Ticker

Sakayya Bayan Taimako

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Mutum ne na yi masa hanya ya samu aiki kamar na sa canopy a masallaci. Bayan an biya shi haƙƙinsa sai ya ba ni wani abu, ko ya dace in karɓa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Idan tun kafin ya fara aikin kun yi yarjejeniyar hakan cewa, zai biya ka wani kaso daga cikin abin da ya samu, to wannan ne bai halatta ba. Domin ya shiga cikin (Al-Aklu Bis-Shafaa’ah), watau: Ci da ceto kenan, wanda As-Shakh Abdurrahman Al-Akhdariy (Rahimahul Laah) ya lissafa shi daga cikin haramtattun abubuwa. Sannan kuma hanya ce ta cin dukiyar mutane da ɓarna wadda Allaah ya hana.

Amma a lokacin da ya zama babu wani abu irin wannan, shi ne dai kawai a bayan ya karɓi ladan aikinsa ya ga ya dace ya yi maka ihsani, ban san wani dalili da ya hana ka karɓa ba. Domin tun da dai wanda ya kawo biyan bashi tare da ƙarin da ba a yi yarjejeniyarsa tun da farko ba bai yi laifi ba, to me zai janyo a samu laifi a cikin wannan.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments