Tarbiyyar Hausawa A Matsayin Ginshiƙi na Samar da Ingatacciyar Al’umma

    Published from proceedings of a Three Day 1st National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organised by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero Uniɓersity, Kano, from 14th – 16th January, 2013, Page 708 – 727

    English Rendition as, “Hausa Moral Behaviour as a Pillar in Building a Better Society”

    Dr. Bashir Aliyu Sallau
    Department of Nigerian Languages
    Umaru Musa Yar’adua Uniɓersity
    Katsina – Nigeria

    TSAKURE

    Ci gaban kowace al’umma yana tafiya ne tare da ire-iren tsare-tsare da shirye-shiryen wannan al’umma dangane da yadda take tafiyar da harkokinta waɗanda suka shafi al’adunta da aƙidunta musamman waɗanda suke da alaƙa da tarbiyya. Dukkan al’ummar da ‘ya’yanta ba su da kyakkyawar tarbiyya yana da matuƙar wuya ta zauna lafiya. Idan kuwa babu zama lafiya babu yadda za a yi wannan al’umma ta sami bunƙasar da za ta taimaka mata ta sami dauwamammen zaman lafiya da ƙaruwar arziki yadda kowa zai yalwata ya sami ci gaba. Domin ba da tawa gudummuwa wajen samar da mafita ga halin da al’ummar Hausawa suke ciki a wannan zamani, ya sa a wannan takarda za a yi bayani a kan irin kyakkyawar tarbiyyar Hausawa kafin su sami cuɗanya da wasu baƙin al’umma, waɗanda koyi da al’adunsu ne ya kai al’ummar Hausawa shiga cikin wannan mummunan hali da muke ciki a yau. Domin kuwa, matuƙar aka waiwayi kyawawan al’adun Hausawa musamman waɗanda suka shafi tarbiyya aka yi masu ‘yan gyare-gyare, za su taimaka a sami ingantaccen shugabanci ba a ƙasar Hausa ba kawai, a’a, har ma da Tarayyar Nijeriya baki ɗaya. Wannan ne zai sa Tarayyar Nijeriya da dukkan al’ummomin da suke cikinta su sami dauwamammen zaman lafiya, a kuma sami bunƙasa, matasa su sami abubuwan yi yadda arzikin ƙasa zai ƙara yalwata.

     

    1.0    Gabatarwa

     

    Hausawa na cewa, “zama lafiya ya fi zama ɗan sarki”, har abada ba za a sami zama lafiya da kwanciyar hankali ba idan babu tarbiyya mai kyau. Kyakkyawar tarbiyya ke sa a sami ingantaccen shugabanci da zaman lafiya da ƙaruwar arziki ga kowace al’umma.  Hakika, idan muka dubi wannan bayani da ya gabata muka kuma waiwayi irin zaman da Hausawa suka yi kafin shigowar wannan zamani, watau lokacin da suke yin cikakken riƙo da kyakkyawar tarbiyyarsu wadda ta yi koyi da yin biyayya ga dokokin addini, da bin gaskiya da riƙon amana, da sadar da zumunci da taimakon juna, da yin biyayya ga tsarin shugabanci irin na Hausawa, da riƙe sana’o’in gargajiya, da yin juriya da gwada jarunta, da nuna kunya da kara, da kuma kyakkyawar mu’amala a tsakaninsu, sannan kuma idan muka kwatanta shi da halin da Hausawa suke a yau, lokacin da waɗannan kyawawa al’adu suka ɓace, ma iya yanke hukunci da cewa, watsi da kyakkyawar tarbiyyar Hausawa ne ya kai mu shiga cikin wannan hali na rashin tabbas. Watau halin da ƙarami ba ya yi wa na gaba da shi biyayya, don idan wata rashin jituwa ta shiga tsakaninsu, ƙarami ba ya jin kunyar cin mutunci wanda ya girme shi ko da kuwa ya kai tsarar mahaifinsa. Iyaye sun koma su ne ‘ya’ya, don kuwa ‘ya’yan suna juya su yadda suke so. Zaman banza da yaudara da cuta da yin banga ga ‘yan siyasa marasa kishin ƙasa sun zama abubuwan yi a wannan zamani. Haka kuma, rashin gaskiya da cin amana sun zama ruwan dare, kuma ba a ɗauke su wani abin kunya ba. Shiga cikin irin wannan hali ga dukkan al’ummar da ta san ciwon kanta, al’amura ne waɗanda suke bukatar dubawa da idon basira don samun mafita. Matuƙar ana son a sami mafita dole ne a koma wa tarbiyyar Hausawa ta gargajiya da kuma ta addinin Musulunci wanda ya yi naso cikin al’adu da ita kanta tarbiyyar ta Hausawa. Dangane da haka, wannan takarda za ta yi bayani ne kan wasu daga cikin hanyoyin tarbiyyar Hausawa na gargajiya waɗanda aka danganta su da na addinin Musulunci don kawo shawarwarin da za su taimaka a sami mafita cikin wannan hali da ƙasar Hausa da Tarayyar Nijeriya take ciki na rashin ingantaccen shugabanci a wannan zamani.

     

    2.0 Waiwaye a kan Tsarin Tarbiyyar Hausawa a Jiya

    Tun lokaci mai tsawo da ya gabata kafin shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa al’ummar Hausawa suke gudanar rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya. Wannan kuwa ya faru ne saboda suna da kyakkyawan tsarin tarbiyya wanda ya ba kowa damarsa yadda wani ba ya shiga cikin harkar da ba ta shi ba. Wannan dalili ne ya sa ko da addinin Musulunci ya shigo ba a fuskanci wasu manyan matsaloli ba dangane da halin zamantakewar wannan al’umma. Matuƙar ana son kwalliya ta biya kuɗin sabulu, yadda za a sami ingantaccen shugabanci a wannan zamani na ga ya dace a waiwayi tsarin tarbiyyar Hausawa ta jiya.

     

    2.1 Biyayya ga Addini

    Hanyar bauta wa wani abu wanda mutum yake tsammanin shi zai biya masa buƙatun rayuwa na yau da kullum shi ne addini. Addinin farko na mutanen ƙasar Hausa shi ne addinin gargajiya watau bautar gumaka. Addinin gargajiya ya faru ne ta bin wasu hanyoyi da mutane suka ƙirƙiro wa kansu ta bautar waɗansu abubuwa don cim ma biyan buƙatunsu. Irin wannan hanyar bauta ta daɗe ƙwarai a dukkan sassan duniya ba ƙasar Hausa kaɗai ba. Mutanen da suka fara zama a duniya ne suka ƙirƙiro ta, daga nan abin ya zama al’ada ga sauran ƙabilun da suke biye da su har ya zo ga Hausawa. Irin wannan addini ya sami rauni sakamakon zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa da kuma karɓar shi ga al’ummar Hausawa. Amma duk da haka ba a bar yin wasu abubuwan da suka danganci addinin gargajiya ba, don kuwa za a ga yakan yi naso a wasu al’amuran rayuwar Hausawa na yau da kullum.

     

    Ta wannan fuska idan muka yi waiwaye muka duba yadda al’ummar Hausawa suka gudanar da addininsu na gargajiya, za a ga ba suna sassaƙa wani gunki ne su riƙa bauta masa ba, a’a, mafi yawancin bautarsu ta hanyar tsafi ce. Bauta ta hanyar tsafi tana nufin bauta wa wani aljani da aka ɗauka yana zaune a wani wuri na daban. Ire-iren waɗannan aljannu an ɗauka suna zaune ne a wata kwankwamar dutse, ko wata sarƙaƙƙiya, ko wurin wata tsohuwar itaciya, misali kuka ko tsamiya ko marke da sauransu. Ire-iren waɗannan wuraren tsafi a ƙasar Hausa sun haɗa da wurin bautar aljani Tsumburbura wanda aka ɗauka ya zauna a Dutsin Dala ta Kano da Kaina-Fara-Arnan-Birchi masu bautar aljani Ɗantalle da suka ce yana zaune a cikin Dutsin Birchi ta Ƙaramar Hukumar Kurfi a Jihar Katsina. Arnan Kwatarkwashi kuma suna bauta wa Maiki wanda suka ɗauka yana zaune a cikin Dutsin Kwatarkwashi ta Jihar Zamfara. Haka kuma, a duwatsun Kufena ta Zariya cikin Jihar Kaduna, mazaunan farko na wannan wuri sun ɗauka a cikin waɗannan duwatsu, akwai wasu aljannu da suke zaune a wurin waɗanda suke biya masu buƙatunsu. Akwai kuma arnan Suna ta ƙasar Kwatarkwashi da kuma wasu arnan a wasu sassa na ƙasar Katsina da suke bautar aljani Magiro wanda suka ɗauka yana zaune a wurin tsamiya mai sarƙaƙƙiya da duhuwa wadda ba mai iya zuwa wurin da take sai masu yin bautar wannan tsafi.

    Bayan tsafi wani nau’i na addinin gargajiya na Hausawa shi ne bori, watau bautar iskoki ko mutanen ɓoye. A wurin Hausawa bori tsohuwar al’ada ce, domin kuwa an daɗe ana yin ta a matsayin addini, kuma har yanzu da addinin Musulunci ya zama jiki ga Hausawa ba a bar yin ta ba. Hausawa sun ɗauka ban da ma mutane, wannan duniya da muke ciki tana ɗauke da wasu ɓoyayyun halittu masu ɗabi’u irin na mutane. Wannan dalili ne ya sa suke kiran su mutanen ɓoye. A saboda wasu dalilai ‘yan bori sun rarraba iskoki zuwa kashi biyu; baƙaƙen iskoki da fararen iskoki.

     

    Baƙaƙen iskoki su maƙetata ne masu neman mutum da sharri. Idan ana son a yi wa mutum maganin da zai mutu, ko ya haukace, ko ya lalace, ko wani bala’i ya faɗa masa ana neman taimakon yin haka daga baƙaƙen iskoki. Ire-iren su sun haɗa da Uwar-gona da Baƙo da Kure da Gajimare da Danko da Duna da Kakare. Su baƙaƙen iskoki ba a neman su sai ta ɓaci don su ƙara ɓata al’amari.

    Fararen iskoki kuwa na kirki ne kuma suna taimakon mutane ta hanyar bayar da dukiya da kuma sarauta. Bugu da ƙari kuma, suna ba mutane maganin cuce-cuce ciki har da na maganin baƙaƙen iskoki. Daga cikin fararen iskoki akwai Sarkin Makaɗa Dafau da Sarkin Aljan da Sarkin Rafi da Uban Dawaki da Inna (Bafulatana) da Ɗangaladima da Malam Alhaji.

     

    Waɗannan iskoki baƙaƙe da farare,’yan bori sun bayyana, wasunsu na zama tare da mutane, su kuma yi abota da su. Mutanen na hawa borinsu sai su riƙa gaya masu magungunan wasu cuce-cuce. Haka kuma suna gaya masu labarin gaibi, watau abubuwan da za su faru gobe ko baɗi da sauransu. Ire iren waɗannan mutane da suke yin hulɗa da aljannu ne Hausawa suke kira ‘yan bori. Dukkan wanda yake son zama ɗan bori dole sai an yi masa girka. Ana yin girka don a shirya dukkan iskokin da suke kan mutum don ya zauna lafiya da su. Ana kuma yin girka don yin magani ga marar lafiya wanda iskoki suke kansa kuma suka hana shi zama lafiya.

     

    Bayan addinin gargajiya sai addinin Musulunci wanda shi addini ne Allah Maɗaukakin Sarki Ya aiko ta hannun Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, don ya shiryar da al’ummar duniya zuwa ga hanya madaidaiciya a cikin shekara 610 Miladiyya. Addinin Musulunci ne ya biyo bayan addinin Kirista wanda Allah Maɗaukakin Sarki ya aiko ta hannun Annabi Isa, Allah ya yarda da shi. A tsakanin waɗannan addinai akwai shekaru ɗari shida (Ibrahim,1982:63).

     

    Ba kamar sauran addinan da suka gabace shi ba, addinin Musulunci an aiko da shi ga dukkan al’ummar duniya don ya zama hanyar shiriya ga kowa. Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya fara da kiran ‘yan’uwansa Banu Ƙuraish don su karɓi wannan addini.Wasu suka karɓa wasu kuwa ba su karɓa ba. Sannu a hankali yana wa’azi tare da sahabbansa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, sai da dukkan ƙasashen Larabawa suka karɓi addinin Musulunci. Wannan ne ya sa aka kafa ƙungiyar al’ummar Musulmi wadda take da cibiya a Madina. Annabi shi ne shugaban wannan al’umma, kuma dukkan wani abu da za ya zartar, sai ya yi shawara da sahabbansa.Wajen tafiyar da wannan al’umma ba a nuna ƙabilanci ko fifiko tsakanin jama’ar da suke cikinta. Abin da ta sa gaba shi ne haɗin kai da son juna da nuna ‘yan’uwantaka a tsakanin Musulmi. Babban tsarin mulkin wannan al’umma shi ne shari’ar addinin Musulunci. Kafin Annabi ya ƙaura, ya bar wa al’ummar Musulmi Alƙur’ani Maigirma da kuma Hadisai don su yi masu jagora dangane da addininsu (Ibrahim, 1982:63).

     

    Manyan shika-shikan addinin Musulunci biyar ne kamar haka:-

    i)                   Shedawa ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, BawanSa ne kuma ManzonSa ne.

    ii)                 Tsayar da Sallah.

    iii)               Bayar da Zakka.

    iɓ)       Yin Azumin watan Ramalana.

    ɓ)        Ziyartar Ɗakin Allah don yin aikin Hajji ga wanda

    Allah Ya ba iko.

     

    Idan muka waiwaya muka duba al’ummar Hausawa kafin shigowar addinin Musulunci da ma bayan shigowar sa za a fahimci cewa, mutane ne musu matuƙar biyayya ga dokokin addinin da suke bauta wa. Misali, al’ummar Hausawa a lokacin da suke bautar addinan gargajiya suna matuƙar yin biyayya ga abubuwan da suke bauta wa, suna tsoron su saɓa musu don tsoron kar su yi fushin da zai sanya su saukar masu da wani bala’i. Haka kuma, suna kyautata musu don neman yardarsu yadda za su biya musu bukatunsa, su kuma sanar da su abubuwan da ke tafe a shekara mai zuwa, idan na sharri ne su taimaka musu yadda za su yi maganinsu. Dangane da wannan takarda za a ɗauki wani ɓangare na rayuwar Hausawa domin ganin yadda addinin gargajiya ya ɗauke shi don bayar da misali. Za a ɗauki lalata (zina) watau saduwa tsakanin mace da namiji waɗanda ba igiyar aure tsakaninsu don duba matsayinta da irin hukuncin da ake yanke wa waɗanda suka aikata ta a al’adar Hausawa kafin shigowar addinin Musulunci.

     

    Duk da kasancewar a al’adar Hausawa ba a yi wa budurwa aure sai ta kai shekara goma sha takwas ko fiye da haka, watau an tabbatar da ta balaga, an yarda idan saurayi yana neman aure budurwa ya je tsarince wurinta, watau ya kwana gidansu a ɗaki ɗaya da ita bisa shimfiɗa ɗaya, ko ita ta je gidan saurayin nata su kwana tare, amma duk da haka al’ada ba ta yarda ya ko taɓa jikinta ba, balle ma har ya aikata wani abu da ita ba, watau ya yi lalata (zina) da ita ba. Idan ya kuskura ya taɓa ta ko ya yi ƙoƙarin yin lalata da ita, to ya shiga uku ya lalace, don kuwa duk wannan yanki nasu ba zai ƙara samun budurwar da za ta yarda da shi ba. Wannan dalili ne zai kai shi ga rasa matar da zai aura, daga ƙarshe dole ya gudu ya bar ƙasar baki ɗayanta yadda ba a za a sake jin labarinsa ba. Ire-iren waɗannan mutane ne za a tarar sun je wasu garuruwa inda ba wanda ya san su a garin. A wasu lokuta har su mutu ba a sanin daga inda suka zo wannan ƙasa. Wannan hukunci ga namiji ke nan.

     

    Ita budurwa kuwa idan ta kuskura ta yi lalata (zina) tana fuskantar hukunci mai tsananin wanda a wani lokaci yana iya zama dalilin mutuwar ta. Wannan hukunci ya danganta da abin bautar gidansu. Da farko abin da ake fara yi shi ne, za a kira ta a tambaye ta, ko ta san ɗa namiji? Idan ta amsa da cewa ta san ɗa namiji, shi ke nan ta jawo wa kanta da dukkan zuri’arta abin kunya, sai kuma a rage yawan dukiyar aurenta. Idan kuwa ta amsa da cewa ba ta san ɗa namiji ba, sai aka iyayenta su bi hanyar da suka gada ta tsafi don gane gaskiyar abin da ta faɗa. Ga misalin ire-iren yadda ake gane budurwa ta san ɗa namiji ko ba ta san shi ba kafin a yi mata aure a al’adar Maguzawa da kuma irin hukunci da suke yanke wa ‘ya’yansu mata waɗanda ba su kai budurcinsu ba dangane da abubuwan da suke bauta wa na gargajiya.

     

    2.1.1 Masu Bautar Aljanin Magiro

    Maguzawan da suke bautar wannan tsafi sun ɗauka aljanin yana zaune a dutsin Kwatarkwashi. A Kwatarkwashi arnan Suna ne suke bautar wannan gunki, haka kuma akwai wasu arnan a wasu sassan ƙasar Katsina da suke bautar wannan tsafi. A ƙasar Katsina a ƙauyen Kunkunna da Makanwaci da Tamna da Maikada da Daulai cikin ƙaramar Hukumar Safana. Haka kuma a ƙauyukan Barza da Gerecen-Arna da Aidun Gadaje cikin ƙaramar Hukumar Ɗanmusa akwai  arnan da suke yin irin wannan bauta ta tsafin Magiro. Domin yin wannan bauta, suna samun bishiyar tsamiya ko marken da yake da duhuwa da sarƙaƙƙiya. Waɗannan arna na samun yashi mai laushi da kyawo su zuba a gindin wannan tsamiya ko marke, sai kuma su kawo baƙin zane da baƙin rawani da baƙar hula da baƙar riga da baƙin wando dukkansu na saƙi sai a ɗaɗɗaura su wurin wannan tsamiya. Daga nan, sai a sami tulunan giya biyu a ajiye gindin wannan tsamiya ko marke, sai kuma a yanka baƙin bunsuru a gindin tsamiyar. Dukkan wanda ya ga waɗannan alamomi zai fahimci akwai wani abu da ke faruwa a wurin, kuma ana gargaɗin mutane da su yi nesa da wurin don ba mai zuwa wurin sai wanda yake kula da tsafin ko wani daga cikin zuri’arsa. Ana tsorata mutane da cewar, dukkan wanda ya je wurin, idan ba waɗannan mutane ba, dukkan abin da ya same shi ya kuka da kansa.

     

    Mabiya tsafin Magiro sun ɗauka wannan aljani na kare su daga dukkan bala’o’i, kuma yana biya masu dukkan buƙatun da suka nema daga gare shi. Haka kuma, suna ikirarin cewa, dukkan wanda yake da shakka kan gaskiyar tsafinsu suna iya nuna masa ta hanyar kiran aljanin. Akwai dalilan da kan sa a kira aljanin Magiro waɗanda suka haɗa da idan ana biki gidan mabiyansa, yana zuwa don ya bayyana wa jama’a da mahaifan wannan yarinya da za a yi wa aure ba ta yi lalata (zina) ba a lokacin da take budurwa. Hanyar da ake gane haka shi ne, a ranar da za a ɗaura wa yarinyar aure, tun da asuba sai mahaifanta su kira ta, sai a ajiye turmin daka a tsakiyar gidansu ta hau kansa ta zauna. A wannan lokaci ne za a kira wannan aljani na Magiro. Da ya iso gidan, sai ya yi ta zagaya gidan kamar iskar guguwa, ya kuma yi ta yin ruri kamar bajimin sa. Idan wannan yarinya ta taɓa yin lalata, sai ya kashe ta. Idan kuwa ba ta taɓa yi ba, sai ya yi ta zagaye-zagayensa har ya gama ba abin da zai sami wannan yarinya. Ko kuma, idan ya rage saura kwana ɗaya a yi bikin, sai a sami baƙin ɗan’akuya da jan zakara da goran giya a kai su wurin da ake yin tsafin Magiro. Idan gari ya waye, sai a je wurin a duba. Idan an tarar ɗan’akuyan da zakaran sun mutu, kuma goran giya babu kome cikinsa, alama ce wadda take bayyana cewa wannan yarinya ba ta yi lalata ba, Magiro ya yi maraba da ita ke nan. Idan kuwa aka tarar ɗan’akuyan da zakaran, kuma ba a taɓa goran giya ba, alama ce wadda take bayyana wannan yarinya ba ta kai budurcinta ba, Magiro bai yi maraba da ita ba ke nan, sai ya kashe ta. Daga nan, sai iyayenta su yi ta murna saboda ɗiyarsu ta kai budurcinta. Daga nan, sai a ɗauki wannan yarinya a kai ta ɗakin mahaifiyarta inda za a yi sauran al’adun da suka dace a yi mata don kai ta gidan miji (Ibrahim, 1982: 172).

     

    Su kuma Maguzuwa masu bautar tsafin Uwar-Gona a lokacin da ‘yarsu budurwa za ta yi aure, hanyar da suke bi don su gane cewa wannan yarinya wadda za a yi wa aure ta yi lalata ko ba ta yi lalata ba ita ce, sai a sa waɗanda za su auri wannan yarinya su kawo ɗan’akuya. Daga nan sai a samo turamen daka uku, a kuma samo mutane uku, sai a jera turame biyu kusa da kusa, sai a sanya turmi na cikon ukun a gefen waɗannan turame biyu. Daga nan, sai mutane biyu daga cikin mutanen nan uku su hau kan turmi ɗaya - ɗaya, shi kuma na cikon uku sai ya hau kan ɗaya turmin. Sai a kawo wannan ɗan’akuya a ba waɗannan mutane biyu waɗanda suke kan turame biyu da suke kusa – kusa. Ɗaya ya riƙe ƙafafun gaba, shi kuma ɗayan ya riƙe ƙafafun, shi kuma wanda yake kan ɗayan turmi na cikon uku, sai a kawo masa wani takobi na tsafi wanda aka ajiye ba a amfani da shi sai irin wannan rana. Lokaci da ya amshi wannan takobi, sai ya sari wannan ɗan’akuya da shi. Idan wannan yarinya ba ta san ɗa namiji ba, sari ɗaya zai yi wa wannan ɗan’akuya ya raba shu biyu, shi ke nan sai iyaye da abokan arziki su yi ta murna, ‘yarsu ta kai budurcinta. Idan kuwa wannan yarinya ta san ɗa namiji ko sara nawa ya yi wa wannan ɗan’akuya ba zai yi masa ko ƙwarzane ba balle ya raba shi biyu. Daga nan,  nan take wannan yarinya za ta faɗi ta mutu.

     

    Maguzawan da suke bautar tsafin Kurmawa waɗanda ake samu a ƙasar Katsina da Kano da Zamfara, a lokacin da za su yi wa ɗiyarsu budurwa aure, idan an tambaye ta ce ba ta san ɗa namiji ba, sai a samo ɗan kwikwiyo da rago a yanka su, a feɗe naman a kuma yayyanka su a haɗe su wuri ɗaya a soya. Bayan ya naman ya soya, sai a kira wannan yarinya a ba ta naman ta ci. Idan ba ta san ɗa namiji ba, duk lokacin da za ta ɗauko tsokar naman ta ci, sai ta ɗauko ta ragon, za ta ci har ta ƙoshi ba abin da zai same ta. Idan kuwa ta san ɗa namiji ba za ta bambance naman kare da na ragon ba, sai ta haɗa su ta yi ta ci har sai ta ƙoshi. Daga nan sai ta faɗi ta mutu nan take. Idan kuwa a lokacin da aka tambaye ta, ko ta san ɗa namiji? Ta amsa da cewa ta sani, sai a ba ta wannan kwikwiyo ta riƙa yawo da shi, don bayyana wa jama’a ba ta kai buturcinta ba, sannan kuma a rage yawan dukiyar aurenta. Wannan dalili ne, ya sa Hausawa yin karin maganar da ke cewa, ‘sharri kwikwiyo ne mai shi yake bi’.

     

    Su kuwa Maguzawan da suke bautar tsafin Maƙera waɗanda su ma ana samun a ƙasar Katsina da Kano da Zamfara, a lokacin da za su yi wa ‘yarsu budurwa aure, idan ya rage saura kwana ɗaya a ɗaura mata aure, sai a kira ta a tambaye ta ko ta san ɗa namiji? Idan ta amsa da cewa ba ta san ɗa namiji ba, sai a samo jan zakara. Daga nan, sai a ɗebo jar dawa a sami mata uku ko huɗu, sai a kamo wannan zakara a sanya shi ƙarƙashin turmin da ake daka, a zuba wannan jar dawa cikin wannan turmi, sai waɗannan mata su yi ta dakan wannan dawa har sai sun mayar da ita gari. Lokacin da suke dakan wannan dawa wannan zakara na ƙarƙashin turmin da suke dakan. Idan wannan yarinya ba ta san ɗa namiji ba, duk tsawon lokacin da aka ɗauka ana dakan wannan dawa ba abin da zai sami zakaran, hasali ma, washegari ranar da za a ɗaura auren wannan yarinya, zakaran ne zai fara cara da asuba don tayar da mutanen wannan gida daga barci. Idan kuwa wannan yarinya ta san ɗa namiji, da safe idan aka ɗaga turmin da aka sanya zakaran za a tarar ya rududduge ya saje da ƙasa, ana ganin haka, ita kuma wannan yarinya tana faɗuwa nan take ta mutu (Ibrahim, 1982: 173 - 175) .

     

    Kamar yadda aka gani ta wannan hanya ce al’ummar Hausawa kafin su karɓi addinin Musulunci suke hukunta waɗanda suke aikata lalata (zina), wannan ne ya sa a wancan zamani suka zauna lafiya ba yawan zinace-zanace aka kuma sami sauƙin tafiyar da shugabancin al’umma ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba. Yanzu kuma, za mu duba irin hukuncin da addinin Musulunci ya yi umurnin a yanke wa waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki. Da farko za mu duba cikin Alƙur’ani Maigirma, cikin sura ta 17 Aya ta 32, inda Allah, Maigirma da ɗaukaka Yake cewa:

     

    “Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya” (Gumi, 1979: 419).

     

    Allah, Maigirma da Ɗaukaka, a cikin Sura ta 24 Aya ta 2 da ta 3, Ya ƙara da cewa:

     

    “Mazinaciya da mazinaci1, to, ku yi bulala ga kowane ɗaya daga gare su, bulala ɗari. Kuma kada tausayi ya kama ku game da su a cikin addinin Allah, idan kun kasance kuna yin imani da Allah da Ranar Lahira. Kuma wani yankin jama’a daga muminai, su halarci azabarsu” (Gumi, 1979: 528).

     

    “Mazinaci ba ya aure2 face da mazinaciya ko mushirika, kuma mazinaciya babu mai aurenta face mazinaci ko mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan muminai” (Gumi, 1979: 528).

     

    A cikin Sura ta 25 Aya ta 60 – 70, Allah, Maigirma da Ɗaukaka, Ya ƙara da cewa:

     

    “Kuma waɗanda ba su kiran wani ubangiji tare da Allah, kuma ba su kashe rai wanda Allah Ya haramta face da hakki, kuma ba su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka” (Gumi, 1979: 551).

     

    “A riɓanya masa azaba a Ranar Ƙiyama. Kuma ya tabbata a cikinta yana wulakantacce” (Gumi, 1979: 528).

     

     

     

     


    1. Hukuncin waɗanda ba su yi aure ba ne, amma waɗanda suka yi aure, hukuncinsu a jefe su har su mutu, bayan sharuɗɗa sun cika, kamar yadda yake ga sunna. Kuma wannan ga hakkin ‘ya’ya ne, amma bayi, hukuncinsu bulala hamsin kawai.
    2. Auren mazinaci ko mazinaciya makaruhi ne ga wanda ba haka nan yake ba, domin tsaron mutunci da kore tuhuma.

     

     

     

     

     

    Sai wanda ya tuba3, kuma ya yi imani, kuma ya aikata aiki na ƙwarai, to, waɗancan Allah Yana musanya miyagun ayyukansu da masu kyau. Allah Ya kasance Mai gafara Mai jin ƙai” (Gumi, 1979: 528).

     

    Mun ga irin hukunce-hukuncen da Allah, Maigirma da Ɗaukaka Ya yanke wa mazinata a cikin Alƙur’ani Maigirma, yanzu kuma za mu duba Hadisan Annabi, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, don samun ƙarin bayani.

    A wani Hadisi da Bukhari ya ruwaito, ya bayyana cewa Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya ce:

     

    “Mazinaci ba zai kasance mai imani ba a lokacin da yake aikata zina……” (Emarah, 1430 AH/2009: 63).

     

    A wani Hadisi da aka karɓo daga Ubaidah ɗan Samit ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya ce:

    “Ku riƙa daga gareni! Ku riƙa daga gare ni! Haƙiƙa Allah Ya sanya mafita a gare su: Saurayi da budurwa (idan suka yi zina) to, bulala ɗari ne da korewar shekara; kuma bazawari da bazawara bulala ɗari ne da rajamu” (Kani, Ba Ranar Bugu:212).

     

    Wani Hadisin da aka karɓo daga Ɗan Umar, ya bayyana cewa, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya ce:

    “Ku nisanci waɗannan (ayyuka) munana wacce Allah Maɗaukaki Ya yi hani gare ta. Kuma wanda ya aikata ta, to, ya suturu da suturcewar Allah Maɗaukaki; kuma ya tuba ga Allah Maɗaukaki. Saboda, lallai wanda ya bayyanar da haƙiƙanin lamarinsa a gare mu za mu tsayar da hukuncin Allah Maɗaukaki a gare shi” (Kani, Ba Ranar Bugu:215).

     

    2.2 Biyayya ga Tsarin Shugabanci Irin na Hausawa

    Shugabanci yana nufin yi wa al’umma jagora a halin zamantakewarsu na yau da kullum. A nan duk wanda aka ba ragamar tafiyar da mulkin al’umma, nauyi ya hau kansa na tsare lafiyarsu da dukiyarsu da mutuncinsu. Su kuma waɗanda ake shugabanta haƙƙinsu ne su ba wanda yake shugabancinsu haɗin kai, da bin ummurnin sa ta hanyar bin doka da oda, da yi masa biyayya don ya sami sauƙin tafiyar da mulkinsu cikin kwanciyar hankali.

     

    1. Wanda ya tuba daga kowane irin zunubi, waɗanda aka ambata da waɗanda ba a ambata ba, ko da laifinsa kafirci ne, to, sai ya tuba zuwa ga Allah kawai, tuba ta gaskiya, lalle ne Allah zai karɓi tubarsa matuƙar ajalin mutuwa bai sauka a kansa ba.

     

    A ƙasar Hausa shugabanci yana farawa daga gida, a kowane gida wanda yake ƙunshe da mutanen da suka kai biyu ko waɗanda suka wuce haka, akwai maigida wanda nauyin dukkan mutanen wannan gida yana kansa. Shi ne yake shugabancin harkokin rayuwar yau da kullum na mutanen da suke wannan gida. A saboda haka dukkan mutanen wannan gida waɗanda suka haɗa da matansa da ‘ya’yansa da ƙannensa da jikokinsa da barorinsa duk da matansu da ‘yan cin arziki suna bin ummurninsa. Haka kuma, shi ne yake ɗaukar nauyin yi masu dukkan abubuwan da suka shafi sutura da abinci da tsaro da kare mutuncinsu. Idan ire-iren waɗannan gidaje suka yi yawa, sai su kafa unguwa. Daga cikin masu waɗannan gidaje, sai a sami wani mai kwarjini da iya tafiyar da harkokin al’ummarsa a ba shi muƙamin mai’unguwa. Mutanen wannan unguwa ne suke zaɓar sa su kai shi ga dagacinsu wanda shi ne zai amince da shi. Daga nan nauyin tafiyar da harkokin mulkin al’ummar wannan unguwa ya hau kansa. Shi ne kuma zai riƙa wakiltarsu a duk wasu harkoki da kuma yin sasanci a tsakanin talakawan wannan unguwa. Haka kuma, shi zai riƙa tattara kuɗin harajin mutanen wannan unguwa don kai wa dagacinsu (Usman, 1972:176).

     

    Samuwar unguwanni da yawa ke sa a sami dagaci wanda shi yake shugabantar masu unguwanni. Dukkan abubuwan da ke faruwa a waɗannan unguwanni sai an sanar da shi. Haka kuma, duk wani sasanci da ya gagari mai’unguwa, sai ya kai wa dagaci don ya sasanta. Dagaci ne yake wakiltar al’ummominsa waɗanda suke zaune a unguwanni a wasu al’amuran da suka shafi waɗannan unguwanni, kuma shi masu unguwanni suke kai wa kuɗin harajin unguwanninsu don ya kai wa hakimi.

     

    Garuruwan dagatai da yawa suke samar da ƙasar hakimi wanda shi yake shugabancin dukkan garuruwan dagatai da suke ƙarƙashinsa. Dukkan abubuwan da ke faruwa a garuruwan dagatai sai an sanar da hakimi, kuma shi yake wakiltarsu a wasu ma’amalolin da suka shafi wannan ƙasa tasu. Idan dagatai sun gaza wajen yin sasanci a tsakanin talakawansu, sai su miƙa maganar ga hakimi wanda zai yi iyakar ƙoƙarinsa ya yi sasanci. Bayan dagatai sun kammala tattara kuɗin harajin ƙasashensu, sai su kawo wa hakimi daga nan sai ya kai wa sarki.Waɗannan ƙasashe na hakimai su ne suke taruwa su kafa ƙasar sarki wanda shi ne wuƙa da nama a duk harkokin da ke faruwa a wannan masarauta. Dukkan mutanen da suke zaune a wannan ƙasa na ƙarƙashin ikonsa, kuma hakimai na sanar da shi dukkan abubuwan da ke faruwa a ƙasashensu. Idan hakimai sun gaza wajen yin sasanci tsakanin talakawansu, sai su kai maganar ga sarki, wanda ta hanyar shawartar ‘yan majalisarsa zai yanke hukunci na ƙarshe ko da daɗi ko ba daɗi.Wanda hukuncin bai yi wa daɗi ba, dole ya yi haƙuri (wannan dalilin ne ya sa ake yi wa sarakunan gargajiya na ƙasar Hausa laƙabi da sunan wuƙar-yanka). Idan hakimai suka kammala tattara kuɗin haraji na ƙasashensu, sai su kai wa sarki, wanda zai sa a saka su cikin Baitulmali don gudanar da harkokin mulki na wannan masarauta (Usman, 1972:176).

     

    A kowace masarauta akwai ‘yan majalisar wannan sarki, su ne suke taimaka wa wannan sarki da shawarwarin aiwatar da mulkin wannan ƙasa cikin nasara da adalci. Waɗannan ‘yan majalisa sun haɗa da waziri wanda shi ne babban mai taimaka wa sarki, kuma a mafi yawancin lokaci shi yake wakiltarsa a lokacin da ya yi wata tafiya wajen masarautarsa. Bayansa, akwai alƙali da magatakarda da ma’aji ko ajiya da sarkin fada da shamaki da shantali da galadima da sarkin gida da sauransu da dama.

     

    Bayan waɗannan sarautu, akwai waɗanda ake ba masu yin sana’o’in gargajiya. Kowace sana’a tana da wanda ake ba jagorancin masu yin wannan don ya yi jagoranci da sasanci a tsakanin masu yin wannan sana’a da kuma tafiyar da sana’ar bisa ingantaccen tsari. Ire-iren waɗannan sarautu sun haɗa da sarkin noma ga manoma da sarkin maƙera ga maƙera da sarkin aska ga wanzamai da sarkin makaɗa ga makaɗa da sanƙira ko sarkin roƙo ga maroƙa da sarkin fawa ga mafauta da sauransu da dama (Adamu,1978:5).

