Ticker

Sana’ar Snooker

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Yayansa ne ya saka teburin snooker a ƙofar gidansu kuma ya ce, shi ne zai riƙa kulawa da shi, ya riƙa tara kuɗin. Shi ne yake tambaya: Ko ya halatta ya amince?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Galibin wasannin zamanin yau an ƙirƙiro su ne musamman domin su ɗauke hankulan mutane, su mantar da su abubuwan da suka fi zama muhimmai a gare su a cikin duniyarsu da makomarsu. Shagaltarwa kawai suke yi daga sallah da ambaton Allaah da hana matashi zuwa wurin sana’a don neman dukiya ta halal. Ko kuma su kai ga cin dukiyar mutane ba da haƙƙi ba, kamar ta hanyar caca da sauransu. A daidai lokacin da manyan maƙiyan jamaar duniya, waɗanda suke ɗaure wa irin waɗannan wasannin gindi kuma suke tallata su a cikin matasa a faɗin duniya, suke can suna ta tsare-tsare da ƙulle-ƙullen yadda za su mallaki jamaar duniyar, har sai sun yi musu ɗaurin deman-minti sun saka su a cikin aljihu, ta hanyoyin yaudara da makirci iri-iri.

Daga cikin wasannin da ni dai ban ga wani amfaninsu ga jiki ko tunanin ko lafiyar mutum ba akwai snooker. Watau, wasan da ake zuba ’yan ƙwallaye a kan tebur a riƙa zungurar su da wata sanda, suna faɗawa a cikin wani rami.

A fahimtata babu wani abu da ake samu daga wannan a zahiri ta fuskar ƙara wa jiki ko wata gaɓa lafiya. Haka nan dai ban ga wani abu a cikinsa mai janyo ƙarin kaifin gani ko basira ko tunani ba. Abin da ke cikinsa kawai ɓata lokaci ne, ɗaga murya ne da ihu da hayaniya da sauran maganganun banza. Sai aukar da gaba da ƙiyayya a tsakanin masu wasan da yan kallo, da shagaltarwa daga yin sallah da ambaton Allaah, da kuma cin dukiyar mutane da ɓarna kamar ta hanyar caca da sauransu. Waɗannan kuwa duk haramtattun abubuwa ne a mahangar addinin musulunci, wanda kuma kowa ya san haram ne.

Idan kuwa haka abin ya ke, to bai halatta musulmi ya taimaka a kan hakan da dukiyarsa ko jikinsa ko lokacinsa ko ma shawararsa a kan cigaba da wannan aikin ba. Wajibin kowane musulmi dai shi ne, ya rabu da irin waɗannan sana’o’in ya kama waɗanda suka halatta, kamar kasuwanci ko noma ko kiwo na halal da sauransu.

Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce:

... وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَى، وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ، وَاتَّقُوا اللَّهَ، إِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَاب ٢۝

Kuma ku taimaki juna a kan aikin alheri da ƙarin taqawa (tsoron Allaah), kuma kar ku taimaki juna a kan zunubi da ƙetare iyaka. Kuma ku ji tsoron Allaah. Haƙiƙa Allaah mai tsananin uƙuba ne. (Surah Al-Maaidah: 2).

Allaah ya datar da mu ga abin da yake so.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments