hausawa ana yanka dabbar suna a ranar da za a raɗa wa abin da aka haifa suna.A wannan rana ana yanka rago ko tunkiya ko ɗan akuya ko akuya ko sa. Bayan an yanka, sai a feɗe a kuma rarraba naman kamar yadda al’ada ta shimfiɗa a yi. A al’adar Hausawa dabbar suna tana da babban matsayi wanda kan tilasta wa dukkan wanda ya ga matarsa tana da ciki ya yi tanadin dabbar da zai yanka wa maijego. Abin gori ne ga dukkan wanda matarsa ta haihu bai yanka dabbar suna ba.Wannan gori zai iya shafar abin da aka haifa a lokacin da ya girma, don kuwa tsararrakinsa za su riƙa yi masa gorin cewa,ba a yanka masa dabbar suna ba.Haka kuma akwai masu yin rantsuwa su danganta ta da dabbar suna, misali, idan saɓani ya shiga tsakanin wasu mutane, wani na iya yin rantsuwa ya ce: “idan ban yi maka abu kaza ba, to ubana bai yanka min ragon suna ba”, da dai sauran abubuwa iri daban-daban.

     Ga yadda ake karkasa naman dabbar suna a al’adance (Ibrahim, 1982:146).

    2.2.1 Wanzami

    Ana ba wanzamin da ya cire wa abin da aka haifa belun-wuya da askin suna kushekara wadda ake fitarwa daga ƙashin baya kusa da wuyan dabbar sunan. Wasu kuma karfata suke bayarwa, watau ƙafar gaba haɗe da kafaɗar dabbar sunan. Wasu kuwa wuyan dabbar sunan ake datsowa a ba wanzami, ana kuma yanko guntu-guntu na kowane daga cikin kayan ciki na dabbar suna, ana kiransu da suna ‘ya’yan kushekara. Dukkan waɗannan abubuwan da aka ɗebo daga dabbar suna,ana bayar da su ga wanzami a matsayin wani ɓangare na ladar aikinsa.

    2.2.2 Ungozoma

    Ita kuma Ungozoma ana ba ta kai da ƙafafuwa da fatar dabbar sunan. Ana kuma haɗa mata da uwar hanji da tumburƙuma a matsayin wani ɓangare na ladar aikin da ta yi. Dalilin da ya sa ake ba ungozoma tumburƙuma shi ne, wai don a lokacin da aka haihu, ita ce ta zo ɗakin da aka haihu ta ga ƙazanta iri-iri ta kuma share ta duka. A saboda ganin wannan ƙazanta ne ya sa ake ba ta tumburƙuma don ta gasa ta yi wa idanunta gashi.Wai yin haka zai magance dukkan wata cuta da idanunta suka gani na ƙazantar haihuwa.

    2.2.3 Maroƙi          

    Maroƙi wanda ya yi shelar sanar da mutanen da suka taru a lokacin raɗin suna,ana ba shi mashafa wadda ita mashafa maƙogoron dabbar suna ne tattare da naman da ya lulluɓe shi. Dalilin da ya sa ake ba maroƙi mashafa shi ne, wai don ya yi amfani da maƙogoronsa wajen sanar da mutane sunan abin da aka haifa. 

    2.2.4 Dangin Uba da na Uwa

    Ana ba dangin wanda matarsa ta haihu karfata ta ɓangaren ƙafar dama ta dabbar suna da kuma rabin kayan ciki. Su kuma dangin wadda ta haihu ana ba su karfata ta ɓangaren kafaɗar hagu da rabin kayan ciki don su dafa ko a gasa ko a soya a rarraba wa ‘yan uwa da abokan arziki shedar an haihu lafiya.

    2.2.5 Maƙeri

    Shi kuma maƙerin da ya ke yi wa mutanen wannan gida da aka haihu aikace-aikacen ƙira na yau da kullum, ana ba shi mutum-tsugunne a matsayin wani ɓangare na ire-iren ayyukan ƙira da ya ke yi wa mutanen wannan gida.

    2.2.6 Wanda ya yi Fiɗar Dabbar Suna

    Wanda kuma ya yi fiɗar dabbar suna ana ba shi murfi watau naman da ya rufe cikin dabbar da kuma saifa da wani ɓangare na hanji da tumbi da ‘ya’yan golayen dabbar suna. A al’adar Hausawa ba mahauta ne suke yin fiɗar dabbar suna ba, abokan wasan barkwanci ne suke yin fiɗa a gidajen abokan wasansu. Misali, idan aka haihu a gidan Bakatsine, to Bagobiri ne ko Bakabe ko Bahaɗeje zai yi fiɗar dabbar suna. Haka su ma a lokacin da aka haihu a gidajensu Katsinawa ne za su yi fiɗar dabbar suna.

    2.2.7 Mai Kitso

    Matar da take yi wa wadda ta haihu kitso ana ba ta naman da ya haɗe tumburƙuma da uwar hanji a matsayin wani ɓangare na ladar kitson da take yi wa wadda ta haihu a yau da kullum.

    2.2.8 Mai Jego

    Ita kuma wadda ta haihu watau maijego ana ba ta kwankwason dabbar suna a matsayin nata rabon na naman dabbar suna.Dalilin haka shi ne, wai don tsawon lokacin da ta ɗauka tana ɗauke da cikin.Idan ta ci naman kwankwaso zai taimaka wa kwankwasonta ya yi lafiya ta kuma ƙara samun ƙarfin ɗaukar wani cikin. Ana kuma haɗawa da sauran naman da ya rage a dafa ko a soya. Daga cikinsa ne ake ɗibar wa mijin mai jegon da sauran ‘yan uwa da abokan arziki.

    Kafin a yanka dabbar suna ana bin wasu ƙa’idoji na al’ada waɗanda rashin bin su yake haifar da wasu matsaloli ga mutanen da suka yi imani da su. Da farko dai ba a yanka dabbar suna, sai an tabbatar da abin da aka haifa ba ya barci, wai idan an yanka a lokacin yana barci, kakarin mutuwa da dabbar take yi zai aibaci abin da aka haifa. Waɗanda suka yarda da wannan al’ada suna bayyana cewa, a lokacin da abin da aka haifa ya fara girma, idan yana barci, zai riƙa minshari da kakari mai ƙarfi kamar irin wanda dabbar da aka yanka masa ta suna ta riƙa yi a lokacin da aka yanka ta. Wannan dalilin ne ya sa a lokacin da za a yanka dabbar suna, sai an tayar da abin da aka haifa daga barci.

    Haka kuma bayan an yanka dabbar suna ba a son a karya ƙashin dabbar.A al’adance idan aka karya ƙashin dabbar suna abin da aka haifa wanda aka yanka dabbar a lokacin raɗa masa suna, idan ya girma zai fuskanci matsalolin rashin ƙwarin ƙashi.

    3.1 Raɗin Suna da Dabbar Suna a Musulunci

    Shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa da kuma karɓar shi da Hausawa suka yi, ya yi babban naso akan yadda Hausawa suke tafiyar da harkokin haihuwa.Addinin ya kawo wasu sababbin abubuwa kamar addu’ar kwana uku ko huɗu da haihuwa da kuma addu’ar raɗin suna ta kwana bakwai, bayan waɗannan kuma addinin Musulunci ya kawo wa Hausawa sauyi dangane da al’adun da ake yi ga dabbar suna.

     

    3.1.1 Addu’ar Uku

    A shari’ar addinin Musulunci an yi horo ga mabiyansa da su roƙi Allah, Maigirma da ɗaukaka, dukkan abubuwan da suke buƙata ta hanyar yin addu’a.Wannan dalili ne ya sa idan aka haihu ake yi wa abin da aka haifa addu’a don roƙon Allah, Maigirma da ɗaukaka, Ya tsare shi daga dukkan sharri, ya kuma zama mai amfani ga kansa da kuma sauran al’umma. A saboda haka wasu idan abin da aka haifa namiji ne, sukan yi masa addu’a, a rana ta uku da haihuwrsa.Idan kuma mace ce aka haifa, ana yi mata addu’a a rana ta huɗu da haihuwarta.Irin wannan addu’a ana kiranta da sunan “Huɗuba” ko “Wazana”. Abin da ake yi a lokacin huɗuba shi ne, ana yin kiran Sallah a kunnen dama, a kuma yi iƙama a kunnen hagu na abin da aka haifa. Daga nan sai wanda ya yi huɗubar ya tauna dabino ya zuba ruwan dabinon a cikin bakin abin da aka haifa.Yin haka zai ƙara wa abin da aka haifa ƙwarin haƙora. A shari’ar addinin Musulunci an bayyana cewa, an fi son a yi huɗuba da an gama wanke abin da aka haifa namiji ko mace ba, sai an ɗauki wasu kwanaki ba.Bayan an gama huɗuba, idan akwai halin a yanka dabbar suna a rana ta bakwai da haihuwa, sai a ɓoye sunan da aka zaɓa har sai ranar ta zagayo (watau kwana bakwai) sannan a bayyana sunan ga al’umma. Idan kuwa babu halin da za a yanka dabbar suna, ko ba a yi nufin yankawa ba, bayan an yi huɗubar nan take ana iya sanar da jama’a sunan da aka zaɓa wa abin da aka haifa don kowa-da-kowa ya sani (Al-Imam Ahmed, Ba Ranar Bugu: 286-290).

     

    3.1.2 Addu’ar Kwana Bakwai ta Raɗin Suna

    A rana ta bakwai da haihuwa wasu na gayyatar ‘yan’uwa da abokan arziki don yin taron addu’ar raɗin suna don a raɗa suna ga abin da aka haifa namiji ko mace. Wasu kuma ba sa gayyatar kowa don yin taron addu’ar raɗin suna.A nan Musulmi mabiya Ɗariƙun Ƙadiriyya da Tijjaniyya da ‘yan’uwa Musulmi suna gayyatar ‘yan’uwa da abokan arziki don yin taron addu’ar raɗin suna, amma mabiya aƙidar Izala ba sa gayyatar jama’a don yin taron addu’ar raɗin suna a lokacin da jaririn da aka haifa masu ya kwana bakwai. Abin da suke yi shi ne a lokacin da abin aka haifa ya kwana bakwai, idan an zo yin sallar asuba, sai a sanar da limamin masallacin don ya sanar da jama’ar da suka halarci wannan salla kamar haka; ‘Allah ya albarci ɗan’uwanmu wane da samun ƙaruwa, matarsa ta haifi ɗa namiji ko ‘ya mace kuma ya sanya wa abin da aka haifa masa suna wane ko wance, a saboda haka yake roƙon ‘yan uwa musulmi da su taya shi addu’a Allah ya yi wa abin da aka haifa albarka, ya kuma sanya shi cikin inuwar Musulunci da sauran addu’o’i na neman yardar ubangiji’. A wurin yin wannan addu’a, ba a jagorancin yin ta, kowa zai yi tasa ne a cikin zuciyarsa.Dukkan waɗannan Musulmi masu bin aƙidu daban-dabam a addinin Musulunci, kowannensu suna da dalilan da suka sanya su ɗaukar irin wannan mataki kan raɗin suna.