     

    Dukkan waɗannan sarautu da aka yi bayani a kansu tun daga mai unguwa zuwa ga sarki da ‘yan majalisarsa da masu riƙe da sarautun sana’o’in gargajiya, an tsara su ne bisa tafarkin gado.Watau idan wanda yake riƙe da sarauta ya rasu ko aka tuɓe shi, a mafi yawancin lokaci ana zaɓar wani daga cikin ‘ya’yansa ko ɗan’uwansa don ya gaje shi.

     

    Babban ginshiƙin tafiyar da kowane irin mulki shi ne adalci, watau shugaba ya zama adali wajen tafiyar da mulkinsa ba tare da nuna bambanci ba, ya kuma ba kowa haƙƙinsa ba tare da la’akari da nasabarsa, ko muƙaminsa ba. Dukkan ƙasar da take da shugabanni masu yin adalci ga talakawansu, wannan ƙasa za ta zauna lafiya ta kuma sami ci gaba da ƙaruwar arziki. Idan muka waiwayi yadda aka riƙa gudanar da mulki a ƙasar Hausa kafin zuwan wannan zamani za a ga cewa, ana gudanar da shi ne bisa adalci, don kuwa akwai zaman lafiya tsakanin al’ummomin wannan ƙasa. Misali, a cikin gida ko unguwa ko cikin gari, manya suna iya yin hukunci idan suka ga na ƙasa na yin rashin daidai ko da kuwa ba su da wata dangantaka ko nasaba ta jini. A tunaninsu yaro duka na kowa ne, matuƙar ka ga yana yin wani abu na rashin daidai matuƙar ba ka tsawata masa ba, to, a al’adar zamantakewa ta Hausawa ba a yi daidai ba, kuma ba za a ɗauki wannan mutum wanda ya san daidai ba. A wancan zamani takan kai matakin idan babban mutum ya tarar ana yin rashin daidai yana iya yin hukunci mai tsanani4 (ko da kuwa zai kai matsayin duka) ga waɗanda ya tarar suna yin rashin daidai ɗin ko ya san su, ko bai san su, ko da dangantaka ko ba dangantaka tsakaninsu.

     

    Domin cim ma wannan buri ne ya sa addinin Musulunci ya shimfiɗa yadda za a gudanar da mulkin adalci ga kowace al’umma yadda za a zauna lafiya, kuma wannan al’umma ta sami dauwammen ci gaba da zama lafiya. Dangane da haka, ga irin yadda addinin Musulunci ya tsara gudanar da mulkin adalci kamar yadda Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rubuta maƙala mai taken Usul al-Siyasa ya ba Malam Umaru Dallaji wanda aka ba tutar jihadi a ƙasar Katsina. Domin fito da wannan tsari na shugabanci ga kaɗan daga cikin bayanan wannan maƙala:

    \

     


    4.  Wani dattijo ya tarar da wata mata ta yiwo yaji mutane sun taru ana ta ba ta haƙuri don ta koma ta ƙi komawa, da ya ce ta koma ta ƙi, sai ya ɗebo tsabgar bedi, ya yi ta dukan ta da ita, ya tasa ta gaba sai da ya mayar da ita gidan mijinta. Da mahaifanta suka ji labari, sai suka tarar da wannan dattijo har gida suka yi masa godiya bisa ga wannan taimako da ya yi masu. Ita kuma wannan mata daga wannan rana ba ta ƙara yin yaji ba.Wannan al’amari ya bayyana irin muhimmancin shugabanci da yadda ake girmamma na gaba, ba kamar wannan zamani ba wanda ake son ‘ya’ya, har ta kai matakin iyaye ba sa iya hukunta ‘ya’yansu.

     

    Ya fara da ambaton Umarun Dallaji a matsayin mutum mai gaskiya da riƙon amana da yin ayyuka domin neman sakamako daga Allah. Daga nan, sai ya yi masa addu’a yana roƙon Allah Ya taimake shi bisa ga gudanar da mulkinsa, Ya ba shi tsawon kwana bisa ga wannan mulki da yake yi, sannan kuma ya ƙara da roƙon Allah Ya ƙara nunnuka yawan masu goyon bayansa. Daga nan sai wannan maƙala ta fara da cewa:

     

    “Ka sani ya kai ɗan’uwa, babbar ƙaddarar da za ta faɗa a kan bawan Allah, ita ce, a ba shi shugabancin jama’a, domin kuwa ka sani, za a tambayi kowane mutum abin da bakinsa ya faɗa, ayyukan da ya yi, da abubuwan da suka biyo bayansu. Idan ya kasance shi shugaba ne, za a ƙara da tambayar sa yadda ya gudanar da mulkinsa tsakaninsa da talakawansa. Idan ya kasance ba ya iya sauke nauyin kansa, to, ta yaya zai iya sauke nauyin jama’ar da take ƙarƙashinsa? Dangane da haka ne wasu suke cewa, dukkan wanda Allah bai ɗora masa wani nauyi na shugabanci ba ya ƙara yi maSa godiya, don Ya sauke masa nauyin da za a tambaye shi yadda ya gudanar da shi. Saboda haka, Allah Ya cece shi daga fitunun duniya, don kuwa babu kome cikinta sai tashin hankali da azabtarwa a gobe lahira”.

     

     

    Saboda matsalolin da suke tattare da shugabanci ne, ya kawo wani hadisin Annabi, inda yake cewa:

     

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya tambayi sahabbansa, “ko kuna son in gaya maku wani abu dangane da shuganaci”? Sai suka amsa masa da cewa: “Ya Manzon Allah muna so”. Daga nan sai ya ce: “Farkon shi akwai kushewa, tsakiyarsa, akwai nadama. Ƙarshensa kuma, akwai azaba a ranar lahira”.

    A wannan maƙala Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ya ci gaba da bayanin cewa:

    “Wanda Allah, Maigirma da Ɗaukaka, Ya ba shi shugabanci, to, ya yi iya ƙoƙarinsa don ganin ya sauke dukkan nauyin da yake a kansa, ta hanyar ba dukkan al’ummomin da suke ƙarƙashinsa haƙƙoƙinsu”.

    Ya ƙara da bayyana cewa, duk da yake shugabanci abu ne mai nauyi da wuyar ɗauka, amma duk da haka nan, kyauta ce babba. Dukkan shugaban da ya yi wa Allah godiya, ya kuma sami nasarar sauke nauyin shugabanci, to, zai sami babban rabo wanda ba a iya misalta shi. Haka kuma, dukkan shugaban da bai yi wa Allah godiya ba, ya kasa sauke nauyin shuganci, zai fuskanci matsananciyar uƙuba wadda ba ta misaltuwa.

    A dai wannan maƙala Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ya kawo hadisai masu yawan gaske waɗanda suka bayyana matsayi da hukuncin da ke kan shuganni masu adalci da marasa adalci kamar haka:

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya ce: “A ranar Lahira, babu wata inuwa ko wurin hutawa, sai inuwar Allah. A wannan rana mutane bakwai ne kawai za su sami wannan inuwa; shugaba adali wanda ya gudanar da mulkinsa kamar yadda shari’a ta shinmfiɗa, sai saurayi wanda ya girma yana bautar Allah, sai ɗan kasuwa wanda a lokacin da yake gudanar da kasuwancinsa hankalinsa yana masallaci, mutane biyu waɗanda suke ƙaunar junansu saboda bautar Allah da suke yi, sai kuma mutumin da a duk lokacin da ya kaɗaita yana bautar Allah, idan ya tuna Allah, sai ya yi ta zubar da hawaye, sai kuma mutumin da wata mata kyakkyawa wadda yake so, ta kaɗaice da shi, ta kuma bukace shi da ya yi lalata (zina) da ita, amma sai ya ƙi amincewa, ya bayyana mata, ‘ina tsoron fushin Allah Maigirma da ɗaukaka’, sai kuma mutumin da ya ba da sadaka don Allah, ba don riya ba, har ta kai lokacin da zai bayar da sadakar hannunsa na hagu bai san abin da hannunsa na dama ya yi ba”.

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya ce: “Wanda Allah Ya fi so, kuma wanda yake kusa da Allah, shi ne shugaba adali, wanda Allah ba Ya so, kuma wanda yake nesa da rahamar Allah, shi ne azzalumin shugaba”.

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya ce: “Na rantse da wannan wanda rayuwata take a hannunsa, cewa, ayyukan alherin shugaba adali ana tattara su a Aljanna daidai da ayyukan alherin da dukkan talakawansa suka aikata. Haka kuma, idan aka ba da lada ɗaya ga ibadar da talakawansa suka yi, shi ana ba shi lada 70, 000 sakamakon dukkan ibadar aiki ɗaya da ya yi kwatankwacin wadda talakawansa suka yi.

