Tasirin Addinin Musulunci ga Al'adar Haihuwa daga Haihuwa zuwa yaye

    Gabatarwa:

    "Haihuwa maganin mutuwa, ba dan ke ba da iri ya ƙare"

    Haihuwa ita ce  mataki na biyu cikin matakan rayuwa na kowane abu mai rai sai dai kowace al'umma da nata al'adun da suka amince da su wajen gudanar da matakan rayuwarsu. Haka suma  al'ummar Hausawa suna da Al'adun da suka amince da su wajen gudanar da matakan rayuwarsu na Aure da Haihuwa da Mutuwa, ba a buƙatar ko jin sunan Haihuwa matuƙar aure bai riga ta ba. Wannan ya nuna Hausawa sun ƙyamace miyagun halaye tun kafin su karɓi addinin musulunci.

    Addinin Musulunci Addini ne da ya riske Hausawa suna bautar iskoki, Kasancewar Hausawa masu sauƙin al'amari da nagartattun halaye, ya sa suka karɓi Addinin Musulunci hannun biyu har ake ganin duk mai magana da Hausa musulmi, suma kan su Hausa ke kallon wasu al'ummomi da suka karɓi addinin musulunci Tubabbu saboda nashewar da addini ya yi cikin al'adun Bahaushe ta kowace fuska cikin al'adun Hausa. Kuma shi kan shi Bahaushe duk inda ya samu kan shi yana tafiya da abubuwa biyu addini da al'ada haka yake tafiya dasu har a kasa bambancewa tsakanin addini da al'ada. Irin daɗewar da Bahaushe ya ya da addini sai ya haifar da Bahaushe ya shigar da addini sosai cikin dukkan al'amurransa ciki har da sha'anin haihuwa.

    Manufar wannan aikin ita ce bayar da ma'anar haihuwa da muhimmancin haihuwa da bayyana tasirin da addinin musulunci ya yi a sha'anin haihuwa tun daga shigar cikin har yaye sannan a kammala aikin tare da madogara/Manazarta.

    Ma'anar Haihuwa:

    Ita kalmar Haihuwa a Hausance tana nufin ƙaruwa ko Daɗuwa don kuwa a kan ce wane ya samu ƙaruwa idan an yi masa haihuwa ko kuma a ce wance ta sami ƙaruwa idan ta haihu. Haka ma kuma akan ce dukiya ta haihu Kai tsaye idan ta ƙaru. Amma dai fitacciyar ma'ana ta kalmar haihuwa ita ce fitar da ɗa daga ciki wato dai mace ta haife abin da ke cikinta (M T Adamu 2015).

    Haihuwa ita ce fitar abu mai rai cikin abu mai rai bayan ɗaukar lokacin da Allah ya ɗibarma wannan abin na zama cikin ciki ko ƙasa ko kwai. Duk kan abin da ke haihuwa ba zai sami ciki ba har sai aure ya ƙullu da jinsin namiji na wannan halittar mace mai haihuwa.

    Muhimmancin haihuwa:

    Babu ko shakka a kan muhimmancin haihuwar domin kuwa duk wanda ya haihu ya alfahari da 'ya'yansa haka mai dukiya na alfari da yaɗuwar dukiyarsa haihuwa ta ƙunshi muhiman abubuwa kamar haka:

     - Tabbatar da irin/ Hana kuɓucewar irin

     - Alfahari da yawa

     -  Barin magaji

     - Samun mataimaki

     - Hana gori da sauransu da yawa.

     • Shigar ciki:

    Da zaran an yi aure abu na farko fa kowa ke saurare shi ne samun ciki, har a ƙosa da jira idan anyi jinkirin samun ciki har dangi su fara tambaya ko lafiya wance shiri?

    Da an ce matar wane ciki gareta abin murna da farin ciki ya samu ga 'yan uwa da abokan arziki. Addinin musulunci tun da sha'anin bayyanar ciki ya fara tasiri don kafin Hausawa su karɓi addini, Amarya baza ta san tana da ciki ba har sai an yi mata al'adar  'Karan ƙirji' al'adace ta sanar da 'yan uwa da abokan arziki da dangin miji da na mata cewar aure ya yi albarka ko da ba ayi al'adar a gabansu ba duk wanda ya ganta da ɗaure da zane a ƙirji an san albarkar aure ta samu  (Sarkin Sudan B S).

    Kenan tun kayaking farko na haihuwa addinin musulunci ya kawar da wannan al'ada ya kawo sutura ya kuma hana wasar kanin miji irin ta al'adar maguzawa, ta hanyar dokokin da addinin musulunci ya tanadar ma zamantakewa.

     •Renon Ciki:

    Bayan bayyanar ciki kuma sai kowane ɓangare na 'yan uwa kowa ya duƙufa wajen sauke nauyin da ya jingina garai na renon ciki da kula da mai ciki don tabbatar da lafiyar uwa da abin da ke cikinta. Ba a cika ba mai karamin ciki magain sha har sai ya kai wata bakwai, da yakai wannan lokacin za a fara bata maganin zaƙi da sauƙin guiwa kamar:

     - Sayen Danyi da Ƙayoyinta da Sassaƙen Daniya da Ganyen Loda da Karan dafi.

    Sai a jiƙa su cikin kasko a aje wuri mai sirri, da ta riƙa tsarki da ruwan maganin har ta haihu don maganin fason farji (matucci). Haka kuma bayan cikin ya kai wata bakwai sai a jiƙa mata waɗannan magunguna a wuri mai kyau su zata sha lokaci lokaci har ta haihu.

     - Gadon Maciji da Sasssaƙen Bubuƙuwa da Saiwar Namijin yaɗiya wato Kulumbo.

    A irin wannan ma addinin musulunci ya zo da wasu magunguna da ake ba mai ciki kamar: Na'a Na'a da Hulba da Ruwan zam zam da sauransu.

    • Naƙuda:

    Naƙuda ita ce babbar alama ta ƙarshe dake nuna kusan towar haihuwa, don kuwa wani hali ne na damuwa da zafi da raɗaɗi marar misali da mai ciki take shiga kafin haihuwa. Akwai alamomi da dama da akan gane cewa naƙuda ta zo musamman in ciki ya tsufa ya kai wata tara. Naƙuda tana ɗauke  da tsananin zafi da zogi da shiga halin damuwa ga makusantar mai naƙuda, don ansan tashiga halin ko a haihu lafiya haka aka fi  so ko a rasa ta ko arasa jariri ko a rasa su baki ɗaya wanda ba'a fatar haka. A irin wannan halin na naƙuda addinin musulunci ya zo da sauyi mai cike da sauƙi ga mata, don kuwa kafin zuwan musulunci:

    Kafin zuwan Musulunci bayan jiƙe_jiƙen da ake ba mai ciki a kwai magunguna da aka tanada domin ba mai naƙuda na jiƙe_jiƙen itatuwa da saiyu da tsirrai da sauransu. Misali. Jiƙa ƙasar ƙofar ɗakin mai naƙuda ungozoma takan samo tsohuwar wuƙa ta sassaƙo ƙasar ƙofar ɗakin da mai ciki take ciki ta sama da ta ƙasa ta jiƙa abaiwa mai naƙuda dan haihuwa da sauri kuma cikin tsauƙi. Idan an sha waɗannan abubuwa kuma ba'a haihuwa sai abi waɗannan matakan:

    • Sa muciya a bakin mai naƙuda:  Idan naƙuda ta yi nauyi, mai naƙudar ta galabaita kuma ga ɗa yana son fitowa ƙarfin uwar ya ƙare sai ungozoma/mai taimakon mai haihuwa ta sa akawo mata mucciyar tuƙa tuwo ta tura ma mai naƙuda ita abaki da muciyar ta taɓa maƙoshi ta sai ta fara kakarin amai wannan kakarin da mai ciki ke yi sai ya taimaka wa yaro ya fito, shi ke nan sai murna da kula da uwar da abin da aka haifa bisa ga al'ada. Wannan kakarin ya zama maimakon nishin da ake buƙatar tayi kuma ƙarfinta ya ƙare saboda zafi da wahalar naƙuda.

    • Yin turare tanka: Idan aka sa muciya ba a haihu ba sai a ɗebo wuta a daka tanka a fara rufe ɗakin da take a zuba tankan cikin wutar sai hayaƙin ya game ɗakin ga yaji sai ta fara  tarin kafin hayaƙin ya gama ta dalilin tarin tuni an haife abin da ke ciki.

    Wadannan duk hanyoyi ne na ƙarin azabtar da mai naƙuda da musulunci ya zo sai aka samu abubawa da suka haɗa da:

     • Yi wa abin da ke ciki Sallama: Ungozoma takan tsaya a gaban mai naƙuda tana yin sallama ga abin da ke ciki, tana cewa " Assalam salam, Assalam salam gade Rakayyadi ko Rakayyada, muna lale marhabin cikin farin ciki da walwala, muna lale da zuwa cikin Duniya gidan ƙarya. A sauko a sauko a sauko salamun salamun, Allahumma amin. Za ta fadi haka har sau uku.

    •Idan naƙudar tayi nauyi ba a haihu ba sai a jiƙa wani abu da ake cema Hano ko Hannun Fatcima, wani abu ne mai yatsu biyar amma a dunƙule yake in an jiƙa wa mai naƙuda in haihuwar babu matsala kuma lokaci yayi ana jiƙa shi sai yatsun su buɗe sai aba mai ciki tana sha sai haihuwa. In ko akwai sauran lokaci ba zai buɗe ba. Abin ya ƙiya kenan.

    •karɓo Rubutu wurin malamin da ke ba da rubutu a unguwar. Cikin waɗannan hanyoyin sai a haihu da yardar Allah. Kuma duka babu inda tasha irin wahalar da ake sha a baya.

    • Haihuwa:

    A wasu lokutan haihuwa ta kan zo farat ɗaya bagatatan babu shiri sai mace kawai ta haihu ba wata gargada,  Ungozoma bata kusa. A wannan yanayin sai a ɗauki jaririn a ɗora kansa bisa sabuwar tsintsiya a kusa da mai haihuwa kafin zuwan unguwar zoma.

    Haka kuma ana haihuwar wasu yara da riga har ana yi wa irin wanɗannan yaran laƙabi da 'Mai riga'. Ana gutsura jikin rigar ta haihuwa ayi wa yaro laya da ita, maganin baki da tsari daga Ibilishi.

     • Wanka Jariri:

    Wajen Hausawa rashin wanke Jariri da farko ya fita fes fes yakan haifar da warin jiki idan mutum ya girma, shi ake kira warin ƙashi. Ana wanke Jariri sau uku idan namiji ne mace kuma sau huɗu, kuma idan an yi wankan in za a zubar da ruwan wankan wadda za ta zubar sai ta fashe da dariya wai don yaron ya yi fara'a in ya girma, haka za a yi ta yi har a gama wankan, ana ba yaro ruwan wankan shi na ƙarshe ya sha wai don ya tashi da abin kai nai ya iya dogaro da kai da neman na kai.

    wannan duk tasiri ne da Musulunci ya yi a kan al'adun Hausawa da na haihuwa, game da sallamar da ake yiwa jariri yana ciki, da wadda ake yi mai in anyi mai wanka, wannan sallamar a maimakon kiran sallar da addini ya tana ce.

    Ana gama yiwa yaro wanka sai Ungozoma ta yi wa jariri sallama ta ce " Assalam salam Rakayyadi in namiji ne, Assalam salam Rakayyada in mace ce".

    A rana ta uku sai kakan jariri ko ubansa ya je wurin wani malami ya sanar da shi an samu ƙaruwa, kuma ga sunan da ya ke so ko ya bar wa malamin ya zaɓa masa. In malamin ya je sai a fito da jaririn malam ya yi masa "Kiran sallah a kunnen dama iƙama ga kunnen hagu" wato huɗuba.

    Haka kuma a ranar zanen suna musulunci ya yi tasiri ga sha'anin zanen suna tun daga fara salati ga Annabi da karanta Fatiha da addu'o'in da ake aiwatar a ranar duk addinin musulunci ya zo da su.

    Wannan duk tasiri ne da Musulunci ya yi a kan al'adun Hausawa da na haihuwa, game da sallamar da ake yiwa jariri yana ciki, da wadda ake yi mai in anyi mai wanka, wannan sallamar a maimakon kiran sallar da addini ya tana ce.

    • Camfe-Camfen Haihuwa: Camfi wata hanya ce ta ƙudurce afkuwa ko faruwar wani abu da sakamakonsa zai iya zama mai kyau ko amfani ko mummuna mai cutarwa kuma ya danganci yarda da amincewa.. Adamu T. M (2015).

    Camfi yarda ce da al'ummar Hausawa su ke da suma suke tafiyar da rayuwarsu tare da shi, duk zamanin da Bahaushe ya tsince kansa zai ƙirƙiri camfi daidai da wannan zamanin. Haka abin yake ga sha'anin haihuwa akwai camfe-namfen da suka keɓanta ga mai ciki har tayi yaye tana, kamar:

    Rowa, ɗaibar ruwa Rijiya da dare, kallon mai naƙasa, zuwa kasuwa, Tsallake rafi, Leƙe, Zama ƙasa, Hujin hanci Tsiwa (rashin kunya),  Taɓa kayanta kafin wankin nono, Fita waje kafin suna da kuma bayar da nono tsaye da zubar nono ga jariri.

    Waɗannan da ma wasu camfe-camfe ne da addini ya kawar da ci a sha'anin haihuwar Hausawa.

    • Sunaye:

    Kafin Zuwan Musulunci Hausawa na amfani da lokaci ko sanadi ko yanayi ko sifa wajen rada wa yaro suna.

    Misali: Sunayen lokaci, Ɗan dare da Tarana Magawata/ Harande da Malka Anaru da sauransu.

    Sunayen Sanadi sun haɗa da: Korau da Hana da Audi da Kamaye da Bakuso da Tuni ko Tunau da Tumba da Dela/ igge/ kande da Tanko/ Mati da sauransu.

    Sunayen Yanayi: sun danganci yanayin da aka haifi yaro, irin su sun haɗa da: Mai riga/ Sutura da Gambo da Ayashe da Gwamma da Kyauta da Makwashi da Auta da sauransu.

    Sunayen Sifa: Irin waɗannan sunayen suna samuwa ne da dalilin sifar yaro. Kamar: Zabaya da Cindo da Cibi da Jatau da Kumatu Dodo da sauransu.

    Amma da addinin musulunci ya zo cikin rayuwarsu sai suka sauya sunayensu zuwa na addinin musulunci suma kuma sun kasu kamar haka sunayen Allah da na Annabawa da na Mala'iku da na Sahabbai da na Waliyyai da na Alƙur'ani da  sunaya daban daban da na Sha'awa.

    Sunayen Allah: Su ne sunayen da aka samu dalilin karɓa Musulunci kuma Hausawa a ko'ina a faɗin duniya suna sa wa yaransu su, sunayen sun haɗa da: Abdullahi da Abdurrahman Abdulkarim da Abdulhamid da sauransu.

    Sunayen Annabawa: Daga cikin sunayen Annabawa Hausawa sun sa wa yaransu su, wasu sun barsu yadda yake wasu kuma sun yi kwaskwarima, misali: Adamu ,Ado, Ada da Ibrahim, iro Yunus,yanusa Inusa Muhammad, Mamman,Na'Allah Na Ta'ala da sauransu

    Sunayen Matan Annabawa: Nana Khadijah, Hajo, Hadi, Dije. Nana Saudat, Saudi, saude. Nana Aisha, Ai, Shatu, Indo. da sauransu.

    Sunayen Mala'iku: Jibiril da Mika'i da Ridwan da sauransu.

    Sunayen Sahabbai: Abubakar da Umar da Usman da Aliyu da Bilal da Hamza da Jafar da Barira da Suwaiba da Sauransu.

    Sunayen Waliyyai: Sayuɗi da Hambali da Hanafi da Gazali da Shehu da Inyas da malik da sauransu.

    Sunayen daga Alƙur'ani: Suna ye ne da aka ci karo da su ciki Al'ƙur'ani irin su Lantana daga "Lantanalul birra" Falyata daga "Falyatana fa silmutana fisun" da Raihan/Raihanat dana "Walhabbu zul asfi war raihan" da Sauransu.

    Sunayen daga Abubuwa daban-daban: waɗannan sunayen sunaye masu naso na musulunci da dama waɗan da Hausawa ke la'akari da su wajen sanya wa lya'yansu kamar sunayen ranakun mako, irin su Jimma da Asshibi da Ladi da Tanin Balaraba da sauransu. Sunayen lokaci Kuma kamar Masalaci da Imam da Azumi da Hajiya ko Alhaji da Sunayen sha'awa kamar Aziza (Madaukakiya) da Aliya ( Mai girma) Kausar da Huda da Hamida da Fa'iza da Bushra da sauransu  Adam T.M (2015).

    Sunayen Sha'awa: mafi yawa Hausa lakabi suka fi yi wa yaransu da irin waɗannan sunayen misali: Aman da Aarif da farhan da Fu'ad da Mahir da sauransu. Anan Addinin Musulunci ya bada gagarumar gudummawa a sunayen 'ya''yan Hausawa.

    • Shayarwa:

    Shayarwa na nufin aikin ciyar da Jariri da nono kai tsaye daga nono Uwa. Hanya ce ta ɗabi'a ta samar da abinci mai muhimmanci da kariya ga jariri a farkon rayuwar. Nono na ƙunshe da abubuwan da jikin jariri ke buƙata wajen haɓaka girman yaro. Shayarwa na inganta haɗin gwiwa tsakanin uwa da yaro kuma tana da fa'idoji da yawa na koyon lafiya ga uwa da jaririnta.

    Addinin Musulunci ya zo da hukuncen hukunce game da  abin da ya shafi shayarwa da lokacin da ya dace a yaye yaro. Saɓanin abin da aka saba kafin musulunci ya nashe dukkan al'adun Hausawa ta kowane ɓangarorin rayuwa.

    Akwai ayoyi da hadissai da ke ɗauke da hukuncen hukunce da suka shafi shayarwa da yaye kamarhaka:

    والوالدت يرضعن اولدهن حولين كاملىن لمن اراد أن يتم الرالرضاعة  

    Kuma masu haihuwa (sakakku ) suna shayar da abin da suka haifa shekaru biyu cikakku ga wadda ta yi nufin cika shayarwa.(Sura ta 2 aya 233).

    ووصينا الإنسن بوالديه حملته ٱمه وهنا عل وهن وفصاله في عامين أنشكرلي ولوالديك الي المصير

     Kuma munyi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu (uwa da uba). Uwarsa ta ɗauke shi a cikin rauni akan wani rauni kuma yayensa a cikin shekaru biyu (Muka Ce Masa) Ka gode MINI da kuma Mahaifanka biyu makoma gare Ni kawai take. (Sura ta 21aya 41).

    Manzon Allah (S A W) ya ce " Nonon Uwa shi ne Mafificin Nono ga yaro, kuma a shayar da Yaro har ya Kai shekara biyu" ( Sahih Muslim).

    A wani hadisin kuma cewa ya yi, Annabi Muhammad (S A W) ya ce " Babu Nonon da ya fi na Uwa,

    Waɗannan ayoyi ne da hadisa da suku nuna yadda mace ke wahala game da ɗaukar ciki da kuma lakaci yaye.

    Haka kuma a lokacin shayarwar aiki biyu ta ke yi aikin shayarwa da ba da tarbiyya ga yaro ta fuskar umuni da hani akan koyarwar addinin musulunci kamar bashi nono da Bismillah da fara bashi na dama tun yana jariri daga nan har ya girma ta fara bashi abu ga hannun da umutar yaro yaci ya ya sha ya sa duk da hannun dama tare ya yin Bismillah yi wa yaro addu'ar safiya da ta yamma fara koyar da yaro addu'a idan ya fara magana haka dai za'a aza yaro a kan halaye da ɗabi'u da addini ya tana da. Bayan yaro ya kai lokacin yaye kuma akwai abubuwan da ake gudanarwa na al'ada da addini ya yi tasiri akai kama ana kan yi, ita ce al'adar ba dan yaye rubutu don kar ya yi rigima ana ba yaro rubutun daidai rigimar yaro in yaro bai da rigima sosai ba a bashi da yawa.

    A sha'anin haihuwa addinin musulunci ya yawo sauyi sosai da duk da al'ummar Hausawa suna da tsarin tafiyar da rayuwarsu daidai kaifin tunaninsu, kusan duk wani mataki da kula da mai ci al'adar Hausawa ta tanade shi, sai dai addini ya kore wasu ya tabbatar da wasu ya ƙara kyautata wasu.

    Kammalawa:

    Anga ma'anar haihuwa bayan bayanin buɗewa da muhimmancin haihuwa da tasiri Addinin Musulunci ga al'adun haihuwa tun daga shigar ciki har yaye.

    Manazarta:

    Adamu T. M ( 2015).  Haihuwa da Suna. Salma- A'aref Publishers Kano Nijeriya.

    Ibrahim A. S Sudan. Karan Kirjin Maguzawa. Sashen koyar da Al'adun Hausawa Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sokoto.

    Inno Shenu

    Raihanatu Umar Garba

    08100887109

    Aisha Hassan Hassan

    Fatima Yahya kamar

    Aisha Abubakar D/daji

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.