Tasirin Addinin Musulunci A Kan Sunayen Hausawa Na Gargajiya

    Takarda da aka gabatar a taron Æ™ara wa juna ilimi na É—alibai masu karatun Digiri na Uku (PhD) a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ÆŠanfodiyo, Sakkwato, Satumba, 04-09, 2023.

    UMAR MUHAMMAD

    +234 806 057 0930

    Tsakure

    MaÆ™asudin rubuta wannan takarda shi ne gano irin wainar da ake toyawa a kan tasirin addinin Musulunci kan sunayen Hausawa na gargajiya, kasancewar addinin Musulunci ya ratsa dukkanin É—angarorin rayuwar É—an Adam baki É—aya. Domin cimma nasarar wannan takarda, bayan gabatarwa an yi Æ™oÆ™arin gano su wane ne Hausawa? Kuma a ina suka fito? Sai kuma mu É—an yi ratse game da ma’anar addini da sunayen Hausawa na gargajiya na Bahaushe da kuma bayani kan addinin Musulunci, uwa-uba sai bakandamiyar aiki da ke nuna tasirin addinin Musulunci ga sunayen Hausawa na gargajiya kuma da ita ce aka naÉ—e wannan aikin.

    1.0 Gabatarwa

    Kasancewar addinin Musulunci shi ne addini na Allah MaÉ—aukakin Sarki mai kowa da komai da ya aiko Annabin rahama. Annabi Muhammad (S.A.W.) da shi ga dukkanin al’ummun duniya baki É—aya domin ya zama shiryarwa ga mutane bisa ga kyakkyawar hanyar bauta masa da gaskiya.

    Bisa ga wannan haƙƙin ne al’ummar Hausawa suka rungumi kiran nasa sau da Æ™afa har ya yi tasiri ta kowace irin rayuwa ta Bahaushe, kamar yadda ya yi tasiri ga sauran al’umma baki É—aya.

    Bisa wannan dalilin ne wannan bincike zai mai da hankali kan tasirin addinin Musulunci a kan sunayen Hausawa na gargajiya ta yadda wannan tasirin na addinin Musulunci ya fitowa Bahaushe da sunaye kyawawa nagartattu da suka Æ™ara fitowa da Æ™ima da darajar Bahaushe a matsayin mai addinin da Allah ya aiko Manzonsa Annabi Muhammad (S.A.W.) don musanya Bahaushe da sunansa na Æ™warai “Bahaushe” ba “Bamaguje” ba.

    2.0 Ƙasar Hausa Cikin Tarihi A Taƙaice

    Masana da manazarta sun tofa albarkacin bakinsu dangane da muhallin da ake kira ƙasar Hausa, amma zan taƙaita kan wasu daga cikinsu.

    Habib da wasu (1980:iv) sun ruwaito Adamu ya ce, ƙasar Hausa ta asali ta faro ne daga Lalle Asadu can Arewa-maso-Gabas da Agadas daga nan ne Gobirawa suka taso da kaɗan-kaɗan har suka iso inda suke a yau Nijeriya, a yanzu kuma Hausa tana yaɗuwa ne tana ƙoƙarin komawa har zuwa gidanta na jiya. Ƙarshen iyakar ƙasar Hausa a Kudu shi ne Yauri da Zaria da inda Bauchi ta yi iyaka da Kano.

    Garun Gabas (wato Birom) ita ce iyakar Æ™asar Hausa daga Gabas. A Yamma kuma Filinge, ya kuma Æ™ara da cewa, Æ™asar Hausa ita ce inda ba a buÆ™atar naÉ—a Sarkin Hausawa. Wato, wannan bayani ya ware duk wasu zango-zango inda ake Magana da Hausa. Dangane da yanayin Æ™asar Hausa kuwa, galibinta shimfiÉ—aÉ—É—iya ce, mai yawan sarari, akwai ta da tsaunuka da tuddai jifa-jifa kuma duk yawan wannan Æ™asa manyan koguna biyu suka ratsa a cikinta da Kogin Rima da Kogin HaÉ—eja, Kogin Kwara ya zama kamar iyaka daga Yammacin Æ™asa, Kogin Rima shi ne ya ratso daga Æ™asar Zamfara ya gangara ya yi Arewa zuwa Nijar sannan ya karkata Kudu ya bi ta Yamma da Sakkwato ya je ya faÉ—a cikin Kogin Kwara. Shi ma Kogin HaÉ—eja ya fara ne a Æ™asar kano daga nan ya gangara Gabas ya bi ta  Gashuwa da Gaidam ya je ya haÉ—e a Tafkin Chadi. Ƙasar Hausa tana da dazuzzuka iri biyu Sahel daga É—angaren Arewa, sai kuma Kudu akwai dajin Sabana. Haka kuma, yanayin shekara a Æ™asar iri biyu ne lokacin damina da rani, wato hunturu da zafi.

