Takardar da aka gabatar a taron Ranar Hausa ta Duniya, ƙarƙashin Jagorancin Dandalin Fasaha da Adabi na Daular Usmaniyya (Caliphate Arts and Literary Forum B18, K7 Mall, Agai Road, Sokoto) Ranar Lahadi 18 ga Agusta, 2023 a ɗakin taron Kwalejin Fasaha da Ƙere-Ƙere ta Umaru Ali Shinkafi, Sakkwato da ƙarfe 10:30 na safe: Uban Taro Mai Martaba Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’adu Abubakar III.
TAFIYA DA WAIWAYA TANA MAGANIN
MANTUWA
(Duba Cikin Gurabun Zangunan Gwagwarmayar Ƙasar Hausa, Harshen Hausa da Hausawa Jiya da Yau)
Daga
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo
24th
ga Ogusta, 2023
Tsakure
Tunanin
wannan bincike ƙyallaro
matsayin Hausa da Hausawa da harshensu da al’adunsu na jiya a faifan karatun
yau. Binciken ya waiwayi Hausawa
mataki uku: Ya dube su tun shekaran jiya ban da jiya. Ya sake leƙo su shekaran-jiya, ya waiwayi inda aka
kwana jiya, ya yanke hukunci a yau. An
tsurawa matsayin harshen Hausa ido a cikin harsunan duniya da Afirka da Afirka
ta Yamma da kuma gida Nijeriya, An ɗan ƙyallaro giɓin
adadin matsayin da aka yi wa Hausa na zama harshe na (11) mai adadi masu magana
da shi (150,000,000) a shekarar 2020/21. Da aka sake bita aka yi kirdadon yawan masu magana da
harshen za su tunkari (250,000,000) zuwa 300,000,000). An gano a halin da ake
ciki harshen Hausa na da dukkanin abubuwan da harshe ke buƙata ya zama harshen ƙasa a yi karatun ilmi da
shi. Binciken ya gano lallai mulkin mallaka bai yi tasiri ga zukatan Hausawa yadda ya yi tasiri a
zukatan wasu al’ummomi da aka yi wa shi. Keɓe
Ranar Hausa Ta Duniya wani ƙalubale
ne ga Nijeriya ta gaggauta ɗabbaka
dokar amfani da harsunan gado a makarantu. Lokaci ya yi na hukuma ta sa
hannunta ga bukukuwan “Ranar Hausa Ta Duniya” domin fito da dokokin da za a
tallafa wa harshen Hausa ya kai na hannu
gida.
Gabatarwa
Ƙarni da muke ciki ya saɓa wa dukkanin ƙarnukan da suka gabace mu. Abin lura a nan shi ne, ƙarni ne da addinai suka bunƙasa aka durƙusar da maguzanci. Na biyu, ƙarni ne da ilmukan addinai da sana’a suka wanzu aka yi wa jahilci kushewa. Haka kuma wayewar kai ya samu aka gargaɗi mulkin mallaka. Yancin da ya biyo bayan waywar kai ya harantar da bauta da yaƙe-yaƙe da makaftaccen mulki da ƙazantattun hukunce-hukunce. Da haka jama’a suka samu tazarar zirga-zirga, da ƙaurace-ƙaurace, da cuɗanya da wasu al’ummomi, da kaka gida a wurare daban-daban duniya ta yi kusan zama abu ɗaya. Cikin haka aka samu kutsawar taɓarɓarewar al’adun mutane na gargajiya, da masassara tare da mutuwar wasu al’adu, da salwantar harsunan asali, da ɓatan dabon tarihi da al’adunmu nagartattu. Wannan shi ne dalilin yi wa bincikenmu take: Tafiya da Waiwaya Tuna Maganin mantuwa. To bisimillah! An haɗa malamai faɗa.
Shimfiɗa
Duniyar jiya ɗauke take, kowa kansa kawai ya sani da harshensa da
masu magana da shi, da nahiyar da suka mamaye. Kimanin farfajiyar ƙasar da al’ummomin duniya suka mamaye an kasa su kashi
bakwai (7) wanda a Ingilishi ake kira “Continent” na fassara shi da “Nahiya”.
Ga yadda tsarinsu yake a tartibin girmansu daga babba zuwa ƙarami:
Yawan Ƙasashensu:
1.
Asia Asiya 48
2.
Afirca Afirka 54
3.
North America Amerika-ta-Arewa 23
4.
South America Amerika-ta-kudu 12
5.
Antaractica Antatika/Tsibirin
Ƙanƙara (Kango)
6.
Europe Turai 44
7.
Australia Astraliya 14
Wayewar kai na duniya da fahimtar juna ya sa aka fasa duniya
zuwa farjajiya bakwai (7). Daga nan mazaunan nahiyoyin suka karkasa kansu zuwa
farfajiyoyin da suka mamaye aka samu ƙasashe ɗari da tis’in da
biyar (195) a duniyarmu ta yau. A cikin wannan farfajiyar nahiyar Afirka tana
da ƙasashe hamsin da huɗu (54). Ƙasar Hausa inda
Bahaushe yake tana nahiyar Afirka, ko a nahiyar Afirka tana sansanin duniya baƙaƙen fata da aka yi wa ɓangaren sunan West-Africa Afirka ta Yamma.
1.
Benin
2.
Burkina Fasso
3.
Cape Verde
4.
Cote D’Ivoire
5.
Gambia
6.
Ghana
7.
Guniea
8.
Guniea-Bissan
9.
Ivory Coast
10.
Liberia
11.
Mali
12.
Manritania
13.
Niger
14.
Nigeria
15.
Senegal
16.
Sierra Leone
17. Togo
Hausawa da harshen Hausa da al’adun Hausawa da sana’o’insu babu ƙasa daga cikin waɗannan ƙasashe da ba su ratsa ba. Cikin ƙwazon Bahaushe da cigaban duniya sai harshen Hausa ya kutsa nahiyoyi daban-daban na duniya har ya kai ga ficen da yake da shi a yau (2023). Wannan ‘yar shimfiɗar ba ta tsayi da ƙafafunta sai an san wane ne Bahaushe?
Wane ne
Bahaushe?
Taƙaddamar tantance wane ne Bahaushe tana buƙatar a nazarci kalmar “Bahaushe” bisa ga tunanin masu
harshen. A ginin kalmomin Bahaushe yakan dasa harafin “b” da wasalin “a” ga
sunan ƙabila ko harshen, mutane ba tare da taɓin ainihin sunan
da suke yi wa harshe ko ƙabilarsu ba. A wasu lokuta hausantaccen sunan da ya ƙaga wa al’ummar da yake tare da ita, yakan dasa wannan
harafin “b” da wasalin “a” watau “ba” a gaɓar farko na sunan. Dubi sunayen ƙabilar Yoruba da Fulani da Gurma da Arab da India da
za a ga ya ce: Bayarbe, Bafulatani, Bagurme, Balarabe, Ba’indiye, haka zuwa.
