Ticker

Ta'aziyyar Malam Giro Argungu

Amshi:

Dubun jama’a na alhinin,

Rashin masanin dattijon nan,

Mu dau darasin mutuwa dangi,

Allah ya jikan malam Giro.

 

1. Tabaraka Sarki Ya Allah ka amshi batun angon Mero,

Ka min fatahi na yi ‘yan baiti akan mutuwar Malam Giro,

Mazaunin Kebbi na Argungum fagen da’awa babban kwaro,

Abinda ka yo duka mun shaida Ilahu Ya Yarda ka yo moro.

 

2. Abar fahari Sunna TV tana ta’aziyya gun kowa,

Musulmai harda kiristoci akan rasa malam dan baiwa,

Mu dau hakuri jama’ar yankin Arewa da ku na Kudadawa,

Da Ghana da Niger har Camaru fari da baki duka na jero.

 

3. Cikin hidimar da’awar sunna a Burkina Faso ya bar baya,

Ya assasa tushen alkairi kamar wanka da farin kaya,

Hakan yayi ma a  kasar Benin Kwadebuwa basu sahun baya,

Gabon ma ya musu alkhairi da mai aurensu da ma gwauro.

 

4. Abin sha’awa a halin malam abubakari bai son girma,

A duk matsayinsa abokansa yakan yi makaho har kurma,

Yakan dauko karamin yaro abokai nai ku sako ni ma,

Hakan ya saka dukkan jama’a suke kaunar malam giro.

 

5. Ku duba ma a fagen da’awa da kaifi dai yaka yin zance,

Kasancewarsa cikin JIBWIS da su da wasunsu yana dace,

Yakan bi sahun yin adalci dukan rikicinmu ya magance,

Izala in wani yai laifi mu kai kara a wajen Giro.

 

6. Kamar gaushi yake gun zafi da an taba sunna ba wasa,

Yakan cire dukka makami nai wukarsa yaje shi ya wawwasa,

Idan ko da shi kaka yin rigima Sadiqu baza shi ya dau fansa,

Abubakari mutumin kirki Allah ya jikan malam Giro.

 

7. Dukan jama’a sun yo shaida akan mutumin kirki Giro,

Kafafen sada zumunci kaf da ka shiga sai maganar Giro,

Yana wa’azinsa yana kuka hisabi dai yaka yin tsoro,

Yana neman afuwar bayi Ilahu ka haskaka Sheik Giro.

 

8. Aboki sai ka yi hankalta abinda ka yo shi za a fada,

Idan ka bar abu mai kyawu status za a saka mu nada,

Da ka mutu sai a ta yin fostin ana jama’a ku ga wannan da,

Mala’inku kuwa su shaidar mutane dai suka sauraro.

 

9. Akwai wasu wanda a halinsu sukan yi rawa da kidan ganga,

Mazansu da mata na shewa tsiraici nasu ana hanga,

Su dauka sai su saka tiktok da youtube tunda hakan suka ga,

Garesu kamar shine mafita suna watsi da fadin Giro.

 

10. Tashar Sunnarmu tana ta kiran ku dauki halinga na babana,

Ina kuke limaman sunna da ma mabiyanku abokaina,

Ku taru ku kama irin tsarin Abubakarinmu masoyina,

Idan kuka zo mutuwa kuma a dinga yabonku kamar Giro.

 

11. Ku dau hakuri ‘ya’yan malam da mata nai da abokai ma,

Irin wannan mutuwa kowa ta shafa dan abu ya girma,

Rashin Malam da akwai zafi a da can mun rasa Manzo ma,

Kawai sai dai muta yin adu’a Allah ya jikan malam Giro.

By:

Mahmud Ahmad Musa (Mahmudul Khalam) +234 902 019 4569

Post a Comment

0 Comments