    2.1  Su Wane Ne Hausawa?

    Masana ilimin kimiyyar harshe da tarihi da adabi da al’ada sun tofa albarkacin bakinsu kan asalin su wane ne Hausawa?

    A ra’ayin wani masani, ya bayyana cewa Hausawa su ne waÉ—anda suke zaune a Æ™asar Hausa tuntuni, kuma suna magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa (Ibrahim, 1992:2). Wani masani kuma yana ganin Hausawa sun haÉ—a da mutanen nan waÉ—anda saboda Æ™aura da magabatansu suka yi daga Æ™asar Hausa zuwa wasu sassa da ke maÆ™wabtaka ta kusa ko ta nesa da Æ™asar Hausa, ko da kuwa ba sa magana da harshen Hausa ko yin al’adu ko abubuwan Hausawa, sun É—auke su Hausawa ne. Misali: Abakwariga da kuma wasu waÉ—anda suke iÆ™irarin su Hausawa ne da suke zaune shekaru da daÉ—ewa da suka gabata a Æ™asashen Cote de Voire da Burkina Fasa da Mali (Adamu, 1978:3).

    Akwai kuma waÉ—anda saboda zama cikin Æ™asar Hausa sun manta da harshensu da al’adunsu na asali, sun É—auki na Hausa a taÆ™aice. Sun koma Hausawa a harshe da al’ada da adabi. Misali: Kambarin Barebari da Barebarin Katsina da Buzaye (Sallau, 2007:71).

    Magaji (1986:33) ya bayyana Hausawa don su ne mutane waÉ—anda harshensu shi ne Hausa, sannan dukkan al’adunsu da tadodinsu na Hausawa ne. haka kuma, addinin Musulunci ya yi cikakken tasiri a kansu. Hausawa dai su ne mazauna Æ™asar Hausa tun asali, masu Magana da harshen Hausa, kuma ba su da wani harshe in ba Hausa ba. Idan suka saÉ—a haka, to barbarar yanyawa ne. (Bunza, 1990:12).

    A nawa ra’ayi, Hausawa su ne waÉ—anda Hausa ita ce harshensu na asali, ba su da wata Æ™asa in ba Æ™asar Hausa ba.

    3.0 Ma’anar Addini

    Safana (2010) ya fassara addini da cewa hanyar bautawa wani abu wanda mutum yake tsammani shi ne zai biya masa buƙatun rayuwar yau da kullum. Addinin farko da mutanen ƙasar Hausa shi ne addinin gargajiya, wato tsafi, ta hanyar bautar Iskoki ko mutanen ɗoye sai kuma takwarorinsa Bori da camfi. Irin wannan addini ya faru ne ta bin wasu hanyoyi da mutane suka ƙago wa kansu na bautar waɗansu abubuwa don cimma biyan buƙatunsu na rayuwa. Wannan hanyar bauta, ta daɗe ƙwarai da gaske a duk sassan duniya ba ƙasar Hausa kawai ba, har ma da sauran ƙasashen duniya baki ɗaya. (Safana, 2010).