Asalin sunan Bahaushe shi ne “Hausa” shi ne sunan harshensa, sunan ƙasarsa, da sunan al’adunsa, da sunansa shi kansa da
yake yi wa kansa da wanda wasu ƙabilu ke yi masa.
Cikin wannan rugumutsin nahawu wasu ke ganin cewa,
asalin kalmar Hausa daga “Baushe” ne gawurtaccen mafarauci. Wurin da gizo ke saƙa shi ne, wa ya raɗa masa sunan? Shi kansa, ko wasu? Masu ra’ayin “Hau +
sa = Hausa” mai hawan sa, to gabanin ya samu san hawa, mene ne sunansa? A wata
fatawa an ce, daga “Habasha” ne aka samu Hausawa. To a can habasha ba sunan
harshen su ba ne wato ba “Habasha” suke kiran harshensu ba. Haka kuma, ba
“Habasha” suke kiran ƙasarsu ba, Larabawa ke kiranta haka. Zancen Abu Yazid
As-Sulɗani “Bayajida”
ya yi kama da tatsuniya domin ya taras da ƙasa, da
garuruwa, da sarauta, da harshe. Me ya ƙago a ciki? Har
yanzu ba a ambace shi ba. Yin wannan dogon tunani ya ba ni damar dafa kafaɗar masana irin
su Adamu (1975) na ce, a tunanina Bahaushe shi ne, wanda:
1.
Ya yarda Bahaushe ne
da kansa.
2.
Ba ya da harshen gado
sai Hausa.
3.
Da al’adun Hausawa
yake tinƙaho.
4.
Mahaifinsa da kakansa
da kakanin kaninsa Hausawa ne.
5.
Ba ya da wata ƙasa sai ƙasar Hausa.
6.
Ya kasance yana cikin
wata zuriya daga cikin zuriyar Hausawa.
7.
A same shi da karin
harshen zuriyarsu na Hausawa.
8.
Taƙadarun santukan Hausa su gogu a lafazinsa.
9.
Samun tsagar gado
walkam ne shiga rijiya da dawo.
10.
Matsakaicin zati da
gajeruwar suma/gashi kai cikon sunna ne makaho da waiwaya.
11.
Samunsa baƙar fata ya kasance nashin ƙasa babu kure.
A da, gabanin duniya ta kasance gida ɗaya lokacin da
mutanen nahiyoyi da farfajiya ba su fara cuɗanya wajen kadadarsu ba, da waɗannan ma’auni
goma sha ɗaya (11) ake gane Bahaushe da zuriyar da ya fito ciki.
Lura da waɗannan turaku ya ba ni damar cewa:
Bahaushe shi ne,
wanda ya tsira a ƙasar Hausa, ya yarda da zamansa Bahaushe, kuma ba ya da harshe sai
harshen Hausa. A taliyon salsalarsa, duk da harshen Hausa da al’adun Hausawa
ake bugun gaba. Samunsa cikin gurbi daga gurabun zuriyar Hausawa tilas ne,
kamar yadda harufan Hausa na asali ba sa tangarɗa a lafazinsa. Bayyanar tsagar gargajiya (ta fuska) da ƙirar zati ta kakani wata madogara
ce babba.
Bahaushe A
Shekaran-jiya-Ban-da-Jiya
Tunani na a nan kallon Bahaushe tun ana zaman nahiyoyi
gabanin a ɓaɓɓarke zuwa farfajiya. A wannan zamanin zuriyar Hausawa
wuri ɗaya suke cikin
nahiyoyi/farfajyar ƙasar da suka mamaye. A shekaran-jiya-ban-da-jiya,
Hausawa na rarrabe junansu ta fuskar:
1.
Harshensu
2.
Zuriyarsu
3.
Al’adunsu
4.
Kirar zatinsu
5.
Ɗabi’unsu.
Za a same shi da tantagaryar harshensa na gado karin
harshen yankinsu da Hausar rukunin da ya kasance lafiya lau. Bahaushen lafazi
ya zauna a bakinsa abin so ne a ji yana furta kalmomin Hausa sambai a tabbata:
i)
Ba a son a ji sauya
lamirin suna: maimakon, “Allah Ya ce”, ka da ya ce: “Ta ce”
ii)
Kalmomi masu ƙugiya su kuɓuta: ɓarawa ba barawo ba, ƙya ba kaya ba.
iii)
Tagwayen sautuka su
samu: tsawa ba sawa ba, gyaɗa ba jada ba.
iv)
Tagwayen wasula a ji
su ragwai: ƙaura ba kawara ba, guiwa ba giwa ba.
v)
Ɗauri ya fita sosai: maiwa ba newa ba, Daura ba Dora
ba.
Zuriyar Bahaushen shekaran-jiya-ban-da-jiya ita ce
fitacciyar zuriya da dangogin Hausawa suka fito a ciki sun haɗa da:
Kabawa
Kanawa
Zamfarawa
Gobirawa
Arawa
Gubawa
Gimbanawa
Katsinawa
Zagezagi
Maraɗawa
Kutumbawa
Al’adunsu sanannu ne na matakan rayuwa da suka haɗa da bukukuwan
aure, haihuwa da mutuwa. Bukukuwan kafa gari, kafa kasuwa, da sauran daji. Daga
cikinsu akwai bukukuwan sana’ar noma da su da farauta da gayya da sarakkuci da
tagunanci, da cimaro da dai sauransu. Bahaushe bai gaji rawan mata da maza wuri
ɗaya ba ko cikin
rawar bankaura. A Hausance ba a san dottijo da yin rawa ko ya yi kirari ko da a
fagen yaƙi ne, sai dai jiki ya ɗau mazari yara su yi hitara. Bukukuwan aza gemu da
kamun gwauro, da kai bante wasu al’adun tabbatar da ɗiyauci ne da
tsare girma da kamun kai da tabbatar da kamalar mutunci da riƙon amana. Wanda ya aza gemu ya wuce ƙarya, ba ya aikata assha, ba ya shekara gwauro, ya’yan
Hausawa mata da budurcinsu ake kai su ɗakunan mazansu.
Ɗabi’unsu ɗabi’un gado ne da aka taras kaka da kakani. Waɗannan ɗabi’u su ne:
1.
Gabaci
2.
Gaskiya
3.
Nagarta
4.
Biyayya
5.
Kunya
Gabaci
A jiya Hausawa da girmama gabaci aka san su. Babu wani
rukuni na Hausawa da ba shi da gabaci. Cikin yara akwai sarautar Maiyara. Cikin
matasa akwai Maisamari. A wajen budare akwai Maduga. Matan aure na da uwar
Adashi, suna da Magajiya da Uwar Ɗaki. Fatake na
da Madugu, tsofaffi na da Jagaba, cikin ƙattan gari ake
samun Kartagi. Babu sana’a daga cikin sana’o’in Bahaushe da ba ta da sarki. A
da ƙasar Hausa cikakken tsaro gare ta duk abin da ya faru
akwai wanda ake tunkara a gano dalili: A yanayi da tsarin iko a ƙasar Hausa ba a san tawaye da zanga-zanga, da bore, da
tashintashina, da juyin mulki ba. Komai tsananin adawar sarauta da iko da an
ayyana shugaba Bahaushe ya gaji miƙa wuya da jiran
nasa lokaci. Ya gaji bar wa Allah al’amari da miƙa wuya ga
hukuncinSa. Dr. Ibrahim Narambaɗa ya yanke hukuncin haka a faɗarsa:
Jagora: Sarauta ban da nufin Allah ce
Yara: Da ɗibat ta akan yi da ƙarfi,
: Waɗanga da nag gaza ganewa
: Da sun ga ana haka
nan da sun yi
Jagora: Wane a dangana tun ga uwaye
Yara: Ba duka ɗan sarki ba ka samun sarki
Gindi: Gogarman Tudu jikan sanda
: Maza su ji tsoron
ɗan mai Hausa.
Magabata sun ce, wanda duk ya bi ana bin sa, wanda ya ƙi kuwa ya san cewa, ba ka tuɓe sarki ka yi
sarki.
Gaskiya
Duk wani abu da yake daidai yadda ya kamata ya kasance
ya kasance, a wajen Bahaushe sunansa “gaskiya” don haka yake da karin magana
“gaskiya sunanta gaskiya”. Duk wani abu da ba daidai ba, a wajen Bahaushe
sunansa “rashin gaskiya” da wuya kalmar ƙarya ta yi jewaɗi cikin adabinsa
domin bai yarda da ita ba, bai kuma yarda ana yin ta ba. Hatta da addini a
tantagaryar Hausa sunansa “Ban Gaskiya”. Ai don haka yake cewa: “Tsafi gaskiyar
mai shi”. Marashi gaskiya ba a abota da shi, ba a ba shi aure, ba a doguwar hulɗa da shi, balle
ya shugabanci wani muhimmin al’amari na al’umma. Dalilin Dr. Narambaɗa ke nan na yi
wa Sarkin Gobir Amadu suna da gaskiya:
Jagora: Na hore ki gaksiya bari tsoron ƙarya
Yara: Mai ƙarya munahuki Allah su Yaƙ ƙi,
Jagora: Har yau ba mu ga in da anka yi mai ƙarya ba.
Yara: Amma ita gaskiya
Gindi: Gari da mutane tay yi
: Gwarzon shamaki na
Malam toron giwa
: Baban Dodo ba a tamma da batun banza.
Nagarta
Shekaran-jiya-ban-da-jiya babu Bahaushen da ba manomi
ba, babu wanda ba mafarauci ba. Da sarki da talaka da mai akwai da moro kowa
noma ne sana’arsa ta farko. Babu zauna gari banza, da ɗan dandi, bale
sata da fashi su samu mai belinsu. Ayyukan ƙwazo da nagarta
sarautu gare su na musamman domin fitar da maza tsakanin mazaje. Muna da
sarautu irin su:
Zarummai: Babbar
sarauta ce ta gari
Barade: babbar
sarauta ce ta gari da sana’a
Barde: Babbar sarauta
ce ta sana’a da ƙwadago
Sadauki: Sarauta ce ta jajirtacce namijin tsayayye ga
hidimomi
Sarautun nagarta akan same su a fagen noma, farauta,
fatauci, dambe, kokuwa, da makamantansu. Dubi yadda Amali Subugu ya koɗa Zarummai
Aikau:
Jagora: Yana yi ma aiki kamag gudun ƙato
: In ya hangi gobara
Yara: Muddin yas san gidansu tak kama
Jagora: Ban san mai tare shi ba
Yara: Rannan ko galɓi an kawa hanya
: Sai dai yai ƙire biyu
Gindi: Ya riƙa aiki da gaskiyar Allah
: Bai saba ba da zama
: Aikan jikan Tayawa ɗan Mamman
: Kunkelin fashin ƙasa.
Ire-iren waɗannan ayyuka suka hana samun ɓata gari da
zauna gari banza a farfajiyar ƙasar Hausa. Wanda duk ya kasa kasancewa nagartacce ba
ya da wurin shaƙatawa a ƙasar Hausa. Me
ya haifar da ‘yan daba da ‘yan satar amarya da ‘yan damfara da caca da ‘yan
kore da ‘yan a-ja-mu-a-kai-mu, a wannan ƙarni? Rashin
waiwaya shekaran-jiya-ban-da-jiya.
Biyayya
A wajen Bahaushe biyayya ibada ce, don haka yake da
karin maganan bin na gaba bin Allah. A al’adance gabaci ma’auni ne, don haka
yake cewa, ga na gaba ake gane zurfin ruwa. Idan gaba ta yi wa gabanta biyayya,
dole na baya gare ta su yimata biyayya domin wurin da sanuwar gaba ta sha ruwa
nan ta baya za ta tsoma bakinta. Biyayya ga Bahaushe ta soma tun tsakanin mata
da miji, mahaifa da yaransu, yara da yannensu, babba da yaro, maigida da bara,
malami da ɗalibi, uban gida da bawa, baƙo da ɗan gida, matambayi da mai amsa, mai aike da ɗan aike, mai
bayarwa da mai karɓa, mai kyauta da mai roƙo, mai tukuici
da ɗan aike, ga su
nan dai. Bahaushe ba ƙaramin bibiya yi wa ladabi da biyayya ba. Dubi yadda
Dr. Narambaɗa ya kori biri a fada saboda ƙoƙarin yin ɓatanci da rashin biyayya ga gabaci:
Jagora: Kai tashi biri tsohon maɓannaci
:
Karen ɓiki bai ɗau shawararka ba
Yara: Shi maganar giwa yake riƙe
J/Yara: Ku ce
wa biri duk dabbar da ac cikin daji
Yara: Giwa taka biya
Gindi: Ya ci maza ya kwan shi ne shire,
: Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.
Biyayya ta sa yau daulolin ƙasar Hausa sun fi ƙarni goma da
kafuwa shekara dubu (1000) amma tarihinsu bai kau ba, sarautunsu ba su salwanta
ba, gabacinsu na nan tare da su. Daular Kano ta fi shekara dubu (1000), Katsina
ma haka Zamfara haka domin Kwatarkwashi ta yi shekara (600) Anka ta yi (1000)
har yau 2023 gidajen sarautunsu ba su salwata ba, tsage-tsagen gargajiya na
fuskokin suna nan daram. Babu rubutun da zai yi ƙarni goma in ba
kan dutse aka yi shi ba.
Kunya
A tunanin Bahaushe kunya wata ƙawa ce ta mutuncin mutane a ko’ina aka rasa ta an rasa
mutunci. Manyan laifuka na kunya sun haɗa da: sata da shige da fyaɗe da kushuli da
nema da kwartanci da danke, da karya alkawali, da zamba cikin aminci, da ƙarya, da sara da mutum sama, da shaidar zur, da shigan
burtu, da sojan gona, da ƙin biyan bashi, da kasa mayar da buki, da dai
makamantansu na sa a gudu a bar gari har abada. Al’ummar da ke da irin wannan
tsari wane irin cigaba ke gagararta? Dottijon Bahaushe idan aka tambaye shi abu
ya ba da bayani, aka sake tambayarsa domin gaskatawa kuka yake yi, wai ba a ɗauke shi mutumin
kirki ba (Mungo Park da H. Birth). Akwai kunyar juna tsakanin ɗiya da mahaifa,
surukai, sarakai da talakawa, maigida da yaransa/barorinsa, mata da maza, miji
da mata, babba da yaro. A irin wannan halin yaya fitsara za ta yaɗu? Dole laifuka
da ayyukan assha su ƙaura. Zaman lafiya da lumana ya shimfiɗa wa mazauna ƙasa tabarma. Dubi yadda aka gina wa yara tawakkali da
gudun kunya a wasannin dandali yara maza:
Mai bayarwa: Kililin-Kililin!
Masu karɓi: Cilo Cilo!
Mai bayarwa: Wata rana kuɗi,
Masu karɓi: Wata rana
tsiya.
Mai bayarwa: Mai mota
Masu karɓi: Ya shiga
motatai.
Mai bayarwa: Ba’askare
Masu karɓi: Hura wuta
balbal!
Mai bayarwa: Kutumbi,
Masu karɓi: Mai babban
tako
Mai bayarwa: Da sata
Masu karɓi: Gara a
lalace.
Ai ko kallon raini aka yi wa Bahaushe za ka ji ya ce: “Kai!
Lafiya? Sata ko maita ko bashi”? A rayuwar Bahaushe ya ɗauki aikata
aikin kunya shi ne ƙarshen zubar da mutunci, shi ya sa ko fagen wasa
taurari kan yi kirari da faɗar:
Kunya muka tsoro
Mutuwa ta zama gado.
Wannan shi ne ɗan share fagen karatun ƙasar Hausa da
Bahaushe da harshensa a shekaranjiya-ban-da-jiya. Yanzu sai shiga sabon karatu.
Bahaushe A
Shekaran Jiya
A shekaran jiya abubuwa biyu suka riski Bahaushe a
cikin ƙasarsa. A tarihin ƙasar Hausa waɗannan abubuwa
sun yi tasiri sosai a rayuwar Bahaushe. Abubuwan da suka riski Bahaushe a ƙasarsa su ne:
1.
Baƙin al’ummomi
2.
Saukakkin Addinai.
Shekaran jiya ana cikin girkakkun dauloli, kasuwancin
fataucin na bunƙasa, sunan manyan birane na bunƙasa musamman: Kano da Katsina da Zariya da Gobir da
‘Yandoto suka shahara. Daga nan aka fara hulɗa da manyan dauloli maƙwabta irinsu
Daular Borno da Daular Nupe da Daular Oyo. Hulɗoɗi da yaƙe-yaƙe, da kasuwanci suka ƙara kusantar da
Daulolin ƙasar Hausa da Daular Shongai da Gahana da Agades da
Libya musamman Murzuk da Gat da Sebha ya zuwa cikin Morocco da Daular Mali da
sauransu. Wannan hulɗar ta yi naso sosai a rayuwar Hausawa
shekaran-jiya-ban-da-jiya ta rage tsawo zuwan shekaran jiya, domin:
1.
Harshen Hausa ya sadu
da wasu harsuna masu ƙarfi irinsa, sun yi naso cikinsa, shi kuwa ya yi naso
cikin wasunsu. Daga nan ne wasu kalmomin Hausawa suka fara rikiɗa, wasu suka
kumbura, wasu suka salwanta aka aro wasu suka wakilci wasu.
2.
Al’adun Hausawa na
matakan rayuwa da na siyasa da na bukukuwa suka fara rikiɗewa. Abubuwan da
suka haddasa haka su ne zumuntar auratayya, ƙaura, kakagida,
da yada zango da kiyon lafiya da tsaro da tattalin arziki.
Bayyanar saukakkin addinai wani babban juyin juya hali
ne ga tarsashin rayuwar Hausawa. Ƙasar Hausa ta
sadu da addinin Masihi ta hanyar Kano-Borno-Masar. Haka kuma, ta ɓangaren sahara
saduwarsu da Buzaye jajaye. Cikin Sarakunan Gobir (384) wasu sun wanzu a
zamanin. Haka kuma Daular Zamfara da Kabi da Katsina ba za su rasa shaƙen wasu aƙidojin addinin
Masihi ba. A cikin littafin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Sardul kalami fi maa jaraa baini wa baina Abdus salaami an hararo
maganar a riwayar tarihin Abdus Salami. Mujaddadi Danfodiyo ya ɗan ƙyallaro dasisar da suka dasa a littafansa wasiiƙatul Ikhwaani da
Nurul Albaabi. Bayyanar addinin
musulunci ya zama sha kundum. Tasirin da aka samu shi ne:
1.
An kawar da addinan
gargajiya da aƙidojinsu aka musanya da na saukakken addini
daidaitacce.
2.
Yaƙe-yaƙen jihadi da siyasarsa ya shiga cikin siyasar daulolin
ƙasar Hausa ya raunana wasu, wasu sun salwanta gaba ɗaya.
3.
Al’adun gargjaiya na
shekaran-jiya-ban-da-jiya an rusa wasu, wasu an garwaya su, wasu an salwantar
da su, wasu kuwa sun samu fasahar rubutu ta taskace su, sai suka samu ma’adana.
4.
Jaddada addini kamar
sake wa maras lafiya jini ne a ɗura mai wani sabo, babu gehen da ba a taɓa ba. In haka ne kuwa babu wata al’ada da za ta
tsira.
5.
Juyin juya halin
addini kawai ya taɓa, bai yi wa harshe da adabi garambawul ba. Haka kuma
bai ci nasarar rusa tarihin daulolin Hausa da zuriyar Hausa da farfajiyar
daulolinsu da yawansu na matsayin mutane ba.
Bahaushe
a Jiya
Bahaushe
da ƙasarsa
a jiya ina nufin bayan karɓar
iko daga Hausawa zuwa ga Fulani, daga Fulani zuwa ga Turawa, daga Turawa zuwa
ga ‘Yan ƙasa,
Ɗaulolin Hausawa na gargajiya, masu jihadi sun tarar da
Musulunci cikinsu
jaddadawa suka yi. Turawa suka
rusa jaddadawar domin ta yi taƙin
saƙa da
aƙidojin
addininsu; suka kafa mulki irin na al’adunsu da addininsu. Bayan da aka ci
nasarar koran Turawa suka dasa
dasisoshi na a bi turbarsu ko a tabbata kanu rarabe.
1.
Na farko suka cire hannun
kowane addini a tafiyar da siyasar ƙasa
da Hausawa da sauran ƙabilun
da ke ƙasarsu
aka ɗora su a kan dokokin addinin
masihu a kaikaice.
2.
Na biyu aka cire hannun kowane harshe na
gado da na addini a tafiyar da mulkin ƙasa aka ba Ingilishi dama
shi kaɗai
3.
Na uku aka rusa tsarin
karatu da ilmin da aka taras wanda harshen Hausa da Fulatanci da Larabci ke
jagoranci aka haddasa boko aka sallami
sauran ilmuka a hukumance.
4.
Aka tsattsage daulolin ƙasar Hausa wasu aka kai su
ikon wasu ƙasashe
mulkin Faransa, wasu mulkin Ingilishi, wasu aka yi musu goyo da ƙabilu daban-daban domin a
rage musu ƙwarjini
da ƙarfi.
Ingilishi ya samu tazarar bunƙasa.
Maƙasudi
A
fafitikar samawa Nijeriya ‘yancin kai ga Turawan Ingila babu wanda ya yi
gwagwarmayar da Hausawa suka
yi. Bature ba don kowace ƙabila
ya gudu ya bar Nijeriya ba face Hausawa. Babu ƙabilar da yake shakkar
barazanarta da gaba-da-gaba da ita kamar Hausawa. Babban abin da ya lura da
Bahaushe da Hausawa da daulolinsu na riƙo
damaƙui ga harshensu da addininsu da al’adunsu da
siyasarsu su suka tilasta shi salon ikon “Indirect Rule” domin ya fahinci
Bahaushe harsashe ne makarinka a kwanta, amma ba gaba da gaba ba. Daga cikin
abubuwan da
ya hanga akwai:
1.
Yana da tarihin daulolin ƙasar Hausa sun yi yaƙe-yaƙen cikin gida tsakaninsu
amma babu wadda ta rushe, babu wadda ta karaye, babu wadda ta miƙa wuya ga wata ko da na
gurgusa in zanna ne. don haka mulkin ci-da-ƙarfi
irin na mulkin mallaka ba ya razana su bale ya sake musu shawara.
2.
Turawa sun tarar da Fulani
sun jagoranci jihadin jadda addini a ƙasar
Hausa, an ƙare kare jini biri jini Hausawa
sun ƙi su
ba da kai bori ya hau a siyasance domin babu daularsu da aka sake wa suna bale
gidan sarauta. Wannan jajircewa ta Bahaushe, dole Turawa suka hau fatawar karin
maganan yaya za ni yi da abin da ya gagari wuta inji kishiyar ƙonanniya?
3.
Bature ya lura da cewa,
Bahaushe taubashin mutuwa ne abin kunyarsa ya gan ta ya ruga. Ya lura da
Hausawa aka ƙwato wa Ghana ‘yanci da su
Asante suka yi amfani aka yaƙi
Turawa. Su ke gaba a yaƙar
Turawan Faransa a jamhuriyar Nijar. Da su aka yi artabun saturu 1906, aka kashe
musu mutum dubu goma (10,000). Artabun da aka
yi a Hadeja shahada suka ɗauke
shi. Don haka
a duk wurin da Hausawa ake da rinjaye Bature na tsoron
shimfiɗa ikonsa na yaudara a nan.
4.
Hausawa na da tsarin yaƙi daban-daban. Akwai na
kwanton ɓaura, akwai na sari-ka-noƙe, akwai na shigan burtu,
akwai na amazaya, akwai na ƙunar
baƙin
wake, akwai na komi taka zama ta zama, akwai na ga wuta ga masara, ga su nan
dai. Ƙasashe
da ƙabilu
da daulolin da Bature ya ci da yaƙi ba su da waɗannan
dabarun. Da ya yi yaƙin
Maji-Maji da Mawo-Mawo a Tanganyika sai da ya zo Satiru (1906) Ya tarar da shan ruwan Rijiyar Satiru na maganin bindiga da
Salon “Sakatari”.
5.
Babban abin da ya tayar wa
Bature da hankali ga Bahaushe shi ne, duk tsananin ikon da ya shimfiɗa
ƙasar Hausa ba ya da Bahaushe
ɗan
leƙen
asiri, ba ya da kuku. Hausawa sun ƙi
yarda da Bature na yi masa leƙen
asirin daulolinsu sai dai ya yi amfani da waɗanda
suka ji Hausa, amma ba Hausawa ba. Haka kuma Bahaushe ya ƙi ba da kai bori ya hau ya
kasance matar Bature mai tuƙa
masa tuwo har mulkinsa ya ƙare,
Ashe ba don Hausawa ba,
da Ingila ta daɗe da gamawa da
Nijeriya.
6.
Bature ya kasa cusa
soyayyarsa a zukatan Hausawa tsawon ikon da ya shimfiɗa
a ƙasar
Hausa. Ya lura sosai cikin ƙabilun
duniyar baƙar
fata da ya mallaka Bahaushe ne
kaɗai da ya ƙi ya zama Bature a ɗabi’ance.
Ya karanci Bahaushe sosai cewa:
a)
Bahaushe bai sa kuncen
Bature ko ya cire kaya ya ba Bahaushe, Bahaushe bai yarda da taba-jikin gajeren
wando ba, bale ɗamarar Yahudu.
b)
Bahaushe ya ƙi ya bar gashi/suma a kai
irin yadda Bature ke yi.
c)
Bahaushe ya ƙi yarda da fitsari da tsaye ko da Bamaguje ne
d)
Har Bature ya gama wayonsa
Bahaushe bai yarda da cin abinci da cokali/ƙoshiya (in ba kuturu ba) bale ci
da hagu.
e)
Ya kasa ara wa Bahaushe
al’adarsa ta gaisuwar tsaitsaye ga gabaci, da ƙin cire takalmi, da tafiyar
banga-banga tare da jagora.
f)
Yau fiye da shekara ɗari
(100) ya kasa
cin nasarar gaisuwa ƙato
da ƙatanya
ta haɗa tafin hannu
g)
Saka hular
baba-ban-gan-ka-ba (ƙisalla)
da sa kayan maza ga mata ya kasa samun maraba ga Hausawa a zamanin ikon Bature.
Hausawa
na daga cikin ƙabilun
baƙar
fata da suka ƙi
yarda Turawa su wulaƙanta
su. Hausawa sun ƙi
yarda da Bature a raye ko mace.
Bahaushe ko ya karɓi
addinin Turawan Mulkin Mallaka ba ya sauya
sunansa zuwa ire-ien sunayensu. A ƙasar
Hausa kawai aka ƙi
a girmama matattun sojojin Turawan Mulkin Mallaka. Duba zuwa ga gawar Alavanta
a garin Maikwari ta ƙaramar
Hukumar Suru, da kaftin Kyias a garin Sawwa (1903), da Cleparton a garin
Jangebe (ta gangaren kasuwar ganye/kayan Gwari a fadamar mazaunin din-din-din
na jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sokoto) da Baturen da Mamman Eha ya kashe a garin Kuryar Madaro a jihar
Zamfara.
Harshen
Hausa a Faifan Hoton Harsunan Duniya a Yau
Fayyace
adadin harsunan duniya da masu magana da su mawuyacin abu ne a duniyar (2023).
Dalili na farko shi ne, a kowace sa’a mutuwa ake yi, haihuwa ake yi. Haka kuma
su ma harsunan duniya wasu na masassara, wasu na suma, wasu na mutuwa, amma ba
a samun masu tsira. Bisa ga kurdadon
shekarar 2023 duniyarmu tana da kimanin mutane biliyan takwas da ɗagwari
(8,000,000.00) a kan wannan
adadin mutane duniya muna da:
1.
Harsunan Duniya (7,500+)
2.
Harsunan Afirka (2000-3000)
3.
Harsunan Afirka ta Yamma (1000+)
4.
Harsunan Nijeriya (525+)
5.
Jiha mafi harsuna na Nijeriya,
Bauchi (60+)
A
Nijeriya jihohin Arewacin
Nijeriya ke da cunkoson Hausawa duk da haka jahar Bauchi da ta fi kowace jaha
harsuna a Nijeriya an ce manyan harsunanta biyu ne. Fulfulde da Hausa. Don haka
babu saɓani ga kasancewar harshen
Hausa na ɗaya cikin harsunan
Nijeriya (525). A rahoton ƙididdigar
adadin yawan masu magana da harsuna a duniya a shekarar 2020/21 an ayyana Hausa
a matsayin gurbi na (11) daga cikin harsunan duniya (7,500) a ƙididdigar an bayyana Hausa na
da masu magana da ita (‘yan asali?) su miliyan ɗari
da hamsin (150,000,000). Ɗan
giɓin da na hanga a ƙididdigar (in har ta
inganta) shi ne:
i.An
mayar da hankali a Nijeriya da Nijar da Ghana kawai. Akwai Hausawa zaunannun ƙasashen duniya fiye da (24)
na tsawon karnuka ba a saka su ba. A sake bita a ga waɗannan
ƙasashe:
ii.Saudi
Arabi akwai Hausawa fiye da shekara (700+)
iii.Sudan
tun 1980 BBC ta ruwaito akwai mutane (3,000,000)
‘yan Arewacin Nijeriya mafi yawansu Hausawa ne.
iv.A
Togo 18/8/2023, Hausawan da ke ciki sun ce sun yi shekara 500 a ciki
v.Eriteria
akwai Hausawa tun ƙarni
na 16th (Shekara 600)
vi.Hausawanda
ke ƙasashen
Turai adadin bai sa da su ba,
vii.A
wasu ɓangarori na Nijeriya ba a
kamo su ba, kamar Lagos Hausawa na ciki tun (1800), akwai adadin Hausawa 1,900
a Jos kimanin shekara (100) akwai Hausawa (900+) ciki. A Ilorin da Oyo akwai
Hausawan da suka Yarbance tun ƙarni
na (19th) har yanzu 2023 da Hausa suke amfani
viii.Harsunan
da Hausa ta cinye a Nijeriya suka mutu ba a saka su a adadin ba.
ix.Daulolin
da ba na Hausa ba, da
ke magana da Hausa a matsayiun harshen mu’amala (Harshe na biyu) irin su: Borno, Nupe,
Damagaran, Yawuri, da Agades ba sa ciki.
x.A ɗan
tunanina idan aka sake bitar adadin za a ga masu magana da harshen Hausa a
duniyar 2023 za su tunkari milinyan ɗari
biyu da hamsin zuwa ɗari
uku: (250,000,000-300,000,000) wanda zai ɗaga
ta zuwa na 8 ko 7 a duniya.
Harshen
Hausa a yau Lahadi 27/8/2023
Harshen
Hausa a daidai watan Ogusta, 28/2023 yana bisa wani babban matsayi da ba ya buƙatar ba ni sani a cikin
harsunan duniya. Yana da darajoji da kowane harshe ke nema ya samu shiga sahun
gawurtattun harsuna. Ga su kamar haka:
1.
Harshen Hausa yana da masu
magana da shi kusan mutum miliyan ɗari
uku (300,000,000) daga cikin mutane biliyan takwas na duniya (8,000,000,000).
2.
Harshen Hausa yana da salon
rubutu guda uku
a)
Rubutun gargajiya (tahi)
b)
Rubutun Ajami
c)
Rubutun Boko
3.
Harshen Hausa ya shiga
ilmuka biyu na addini da na boko akwai Injila na Hausa akwai Ƙur’ani na Hausa
4.
Harshen Hausa a fannin Boko
kowane mataki akwai shi
5.
Harshen Hausa yana da
kafafen yaɗa labarai na cikin
gida da waje fitattu a duniya
6.
Harshen Hausa na da jaridu
da mujallu a cikin gida da waje
7.
Harshen Hausa ya shiga
duniyar intanet da yanar Gizo ƙololuwar
cigaban ƙarninmu.
8.
Harshen Hausa ya samu karɓuwa
a jami’o’in cikin gida da wajen Nijeriya musamman US, UK, Germany, China, Japan
d.s.
Yanzu
hukumar Nijeriya ta yi na’am da fara koyar da ilmi cikin harsunan gida, Hausa
ita ce kan gaba. JIhar Bauchi ta fitar da dokar haka 24/08/2023. Madalla!
Sakamakon
Bincike:
Ƙoƙarin Hausawa na rayar da
“Ranar Hausa Ta Duniya” ba ƙaramin
ƙwazo
ba ne ga rayar da Harshen Hausa. Abin ban sha’awa ne a ce ƙasashen
duniya sun karɓi wannan kira sosai
tare da fito da hanyoyin inganta Hausa da sada zumunta da shirya fuskantar duk
wani ƙalubale.
A ɗan binciken da wannan
takarda ta yi na hango cewa:
Bayar da addadin alƙalaman harsunan duniya da ake yi cikin intanet da Google akwai ‘yar matsala, akwai alamun farfagandar ƙabilanci da kushe wasu harsunan da ake adawa da su ta fuskar siyasa ko aƙida ko addini. Idan za a cire son rai Hausa za ta cira sosai a kan adadin da aka ba ta na 11. Haƙiƙa dole sai an gaggauta koyar da ilmin boko gaba ɗaya cikin harsunanmu na gado, in ana son su rayu ka da ingilishi da faransanci da Larabci su cinye su. Babu makawa ga Nijeriya face tabbatar da ilmukan boko cikin Hausa da Yoruba da Igbo. Na gano cewa daga cikin al’ummomin da Bature ya yi wa juyin mulki Hausawa kaɗai suka gagare shi murƙushewa har yanzu cikin yaƙi da su yake.
Naɗewa:
Hausawa
da harshensu da al’adunsu guguwar juyin juya hali uku suka shiga. Bayan sun
tashi da halayyarsu tsintsa son kowa ƙin
wanda ya rasa wanda na kira da shekaranjiya-ban-da-jiya. Fice da keren manyan
biranensu ya haddasa kwararar baƙi
cikin daulolin su, harsuna da al’adu suka fara taho-mu-gama. Gaguwar jihadin ƙarmina 18th da na
19th sun yi kakkaɓar
gara ga al’adun da suka yi kanta, wata sabuwar rayuwa ta bayyana. Kutsen da
Turawan mulkin mallaka suka yi ya haddasa cikas gaba ɗaya
ga daulolin da rayuwar mazauna ciki. Samun ‘yancin kai wani koma bayan cigaban
mai ginan rijiya ne ga al’ada da siyasa da aƙidun Hausawa Duk da haka
jajircewar Hausawa ta hana kwalliya ta biya kudin Sabulu. Hausawa da daulolinta
da ba su yi ɓatan dabo ba, bale
kirarin matsoraci suna nan daram! Mannanu ƙuda ya faɗa
ƙwaryar alewa. Wanda duk aka
haramta wa amfani da harshensa na gado an bautar da shi kuma an yi masa cutar
da ba ta da
magani face mayar masa da harshensa ya jagoranci rayuwarsa.
Manazarta
Abdulƙadir, M. (2000) “Popular Culture in Advertising
Nigerian Hausa Radio” in Fardon and G. Furniss eds.
African Broadcast Cultures: Radio in Transition. Westport, C.T: Praeger pp.
128-12.
Abraham, R.C. (1962) Dictionary of Hausa Language.
London:Hodder and Stonghton.
Abubakar, A.T. (2011) “Media Consumption and Contestations Northern Nigeria’s Engagement with BBC World
Service” PhD Thesis, London: University of Westminster.
Adamu, M. (1969). “Yawuri in the 19th Century”,
M.A History, Zaria: Ahmadu Bello University.
Adamu, M. (1982). “The
Hausa and the Other Peoples of Northern
Nigeria 1200-1600” in
Okita S.L.O. (ed) Studies in Nigerian Culture Vol. 2. No.1. Zaria: Ahmadu Bello
University Press.
Adamu M. (2010). “The
Major Landmarks in the History of Hausaland”.
The Eleventh Inaugural Lecture, Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.
Adamu, M. U.
(2011). Sabon Tarihin Asalin Hausawa. Kaduna: Espee Printing and Advertising, Kaduna.
Adamu, M. T.
(1997). Asalin Hausawa da Harshensu. Kano: Ɗansarkin Kura Publishers.
Adamu,
M. (1978) Hausa Factor in West African History, Zaria: Ahmadu Bello University
Press.
Adamu,
M. (1979) A Thousand Years of Hausaland
Participation in the Trans-Saharan Trade, 9th to
19th century A.D. in Studies in the History of Sokoto
Caliphate, Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Adamu, Y.M. (2002)
“Print and Broadcast Media in NorthernmNigeria”. http://
www.kanoline.com/dowinload/media-in-north-nigeria.
Adeyanju, A.M. and
Okwarl, J.Z. (2000) African Media Development Initiative: Nigeria Research Findings and
Conclusion. London: BBC World
Service Trust.
Ahmed, A. (1989) “Nazari
a kan Muhimmancin Shago wajen Bunƙasa Wasan Dambe a Arewacin Nijeriya”. Kundin BA,
Sokoto: Jami’ar Sokoto.
Ahmed, U. & Daura,
B. (1970) An Introduction to Classical Hausa and the Major Dialects. Zaria: Northern Nigerian Publication Company.
Allen, J. (2003) “The
BBC News Styleguide, London: BBC Training and Development”
http/agpunjab.goy.in/pdf/bbcstyleguide.pdf.
Amfani, A.H. (2016).
Hausa as an Emerging Official Language in Nigeria: Prospects and Challenges” Paper, Zaria: Ahmadu Bello
University.
Amfani, A.H. (2011).
“Hausa da Hausawa Jiya da Yau da Gobe”, Muƙala, zaria: Ahmadu Bello
University.
Abbas, N.I. (2012)
“Nahawun Sunayen Hausawa”, Kundin MA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bargery, G.P.
(1934) A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary. London: Oxford Univesity BBC World Service History.
http://wikipedia.org/wiki/ BBCworldservice.
Bello, A. (1982) The
Dialects of Hausa. Enugu: Foruth Dimension Company Ltd.
Briggs, A. (1985) A
History of Boradcasting in the United Kingdom, Volume II: The Golden Age of Wireless. Oxford: Oxford
University Press.
Birnin Tudu, S. (2002).
“Jigo da Salon Rubutattun Waƙoƙin Furu’a na Ƙarni na Ashirin”, Kundin PhD, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunza, A.M. (2019).
“Hausa da Hausawa a Duniyar Ƙarni na Ashirin da Ɗaya”. Muƙala, Sokoto: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Bunza, A.M. (2018).
“Karatun Hausa a Farfajiyar Karatun Boko” cikin Wamba et.al. (Editors) Topicla Issues in Language Studies,
Kwantagora: Amaka Printing Press.
Bunza,
A.M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: TIWAL Publishers.
Bunza, A.M. (2009) Narambaɗa. Lagos: IBRASH Islamic
Publication Centre, Surulere.
Bunza, A.M. (2013) In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka:
Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo. Cairo: Elkudus Printing House.
Bunza, A.M. (2021) “Ba a Wane Bakin Banza: Gurbin Daular Gobir da
Gobirawa a Farfajiya rDaular Sudaniyya”, cikin Transformation in Gobir
Kingdom Past and Present (ed).
Bunza, A. M. (2022) Wane ne Bahaushe?
Cikin Fatima Lami Abubakar Journal of Arts and Humanitis, Vol. 1. No. 1. Minna:
Fiti Lami Abubakar Institution for Legal and Administrative studies.
Daniya, U.A. (2013) “Caliph Abdurrahman and the Military Campaigs
in the Metropolitan Region of the Sokoto Caliphate, 1891-1902”, in Arewa Hause journal, vol.2,
December, 2013
Fagge, U.U.
(2001). Rabe-Raben Karin Harshe na Fannu, Kano: Bayero University Press.
Garba, S.A. (2018)
“Language Use in Hausa Radio: The Case Study of Programs of Some International Hausa Radio Stations”, PhD
Dissertation, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Garba, S.A. (2012).
“Hausa a Gidan Rediyon BBC”, Kundin MA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Gatawa,
M.M. (2013) “Hausa Migrants and the
Making of Diaspora, Community in Lagos,
1840-2008”, in Arewa House
Journal, vol. 2, December, 2013.
Gumel, B. (2007) “BBC
Hausa Service celebrates 50th Anniversary” http//www.gamji.com/article6000NEWS6865.htm.
Ibrahim, S. (1994) “BBC
and the Hausa: Attempting to Influence” M.A. Thesis.
Jaja, M. (2004). “Hausa
da Hausawa a Wajen Ƙasar Hausa”. Kundin MA, Sakkwato: Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo.
Jinju, M.H. (1985).
“Asalin Hausawa da Hashensu”. Muƙala, Kano:
Jami’ar Bayero.
Kantar, Media
(2010) BBC world Service Reviews Qualitative
Research on the BBC
Hausa Service. Chariotta Clifford:
Kantar Media.
Khalid, S. (2008). Jega:
A Social, Economic and Political History,
Ibadan: Craft Karaft Books Ltd.
Khalil,
N.W. (2010) “Encoded Ajami: Talisman and
the preservation
of
Arabic and Ajami Manuscrips: Resourse for Development of New Knowledge in
Nigeria” Proceedings of the National
Conference on Exploring Nigeria as Arabic/Ajami Manuscripts, Kaduna: Arewa
House, Ahmadu Bello University.
Labaran, B. (2011) Why
we Boradcast in Hausa BBC: Daily Trust
Newspaper of July, 14, 2011.
Last, M. (1969). Sokoto
Caliphate, Ibadan: Ibadan University Press.
Lami, B.S. (1982) “Karim
Magana”. Kundin BA, Zaria: Jami’ar
Ahmadu Bello.
Liman, M. (2013) Editor
of Hausa BBC Unvailed the “Responsive
Design” Upgrade of the BBC Hausa Website at
Nigeria con in Lagos, on Wed., September 18, 2013.
Mansell, G. (1982) Let
Truth be Told: 50 Years of BBC External
Broadcasting. London: Weiden Feld and Nicolson.
Mani, A. (1966). Zuwan
Turawa a Nijeriya ta Arewa. Zaria: Ahmadu
Bello University Press.
Magaji, A. (1986).
“Gudummuwa a Kan Ƙoƙarin da aka yi na samar
da Cikakken Tarihin Hausawa da Harshensu”. Muƙala, Kano: Jami’ar Bayero.
Mirchandami, R. & Abubakar, A.T. (2014) Britain’s
International
Broadcasting Los Angeles: Figueroa Press.
Nadama, G. (1977). “The Rise and Collpase of Zamfara”. PhD
Thesis,
Zaria: Ahmadu Bello University.
Newman, P. (1991). “Century and a Half of Hausa Studies in
Nigerian
Languages” in Studies
in Nigerian Languages, Literature and Culture, Kano: Bayero
University.
NNPC, (1970). Hausawa da maƙwabtansu na 1 da 2. Zaria: Gaskiya
Corporation.
Pawlak, N. (2002). Hausa Outside the Mother Tongue Area:
Pleateau
Variety. Dialog, Warsaw
Academic Publishing House.
Samaldone, R. (…..) War on the Savannah, The Savannah
Military
Collpase of the Sokoto Caiphate Under the Invension of the British
Bumpie 1897-1903.
Sani, M.A.Z. (2009) Siffofin Daidaitacciyar Hausa.
Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Saulawa,
A.M. (1988) “Origin of Hausa States
Revisited” paper
presented at a workshop of inter-cultural
experience, jointly organized by the fulbright Hayes group Project in Nigeria
and centre for Hausa studies, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Shehu, S. (2015) The Economy of Hausaland
from Europeans Trader’s
Account: A critical Assessment of Paul
Standinger’s Notes on Local Industries in the late 19th Century Ƙasar Hausa, in Arewa
House Journal, Vol. 3 No. 3.
Shehu, M. (2018) “Zama Lafiya ya fi zama Ɗan Sarki: Tunanin
Bahaushe a kan zaman lafiya da Sasantawa” Kundin PhD, Sakkwato:
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Smith, A. (1987). A Little More Light: Selected Historical
Writings of
Abdullahi Smith, Zaria: CHR, Gaskiya Cooperation.
Smith, A. (2006) “Radio France International Launches Hausa News
Service in Nigeria” on July 6th, 2006, 14:03utc.
Sodangi, B.A. (1979) “Narambaɗa da Waƙoƙinsa”. Kundin BA, Zaria:
Jami’ar Ahmadu Bello.
Tangaza, J. (2011) Challenges and Obstacles of Creating
Mobile
Content for Audiencies in Rural Africa: A Case Study of the BBC
Hausa Village Radio Show. Oxford:
Reuters Institutes Fellowship paper.
Tukur, M. M. (1979) “The imposition of Birtish Colonial Domination
on the Sokoto Caliphate, Borno and
Neigbouring States 1897-1914 A Re-interpretation of the Colonial Sources”, PhD. Thesis, Zaria: Ahmadu Bello
University.
Umar, H.A. (2016). “Sunayen Bahaushe a Idon Maƙwabtansa”.
Kundin MA. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Usman, Y.B. (1970). The Transformaiton of Katsina.
Zaria: Ahmadu
Bello University Press.
Walker, A. (1992) A Skyfull of Freedom: 60 Years of
the BBC World Service.
London: Boradside Books Limited.
Yabo, A. M. (2017) Historical Foundation of
Education in Nigeria Sokoto: ULYA Press.
‘Yandaki, (2012) “The Living Traditions Among the Hausas: An
Excursion into History and Anthropology” in Arewa Hausa Journal Vol.1
No.1, December, 2012.
Yunus, A. (1993) “Yanayin Yaɗuwar Hausa a Duniya”
cikin Rufa’i, A,
Yahaya, I.Y. da Bichi, A.Y. (Editoci) Nazari kan Harshe da Adabi
da Al’adun na Hausa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Zariya, A.B. (1982) “Issues in Hausa Dialectology” PhD
Thesis, Indiana: Indiana University.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.