Rama La’asar A Bayan Maghriba

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Matafiyi ne ya isa gida daf da Maghriba alhali bai yi la’asar ba, kuma bai tuna ba sai a bayan ya yi Maghriba. To wai La’asar ɗin ce kaɗai zai yi, ko duk da Maghriba?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

    Malamai sun saɓa wa juna game da waɗannan:

    (i) Wanda ya manta da wata sallah sai a bayan ya yi wacce ta ke a a bayanta sannan ya tuna.

    (ii) Wanda lokacin sallar yanzu ya yi masa ƙunci, ta yadda idan ya ce zai yi wacce ta kuɓce masa lokacin ta yanzun ɗin zai fita.

    (iii) Wanda ya shiga masallaci kuma ya tarar an tayar da iqamar sallah alhali shi bai yi wacce ta ke kafin wannan da aka tayar ɗin ba.

    Waɗansu malamai sun zaɓi cewa, lallai ya gabatar da wacce ta kuɓce masa da farko kafin ya yi ta yanzu, ko da kuwa lokacin ta yanzun ɗin zai fita. Idan kuma ya manta ne, to bayan ya yi wacce ta kuɓce masa sai ya sake maimaita ta yanzun ɗin. Suka ce, domin wajibi ne a jeranta adadin sallolin yini guda.

    Waɗansu malaman kuma sun zaɓi ya fara yin sallar yanzu ɗin, sannan daga baya ya kawo wacce ta kuɓce masa. Suka ce, ai asali Allaah bai wajabta wa musulmi ya maimaita wata sallah a rana guda sau biyu ba.

    Wannan maganar ta ƙarshe ce muka fi natsuwa da ita, domin ba mu ga wani dalili sahihi mai wajabta jerantawar ba. (Tamaamul Minnah: 1/175).

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.