    An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas, Allah Ya yarda da su, ya ce: “Wata rana Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya zo ya tsaya a bakin ƙofar Ka’aba, daga cikin Ka’aba kuma ‘yan ƙabilar Ƙuraish masu yawa, sai ya ce masu, ‘Ya ku shugabanin Ƙuraysh, ku yi abubuwa uku ga waɗanda kuke shugabanta; idan sun bukaci adalci, ku yi musu; idan sun bukaci sasanci, ku sasanta su kamar yadda shari’a ta shimfiɗa a yi; idan kuma kuka yi musu alƙawari, to ku cika alƙawarinku kada ku saɓa. Ya Allah, Kai da Mala’ikunka ku la’anci wanda ya kauce wa wannan tsari. Allah Maigirma da ɗaukaka ba ya amsar ayyukan farilla da na nafila na dukkan mutumin da ya kauce wa wannan tsari”.

    Idan muka nazarci waɗannan bayanai da aka tsakuro daga wannan maƙala, za a fahimci cewa, shugabanci a addinin Musulunci al’amari ne mai matuƙar muhimmanci, wanda idan aka tafiyar da shi kamar yadda shari’a ta shimfiɗa al’umma za ta zauna lafiya a kuma sami ƙaruwar arziki da fahimtar juna. Babbar hanyar da za a sami wannan biyan bukata ita ce, shugabanni su zama masu adalci ga waɗanda suke shugabanta.

    2.3 Bin Gaskiya da Riƙon Amana

    Gaskiya na nufin yin dukkan wani abu wanda zai bayyana zahirin yadda wannan abu yake, watau ba ragi ba ƙari. Riƙon amana kuma na nufin adana wani abu na dukiya ko sirri wanda a lokacin da bukatar shi ta taso a bayar da shi kamar yadda aka bayar. Idan kuma wani sirri ne ba za a sanar da kowa ba, daga kai sai wanda ya sanar da kai. Kafin zuwan wannan zamani an san Hausawa da bin gaskiya da riƙon amana ga dukkan al’amuransu na rayuwa. Wannan dalili ne ya sa a wancan zamani kafin shigowar addinin Musulunci al’ummar Maguzawa ba sa faɗin ƙarya komin tsanani5 ko daɗi. Haka kuma, al’ummar Hausawa mutane ne masu riƙon amana. Abin nufi a nan shi ne, a wancan zamani duk irin halin matsi da tsananin da aka shiga idan ka kawo wani abu wanda ya shafi dukiya ko kuɗi ka ba Bahaushe ajiya ko ka ba shi saƙo ya kai wa wani, duk irin halin da yake ciki ba za ya yi amfani da wannan dukiya ba har sai lokacin da ka bukata ya ɗauko maka. Haka kuma, idan saƙo ne ka ba shi ya kai wa wani zai kai masa kamar yadda ka ba shi ba tare da ya rage wani abu ba6. Idan kuma ka sanar da shi wani sirri ba za ya gaya wa kowa ba daga kai sai shi. Wannan al’amari ya taimaka matuƙa gaya wajen zaman Hausawa lafiya a wancan zamani. Saboda irin yadda Hausawa suka yarda da bin gaskiya har karin magana suke da su masu yawa waɗanda suke nuna muhimmanci gaskiya kamar haka:

     

    v  Komi za ka faɗi faɗi gaskiya kome taka ja maka ta biya.

    v  Marar gaskiya ko cikin ruwa yake ya yi jiɓi.

    v  Gaskiya dokin ƙarfe.

     

     

     


    5. A al’adar Maguzawa faɗin ƙarya mummunan aiki ne wanda yake sa abin da suke bauta wa ya yanke wa maƙaryaci mummunan hukunci. Wannan dalili ne ya sa idan Bamaguje ba ya lafiya, a lokacin da rashin lafiyar ya tsananta, idan aka tambaye shi, ya ya jiki? Sai ya amsa da cewa, babu sauƙi. Dalilin su a nan shi ne, kar su yi ƙarya su faɗi abin da ba haka yake ba. Shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa ne ya yi horo da cewa, a duk yanayin da mutum yake ciki na rashin lafiya kar ya ce ba sauƙi, don sauƙi daga Allah yake.

    6.  Saboda gaskiya da riƙon amana na Hausawa a wancan zamani ya sa a cikin shekara ta 1975 lokacin ina makarantar Sakandare ta Daura, mahaifina ya je Mai’aduwa, lokacin da zai koma gida, da ya zo bakin ƙofar makaranta, sai ya ga wasu ɗalibai ya kira su, ya tambaye su, ko kun san wani yaro mai suna Bishir Ali Safana ? Suka amsa masa da cewa, mun san shi abokinmu ne. Daga nan sai ya kawo kuɗi ya ba su ya ce su kai min. Ina zaune cikin ɗakinmu, sai na ji waɗannan ɗalibai sun shigo suna kiran sunana. Lokacin da na zo wurinsu, sai suka kawo waɗannan kuɗi suka ba ni suka ce, babanka ne ya gamu da mu a bakin ƙofa ya ce mu kawo maka. Wannan al’amari ya faru ne saboda irin tarbiyyar bin gaskiya da riƙon amana wadda iyaye da magabata na wancan zamani suka ba ‘ya’yansu da mabiyansu. 

    v  Ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi.

    v  Gaskiya nagartar namiji.

    v  A daɗe ana yi sai gaskiya.

    v  Gaskiya akurkin ɗunɗu mai wuyar saka hannu.

     

    Haka al’amarin yake a addinin Musulunci, domin kuwa akwai ayoyin Alƙur’ani Maigirma da Hadisan Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, waɗanda suka bayyana muhimmanci gaskiya ga dukkan Musulmi. Yin biyayya gare su zai sa mutum ya zauna lafiya a wannan duniya, sannan kuma ya sami sakamako da Aljanna ranar lahira, rashin yin biyayya gare su kuma zai sa mutum ya rasa zama lafiya a wannan duniya, sannan kuma ya sami sakamako da wuta a ranar gobe lahira. Misali, a cikin Alƙur’ani Maigirma,Sura ta 3, Aya ta 60, Allah Maigirma da Ɗaukaka na cewa:

     “Gaskiya daga Ubangijinka take, saboda haka kada ka kasance daga masu shakka” (Gumi, 1979:84).

     

    Haka kuma, a cikin Sura ta 4 Aya ta 135 Allah Maigirma da ɗaukaka na cewa:

     

    “Ya ku waɗanda suka yi imani!Ku kasance masu tsayuwa da adalci, masu shaida saboda Allah, kuma ko da a kanku ne ko kuwa mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida ko a kansa) ya kasance mawadaci ko matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al’amarinsu, saboda haka kada ku bibiyi son zuciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, ko kuwa kuka kau da kai, to, lallai ne, Allah Ya kasance Masani ga abin kuke aikatawa” (Gumi, 1979:146)

    Allah Maigirma da Ɗaukaka a cikin Sura ta 33 Aya 35 yana cewa:

     

    “Lallai, Musulmi maza da Musulmi mata da muminai maza da muminai mata, da masu tawali’u maza da masu tawali’u mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu haƙuri maza da masu haƙuri mata, da masu tsoron Allah maza da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata, da masu tsare farjojinsu maza da masu tsare farjojinsu mata, da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambatonSa da yawa mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma” (Gumi, 1979:639).

     

    Idan muka nazarci waɗannan Ayoyi na Alƙur’ani Maigirma za mu fahimci Allah Maigirma da ɗaukaka na bayyana muhimmanci gaskiya da kuma irin sakamakon da dukkan wanda ya tsare ta zai samu a nan duniya da gobe lahira.

     

    Saboda muhimmancin gaskiya ga kowace al’umma ya sa addinin Musulunci ya ƙara fito da ita sosai don ta ƙara zama jagora ga al’umma, dangane da haka, an sami ingantattun bayanai daga Hadisan Annabi Muhammadu, tsira da aminci Allah su ƙara tabbata a gare shi, waɗanda suka ƙara bayyana matsayinta da muhimmancinta ga dukkan al’ummar da take son zama lafiya da ci gaba. Ga misalin wasu Hadisai da aka samu waɗanda suka bayyana muhimmancin gaskiya.

     

    An karɓo daga Abdullah, Allah Ya yarda da shi, ya ce: “Na ji Manzon Allah, tsira da aminci Allah su ƙara tabbata a gare shi, na cewa, gaskiya na kai mutum ga shiriya, ita kuma shiriya tana kai mutum Aljanna. Dukkan mutumen da ya zama aikinsa faɗar gaskiya har ta zama al’ada a gare shi, to ya zama cikakken mai gaskiya. Faɗar ƙarya na sa a yi zalunci, haka shi kuma zalunci na kai mutum wuta. Idan mutum ya zama al’adarsa faɗar ƙarya, to Allah Maigirma da Ɗaukaka, na sanya shi cikin maƙaryata”, (Ma’arouf, 1423 AH/2003: 128, da kuma Khan, 1417 AH/1996: 961-962).

     

    A wani Hadisi da aka karɓo daga Ɗan Abbas, Allah Ya yarda shi, ya ce:

     

    “Na ji Manzon Allah, tsira da aminci Allah su ƙara tabbata a gare shi, na cewa: Dukkan mutumen da yake da waɗannan siffofi guda huɗu ya sami ɗaukaka, waɗannan siffofi su ne: Ya zama mai gaskiya da riƙon amana, da alkunya, da hali na kirki ko hali na gari, da kuma ɗaukar girma”, (Ma’arouf, 1423 AH/2003: 129).

     

    Wani Hadisin da aka karɓo daga Muhammad ɗan Ali Al-Kinani ya ce:

     

    “Manzon Allah, tsira da aminci Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya ce: An gina addinin Musulunci bisa shika-shikai uku kamar haka: Shiriya da gaskiya, da kuma adalci. Shiriya farilla ce a furucinmu, gaskiya farilla ce a hujjojinmu, adalci farilla ne a cikin zukatanmu” (Ma’arouf, 1423 AH/2003: 129).  

     

    2.4 Sadar da Zumunci da Taimakon Juna

    Sadar da zumunci al’amari ne wanda al’ummar Hausawa suke ba matuƙar muhimmanci, don kuwa lokaci bayan lokaci ‘yan’uwa da abokan arziki kan riƙa ziyartar juna don gaisawa da ganin halin da suke ciki. Kafin su tafi ziyartar ‘yan’uwa da abokan arziki sukan riƙa wani abu su kai masu, ana yin haka gwargwadon ƙarfin arzikin mutum. Wasu kuma, saboda rashin abin da za su kai ba za ya hana su yin zumuncin ba, suna zuwa wurin ‘yan’uwansu domin su ga halin da suke ciki ba dole sai sun kai masu wani abu ba.

     

    Domin tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum cikin sauƙi, al’ummar Hausawa suna bin tafarkin rayuwa ta cuɗan-in-cuɗe-ka, watau taimakon-kai-da-kai. Ta wannan fuska, idan abin arziki ya sami ɗan’uwa, ko abokin arziki, ko wanda ake zaune tare da shi a wannan ƙauye ko unguwa ko gari, misali aure ko haihuwa, sai duk a taru don taya shi murna. A lokacin bikin, za a yi ta kawo masa gudummuwa wadda wasu kan kawo hatsi ko abinci ko kuɗi ko sutura da sauransu don dai a taimaka wa wannan ɗan’uwa, ko abokin arziki gudanar da wannan hidima ba tare da ya wahala ba. Irin wannan halayya ce a wannan zamani ta haifar da ƙungiyoyin taimaron-kai-da-kai da kuma ƙungiyoyin ajo domin taimaka wa juna.

     

    Haka kuma idan abin baƙin-ciki ya sami wani mutum, misali rashin lafiya, ko mutuwa, ko wata masifa, ‘yan’uwa da abokan arziki da waɗanda ake zaune tare da su, na kusa da na nesa suna ziyartar sa domin yi masa jaje da taya shi jimamin wannan hali da ya shiga na rashin lafiya ko masifa ko rashin ɗan’uwa.

     

    Bayan wannan al’ummar Hausawa na tafiyar da ayyukan gayya don taimakon-kai-da-kai.Ana yin ayyukan gayya wajen yin sababbin ɗakuna da gyara tsofaffi da yin darnin gida da na garka a gonaki da ɗorin ɗan bisan ɗaki da na rumbu. Haka kuma ana yin ayyukan gayya a gonaki don yin sassabe da huɗa da shuka da noma da girbi da ɗaurin amfanin gona da kuma kawo shi gida. A cikin ƙauyuka da garuruwa ana yin ayyukan gayya don gyaran masallatai da maƙabartu da magudanun ruwa da mashayar ruwa ta mutane da ta dabbobi da kuma gyaran hanyoyin da ake bi don kai amfanin gona gida da kasuwanni (Sallau, 2010: 5-6).

     

    Shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa ya ƙara jaddada waɗannan ayyuka na alheri, watau sadar da zumunci da taimakon kai-da-kai, don kuwa a cikin Alƙur’ani Maigirma, Sura ta 2, Aya ta 27, Allah Maigirma da Ɗaukaka, na cewa:

     

    “Waɗanda suke warware alkawalin Allah daga baya ƙulla shi, kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sadar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa, waɗannan su ne masu hasara” (Gumi, 1979: 9).

     

    A wata faɗar cikin Alƙur’ani Maigirma, Sura ta 13, Aya ta 21, Allah Maigirma da Ɗaukaka, na cewa:

     

    “Ya ku mutane! Ku bi Ubangijinku da taƙawa, Wanda Ya halitta ku daga rai guda, ma’auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata. Kuma ku bi Allah da taƙawa, Wanda kuke roƙon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta. Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.

     

    Haka kuma, cikin Alƙur’ani Maigirma, Sura ta 13, Aya ta 21, Allah Maigirma da Ɗaukaka, na cewa:

     

    “Kuma su ne waɗanda suke sadar da abin da Allah Ya yi umurni da shi domin a sadar da shi7, kuma suna tsoron Ubangijinsu, kuma suna tsoron mummunan bincike” (Gumi, 1979: 366).

     

    Domin ƙara bayyana matsayin zumunci da falalarsa ga dukkan wanda ya sadar da shi, da kuma irin hasarar da take baibaye da dukkan wanda ya yanke shi, an sami hadisan Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, waɗanda suka fito da waɗannan bayanai kamar haka :

     

    An karɓo daga Jubair bin Mut’im, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, Ya ce: “Dukkan wanda ya yanke igiyar zumunci, to ba ya shiga Aljanna” (Khan, 1417 AH/1996: 952 da kuma Emarah,1430 AH/2009: 60).

     

     

     


    7.  Waɗannan Ayoyin Alƙur’ani Maigirma da aka kawo, Aya ta farko da ta uku a nan waɗanda suka bayyana ‘a sadar da shi’, watau a sadar da zumunci domin samun sakamako mai kyau. Wanda kuma ya yanke shi ya yi babbar hasara. Ita kuma Aya ta biyu a nan ta bayyana zumuntar ne fili ba tare da an sakaya ta ba. Ta bayyana cewa, dukkan wanda ya tsare zumunta ya kyautata, lalle Allah, Maigirma da Ɗaukaka zai tsare shi.

     

    A wani hadisin da aka karɓo daga Abu Huraira, Allah Ya yarda da shi, ya ce:

     

    “Na ji Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya ce: Kalmar Ar-Rahm (watau mahaifa) ta samo asalinta ne daga kalmar Ar-Rahman (watau ɗaya daga cikin sunayen Allah, Maigirma da ɗaukaka). Dalilin haka ne Allah Maigirma da ɗaukaka, Ya ce: “Zan kyautata wa dukkan wanda ya kyautata wa mahaifa”, (watau ya sadar da zumunci tsakaninsa da ‘yan’uwansa da abokan arzikinsa). Haka kuma, “Zan tozarta dukkan wanda ya tozartar da mahaifa” (watau wanda ya yanke zumunci tsakaninsa da ‘yan’uwansa da abokan arzikinsa), (Khan, 1417 AH/1996: 953).

     

    2.5 Riƙo da Sana’a

    Kafin zuwan wannan zamani al’ummar Hausawa mutane ne waɗanda suka riƙe sana’o’insu na gargajiya waɗanda suka haɗa da noma da kiwo da fatauci da dukanci da ƙira da jima da saƙa da sassaƙa da wanzanci da sauransu. Mata ma ba a bar su baya ba, don kuwa sun riƙe sana’o’insu da matuƙar daraja irinsu kaɗi da dakau da kitso da sauransu. Riƙo da waɗannan sana’o’i ya taimaka al’ummar Hausawa a wancan zamani sun zauna lafiya ba tare da fuskantar matsalolin da a yau shugabannin wannan zamani suka gaza wajen warware su, musamman rashin ayyukan yi ga matasa. A ra’ayina akwai ayyukan yi ga dukkan mazauna ƙasar Hausa ‘yan gida da baƙi. Matsalar ita ce, kowa ya mayar da hankalinsa wajen aikin gwamnati ko na kamfanoni don a waɗannan wurare ne za a sami kuɗi ba tare da an yi wata wahala ba. Matuƙar an koma ma tarbiyyar riƙe sana’o’in gargajiya na Hausawa za a warware wannan matsala.

    Dangane da haka ne, addinin Musulunci ya yi horo ga mabiyabansa da su yi riƙo da sana’o’i, don kuwa su sana’o’i hanyoyi waɗanda za su taimaka wa al’umma ta zama mai arziki da dogaro da kai, kuma ta zama ingantacciya. An bayyana cewa dukkan Annabawan da Allah, Maigirma da ɗaukaka, Ya aiko sun gudanar da sana’o’i iri daban-daban. Misali, an bayyana cewa, Annabi Adamu manomi ne kuma masaƙi, ita kuma matarsa Hauwa’u kaɗi take yi. Haka kuma, Annabi Idrisu maɗunki ne, kuma gwani iya rubutu. Shi kuwa Annabi Nuhu da Annabi Zakariya’u kafintoci ne, Annabi Salihu kuwa ɗan kasuwa. Haka al’amarin ya yi ta gudana har zuwa ga Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, wanda shi ya kasance makiyayi ne (Gusau, 2004:1).

