𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Gafatta malam ni ne na siya kaya
naira ɗari (₦100), sai na siyar naira ɗari biyu (₦200), shin na ci haram ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam. Lallai ɗan'uwa ba haramun ka ci ba, saboda babu
wani dalili a littafin Allah ko a sunnar Manzon Allah ﷺ ko a ijmá'in malamai da ya iyakance iya
riba a kasuwanci. Sai dai fa hakan bai zama hujja na gallazawa bayin Allah
farashin kayayyaki ba, saboda Allah na sa wa kasuwanci albarka matuqar an
sauqaqa, kuma an yi gaskiya.
Kawai dai a tabbatar mai sayen kaya ya san qimar
kayan da zai saya, bai jahilci kayan ba, saboda wani akan buga masa tsada ne ta
hanyar la'akari da bai da ilimin wannan abu da zai siya, Allah ya shiryar da
mu.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance
Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.