Sana'ar Gini

    Sana'ar Gini

    Sana'ar Gini sana’a ce da ake sarrafa abubuwan da suka shafi Æ™asa kamar irin su yumÉ“u, taÉ“o, yashi da sauransu domin su zama masu amfani. Kamar gina muhalli da kuma gina mazubi kamar irin su tukunya, tulu, da sauransu.

    Wannan sana’a ta gini daÉ—aÉ—É—iyar sana’a a ce. Asali mutane kan gina bukka ne ta hanyar amfani da kara sannan kuma daga baya a yaÉ“e shi da Æ™asa. Daga nan kuma sai aka samu cigaba, aka koma ana gina É—aki da zallar tubalin Æ™asa, kama-kama har zuwa yin bulon Æ™asa sannan a gina É—aki da shi.

    Sana’ar Gini ta kasu gida uku:

    1 .Akwai ginin muhalli da ya shafi gina gida baÆ™i É—ayansa da dukkan nau’ukan É—akuna kamawa tun daga É—akin kwana, É—akin hutu, É—akin girki, É—akin karatu da sauransu.

    2. Ginin Tukwane da sauran kayayyakin adana ruwa, abinci da sauransu.

    3. Ginin Rijiya, sana’a ce da ake haÆ™a rami domin samo ruwan amfanin yau-da-kullum, ko kuma masai (shadda ko sarga).

    Daga Zauren:
    Hausawa da Harshensu

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.