Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
Tagwayen Baƙaƙe
53. Baƙaƙen ƙi-jima ka ji
sauƙaƙa ke nan,
Su ne muka bibiya a babi
na
ɗayan nan,
Duk furucinsu guda-guda ne
su ɗin nan,
In aka ce ‘tagwai’ baƙaƙe biyu ke nan,
Masu zuwa a tare can gun zanawa.
54. Za su taho a jere
ga wasali ƙarshe,
Gun furta su nan amonsu ya zo tarshe,
Ba wasali tsakansu sai dai daga ƙarshe,
Zanka kula da wanga tsari ko yaushe,
Dole su zo hakan gabanin furtawa.
55. Yanzu biyo ni za
ni zano siffarsu,
In muka ɗauki ‘k’ da ‘w’ mun ka
haɗa su,
‘Kw’ ke nan kamar a kalmar “kware” su,
Ke nan dai ‘k’ da ‘w’ an
manne su,
Sun zame ‘kw’ tagwan
baƙi
babu musawa.
56. Akwai wasulan da
‘kw’ ya zam bai kamawa,
Ka taɓa jin ‘kwi’ ‘kwe’ ga bakin
Hausawa?
Duba misalan da ke biye
don ganewa,
Ka ga muna da Kwaire, kwasau, kwantawa,
Lura akwai Kwari,
Kware ga kwashewa.
57. In aka ɗauki ‘g’ da ‘w’ an ka
haɗa su,
To sun komo baƙi guda ne tsarinsu,
Akwai wasullan
da ba sa taɓa bin su,
Lura da ‘g’ da ‘w’ in ka haɗe
su,
Sai a kira su ‘gw’ ga tsarin
furtawa.
58. Ga Gwafadi, Gwanda, Gwaiba da Tukwane,[1]
Ga gwanjo, agwada sa gwado duk sutura ne,
Ga Gwadabawa, Gwandu ga Gwashi
birane,
Gwaggo, gwaggiraɓe suna na mutane
ne,
Ga gwauro da gwauruwa
sai ganawa.
59. ‘S’ na zuwa ga
‘t’ su zam tare tsaye,
Sai su zamo baƙi guda ka ji tagwaye,
Gun furucinsu
‘t’ ta zo sai ‘s’ goye,
Gamuwar ‘t’ da ‘s’ wurin nan
a kiyaye,
Su muka ce wa ‘ts’ ga
furucin Hausawa.
60. ‘Ts’ na ɗaukar dukan
wasal in an jero,
Tsa, tsi, tso da tsu da tse in an tsaro,
Duba misalai a nan ƙasa an tsattsaro,
Za ka rubuta tsamiya,
tsawa, tsoro,
Tsufa, tsegumi bala’i yaka
sawa.
61. Akan ma haɗa ‘s’ da ‘h’ wajen
furta su,
Sai su haɗe su zam baƙi ɗaya duba su,
Za a haɗe su jumlatan don furta su,
Harafin ‘s’ da ‘h’ idan an gwama su,
Sun zama ‘sh’ ga Hausa gun zanawa.
62. Dukkanin wasal sukan bi masa shirye,
Sha, shi, sho, shu, da she bi su a shirye,
Duba misalansu nan ƙasa don ka kiyaye,
Shanun Sharubutu shuka
suka cinye,
Shashashan shina gani bai
korewa.
63. Haɗuwar ‘g’ da ‘y’ halas
ne ga rubutu,
Sai mu kira su ‘gy’ ga tsari na karatu,
Sa wasali gare shi
kominsa ya saitu,
In aka sa wasal garai sai ko ya
furtu,
Nan muka samu ‘gy’
tagwai mai dacewa.
64. Ka ga a ‘gy’ ‘a’ kaɗai ake iya ɗorawa,
Ba a ‘gyu’, da ‘gye’ ga
tsarin Hausawa
Ku duba misalai a yanzu domin ganewa,
Gyashin gyatuma gyaɗa na tasowa,
Gyartai shi ka ɗinka ƙorai ɗinkewa.
65. Ka ji ajin tagwan
baƙi
ga bayaninsu,
Harhaɗa sautuka ake gun
furta su,
Ka ga akwai ‘kw’ da ‘gw’ cikin tsarinsu,
Sa mana ‘ts’ da ‘sh’
da ‘gy’ ka ji cikonsu,
Ga jimillarsu su biyar gun ƙirgawa.
66. Sai dai su tagwan
baƙi
gun zanawa,
Kwai wasulan da ko kaɗan ba a sakawa,
Ka ga da ‘kw’, da ‘gw’ rinƙa kulawa,
Bisa tsarinsu in wasulla aka sawa,
Wasalin ‘a’ ka barbararsu ga zanawa.
67. Sai sauran tagwan
idan an duba su,
‘Fy’, ky, ƙw da ƙy da ‘ya ne a zubinsu
Su duka goma ne a duba jimillarsu,
Harufan ‘ts’ da ‘sh’ idan an duba su,
Ba wasalin da za su tadan furtawa.
[1]
Da “Gwafari” da “Gwanda” da “Gwaiba”
da “Tukwane” duka sunayen ƙauyuka ne da ke mabambantan ƙananan hukumomi a jahar
Kebbi a Nijeriya. Gwafari tana ƙaramar hukumar Suru-Ɗakingari. Gwanda tana
ƙaramar hukumar Maiyama. Gwaiba da Tukwane suna ƙaramar hukumar Koko-Bese.
1 Comments
What is Tagwayen babaken in English
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.