Ticker

Shin Zulaihat Ta Auri Annabi Yusuf As

TAMBAYA (23)

Sai tambaya ta ukku tarihin annabi Yusuf shin matansa nawa km yayansa nawa km ance wai y auri zulaihat matar d tayi mashi sharri akakaishi kurkuku d gaske ne

AMSA

A magana mafi rinjaye babu wata hujja a Qur'ani ko Sahihin Hadisi wanda akace Zulaihat matar sarki Aziz na Misrah (Egypt) ta auri Annabi Yusuf idan ma akwai hujjar to Isra'eliyat ce wanda mu kuma a matsayinmu na musulmai al-Qur'ani da Hadisan Ma'aiki SAW sun ishemu kafa hujjar ilimi

Ya tabbata a cikin Qur'ani mai girma cewar Matar Sarki Aziz ta nemi Annabi Yusuf AS da fasiqanci sai Allah SWT ya kiyayeshi:

( وَقَالَ نِسْوَةٌ فِي الْمَدِينَةِ امْرَأَتُ الْعَزِيزِ تُرَاوِدُ فَتَاهَا عَن نَّفْسِهِ ۖ قَدْ شَغَفَهَا حُبًّا ۖ إِنَّا لَنَرَاهَا فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ )

يوسف (30) Yusuf

Kuma waɗansu mãtã a cikin Birnin suka ce: "Matar Azĩz tanã nman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin ta cikin ɓata bayyanãnna."

Nan da nan ta hada liyafa domin ta bayyanawa yan uwanta mata dalilin da yasa ta nemi shi, kyawunsa ne silar abin da ya rudeta:

( فَلَمَّا سَمِعَتْ بِمَكْرِهِنَّ أَرْسَلَتْ إِلَيْهِنَّ وَأَعْتَدَتْ لَهُنَّ مُتَّكَأً وَآتَتْ كُلَّ وَاحِدَةٍ مِّنْهُنَّ سِكِّينًا وَقَالَتِ اخْرُجْ عَلَيْهِنَّ ۖ فَلَمَّا رَأَيْنَهُ أَكْبَرْنَهُ وَقَطَّعْنَ أَيْدِيَهُنَّ وَقُلْنَ حَاشَ لِلَّهِ مَا هَٰذَا بَشَرًا إِنْ هَٰذَا إِلَّا مَلَكٌ كَرِيمٌ )

يوسف (31) Yusuf

Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: "Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika ne mai daraja!"

Da taga suma sun kidima da ganin kyawunsa sosai, sai tace musu

( قَالَتْ فَذَٰلِكُنَّ الَّذِي لُمْتُنَّنِي فِيهِ ۖ وَلَقَدْ رَاوَدتُّهُ عَن نَّفْسِهِ فَاسْتَعْصَمَ ۖ وَلَئِن لَّمْ يَفْعَلْ مَا آمُرُهُ لَيُسْجَنَنَّ وَلَيَكُونًا مِّنَ الصَّاغِرِينَ )

يوسف (32) Yusuf

Ta ce: "To wannan ne fa wanda kuka, zarge ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga ƙasƙantattu."

Sai ya zabi zaman kurkukun

( قَالَ رَبِّ السِّجْنُ أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا يَدْعُونَنِي إِلَيْهِ ۖ وَإِلَّا تَصْرِفْ عَنِّي كَيْدَهُنَّ أَصْبُ إِلَيْهِنَّ وَأَكُن مِّنَ الْجَاهِلِينَ )

يوسف (33) Yusuf

Ya ce: "Yã Ubangijina! Kurkuku ne mafi sõyuwa a gare ni daga abin da suke kirã na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jãhilai."

Akan wannan gabar zan ja hankalin musulamai cewar sanin ko Zulaihat Matar Sarki Aziz ta auri Annabi Yusuf AS ba shine al-muhim a cikin kissar ba saidai darussan da tarihin ya kunsa ya fi kamata a lura

Akwai darasi a cikin wannan tarihi na Annabi Yusuf AS bin Yaqub AS bin Ishaq AS bin Ibrahim AS, wanda qalubale ne ga wadanda suke bin son zuciyarsu su amsa gayyatar shaidan su aikata alfasha

Muna roqon Allah ya bamu ikon kiyaye kanmu yasa mufi karfin zuciyarmu

Walahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments