Shin Zan Iya Sallah Da Tufafin Da Kafiri Ya Ba Ni?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, malam dan Allah idan mutum yana da 'yar uwa Kiristan ta ba shi kayan sawa idan ya karba zai iya salla da shi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀

    Wa'alaikumus salam, ya halasta mutum ya karbi kyautar kayan sawa a wurin Kirista, kuma ya halasta mutum ya yi sallah da kayan idan ya tabbatar da tsarkin kayan, idan kuma mutum yana kokwanto a game da tsarkin kayan, to ya wanke su ya sa abinsa ya yi sallah da su, sallarsa ta inganta da ikon Allah, saboda asalin al'amari game da kayan sawa shi ne halasci, in banda abin da Shari'a ta haramta.

    Kayan da bai halasta a karɓa a sa ba su ne kayan da suka keɓanta kaɗai da kafirai, wanda gaba ɗaya ba mai amfani da shi sai su, to wannan shi ne bai halasta mutum ya karɓa ya sa ba, ballantana har ya yi ibada da su, saboda addini ya hana mu yin kamanceceniya da kafirai.

    Allah S.W.T ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.