Takardar da Aka Gabatar a Taron {ara wa Juna Sani na [aliban Babban Digiri na Uku da na Biyu (Ph.D & M.A) a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato Ranar Asabar, 05/08/2023 da Misalin 10:00 na Safe.
RUWA NA {ASA SAI GA WANDA BAI TONA BA
(Muhallin Karin Magana A Farfajiyar Binciken Ilmi)
Daga
Aliyu Muhammad Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto
Email: mabunza@yahoo.com
Website: www.alibunza.com
Phone Number: 08034316508
Tsakure
Ga al’ada, duk harshen da
ba shi da wadatattun karin magana akan yi masa kallon naƙasasshen harshen da ba zai iya miƙewa ya yi kuka irin na kakansa mai nisa
ba. Wannan bincike, an tsara shi da manufar fito da irin gudunmawar da Karin magana ke
bayarwa ta fuskar haska wa masana da ɗalibai zurfin ilimin kakanninmu na naƙaltar
makamar ƙabali
da ba’adin rayuwar zamaninsu da namu. Hakan na daga cikin dalilan da suka
hana al’adunmu su yi ɓatan dabo. Sakamakon haka, takardar tana
da muradin ]ora mai bincike kan tafarkin da ya kamata ya bi, ya kai ga
nasarar kowane irin bincike da yake so ya
gudanar. Takardar
ta yi ƙoƙarin
sarrafa karin maganganun da suka taɓo ɓangarorin zamantakewar Hausawa guda 125. Alaƙar
da ke tsakanin fasahar karin magana da waƙa ita ta sanya aka ƙawata
wasu bayanan da waƙoƙin baka guda 10, sai rubutacciyar waƙa
guda 1. Takardar ba ta kawar da kai ga bibiyar hanyoyin bincike tare da hanyar ɗora
aiki ba. Wasu daga cikin sakamakon da binciken ya gano sun haɗa
da: Duk wata dabara da za a bi ta binciken kimiyya, ko fasaha ko
wani ilmi na ko mene ne, idan aka sa adabin karin maganan Hausa gaba za a samu
sirrin gudanar da shi. Karin magana taron
dangin masana ne da
}wararru a fannoni daban-daban, don haka hannu da yawa ne an ko ce, yana maganin miya yamamma. a ƙarshe,
an raɗa
wa takaradar suna da: RUWA NA {ASA SAI GA WANDA BAI TONA BA (Muhallin Karin Magana A Farfajiyar Binciken Ilmi).
Gabatarwa
Al’ummar da
duk aka arzuta da harshe an ba ta abin da za ta zauni duniya a ilmance, da karatun abubuwan da ke wakana a ciki. Babu
wani zamani da adabin masu adabi ba ya aiki, sai zamanin da masu adabi suka
wofintar da adabinsu. Tunanin wannan bincike shi ne,
kallon irin gudunmuwar da karin magana ya yi wa magabatanmu suka kasance
nagartattu wajen karatun duniyar lokacinsu. Idan aka sake sa natsuwa, za a ga
duk wata dabara, da fasaha, da kimiyyar lokacinmu, karin maganganunmu sun da]e
da }yallaro su, tun ba mu kasance a duniya ba. Don haka nake son kalato wasu
sassa na karin magana da suka yi zuzzurfan karatun bincike, da ]ora mai bincike
kan tafarkin da ya kamata ya bi, ya kai ga nasarar kowane irin bincike yake
}udurin yi. Tunanin masu ganin a yi dai mu gani, da masu fa]ar: “anya!”, Da
masu yi wa adabinmu kallon hadarin kaji, ya sa na
yi wa binciken take: “Ruwa na }asa sai ga wanda bai tona ba”.
Kadabar Bincike
[alibin ilmi
zai so ya ji ina ne iyakokin wannan tunani? Domin sanin farfajiyar karin magana
yawa gare ta. To! Ba kwasan karan mahaukaciya zan yi wa karin magana ba, ba kuma salon za~i son ka zan yi
ba. Duk wani karin magana da bincike ke iya kasancewa babban jigonsa ire-irensu
ne zan kalato. Ban ke~e wa zamani, ko rabe-raben karin magana, wani fasali mai
cin gashin kansa ba, domin wani fage ne da ake son a yi wa kadada cikin
farfajiyarsa. Ba tare da rarrabewa ba, za a tsintsinto karin magana da ke da
}unshiyar bincike, na kowane mataki na bincike, a yi fashin ba}insa, a ga
hasken da ya bai wa masana da ]aliban ilmi na bincike. Kadadar wannan bincike
ta farko ita ce, karin magana. Kadada ta biyu, karin
maganar da ke da }unshiyar bincike na kowane mataki. Kadada ta uku,
ya kasance karin magana gama-gari da ya da]e
cikin kunnuwan Hausawa da suka taras kaka da kakani.
Mene ne karin Magana?
Bisa ga tsarin
fashin ba}in, ‘ba ni ba}i in ba ka fassara’, za mu ce, karin magana, kalmomi
biyu ne ]aya ta goyo ]aya suka kasance kalma ]aya. Za a ce, magana ce da aka
kakkarya ko aka dun}ule aka ta}aita ta domin adana ko isar da wani sa}o. Wannan
ne dalilin magabata da ke ce wa karin maga gajeruwar jimla mai }unshe
da babban sa}o (Galadanci, 1975, Kiyawa: 1980 Bada, 1995, Furnis, 1996, da
[anyaya, 2017). Ban }i su ba, amma na so in ji, wa ke }ago jimlolin? Mene ne
}unshiyarsu? Me za a taras ciki a ce musu karin magana? A ]an nawa bincike na
gano “}wararrun magabata” ke }ago jimlolin. {unshiyar jimlolin wani karatun
hikima ne na fannoni daban-daban na rayuwa. Matu}ar ba a samu }ololuwar
tunanin hikima wanda ya yi canjaras da gaskiyar rayuwa ba;
ba zai kasance karin magana ba. An ce, cikin }ira aka da]i, don haka nake
ganin:
Karin magana gajeruwar jimla ce da magabata }wararru a
fannonin rayuwa daban-daban, gogaggu ga sanin jiya da yau, wayayyu ga rayuwar
zamunansu suka }ir}iro. Za a samu jimlolin }wangaggu ga nahawunsu, tare da hikimomin gagara
misali wa]anda ba sa musantuwa ga wanda suka taras kuma babu zamanin da zai
wofintar da su.
Mene ne Bincike
Bincike a
matsayinta na kalma tana da fassarori da
lafuzan furucinta daban-daban a karuruwan harshen Hausa, (Bunza 2017:2). A
fagen nazarin ilmi kalmar da ta shahara ga fashin ba}in bincike ita ce:
“Research” kalmar “research” tana da ]agwarin “re”. Idan aka cire ]agwari sai
ta koma “search”. To! Idan kalmar “search” ita ce, “bincike” a Hausa. Kalmar
“research” tana ]aukar ma’anonin; tottoniya, tone-tone, sake bita, mayar da
gani, sake lisafi, kokkomawa, sake lale, ga su nan dai. A wajen Bahaushe:
Bincike na ]aukar ma’anar biyar abi daki-daki, da nufin gano
wani abu da aka sani, ko ba a sani ba, ko ake son a }ir}iro, ko ake son a sake
wa fasali. Sai an kammala bincike ake yin tottoniyar sake bita domin a mayar da
ganin da ake son a yi wa wata matsaya muhimmiya a kai.
A yau,
dukkanin harkokin cigaban duniya na ilmi na kowane fanni ga bincike ya dogara.
Masana koyaushe kan bincike suke domin fito da wani abu sabo, ]aliban ilmi
koyaushe a kan bincike suke domin gano wani abu sabo. Ke nan, bincike ya
kasance na kowa, don haka yake da darasi mai cin gashin kansa a kowane fannin
ilmi. Don haka nake son in }yallaro; shin kafin a haifi uwar mai sabulu yaya
belbela take? Tana da farinta? Ko sai da ta yi wanka da sabulun? Idan da
farinta aka taras da ita, to mai sabulu ta rage kuri, da doro, da kirari, ko
mahaifiyarta haka ta taras da belbela fara tas!
Hanyar [ora Bincike
Kalmomin
matashiyar bincike babu sabon abu a ciki, amma ƙudurin
binciken sabo ne a farfajiyar karin magana. Na ]ora wannan bincike a kan
tunanin Bahaushe da ke cewa: “Rashin sani ya fi dare duhu.” Abin
da duk Bahaushe bai hango ba za a ji shi yana cewa: “Abu kaza ya shige mini
duhu.” Duhun shi ne “rashin sani”. Rashin
sani babban duhu ne domin shi ne ya sa karen gwauro ya kori bazawara.
Da ta san karensu ne, me zai wahalar da ita da ti}a gudu? Idan za a tuna, rashin
sanin shi ya sa kaza ta kwana a kan dami da yunwa. Da ta san kan dami (in
gero/dawa/maiwa) take, ai da komai ya yi, an ba gwauro ajiyar mata. Da ]aliban ilmi sun
fahimci sirrin da ke cikin karin magananmu na bincike; da sun huta da
kama-kamen ra’o’in da ba su kai masu su ganga ba, bale su fitar da wanda ke
tsakiyar kogi. Wannan bincike a kan haka zai tafi, yana yi yana hango
ma}asudinsu bisa ga hanyar da aka ]ora shi.
Kayan Aiki
Babu
aikin da zai kai ga nasarar ma}asudinsa ba tare da an tanada masa nagartattun kayan aiki ba.
Kayan aikin da na tanada wa wannan bincike su ne:
ü Fitattun karin maganar da suka gabata
masu jigon bincike
ü Sababbin karin maganar da zamani ya haifar
masu jigon bincike
ü Karuruwan magana }wararru a fitattun sana’o’in gargajiya
ü Karuruwan magana da ke da ala}a da
fasahohin Bahaushe
ü Wasu labarai na ha}i}a ko }agaggu da ke tabbatar da }unshiyar
karin magana masu }unshiyar bincike
ü Matakan bincike daga masana bincike da suka yi canjaras da
karin maganar bincike
ü Wasu sassan adabin baka da ke fashin ba}in karin maganar
da suka shafi bincike.
Dabarun Bincike
Kayan aikin da
aka tanada akwai dabarun da aka bi wajen tantance su, da nazarin su, da taskace
su, a rubuce:
i.
Na farko, an yi
}o}arin samo wasu ayyukan ilmi da aka yi kan karin magana musamman kundayen
binciken samun wata takardar shaidar samun wata daraja ta karatun Hausa, ko wani fanni da aka yi garkuwa da karin maganar
Hausa.
ii.
An tunkari ayyukan
da suka ke~anta na }amusoshi na karin magana na Hausa domin }yallaro fashin
ba}insu.
iii.
Ba a yi ko oho da
mu}alu da mujallun da aka gabatar ko aka wallafa ba. An yi amfani da su sosai.
iv.
An ce, zamani riga,
don haka aka shiga rigar Intanet, da Kib]au, da Wasap, da kafafen sada zumunta,
domin farautar abin da za a nazarta.
v.
An samu tattaunawa
da wasu masana adabi, da ]aliban ilmin adabi, da na Hausa gaba ]aya, domin
samun gudunmuwarsu.
vi.
An mayar da hankali
ga wasu fitattun ayyukan da aka yi a kan Dabarun bincike cikin harshen Hausa da
Ingilishi, da ke tafiya da duniyar binciken wannan }arni, domin a dace da
abubuwan da ake son a tabbatar na gudunmuwar Bahaushen karin magana.
vii.
An yi duba cikin
ayyukan da aka yi kan karin magana a Ingilishi, da Igbo, da Yoruba, da Larabci,
domin rage wa aikin tsawo idan ya yi canjaras da wani/wasu daga ciki. Rashin
samun haka, ya ba da }arfin guiwa na cewa, a matsa gina, ruwa na }asa sai ga
wanda bai tona ba.
Sai an San Nauyin Kaya Ake
Jingar Daukar Su
A tunanin
karin magana, wajibi ne ga mai bincike ya tsaya, ya san me yake son ya yi
bincike? Tun gabanin a yanke shawarar bincike a kula da shirin shiga ruwa tun daga tudu
ake fara shi. A tuna da tunanin Bahaushe da ke cewa, da muguwar rawa gara }in
tashi. Shin fagen da za a yi bincike sabo ne, ko tsoho ne? In sabo ne, a yi
shawara da magaba, babbar yatsa ko ba ta cin tuwo ta iya ~are malmala. In kuwa
an ta~a bincike mai kama da shi, ga na gaba ake gane zurfin ruwa. A tabbata
}udurin binciken akwai wadataccen }wazo na fuskantar matsalolin da za a tunkara
a ciki, kada a yi rowarsa abin ya kasance gara jiya da yau. Haka
kuma, kada a bu]e gaba da yawa, a yi kwasan karan mahaukaciya, ko shifcin Gizo,
domin Wazirin Gwandu Malam Umaru Nasarawa ya ce:
Komi kakai kai dai bi]o daidai da kai,
Kwa] ]auki kaya sun fi }arfinai ga kai,
Yaf fara hanya tabbata mishi ba ya kai,
Tafiya ka]an na shi kai shi ]ora ta}ai-ta}ai,
Ko dai shi yas, koko shi fa]i su hau shi
Kowa da Bukin Zuciyarsa Ma}wabcin
Mai Akuya ya Sayo Kura
Ka da mai
bincike ya
ru]u da ruɗar da wasu ke yi wa fagen nazarinsu na kirari, ya kula da
cewa, kowane bakin wuta da irin nasa haya}i. Fannonin ilmi ba hanjin jimina ba
ne, da za a ce, akwai na ci akwai na zubarwa, jejjere suke tafiya kamar kashin
awaki. Abin da kake sha’awa shi za ka yi bugun gaba da shi, ya kasance,
zakaranka ra}uminka. Sai akwai sha’awa, da so, }wazon mai }wazo zai bayyana,
domin an ce, dama ka damun dawo in babu dama ana dama shi gaya.A a}idar
bincike, kowane allazi da nasa amanu domin bakin wani ba ya su]e wa hannun wani
miya. Sha’awarka ta jagoranci za~en fagen nazarinka, shi ka]ai
zai ba ka damar fito da wani abu a yi madalla da cewa, ka fitar da suhe wuta.
Masana na cewa, bincike tuwo ne kowa ya ]ebo da zafi bakinsa. Binciken ilmi
sha’awar mai shi ka sa shi nacewa har ya fito da wani abu sabo, ba a ja ta haka
nan ba. Sha’awa ke ba da tazarar }a}ale, da }ara wa Borno dawaki, a sihirce
tunanin mai karatu, abin da ya riga ya sani ya ganshi cikin wata sigar da bai
zata ba. Dubi yadda maka]a Sani [anbol]o Waramu ya fito da sha’awarsa ta noma:
Jagora: Kun san layun tsari
gare ni,
: Mi al layun tsarin ka Mamman?
: Dun}ullan dawo gami da nono,
: Ko wassha su ba shi jin kasala,
: In ko an yi gardama a dama,
: Rabbana Allah Ka taimake mu,
: Mu samu fitak kai cikin tukunya.
Wuyar Aiki Ba a Fara ba
Bayan za~en
fagen bincike da samun sha’awa a kansa, masana bincike sun ce, samun taken
bincike shi ne rage zango, mai zuwa sama ya taki faifai. Nagartaccen take shi
ake ce wa, abin nema ya samu matar Mallam ta haifi allo. Raggon take na nan
zamansa na ba a yi komai ba an raki ba}o ya dawo. Gina take a kan raddi sunansa
“ba ta
mutu ba ta ɓalkace. [ora shi a kan tambaya, zai kasance “ba cinya ba }afar
baya”. Kurakuran nahawu ga take ya zama “Koya sa}a da mugun zare”. Dole a yi wa
take kadada, ka da ya kasance daji ba ka da gambu. An
so }walailaice kadadar take ya zamo nashin }asa babu kure. A yun}urin
}walailaice kadadar take, a kula da abu biyu: Mai ɗaki
]ai shi ya san gefen da yake tarara, duk da haka, mai baibaya, ya san gefen da
ya toshe matararar ruwa. Ka da a yarda taken aiki ya yi takin sa}a da }unshiya,
ita kuwa }unshiya, ka da ta yi wa take reto, bu}ata su kasance, tangam mai zuwa
hajji ya gamu da Annabi (SAW). A fagen bincike, take shi ne fuskar aiki, fuska
kuwa ita ke sayar da riga. Take shi ne uban wa}a, sauran babuka da fasula ‘yan
amshi ne wani ba shi yi sai da wani. Idan tsakanin take da }unshiya kumbu ya
gamu da marufi, abin da duk zai biyo baya cikon sunna ne makaho da waiwaya.
Take da }unshiya tafiyar Buzu da ru}umi suke yi, idan suka yi bambarkwai, an
yanka ta shi, domin maka]a Sani Aliyu [andawo cewa ya yi:
Jagora: An ce kowag ga raƙumi shi ga Buzu ga,
: Ra}umi cikin daji.
Yara: Amma ga shi ban ga Buzu ba.
Gindi: Shehu sauran mazan hwarko,
: Mu zo Gwambe in gano
Sarki.
Sanin Wurin Bugu shi ne {ira
Hausawa sun
tabbatar da cewa, abin da duk wayo ya ~oye hankali na gano shi. A al’adance,
hankali ka gani ba ido. Mai bincike bi]ar wani abu yake yi,
an ko ce mai bi]a ya bar jin gajiya. Dagewa ga mai bincike dole ne domin mai
nema yana tare da samu. Jajircewa ga bincike wani babban makamin dacewa ne,
domin mai ha}uri yakan dafa dutse in mai izan wuta ya jure. Ba a yanke }auna ga
rashin kai ga bu}ata ko da an kai {aura Wambai saboda ko bayan tiya akwai wata
caca. Sanin wurin da za a bincike kamar ganin maciji ne a huta
da biyar sawunsa. Idan mai ginan ramin abu ya kai ga wutsiyarsa, kada ya sake
jiki sai ya kai ga kansa, ya ri}a hannunsa, sanin cewa ganin Dala ba shiga
birni ba. Abin da ake nufi da bincike ha}a ta kai ga wadataccen ruwa. A matsakaiciyar
fassara in ta yi ruwa rijiya, in ba ta yi ba masai. Babu laifi idan ruwanka ba
su isa wanka ba ka yi alwala a ci gaba da tafiya. An fi da son mai bincike ya
kasance ganau ba jiyau ba, in yana matakin jiyau ya matsa }aimi sai hankaka da
mai aya sun gana, a fassarar maka]a [ansani Dabere Bunza:
Jagora: Hankaka mai aya an
gana,
Yara: Kura tai karo da garken jakkai
Gindi: Yau da borin goje kana
da borin tashe
Ba a san Tafkin da ke Makara da Ruwa ba
A }a’idar
bincike, ba a rena hujja, ko wata dama komai }an}antarta. Magabata sun ce, idan
ra}uminka ya ~ata ko cikin akurki ka le}a domin da rashin tayi akan bar arha.
Da yawa ana zaton wuta a ma}era ba a samu ba, a same ta a
masa}a. Tsintuwar dami a kala ba mawuyancin abu ba ne, adabi ya tabbatar da
shi, kamar yadda ya tabbatar da zomo ba ya kamuwa daga zaune.
Ba a rena hujja komai }an}antarta a bincike, sau nawa }ilu ke jawo balau? Ai
]an hakin da ka raina shi ke tsone maka ido. Tottoniya na son
a fe]e biri har wutsiya har sai an ga abin da ya kwance wa Buzu na]i yadda
maka]a Bage [ansala Argungu ke cewa:
Jagora: An ce Buzu inda duk
yake,
: Yay yi na]i bai walwale shi ba,
: Ranar bara da za ni Yawuri
Yara: Na ishe Buzu za shi
yin ji}o,
: Duk rawani nai ya zube }asa.
Gindi: A ci dai ba don a
}oshi ba,
: Garin kwaki ya
yi taimaka
Yawon rangadin
gani da ido ya ba Bage [ansala cin nasarar ganin abin da ya ture wa
Buzu na]i.
Da Haka Muka Fara Kuturu ya ga
mai {yasfi
Kome ake son a
yi bincike a ri}a kulawa da mafarinsa, ko musabbabinsa, ko
tushensa, saboda wurin da an ka hau ice (itaciya/bushiya) duk nan ake sauƙa.
Ga alamu ko mafarin abin da ake son a yi bincike wata ƙofa
ce da za a bi cikin natsuwa domin ba banza ba }uda a warki. Samun tabbacin }uda
ba su bin mai kayan gawai shi zai ba mu damar tambayar in babu }ira me ya ci
gawai? Muradin bincike shi ne, lura da ba}on abu da yadda ya sa~a da al’adarsa
domin masana sun ce, tsuyen da ka zama gwaiwa tun yana }arami ake ganewa. In
ana binciken ilmi, duk wani abu aka ci karo da shi mai ala}a da abin da ake
nema adana shi ake yi bisa ga riwayar Dakarkari da ke cewa, mai ginan ~era ya
tono wutsiyar maciji ya yi sa’a babba. Mai bincike a kan maka]an Hausa ya ci
karo da masassa}in ganga an ta}aita masa jewa]i. Da an ankara da mafarin abin
da ake son a yi bincike, shi za a tunkara gadan-gadan domin Maka]a Gambo Fagada
ya ce:
Jagora: Halin duniya na ba ni
tsoro,
: Wai ga maciji ana ta biyat shayi da sanda,
: To! Ga ~arayi
: Shin mit bi]i mai wa}ar barayi?
A dai sa
himma, in an ga hanya gida ta nufa, domin komai nisan dawa da karkara kusa.
In ba ka san Gari ba Saurari
Daka
Daga cikin nagartattun
dabarun bincike akwai share fagensa da binciken ayyukan da suka gabata a
matakai daban-daban. Mai bincike a koyaushe kunnuwansa a bu]e suke na sauraron
tsegumi, jita-jita, ra]a, ba’a, gaskiya da }arya,
}aramar magana da babba a gunsa duk sunansu magana bincikensa zai tabbata
zubinsu da tsarinsu. Magabata sun tabbatar da matambayi ba ya ~ata,
domin ita tambaya mabu]in ilmi ce. Mai bincike mai neman sanin gari ne, Hausawa
ko sun ce, da ]an gari akan ci gari. Bu}atar ]an gari ga garin da za a kai wa
harin ya}i wata kinaya ce na mai bincike ya san da cewa, hannu ]aya ba ya
]aukar jinka. Tunanin Bahaushe na fa]ar kashin ba}i sai taro, wata fassara ce
ta hannu da yawa maganin miya yamamma. Idan aka yi wa bincike taron dangi ya fi tsafta
da ku~uta ga manyan kurakurai. Saka mataimaka a fannonin bincike daban-daban
zai bu]e wa mai bincike }wa}}afin da zai fito wa aikinsa mabambanta da za su ba
shi damar sanin hanyoyin da zai bi. Tamkar yadda maka]a Dr. Ibrahim Naramba]a
ke cewa:
Jagora: Ah! Ji wanda bai san hanya ba,
: Ya yi sabko,
: Amma fa ya ~ace
ya dawo.
Yara: Ila da yat tahi bai
]ora tambayar kowa ba,
Gindi: Ginshimin Haliru Uban
zagi na Malam Isa
: Gagarun jikan Shehu Iro mai Shanawa.
Tafiya da Waiwaya Tana Maganin
Mantuwa
Babu shakka
tafiya da waiwaya ba mantuwa kawai take magani ba, har makuwa tana magani.
Bitar ayyukan da suka gabata su ake nufi da a ri}a sara ana duban bakin gatari.
Komai }asurar masani da ]alibin ilmi sai da ya dafi kafa]ar wani aka ga
tsawonsa. Muradin bita tabbatar da gaba da gabanta, Muradin babu wanda ya koyar
da kansa masana sun ce, da koyo akan iya. Sanin cewa, kama da wane ba wane ba
ne, ake son kowane bakin wuta a fayyace irin nasa haya}i. Komai }an}antar aiki
a mutunta shi domin du}a wa Wada ba ya hana a tashi da tsawo. Idan mai bincike
ya kiyaye da, ga na gaba ake gane zurfin ruwa, a wajen bita ya sani cewa, cikin
}ira ake ɗa]i. Mai bita mai fa]a]en kama wani abu ne, Hausawa sun ce,
mai fa]a]e ba ya tayar da hannuwansa sama. Manufar bita tanka]e
da rairaya, ba komai ake kwashewa ba, ba komai ake zubarwa ba, dole a kasance
ido ga kifi, ido ga bado. A farautar kayan aikin bita ba a cewa, komai lauje ya
kamo haki ne, kuma tilas a nisanci kirarin matsoraci. Ga fashin ba}in bita a
bakandamiyar Dr. Ibrahim Naramba]a:
Jagra: Na jiya [andawo.
Yara: Ya yi tai uwar wa}a sai nai tau.
Jagora: Na jiya Akwara.
Yara: Ya yi tai uwar wa}a
sai nai tau.
Jagora: Na jiya Gurso.
Yara: Ya yi tai uwar wa}a
sai nai tau.
Jagora: Na jiya Janki]i.
Yara: Ya yi tai uwar wa}a
sai nai tau.
Jagora: Ai tun da Nagaya.
Yara: Ya yi tai uwar wa}a
sai nai tau.
Jagora: Dodo Malamin Wa}a Kundumi
Magajin [an~aidu.
Yara: Ya yi tai uwar wa}a
sai nai tau.
Dr. Naramba]a
ya yi adalci ambaton magabatan da suka riga shi }aga bakandamiya (uwar wa}a),
kuma babu shakka ya ji su, ya saurare su. Kan haka yake son ya }ago tasa sabuwa
bayan bitar da ya yi na wa}o}i irin ta.
In an ga ta |arawo a Dubi ta Mai Kaya
Mai bincike al}ali
ne, dole ya ri}a sara yana duban bakin gatari. Babu hujja ko maganar da ba ta
da muhimmanci gare shi, sai wadda ta kasa tsayi da }afafunta. Idan ya gano
laifin ~arawo na sata, to ya binciki ina ne mai kaya ya ajiye kayansa da aka
sata? In aka tabbatar da in ~era da sata ko daddawa da wari, nan za a gano
matakan hana wa ~era sata, da dabarun rage kaifin warin daddawa. Tilas bincike
ya kasance bugi sa bugi taiki, ta haka ka]ai za a tantance hasashen, ba ni na
kashe zomo ba rataya aka ba ni. Tunanin zama da ma]auki kanwa shi ke kawo farin
kai ke hana mai bincike yi wa hujjoji bugun goro. Faɗar
Bahaushe da ke cewa, ko Kwara tana da tsibiri dogon karatu ne mai rusa gajeren
tunani, domin ba dole ne mai kamar maza ka maza ba. Nagartaccen bincike bai
ta~a yanka ta tashi ba domin ba zai rage tazarar a sake lale ba. Bu}ata dai binciken
ilmi ya kasance raba gardama kamar yadda Alhaji Mamman Gawo Filinge ya yi da
‘yan amshinsa na kore zargin matsegunta inda ya ce:
Jagora: Kura cikin garken rago,
: Ko sau ]aya ba ta fasa garken ba,
: In ta ta~a ku hwa]i ga ku?
Yara : A’a Malam ba ta kutsa ba.
Jagora: Haka nika tammaha!
Gindi: Ya Allah gyara,
: Wahabu Ka taimaki ‘yan Nijar.
Bu}atar Dara a Kasa
A koyaushe aka
]ora harsashen tottoniya wani abu ake son a gano sabo, ko wanda ya ~ata, ko wanda
ake ta}addama a kansa. Buƙata ka da aiki ya
kasance jita-jita hadisin Bamaguje, ka da a yarda ya zamo labarin }anzon
kurege. Dole akwai abin da ka gano cikin jewa]in da aka yi na bincike ka da ya
kasance shigan }adangare Shantu. Tabbatar da binciken wasu kirarin matsoraci
ne, ba bincike ba ne. Kushe kowa ba karatu ba ne, ko da an ga kuskure ba a rama
gayya da hushi. Ana son a ji, shin ya~i ne ka yi wa katangar
ko yaso ne ka yi wa rijiyar. To me ya sa ka yi haka? Le}o sabo ko wace kafa ka
toshe? Matu}ar ba a gano komai ba, to, ba a binciko komai ba. In ta tabbata
haka, aikin ya zama aikin banza yi wa kare wanka.
Binciken duk da ba ya da sakamako an yi sammakon banza domin da mugunyar rawa
gara }in tashi. Maka]a Dr. Ibrahim Naramba]a ya ce:
Jagora: Shin kowag ga wuta
: An ka ce a ]ebo wa ka zuwa?
Yara: Wanda yag gani ka zuwa,
: Kowas shaida shi ka shan rana,
: In bai tai ba yai batun banza,
: Ko can yanzu shi batun banza,
: Da]in hwa]i garai.
Gindi: Ya ci maza, ya kwan
shina shire,
: Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.
Wanda ya ce ya
ga wuta bai ]ebo ta ba, ya yi }arya, haka nan wanda ya ce, zai yi binciken abu
bai ba da sakamakonsa ba yake.
Shirin Shiga Ruwa Tun Tudu Ake
Kimtsa Shi
Idan an daidaita
a kan matashiyar da za a ]ora aiki a kai, a tabbatar da an yi wa fitilun
kalmominta mazarin in til, in ƙwal, rinin
mahaukaciya. A yi wa kalmomin matashiya zubi biyu. Akwai fitilun kalmomin gina
aiki wa]anda a kansu aiki zai tsayu, su za a yi wa twa-da-twa wankin ]an Kanoma
mashaya. Duk wani abin da ya shafe su a nagartar da fayyace shi da gawurtattun
hujjoji. Ka da a bari su yi canjaras da aikin kowa domin kauce zurmugu]]u. Idan
aro kalmomin aka yi a nuna ma}aginsu. A tabbata ba kai ka kashe zomo ba, rataya aka ba ka. Sauran
kalmomi ‘yan rakiya, in sai da su zuciyar aikin za ta
tabbata dole a ware musu babin kansu domin ya zama gadon fe]e aiki irin aikin
sitari da tayoyi ga mota, ko direba bai so ba wurin da suka dosa can mota ta
nufa. Idan nahawun kalmomin matashiya ya diaidaitu, shi
zai yi wa }unshiyar aiki “ki]a” shi kuwa aikin yai
“amshi” daidai da kalmomin da aka girka shi a kai. Hausawa sun ce, in kifi ya
tashi lalacewa ga kai yake ru~ewa. Da an samu matsala ga marshiyar aiki ba ta
da filin gyara mai neman beli ya mari uwar Al}ali. Sake wa matashiya tsari
kasawar bincike ne, cirata daga gare ta zuwa ga wata ya nuna tsuntsun da ya
kirai ruwa, ruwa sun ci shi. {udurin shiga bincike irin na shirin shiga ruwa ne
ga masunci ko fagen artabu ga maya}i. Aliyu Dandawo a wa}ar Sarkin Kabi Sama ya
ba mu shawarar shirin fuskantar ya}i da cewa:
Jagora: In tahiya ta tashi,
: Ka sa a shirya
dawaki,
: A ]aura damman
masu,
: Ko suna taya
fansa,
: A tabbata wa
maza,
: Ba a girsuwar
mai }arfi.
Yara : A yanzu wa am madadin Mainasara ba kai ba?
: Shugaban tahiya
Sarkin Kabi mai Sudani,
: Ila marin rugga
]an Ya}uba sa gurfani.
Idan ba a
shirya kayan farauto hujjojin bincike ba, matashiyar aiki ba ta zama da
gindinta. Idan matashiya ba ta tsaya a kan }afafunta ba, ba a yi komai ba an
raki ba}o ya dawo.
Sakamakon Bincike
Hausawa na da ra’ayin cewa, ~eran gida ba ya da mai. Duk
al’ummar da aka yi wa mulkin mallaka na ci da }arfi a }ar}ashin kowace a}ida,
ko addini, sai an rusa musu kyawawan ]abi’unsu an cusa musu na ba}in haure. A
tsarin ilmin boko, Turawa sun yi tsaye ga kore duk wani ilmi da ba su zo da shi
ba a matsayin ilmin gargajiya. To, su nasu da suka gada kaka da kakaninsu na
mene ne? Ba dai za a a kira shi ilmin zamani ba, domin an yi shi tun gabanin zamunansu?
Wannan ]an bincike nawa ya ]an ba mu haske kan abubuwa uku:
1.
Duk wata dabara da za a bi ta binciken kimiyya, ko fasaha ko wani ilmi na
ko mene ne, idan aka sa adabin karin maganan Hausa gaba za a samu sirrin
gudanar da shi.
2.
Da za mu sa natsuwa sosai a cikin karin maganan Hausa ka]ai za mu iya
}ir}iro ra’o’in bincike da yawa mu huta da kwashe-kwashen ra’o’in da ba su yi canjaras da tunanin
magabatanmu }wararru ba.
3.
Karin magana taron dangin masana ne da }wararru a fannoni daban-daban, don haka hannu da yawa ne an ko
ce, yana maganin miya yamamma.
4.
Karin magana daji ne ba ka da gambu. Babu abin da ke }ar}ashin gizagizan sararin Subhana
da bai ta~o ba. Ilmin bincike wani ]an leza ne daga cikin dakakin ilmi, idan
har an samu rassansa da karin magana ya kakkamo, to a matsa }aimin bincike, da wuya
a samu fannin da bai ta~o ba.
5.
A }arshe, za mu ga cewa, duk wani aikin bincike na ilmukkan karatun Hausa,
idan ba a gayyato karin magana ba ko an yanka tana tashi. Idan an yi ko oho da
karin magana, ba za a samu nagartaccen sakamako ba.
Na]ewa
Ilmi daga cikin al’adun mutane aka }ago shi babu al’ummar da aka yi wa wahayin
yadda za ta tunkari abubuwan da ke yi mata barazana sai dai ta taras da su
cikin al’adunta. Wanda duk aka sa ya wofintar da al’adarsa ya ]auki na wasu an
toshe masa }ofofin bun}asa tunaninsa. A duban wannan ]an bincike, akwai alamar
cewa, lallai mulkin mallaka ya yi tasiri ga zukatan ‘yan boko musamman wa]anda
karatun Hausa ya rufa wa asiri suka dawo suna ya}i da shi. An sihirce musu }wa}walwa
har suna ganin babu wani cigaba ga ilmi in ba Ingilishi aka ]auka tafarkin ilmi ba.
Wannan ta sa, aka manta da irin taskokin hikima da wayo, da ilmi, da fasaha, da
kimiyyar da ke cikin karin maganar Hausa; har wasu suka soma salwanta ba a
adana su ba. Ya kyauta a ce, mun fara rarraba karin magana cikin kowane fanni na
karatun Hausa ya jagoranci bincike-binciken da ake son a yi a fannin. Kowa a ka
rinjaya ga kiyaye karin magana an fi shi wayo da sanin dabarun zaman duniya. Don haka a cikin koyar da
dabarun bincike a kula da “Taskar karin Magana”.
Ratayen Karin Maganar da Aka Sarrfa
1. A ri}a sara ana duban bakin gatari.
2. A yi dai mu gani.
3. Abin da wayo ya ~oye, hankali ke gano shi.
4. Abin nema ya samu, matar Malam ta haifi allo.
5. Aikin banza yi wa kare wanka.
6. An koya sa}a da mugun zare.
7. An nemi wuta ma}era an rasa, an je masa}a aka samu.
8. An rage zango mai zuwa sama ya taka faifai.
9. An yanka ta tashi.
10. Ana cikin gina ga wutsiya.
11. Ba a rama gayya da hushi.
12. Ba a san maci tuwo ba sai miya ta }are.
13. Ba a san tabkin da ka makara da ruwa ba.
14. Ba a yi komai ba, an raki ba}o ya dawo.
15. Ba banza ba, }uda a warki.
16. Ba cinya ba }afar baya.
17. Ba mai kamar maza ka maza ba.
18. Ba ni na kashe zomo ba, rataya aka ba ni.
19. Ba ta da filin gyara, mai neman beli ya mari uwar Alkali
20. Ba ta mutu ba ta ɓalkace.
21. Babbar yatsa ko ba ta cin tuwo ta iya ~are malmala.
22. Bakin wani ba ya su]e wa hannun wani miya.
23. Ban sani ba, ta raba ni da kowa.
24. |eran gida ba ya da mai.
25. Bu}atar dara a kasa.
26. Bugi sa bugi taiki.
27. Bugun goro.
28. Cikin }ira aka ɗa]i.
29. Cikon sunna, makaho da waiwaya.
30. [an hakin da ka raina, shi zai tsone maka ido.
31. Da ]an gari akan ci gari.
32. Da gina sabuwar rijiya gara yaso.
33. Da haka muka fara, kuturu ya ga mai }yasfi.
34. Da koyo akan iya.
35. Da mugunyar rawa gara }in tashi.
36. Da sabuwar katanga gara ya~i.
37. Daji ba ka da gambu.
38. Dama ka damun dawo, in babu dama ana dama shi gaya.
39. Du}a wa Wada ba ya hana ka tashi da tsawonka.
40. Fe]e biri har wutsiya.
41. Fitar da suhe wuta.
42. Fuska ke sayar da riga.
43. Ga maciji ana biyar shayi da sanda.
44. Ga na gaba ake gane zurfin ruwa.
45. Gaba da gabanta.
46. Ganin Dala ba shiga birin ba.
47. Ganau nike ba jiyau ba.
48. Gara jiya da yau.
49. Ha}a ta kai ga ruwa.
50. Hanjin jimina akwai na ci, akwai na zubarwa.
51. Hankali ka gani ba ido ba.
52. Hannu ]aya ba ya ]aukar jinka.
53. Idan ra}uminka ya ~ata ko cikin akurki ka le}a.
54. Ido ga kifi, ido ga bado.
55. In an bi daga-daga na }urya ya sha kashi.
56. In an ga hanya gida ta nufa.
57. In an ga ta ~arawo a dubi na mai kaya.
58. In ba ka san gari ba saurari daka.
59. In babu }ira me ya ci gawai?
60. In |era da sata ko daddawa da wari
61. In da fata ta fi laushi nan ake mayar da jima.
62. In ka ji namu da mai shi.
63. In kifi ya tashi lalacewa, ga kai yake ru~ewa.
64. In ruwanka ba su ishe ka wanka ba, ka yi alwala.
65. In ta yi ruwa rijiya, in ba ta yi ba masai.
66. In til, in ƙwal, rinin mahaukaciya.
67. Jejjere kamar kashin awaki.
68. Jita-jita hadisin Bamaguje.
69. Kallon hadarin kaji.
70. Kama da wane, ba wane ba ne.
71. Kashin ba}i sai taro.
72. {ara wa Borno dawaki.
73. {aramin sani }u}umi ne.
74. {aura Wambai.
75. {ilau! Ya jawo balau!
76. Ko bayan tiya akwai wata caca.
77. Ko Kwara tana da tsibiri.
78. Komai ya yi, an ba gwauro ajiyar mata.
79. Komi lauje ya kamo haki ne.
80. Komi nisan dawa da karkara kusa.
81. Kowa da bukin zuciyarsa, ma}wabcin mai akuya ya sai kura
82. Kowa ya ]ebo da zafi bakinsa.
83. Kowa ya ga ra}umi ya ga Buzu.
84. Kowane allazi da nasa amanu.
85. Kowane bakin wuta da irin nasa haya}i.
86. {uda ba su bin mai kayan gawai.
87. Ko kamin a haifi uwar mai sabulu belbela tana da farinta.
88. Kumbu ya gamu da marufi.
89. Kwasan karan mahaukaciya.
90. Labarin }anzon kurege.
91. Magani sai da bi]a.
92. Mai bi]a ya bar jin gajiya.
93. Mai ]aki shi ya san gefen da yake tarara.
94. Mai fa]a]e ba ya tayar da hannunsa sama.
95. Mai ginan ~era ya gamu da maciji ya yi sa’a babba.
96. Mai ha}uri yakan dafa dutse, in mai izan wuta ya jure.
97. Mai nema yana tare da samu.
98. Matambayi ba ya ~ata.
99. Na babban mahaukaci, “duk duniya”.
100. Nashin }asa babu kure.
101. Rashin sani karen gwauro ya kori bazaura.
102. Rashin sani, kaza ta kwana kan dami da yunwa.
103. Rashin sani ya fi dare duhu.
104. Ruwa na }asa sai ga wanda bai tona ba.
105. Sai an ga abin da ya ture wa Buzu na]i.
106. Sai an san nauyin kaya ake jingar ]aukar su.
107. Sanin gari.
108. Sanin wurin bugu shi ne }ira.
109. Shifcin gizo.
110. Shigan shantun }adangare.
111. Shirin shiga ruwa tun tudu ake fara shi.
112. Tafiya da waiwaya tana maganin mantuwa.
113. Tambaya mabu]in ilmi.
114. Tangam! Mai zuwa Haji ya gamu da Annabi (SAW).
115. Tsintuwar dami a kala.
116. Tsuntsun da ya kirai ruwa, ruwa sun ci shi.
117. Tsuyen da ke zama gwaiwa tun yana }arami ake ganewa.
118. Twa-da-twa wankin ]an kanoma mashaya.
119. Wada duk ka ce, haka na ce kirarin matsoraci.
120. Wurin da aka hau ice nan ake sauka.
121. Wuyar aiki ba a fara ba.
122. Zakaranka ra}uminka.
123. Zama da ma]aukin kanwa, shi kan kawo farin kai.
124. Zamani riga.
125. Zomo ba ya kamuwa daga zaune.
Manazarta
Bunza, A. M. (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal
Publications Limited.
Bunza, A.
M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Al-Ibrash Publication Plc.
Bunza, A. M. (2017) Dabarun Bincike: (A Nazarin Harshe da Adabi
da Al’adun Hausawa).Tetfund Publications, Zaria:
Ahmadu Bello University Press.
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya
(1981). Rayuwar Hausawa. Lagos: Thomas Nelson (Nigeria)Limited.
Ɗangambo, A.
(1984). Rabe-raben Adabin Hausa da
Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Maɗaba’ar Triumph,
Gidan Sa’adu Zungur.
Ɗangambo, A.
(2008). Rabe-raben Adabin Hausa (Sabon
Tsari). Zaria: Amana Publishers
Limited.
Fennegan, R. (1970). Oral Literature In Africa. London:
Oxford University Press.
Furniss,
G. (1996). Poetry,
Prose and Popular Culture
in Hausa,
International
African Library Edinburgh: Edinburgh University Press,Ltd.
Green, K. (1966). Hausa Ba Dabo Ba Ne. London: Oxford University Press.
Koko, H. S. (2011). Hausa Cikin Hausa. ISBN.
978-978-919-267-0.
Madauci, I., Isa, Y., & Daura, B.
(1982). Hausa Costoms. Zaria: Northern Nigerian Publication Company.
Nahuce, I. M. (2008). “Karin Maganar
Hausa a Rubuce.” Kundin Digiri na
Biyu (M.A). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Shuni, M. A. (2023). “Nazarin Amfani da
Karin Maganganun Hausa na Mutane
Masu Bukata ta Musamman.” Kundin Digiri na Biyu (M.A). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Skinner, A. N. (1988). “Lexical
Incompatability As a Mark of Karin Magana.”
Cikin Furniss, G. da Wasu (Editoci). Studies
in Hausa Language and Linguistics
in Honour of F. W. Persons, London.
Umar, M. B. (1987). Dangantakar Adabin Baka da Al’adun
Gargajiya. Kano: Triumph Publishers.
Yakasai, S. A. (2019). “Nazarin Ma’ana
a Muhallin Magana: Tsokaci a Kan Zaɓaɓɓun Karin
Maganganun Hausa na Mutane Masu Bukata
Ta Musamman.” Ɗunɗaye Journal of Hausa StudiesVol. 2, No.
2 Pp.13-22. Sokoto:Department of Nigerisan Languages, Usmanu Danfodiyo University.
Yunusa, Y. (1989). Hausa a Dunƙule. Kano: Maɗaba’ar Trium, Gidan Sa’adu Zungur.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.