Rumbu, abin amfani ne na gargajiya da ake adana kayan amfanin gona da manoma suka noma a cikinsa a ƙasar Hausa.
Ana zuba dukkan nau’ukan kayan amfani da ake son adanawa na tsawon lokaci bayan an girbe su daga gona.
Ana zuba kayayyaki irin su Hatsi, Wake, Gyaɗa, da sauransu kuma a lokaci guda.
Ana amfani da Kara da kuma ciyawar Gamba wajen yin sa. Sannan kuma bayan wannan akwai rumbun ƙasa. Duk dai aiki iri ɗaya suke yi. Kamar yadda ake da ɗakin kara da kuma na ƙasa; Wato ɗakin kago.
Ana yin amfani da Rumbu na tsawon lokaci kuma an tabbatar da cewa, ya na da tasiri don adana abinci.
Daga Zauren:
Hausawa Da Harshensu
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.