     

    3.1 Matsayin Tarbiyyar Hausawa a yau

    Idan muka dubi tarbiyyar Hausawa a yau kuma muka kwatanta ta tarbiyyar Hausa ta gargajiya, watau kafin shigowar wannan zamani, za a ga akwai babban sauyi, wanda wannan sauyi ne ya kai mu shiga cikin halin da muke ciki a yanzu. Idan za mu ɗauki waɗannan hanyoyin tarbiyya na gargajiya da kuma irin yadda zuwan addinin Musulunci ya ƙara masu ƙarfin gwiwa, za a ga cewa, a yau watsi da su ne ya kai ƙasar Hausa da Tarayyar Nijeriya shiga halin da muke ciki na rashin kyakkyawan shugabanci. Misali, idan muka ɗauki biyayya ga addini  za a ga cewa, a yau addini a baka yake kawai, a aikace ya yi rauni saboda ba a bin dokokinsa wajen yanke hukunci kamar yadda suke cikin Alƙur’ani da Hadisan Annabi, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi. Haka kuma, tsarin shugabanci a wannan zamani ya sha bamban da yadda Hausawa suke gudanar da shi kafin zuwan wannan zamani.

     

    Zuwan Turawa ƙasar Hausa ya sa sun kawo sabuwar rayuwa wadda ta shafi yadda ake gudanar da mulki, sun ce mulkin Dimokraɗiyya ne, watau jama’a su zaɓi shugabannin za su yi masu mulki, amma saboda yadda ake son mulkin ya sa ba a barin jama’a su zaɓi waɗanda za su yi masu mulkin adalci. Maimakon haka ana tilasta shugabanni a kan mutane waɗanda suke sace dukiyar al’umma, suka cusa wa al’umma matsanancin talauci wanda ya yi sanadiyyar mayar da wasu mutane bayi, ana juya su yadda aka so, ana sanya matasa suna cin mutunci dukkan wanda ba ya goyon bayansu ko wanda ya ce ba su yi daidai ba. Wannan ne ya sa a yanzu gaskiya da riƙon amana suka ƙaura daga cikin zukatan wasu mutane, abin da ake so kawai shi ne, ta wace hanya za a sami kuɗi a azurta a dare ɗaya ba tare da an yi wata wahala ba. Sannan kuma, zumunci ya yi wuya, don a wannan zamani ana bin aƙidar kowa tashi da fisshe shi. Ɗan’uwa mai arziki ba ya taimaka wa danginsa mabuƙata, maƙwabci ba ya kyautata wa waɗanda yake maƙwabtaka da su. Yara ba su kunyar manya, manya ba su tausaya wa ƙanana. Ayyukan ɓarna (zinace-zinace da ta’addanci da sace-sace da fashi da makami) sun yi yawa cikin ƙasa har ta kai matsayin ba a jin kunyar aikata su a gaban jama’a.

     

    4.1 Shawarwarin da za su Taimaka a sami Ingantaccen Shugabanci a Wannan Zamani

    Matuƙar ana son samun gyara yadda wannan ƙasa tamu za ta sami ingantaccen shuganacin da zai sa a sami zama lafiya, arzikin ƙasa ya dawo yadda kowa zai sami wadata da ƙaruwar arziki ya zama dole a koma wa tsarin tarbiyyar Hausawa ta gargajiya wadda za a yi mata wasu ‘yan gyare-gyare yadda za ta tafi daidai da zamani kuma ba ta saɓa kyawawan aƙidun addinin Musulunci ba kamar haka:

     

    Ø  Dole ne a koma wa bin dokokin addinin Musulunci ta hanyar bin koyarwa Alƙur’ani da sunnonin Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi. Dukkan wanda ya saɓa masu a hukunta shi kamar yadda shari’a ta shimfiɗa.

    Ø  Shugabanni su riƙa gudanar da mulkinsu cikin adalci, kuma da yake a wannan zamani ana mulki irin na siyasa ya zama dole a bar jama’a su zaɓi waɗanda za su shugabance su, tilasta shugaba a kan al’umma zai ƙara ɓata al’amari.

    Ø  Ya zama dole a riƙa tsare gaskiya da riƙe amana wajen gudanar da mulki da sauran ma’amalolin rayuwa a kowane hali mutum ya sami kansa.

    Ø  Ƙara sada zumunci da taimakon juna zai taimaka a ƙara samun fahimtar juna, yadda za a gudu tare a tsira tare.

    Ø  Koma wa sana’o’in gargajiya na Hausawa don samun abubuwan yi maganin zaman banza da yin bangar siyasa da maula.

     

    Kammalawa

    Bisa la’akari da abubuwan da aka tattauna a wannan takarda waɗanda suka danganci tarbiyyar Hausawa ta gargajiya da kuma ta addinin Musulunci don samo hanyar da za ta taimaka a sami ingantaccen shugabanci a wannan zamani, a iya cewa ya zama dole a fahimci cewa, kyakkyawar tarbiyya ita ce ginshiƙin da zai tarbe dukkan wata fitina da za ta fuskanci kowace ƙasa. Kyakkyawar tarbiyya ce za ta taimaka wa ɗan’Adam ya san abin da yake bauta wa, ita ce za ta horar da mutum ya san abubuwan da abin da yake bauta wa yake so da waɗanda ba ya so. Yin biyayya ga dokokin addini musamman addinin Musulunci zai sa a zauna lafiya, a kuma sami biyan bukata ta duniya da ta lahira. Haka kuma, ya zama dole a riƙa gudanar da shugabanci bisa adalci da tsoron Allah, a kyautata wa waɗanda ake shugabanta ta hanyar sauraren koke-kokensu da biya masu bukatunsu. Sannan kuma, ya zama dole a bar al’umma ta riƙa zaɓar shugabannin da za su jagoranci mulkinta. Riƙo da gaskiya da tsare amana na daga cikin abubuwan da matuƙar aka riƙe su za a sami ingantaccen shugabancin da zai taimaka wa al’umma ta sami dauwammen ci gaba da zama lafiya. Dukkan al’ummar da take sadar da zumunci, kuma ‘ya’yanta suna taimakon junansu za ta ƙara samun ci gaban da zai taimaka mata ta zauna lafiya. Idan har muna son samun ingantaccen shugabanci a wannan ƙasa tamu, ya zama dole mu rungumi waɗannan hanyoyi na tarbiyya kamar yadda Hausawa suka riƙa gudanar da su musamman bayan sun karɓi addinin Musulunci.

     

    Manazarta

    Adamu, M. (1978) The Hausa Factor in West African History, Zaria/Ibadan: Ahmadu Bello Uniɓersity Press/Oɗford Uniɓersity Press of Nigeria.

    Al-Bukhari, M.I. (Ba Ranar Bugu) Al-Sahihul Bukhari, Beirut-Lebanon: Dar-al-Fikr.

    Alhassan, H. da Wasu, (1982) Zaman Hausawa.Zariya: Institute of Education Press, ABU.

    Muhammadu Bello, U. Ɗ. (Ba Ranar Bugu) Fassarar Maƙala Mai Taken  Usul al-Siyasa, Babu Sunan Wanda ya Fassara ta Zuwa Harshen Ingilishi.

    Emarah, M.R. (1430 AH, 2009) Fassarar Littafin ‘Al-Kbae’r (The Major Sins) Zuwa harshen Ingilishi, El-Mansoura – Egypt, Dar Al-Manarah.

    Gumi, A.M. (1979/1399A.H.) Tarjamar Ma’anonin Alƙur’ani Zuwa Harshen Hausa.Beirut-Lebanon: Dar-al-Arabia.

    Gusau, A.R. (2004) Faɗakar da Al’umma a kan Riƙo da Sana’a, Fassarar Littafin Tanbitul Ummati Alal Tikhadhil Hirfati, Wanda Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa ya Wallafa. Gusau: Farin Batu Digital Press.

    Ibrahim, M.S.(1982) ”Dangantakar Al’ada da Addini:Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Isah, Z. (2006) “Gaskiya a Tunanin Hausawa”, Kundin Digiri na Farko. Zariya: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Afirka, Tsangaya Fasaha, Jami’ar Ahmadu Bello.

    Kani, S.M. (1999) Fassarar Bulugul Maram, Juzu’i na Biyu, Talifin Ibnu Hajar Al’Asƙalani, Kano – Nijeriya.

    Khan, M.H.(1417 AH/1996) Fassarar Sahih Al-Bukhari  Zuwa Harshen Ingilishi, Riyadh – Saudi Arabia, Dar – us – Salam Publications.

    Kwairanga, A.M.B (2000/1420). Fassarar Littafi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo na Ihya’ussunna wa Ikmadul Bid’a, Kashi na Farko, Kano-Nijeriya: Ba Sunan Maɗaba’a.

    Ma’rouf, I. (1423 AH/2003) Fassarar Littafin Tahzeebu Dalilul Faliheen – Sharhu Riyadus Saliheen (The Meadows of the Righteous Abrdged) Zuwa harshen Ingilishi, Juzu’i na Farko, El-Mansoura – Egypt, Dar Al-Manarah.

    Sallau, B.A.S. (2009) “Sana’ar Wanzanci da Sauye – Sauyen Zamani Jiya da Yau”, Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Sallau, B.A.S (2010) Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kaduna:M.A.Najiu Professional Printers, No. 3 Kenya Road.

    Smith, M.G. (1957) "The Hausa System of Social Status",  in Africa Ɓol. ƊƊƁII. No.1.

    Shu’aibu, M. (2003) “Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”, Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

    Usman, Y.B. (1972) ”Some Aspects of the Eɗternal Relations of Katsina Before 1804”, Saɓanna Ɓol.I.No.2

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.