Takaitaccen Tarihin Zanna Bukar

    Zanna Bukar

    ZANNA BUKAR wadda sunansane hular zanna BUKAR ta samo asalin sunanta ZANNA BUKAR Dan siyasane a jamhuriya ta farko daga jihar borno.

    An haifi ZANNA BUKAR SOLOMON DIPCHARIMA a shekarar 1917 a kauyen dipcharima dake jihar borno, ya halacci makarantar middle ta borno, ya samu horo a matsayin malami a kwalejin horar da malamai ta katsina.

    ZANNA BUKAR ya Fara aiki a matsayin malami inda yayi aiki a makarantu daban- daban daga 1938 zuwa 1946 lokacin Daya shiga harkar siyasa.

    Ya Fara shiga jam'iyyar NCNC jam'iyyar da DR. Nnamdi azikiwe. ke jagoranta 

    Ya sauya sheka zuwa jam'iyyar NPC ta arewa  a shekarar 1954 wadda aka zabeshi a matsayin Mai wakiltan gundumar borno.

    ZANNA BUKAR yazama shugaban jam'iyyar NPC reshen lardin Borno kuma shugaban gundumar yelwa a shekarar 1956 inda aka bashi sarautar gargajiya Mai lakabin zanna.

    Ya samu kujerar Majalisar wakilai ta tarayya a Legas a shekarar 1954 sannan ya Zama sakataren Majalisa a Ma'aikatan Sufuri, yazama Ministan Kasuwanci da Masana'antu a shekarar 1957 .
    ZANNA BUKAR shine Dan jihar Borno na farko Daya Fara rike kujerar mataimakin Fira minista na farko SIR.. ABUBAKAR TAFAWA BALEWA. Kuma kanuri na farko Daya Zama Ministan Kasuwanci da Masana'antu dakuma Ministan sufuri 

    ZANNA BUKAR ya rasu a wani hatsarin Jirgin Sama a shekarar 1969.

    Daga Zauren:
    Hausawa da Harshensu

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.