Shin Sanya Yatsa A Gaban Mace (Fingering) Yana Da Illa?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Aslm malam naga kuna ta magana akan sanya hannu a gaban mace akwai matsala to ni kuma gaskiya matata na riga na saba mata da sanya hannu amman ba can ciki ba, dan kan nan dai shi nake mata wasa da shi a haka na saba mata nake gamsar da ita sannan in yi nima saboda duk abin da za muyi idan na fara to da wuri nake releasing 5 to 10 minutes har na yi releasing to ita kuma a hakan bata yi to da na lura sai in cigaba da yi mata da yatsa har ta yi ko kuma kafin in fara ma sai na yi mata na tabbatar ta gamsu sannan. To yanzu malam me ya kamata inyi naga kace akwai matsala sanya hannu a gaban mace.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Lallai gaskiya ne sanya hannu, watau dan-yatsa, a cikin gaban mace (fingering) domin motsa mata sha'awa yana iya haddasa mata hatsarin kamuwa da kwayoyin cuta. Dalilin fadin haka shine saboda hannu yana dauke da dumbin kwayoyin cuta iri-iri wadanda idanu basu iya ganinsu. Kuma shine dalilin da yasa yawan wanke hannuwa yake ɗaya daga cikin hanyoyin rage kamuwa da cututtuka.

    Idan da ma'aurata zasu rika yin fingering da kulawa, to, da hatsarin kamuwa da cututtukan zai ragu. Kulawar anan ita ce a tabbatar da tsabtar hannu ta hanyar wanke shi sosai a lokacin da za a yi, da kuma tabbatar da an yanke kumba.

    Amma shawara anan ita ce kayi kokarin canzawa daga yi mata fingering ɗin zuwa yin wasanni da wasu sassan jikinta na daban a lokacin da zakuyi Sunnah. Hakan yafi kwanciyar hankali.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.