    Ga waɗanda suke yin taron addu’ar raɗin suna a rana ta bakwai da haihuwa sun kafa hujja ne da cewa, yin irin wannan taro mustahabbi ne, sun bayyana cewa, akwai hadisin Annabi, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, wanda ya bayyana cewa, idan aka yi maku haihuwa ku ciyar da al’umma da abinci, kuma ku shayar da su da abu na halak (Al-Malik, 1913: 224). Wannan ne ya sa suke ganin hanyar da za su yi koyi da wannan hadisi ita ce, ta gayyatar jama’a a yi taron addu’ar raɗin suna a kwana na bakwai da haihuwa.A nan ne za a ba ‘yan uwa da abokan arziki abinci da abin sha waɗanda suka haɗa da tuwo da shinkafa da makamantansu da kuma kunu ko koko ko fura.

    Ga waɗanda suke yin taron addu’ar raɗin suna a kwana na bakwai da haihuwa, tun ana kwana uku ko huɗu da haihuwa kafin ranar suna za a yi ta gayyatar ‘yan uwa da abokan arziki don su zo wurin taron addu’ar raɗin suna.A ranar sunan kuma ana tanadar wadataccen abinci mai kyau a ciyar da mutanen da aka gayyata. Haka kuma ’yan uwa da abokan arziki za su kawo tasu gudummuwar kowa zai kawo bakin ƙarfin arzikinsa, wasu suna bayar da abinci ga mutanen da suka gayyata kafin a yi addu’ar raɗin suna.Wasu kuma sai bayan an yi addu’ar suke bayarwa.

    Bayan an gama cin abinci kuma an tabbatar da ‘yan uwa da abokan arziki na wajen mai jego da na wajen angon jego duk sun zo sai a raba goro ko alawa ko dabino a ba dukkan mutanen da suka sami damar halartar wannan taro na raɗin suna. A wasu wurare musamman a ƙauyuka cikin ƙasar Hausa, ga waɗanda suke yin taron addu’ar raɗin suna ta kwana bakwai, ba za a yi addu’ar ba, dole sai lokacin da dangin wadda ta haihu suka zo. Idan aka yi addu’ar ba tare da an jira su ba, yin haka ka iya kawo babbar matsala a tsakanin ma’auratan. Don kuwa dangin wadda ta haihun za su ɗauka an yi addu’ar ne ba tare da an jira su ba saboda an raina su, musamman idan gidan da ‘yarsu take aure masu arziki ne.A wani lokaci irin wannan matsala ka iya yin dalilin rabuwar wannan aure.

    Daga nan sai a ba limami izinin ya raɗa wa abin da aka haifa suna.Wasu kan zaɓi sunan da za a raɗa wa ‘ya’yansu,sai su sanar da limami, amma wasu kan ba limami damar ya raɗa wa abin da aka samu sunan da Allah ya ciyar da shi. Daga nan sai limami ya umarci maroƙi da ya sanar da mutane za a yi addu’ar raɗin suna. Za a fara da yin salati ga Annabi, sai kuma a ƙara da yin wasu addu’o’i na roƙon Allah ya raya abin da aka haifa, ya zama mai amfani ga jama’a, kuma Allah ya ba mahaifansa abin da za su ciyar da shi.Ana kuma ƙara yin addu’a ga dukkan musulmi (Hira da Liman Ƙasimu Usman Safana, a ranar 26/1/2005). A duk lokacin da aka shafa addu’a maroƙi zai faɗi sunan da aka raɗa wa abin da aka haifa da ƙarfi domin dukkan mutanen da suka taru su ji sunan.Ana yin taron addu’ar raɗin suna tun da sassafe a cikin garuruwa da birane, amma a ƙauyuka ana dakatawa sai hantsi ya yi. A wasu lokuta saboda wasu dalilai ana tsayawa sai rana ta yi sosai. Ana jinkirtawa ne don a jira kowa da kowa ya zo, ciki har da dangin wadda ta haihu don a yi maganin aukuwar irin saɓanin da aka yi bayani a sama. Haka kuma ana jinkirtawa ne don a ba dangi da abokan arziki waɗanda suke kusa da na nesa damar halattar taron addu’ar raɗin suna.

    Bayan kammala addu’ar raɗin suna, sai maroƙa su yi ta yin roƙo ga mutanen da suka halarci addu’ar raɗin suna.

    Su kuma mabiya aƙidar Izala ba sa yin taron addu’ar suna a rana ta bakwai da haihuwa. Sun kafa hujjarsu da cewa, Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, bai yi taron addu’ar raɗin suna ga ‘ya’yansa ko jikokinsa ba, haka kuma sahabbansa ma ba su yi ba. Sun ƙara da cewa, akwai huɗuba da ake yi a lokacin sallar Juma’a da ta Idi da sauransu, akwai kuma wadda ake a lokacin da za a ƙulla aure, dukkan waɗannan huɗubobi sun samo asali daga koyarwar Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, amma ba bu ta raɗin suna. Don haka irin wannan taro ba shi da wani asali a shari’ar addinin Musulunci (Hira da Malam Yahuza Tukur Gwarjo, a Katsina, a ranar 12/12/2002). Ire-iren waɗannan malamai sun ƙara da bayyana cewa, a mafi yawancin ƙasashen Musulmi babu wurin da ake yin taron addu’ar suna sai a ƙasar Hausa kawai.Wannan kuwa ya faru ne saboda al’adar Hausawa kafin zuwan addinin Musulunci ana yin irin wannan taro. A lokacin da Musulunci ya shigo, malaman da suka kawo shi saboda wasu dalilai ba su hana yin irin wannan taro ba.Wannan dalili ne ya sa aka ɗauki irin wannan taro kamar wani ɓangare na al’ada wanda shari’a ba ta haramta ba.

    Malaman Izala da magoya bayansu sun kuma ƙara kafa hujja da cewa, Shehu Usman Ɗanfodiyo ya bayyana a cikin littafinsa mai suna Ihya’ussunna wa Ikhmadul Bidi’a, yin taron addu’ar raɗin suna a rana ta bakwai da haihuwa bidi’a ce wadda aka hana. Abin da shari’a ta yi horo a yi shi ne, idan wanda aka yi wa haihuwa yana da damar yanka dabbar suna (aƙiƙa), sai ya bari sai a rana ta bakwai da haihuwa, idan hantsi ya yi sai ya yanka dabbar suna (aƙiƙa). Daga nan sai ya sanar da ‘yan’uwa da abokan arziki sunan da ya raɗa wa abin da aka haifa masa. A farkon shigowar ƙungiyar Izala an sami saɓani a tsakanin mabiyanta a hannu ɗaya da kuma danginsu da dangin matansu da mahaifansu waɗanda ba su yarda da aƙidojin Izala ba a ɗayan hannun. Irin wannan saɓani an fi samunsa a lokacin da matan mabiya wannan ƙungiya suka haihu.Wannan kuwa ya faru ne saboda ba sa yin taron addu’ar raɗin suna a rana ta bakwai da haihuwa.Wannan dalilin ya sa mahaifansu da danginsu da ‘yan uwan matansu waɗanda suke yin taron addu’ar suna a rana ta bakwai da haihuwa suke ɗauka kamar an raina su. Daga nan sai a yi ta tsegunguma da ƙorafe-ƙorafe waɗanda kan haifar da rashin jituwa da rashin fahimtar juna a tsakaninsu. Wasu mutane musamman maroƙa waɗanda kan sami kuɗi da abinci a lokacin addu’ar raɗin suna a rana ta bakwai, suna bayyana cewa, rowa ce take sanya ‘yan Izala ƙin yin taron addu’ar raɗin suna. A wannan zamani an fara samun sauƙin irin wannan rashin fahimta, don kuwa a wannan zamani kowane mutum na tafiyar da harkokinsa kamar yadda yake ganin shi ne daidai a gare shi.

      Ana so kuma a zaɓa wa abin da aka haifa suna mai kyau da ma’ana. A lokacin da za a sanar da mutane sunan da aka zaɓa ba dole sai an tattara su ba domin yin wata addu’a (Kwairanga, 1986: 113-118).

    Addinin Musulunci ya yi horo da a zaɓa wa abin da aka haifa suna mai kyau da ma’ana cikakka, wannan dalili ne ya sa ake zaɓar sunayen Annabawa ko Sahabbai ga ‘ya’ya maza, su kuma mata ana zaɓar masu sunayen matan Annabawa ko na Sahabbai ko sunayen ‘ya’yansu.Ire-iren waɗannan sunaye su ne Hausawa suke kira sunayen yanka, watau sunayen da aka samu bayan shigowar addinin Musulunci.Ga misalin ire-iren waɗannan sunaye.

    i)                  Sunayen Annabawa

    Adamu

    Nuhu

    Idrisu

    Salihu

    Hudu

    Ibrahim

    Ya’aƙubu

    Isma’ilu

    Yusufu

    Yusha’u

    Ilyasu

    Yahaya

    Zakariya’u

    Dawudu

    Suleman

    Musa

    Isa

    Muhammadu

    Akwai sunaye da yawa waɗanda ake danganta su da Muhammadu, waɗanda suka haɗa da:

    Muhammadu Auwalu

    Muhammadu Sani

    Muhammadu Salisu

    Muhammadu Rabi’u

    Muhammadu Hamisu

    Muhammadu Sadisu

    Muhammadu Sabi’u

    Muhammadu Saminu

    Muhammadu Tasi’u

    Muhammadu Ashiru

    Muhammadu Bashir

    Muhammadu Kabir

     - -da sauransu.

    ii)               Sunayen Sahabbai

    Daga cikin sunayen sahabbai kuma akwai;

    Abubakar

    Umaru

    Usmanu

    Aliyu

    Abbas

    Zubairu

    Sa’adu

    Abdullahi

    Abdurrahman

     - -da sauransu.

    iii)            Sunayen Waliyyai

    Haka kuma, ana sanya sunayen waliyyai kamar;

    Abdulƙadir

    Ahmadu Tijjani

    Ahmadu Rufa’i

    Usmanu

    -da sauransu.

    iv)              Sunayen Matan Annabawa da Sahabbai

     - Su kuma mata ana sanya masu sunaye matan Annabawa da na ‘ya’yansu da kuma na Sahabbai waɗanda suka haɗa da;

    Aminatu

    Faɗimatu

    Maryamu

    Ummu Kulsumi

    Zainabu

    Ruƙayyatu

    Hindu

    Asma’u

    Hadijatu

    Habibatu

    Maimunatu

    Halimatu

     - -da sauransu.

    v)                Sunayen Mala’iku

    Ana kuma sanya wa ‘ya’ya sunayen Mala’iku kamar;

    Jibrilu

    Mika’ilu

    Rilwanu

     - -da sauransu.

    ɓi)  Sauye-Sauyen da Sunayen Musulunci ke Samu a Ƙasar Hausa

    Daga cikin waɗannan sunaye da Hausawa suka samu bayan shigowar addinin Musulunci akwai waɗanda suke faɗar su daidai kamar yadda suke a cikin littafi, akwai kuma waɗanda suke sauyawa.Sunaye irin su Hudu da Nuhu da Musa da Isa da Hindu da sauransu ba a faye sauya su ba, ana faɗar su kamar yadda suke a cikin littafi.Sunayen da ake sauyawa kuma sun haɗa da;

    Adamu   -  -  -  - Ado

    Idrisu -  -  -  -  - Idi

    Salihu -  -  -  -  - Sale

    Ibrahim -  -  -  - Iro, Ibro, Ibra, Buraima

    Zakariya’u -  -  -  - Zakari, Ya’u

    Abubakar -  -  -  - Habu, Bukari, Abu

    Abdullahi -  -  -  - Audu, Audulla

    Zainabu -  -  -  - Abu, Abule, Bulele

    Hadijatu -  -  -  - Dija, Dije, Andijo

    Maimunatu -  -  -  - Maimu, Mune, Munari

    Ruƙayyatu -  -  -  - Rakiya

     - -da sauransu.

    ɓii) Sunayen Ranaku

    Haka kuma, bayan Hausawa sun karɓi addinin Musulunci, bayan waɗannan sunaye na littafi ko na yanka suna laƙaba wa ‘ya’yansu sunayen da suka danganci ranaku da wasu al’amura da suka shafi addinin Musulunci. Ire-iren waɗannan sunaye sun haɗa da;

    Ɗan’asabe ko Ɗan’asibi ga yara maza da aka haifa a ranar Asabar ko Asabe ga yarinya mace wadda aka haifa a wannan rana da sauransu.

    Ɗanladi ko Lado ko Nalado ga yara maza da aka haifa a ranar Lahadi ko Ladidi ko Ladi ko Ladiyo ko Ladingo ga yarinya mace da aka haifa a wannan rana.

    Yaro namiji da aka haifa a ranar Litinin ana yi masa laƙabi da Ɗanliti ko Liti ko Ɗantani, su kuma mata ana kiransu Liti ko Tani da sauransu.

    Shi kuma yaron da aka haifa a ranar Talata ana yi masa laƙabi masa sunan Ɗantala ko Ɗantata ko Tatu ko Maitala. Ita kuma mace wadda aka haifa a wannan rana ana laƙaba mata Talatuwa ko Talatu ko Tatu ko Lanti da sauransu.

    Ana kuma laƙaba ma yara maza da aka haifa a ranar Laraba sunaye kamar Bala ko Balarabe ko Ɗanbala ko Ɗanlarai. Ita kuma yarinya mace ana laƙaba mata sunaye irin su Larai ko Balaraba ko Laraba ko Larabayye ko Tabawa da sauransu.

    Yara maza waɗanda aka haifa a ranar Alhamis ana laƙaba masu sunaye kamar Ɗanlami ko Nalami. Su kuma mata ana laƙaba masu sunaye irin su Laminde ko Lami ko Jume da sauransu.

    Idan aka haifi yaro namiji a ranar Juma’a ana laƙaba masa sunaye kamar Ɗanjuma ko Ɗanjummai ko Jumare ko Najume. Su kuma ‘ya’ya mata ana laƙaba masu sunaye waɗanda suka haɗa da Juma ko Jummai ko Aljumma da sauransu.

    Bayan waɗannan sunaye, wasu iyaye kan laƙaba wa ‘ya’yansu sunayen da suka danganci wasu muhimman ranaku na addinin Musulunci kamar ranar da aka fara azumin watan Ramalana ko salla ƙarama ko babba.

    Idan aka haifi yaro namiji a ranar da aka fara azumin watan Ramalana ana laƙaba masa sunan Labaran ko Ɗan’azumi. Ita kuma yarinya mace ana laƙaba mata sunan Azumi.

    Dukkan yaro namiji da aka haifa a ranar ƙaramar salla ana laƙaba masa sunan Sallau ko Nasalla, su kuma ‘ya’ya mata ana laƙaba masu sunan Tasalla ko Tasalluwa.

    Idan kuma aka haifi yaro a ranar salla babba ana laƙaba masa sunan Alhaji ko Sallau, idan kuma mace ce ana laƙaba mata sunan Hajiya ko Tasalla.

    3.2            Dabbar Suna

    A shari’ar addinin Musulunci dabbar suna ko aƙiƙa tana nufin a yanka rago ko tunkiya ko ɗan akuya ko akuya ga abin da aka haifa a rana ta bakwai da haihuwar sa. Abin da ya fi dacewa ga ɗa namiji a yanka masa dabba biyu, ita kuma ‘ya mace a yanka mata dabba ɗaya. Haka kuma duk hukuncin da ya rataya a wuyan dabbar layya ya shafi dabbar suna, watau ta zama lafiyayya kuma ƙosasshiya wadda ba ta da wani lahani. Bayan an yanka, ya halatta a ci naman duka ko a ɗebi wani ɓangare na naman don a yi sadaka ko kyauta. Amma ba ya halatta a ɗebi wani ɓangare na naman dabbar suna don a ba wani mutum a matsayin wani ɓangare na biyansa ladar aikin da ya yi wa abin da aka haifa ko don gyaran naman dabbar suna.Abin da aka so shi ne, duk wanda zai yi wani aiki ga abin da aka haifa ko ga dabbar suna, kamata ya yi a yi jinga da shi a kuma biya shi da kuɗi ko da wani abu daban wanda shari’a ta yarda a yi amfani da shi, amma ba da naman dabbar suna ba (Abdallahi Al-Zakzaky, 1996:139).

    Kammalawa

    A hakika idan muka waiwayi bayanan da suka gabata za a fahimci al’ummar Hausawa suna da hanyoyin da suke zaɓa wa ‘ya’yansu sunaye waɗanda a wannan zamani ake kira sunayen gargajiya ko sunayen rana ko sunayen kakannin. Shigowar addinin Musulunci da kuma karɓarsa da Hausawa suka yi ya kawo babban sauyi dangane da yadda Hausawa suke zaɓa wa ‘ya’yansu sunaye saɓanin ire-iren sunayen da suka riƙa raɗa wa ‘ya’yansu kafin shigowar wannan addini. Haka kuma, Hausawa suna yanka dabbar suna tun kafin shigowar addinin Musulunci,amma yadda ake yi da naman dabbar suna kafin shigowar addinin Musukunci ya bambanta da yadda ake yi bayan shigowar addinin.Wannan kuwa ya faru ne saboda hukuncin shari’ar addinin Musulunci ya bambanta da yadda al’adar Hausawa ta tsara. Wannan hukunci na shari’a dangane da dabbar suna ya yi tasiri sosai a wannan zamani, don kuwa a yanzu wurare kaɗan ne a cikin ƙasar Hausa suke ba da wani ɓangare na dabbar suna  a matsayin biyan ladar aikin da aka yi wa abin da aka haifa ko dabbar da aka yanka don yin suna. Maimakonsu ana ba da kuɗi ko hatsi da makamantansu kamar yadda shari’a ta yi horo a yi.

    A taƙaice, an duba al’adun haihuwa waɗanda suka shafi zaɓen suna da dabbar suna, an kuma yi bayani kan yadda ake yin su kafin zuwan addinin Musulunci da bayan zuwan addinin Musulunci a ƙasar Hausa.

    Manazarta

    Abdullahi al-Zakzaky, S.Y.S.M. (Ba Ranar Bugu). Fath-al-Jawwad fi Sharh al-Irshad. Kano Nijeriya: Ba Sunan Maɗaba’a.

    Abil Azahari, S.S.A. (Ba Ranar Bugu). Al-Thamaraddani Fi-Takribil Ma’ani Sharh Risalat, Juzu’i na Biyu, Beirut-Lebanon: Dar-al-Fikr.

    Al-Malik, I.M. (1913), Muwaɗɗa Malik, Juzu’i na Farko, Beirut – Lebanon, Dar-al-Fikr.

    Ibrahim, M.S.(1982) ”Dangantakar Al’ada da Addini:Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Kwairanga, A.M.B (2000/1420). Fassarar Littafin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo na Ihya’ussunna wa Ikmadul Bid’a, Kashi na Farko, Kano-Nijeriya: Ba Sunan Maɗaba’a.

    Sabiƙ, A.S. (1990/1411 A.H) Fiƙh al- Sunnah, Juzu’i na uku, Al-Ƙahira (Cairo- Egypt): Dar-al-Rayyan.

    Sallau, B.A.S. (2000) ”Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’a a Ƙasar Hausa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Sallau, B.A.S. (2009) “Sana’ar Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani: Jiya da Yau”. Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.