    3.1  Addinin Hausawa Na Gargajiya Kafin Zuwan Musulunci Ƙasar Hausa

    Mafarin addinin gargajiya shi ne bautar gumaka, wato addinin gargajiya ya wanzu ne ta bin wasu hanyoyi da mutane suka Æ™ago wa kansu ta bautar waÉ—ansu abubuwa don cimma biyan buÆ™atunsu. Irin wannan hanyar bauta ta daÉ—e Æ™warai a duniya. Mutane da suka fara zama a duniya su suka Æ™ago ta, daga nan kuma abin ya zama al’ada ga sauran Æ™abilun da suka biyo bayansu. Da haka abin yana tafiya har ya zo kan Hausawa. Sai dai irin wannan addinin yawanci idan Allah MaÉ—aukakin Sarki ya aiko wani Annabinsa zuwa ga Æ™abilar da aka aiko shi, bayan an sha gwagwarmaya, sai ka ga ya yi sauÆ™i, amma da wuya a bar shi gaba É—aya ba tare da tasirinsa ya dinga bin wannan Æ™abilar ba (Muhammad, 1982).

    Al’ummar Hausawa na addininsu na gargajiya ne ta hanyoyi guda uku, tsafi, bori, camfi. Amma tsafi shi ne babban jigo kuma yana cikin hanyoyin bauta a cikin addinin gargajiya na Hausawa. Sai dai irin wannan bauta ba wani gunki ake sassaÆ™awa ana bauta masa ba. Amma da yake yanzu yawancin Hausawa duk sun shiga cikin addinin Musulunci, rayuwar waÉ—anda ba su shiga ba su ake kira Maguzawa, kuma su ne har yanzu suke bin wannan addini. Ta hanyar tsafi Maguzawa sukan bauta wa wani aljani, wanda yawanci sukan ce yana zaune a kan wani dutse ko a kogon wata bishiya, tsamiya ko kuka. Haka kuma, kowane tsafi a kan sami wani mutum wanda yakan zama mai kula da shi. A taÆ™aice dai, addinin gargajiya kafin shigowar Musulunci shi ne ya shafi tsafi, bori da kuma camfi (Muhammad, 1982).

    3.2 Sunayen Hausawa Na Gargajiya Kafin Zuwan Musulunci

    Wannan É—angaren zan É—an waiga baya ne kawai mu ga sunayen Hausawa na gargajiya a al’adar Bahaushe kafin zuwan Musulunci. Hausawa a gargajiyance, yawanci sukan dubi lokacin da aka yi haihuwa ko halin da aka yi haihuwa ko yanayi su samo sunan, daga nan su sanya wa abin haihuwa.

    Haka kuma, yawancin Hausawa sukan sami sunaye iri biyu: sunan yanka da na kakanni, amma kusan dukkaninsu iri É—aya ne kuma ta hanya É—aya ake samunsu. Ga kaÉ—an daga cikin sunayen Hausawa (Maguzawa) kamar haka:

    1.      Sammako – yaron da aka haifa da sassafe

    2.      Ranau – yaron da aka haifa da rana idan mace ce ta-rana

    3.      Na-hantsi – yaron da aka haifa da hantsi

    4.      Dare ko ÆŠandare – yaron da aka haifa da dare

    5.      Shuka/Shukkau – yaron da aka haifa lokacin shuka

    6.      Nomau – yaron da aka haifa ana noma

    7.      Damina/Damana – yaron da aka haifa da damina

    8.      Malka – yaron da aka haifa lokacin tsululin ruwa

    9.      Anaruwa – yaron da aka haifa lokacin tsululin ruwa

    10.   Ci-gero/Maigero – yaron da aka haifa lokacin cin sabon gero

    11.   Ci-wake/Roro – yaron da aka haifa lokacin cin wake

    12.   Æ˜osau – yaron da aka haifa lokacin Æ™oshi

    13.   Wadata – yaron da aka haifa lokacin wadata

    14.   ÆŠari/TaÉ—ari – yaro ko yarinyar da aka haifa lokacin É—ari

    15.   Kaka/ÆŠankaka – yaron da aka haifa lokacin kaka

    16.   Maidamma – yaron da aka haifa ana É—aura damman hatsi

    17.   Ajuji/Ayas/Ayashe – yaro ko yarinyar da aka haifa bayan an yi ta haihuwa suna mutuwa (ana wabi).

    18.   Mairiga – yarinyar da aka haifa da rigar haihuwa (ta fito cikin yanar rigar haihuwa).

    19.   Shekarau – yaron da ya shekara a cikin ciki

    20.   Tanko/Namata/Mati – yaron da aka haifa bayan haihuwar mata

    21.   Magawata – yaron da aka haifa bayan wata ya tsaya

    22.   Gagarau – yaron da aka haifa bayan an yi Æ™oÆ™arin zubar da cikinsa abu ya gagara.

    23.   Mantau – yaron da ya daÉ—e a ciki kafin a haife shi

    24.   Cindo//Mai Cindo – yaron da aka haifa da yatsu shida

    25.   Cibi/Maicibi – yaron da aka haifa da cibi

    26.   Kanta – yaron da aka haifa tare da mace

    27.   Auta – yaro ko yarinyar da aka haifa a Æ™arshen haihuwa

    28.   Maigiya – yaro ko yarinyar da aka haifa ana dafa giya

    29.  Malka – yarinyar da aka ana tsuga ruwa

    30.   Kande/Dela/Deluwa/Barauki/Ige – yarinyar da aka haifa bayan an haifi maza da yawa.

    31.   Kumatu – yarinyar da aka haifa da kaurin kumatu

    KaÉ—an ke nan daga cikin sunayen Hausawa na gargajiya da suke ambaton ‘ya’yansu kafin Musulunci. Hausawa sun ci gaba da amfani da waÉ—annan sunaye ko bayan shigowar Musulunci domin kuwa kusan dukkanin sunayen ba su da wata alaÆ™a da Musulunci.

    4.0 Addinin Musulunci

    A wannan gaÉ—a, ya kamata a yi É—an bayani a taÆ™aice dangane da ma’anar Musulunci.

    Gusau (1999: 1) ya ce, “Addinin Musulunci shi ne addinin da Allah mai girma da É—aukaka ya aiko Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da shi domin ya shiryar da mutane zuwa ga kyakkyawanr hanyar bauta Masa. Da wannan, mun tabbatar cewa shi Musulunci addini ne da ya zo daga Allah kuma ya wanzu ta hanyar Annabi Muhammad (S.A.W.). Haka kuma, shi addini bai nuna wata wariya a cikin al’umma ba, wai ko don kana shugaba, amma ya yi tanadi a yi wa shugaba É—a’a gwargwadon hali, in dai bai kauce wa shari’ar  Musulunci ba.

    Gusau (1991:2) ya ƙara da cewa Musulunci shi ne gaskatawa da miƙa wuya zuwa ga abin da Manzon Allah (S.A.W.) ya zo da shi daga wurin Allah Subhanahu wata ala, sannan da aiki da shi.

    4.1  Tasirin Addinin Musulunci Ga Sunayen Hausawa Na Gargajiya

    Kafin mu tsunduma ga wannan bakandamiyar aiki wato tasirin addinin Musulunci ga sunayen Hausawa na gargajiya, kamata ya yi mu san kalmar ‘tasiri’ ita kanta.

    Tahar (1990) ya bayyana tasiri da cewa karÉ—uwa da amincewa kuma da mamaye kowace irin harka da ta shafi rayuwar wasu jama’a, Wasagu (2002) ya fassara kalmar tasiri da nufin sauyin da ake samu a cikin wani abu dalilin wani abu.

    Bayan addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa ya yi ƙarfi da tasiri ga kowane ɗangaren rayuwar Bahaushe, sai ya zama sunayen da Bahaushe yake amfani da su a gargajiyance idan an yi masa haihuwa suka ƙara yawa, har suka sauya zuwa ga sunayen Musulunci.

    Ga dai sunayen manyan bayin Allah kamar Annabawa da Sahabbai da mutanen kirki (waliyyai) da ma matansu da na ‘ya’yansu. Ga kuma sunayen Mala’iku da suke sa wa yaransu. Duk waÉ—annan sunayen suna sa musu ne don neman albarka. Ban da waÉ—annan kuma, Hausawa sun ci gaba da amfani da sunayen gargajiya irin na asali don yi wa yaro laÆ™abi. Wato, a taÆ™aice dai, idan an haifi yaro a ranar suna za a sa masa suna wanda zai zama ko sunan Annabi ko na Sahabi ko na mutanen kirki (waliyyai) ko na Mala’iku ko kuma in  mace ce, a sanya mata sunan matar wani Annabi ko ‘yarsa ko matar Sahabi ko ‘yarsa, to bayan wannan suna kuma, sai a sami sunan gargajiya wanda yawanci kakanni ko waÉ—anda ba za  su faÉ—i  sunan ba, saboda kunya irin ta al’adar Hausawa za su sa wa yaro ko yarinya shi. Ga misalan sunayen yanka na Hausawa kamar haka:

    Muhammadu, amma saboda suna son sunansa da yawa, mutum É—aya yakan iya sa wa ‘ya’yansa maza goma (10) duk sunan “Muhammadu” sai dai zai bambanta a cikin Larabci ya ce Muhammadu na É—aya ko na biyu ko na uku har zuwa na goma (10). Misali:

    1.      Muhammadu Auwalu

    2.      Muhammadu Sani

    3.      Muhammadu Salisu

    4.      Muhammadu Rabi’u

    5.      Muhammadu Hamisu

    6.      Muhammadu Sadisu

    7.      Muhammadu Sabi’u

    8.      Muhammadu Saminu

    9.      Muhammadu Tasi’u

    10.  Muhammadu Ashiru

    Sauran sunayen Annabawa da Hausawa kan sa wa ‘ya’yansu su ne:

    1.      Adamu

    2.      Nuhu

    3.      Idrisu

    4.      Salihu

    5.      Hudu

    6.      Ibrahim

    7.      Yakubu

    8.      Isma’ila

    9.      Yusuf

    10.   Yusha’u

    11.   Iliyasu

    12.   Yahaya

    13.   Zakariya’u

    14.   Dawuda

    15.   Suleiman

    16.   Musa

    17.   Isa da sauransu.

    Sannan sukan sanya sunayen Sahabbai kamar:

    1.      Abubakar

    2.      Umaru

    3.      Usmanu

    4.      Aliyu

    5.      Abbas

    6.      Zubairu

    7.      Sa’adu

    8.      Abdullahi

    9.      Abdurarrahman da sauransu.

    A cikin sunayen Waliyyai kuma, sun fi sa sunayen:

    1.      AbdulÆ™adir

    2.      Ahmadu Tijjani (ruwayar ‘yan É—ariÆ™a ce)

    3.      Ahmadu Rufa’i

    4.      Usmanu da sauransu.

    A cikin mata kuma, sukan sa:

    1.      Aminatu

    2.      FaÉ—imatu

    3.      Maryamu

    4.      Ummul Kulsumi

    5.      Zainabu

    6.      RuÆ™ayyatu

    7.      Hindu

    8.      Hindatu

    9.      Habibatu

    10.   Maimunatu

    11.   Halimatu da sauransu.

    A cikin Mala’iku kuma sukan sa:

    1.      Jibrilu

    2.      Mika’ilu

    3.      Ridwanu

    4.      Maliki

    Daga cikin waÉ—annan sunaye akwai waÉ—anda Hausawa suke faÉ—arsu daidai, kamar yadda suke a cikin littafi, akwai kuma waÉ—anda suke jirkitawa. Misalin waÉ—anda suke faÉ—a daidai su ne:

    1.      Hudu

    2.      Nuhu

    3.      Musa

    4.      Isah

    5.      Hindu

    6.      Asama’u

    Misalin sunayen da suke jirkitawa su ne:

    1.      Adamu – Ado

    2.      Idrisu – idi

    3.      Salihu – Sale

    4.      Ibrahim – Iro, Ibran, Buraima, Ibro, Ibra

    5.      Zakariya’u – Zakari, Ya’u

    6.      Abubakar – Abu, Habu

    7.      Abdullahi – Audu, Abdu

    Abdurrahman da sauransu

    8.      Zainabu – Abu

    9.      Hadijatu – Dije, Dija, Dijama

    10.   Maimunatu –  Maimuna, Munari, Muna

    11.   Rukayya – Rakiya, Ruke

    Haka kuma har wa yau, bayan zuwan Musulnci, an sami sunayen da ake sa wa ‘yan tagwaye (’yan biyu) kamar haka:

    Al-Hassan – Na littafi

    Alasan  – sunan É—an tagwayen da aka fara haihuwa namiji

    Hassan – yadda Hausawa kan faÉ—a

    Al-Hussaini – na littafi

    Usaifi – na Hausa

    Alhassanatu – na littafi

    Hasana – na Hausa

    Alhasanatu  – na littafi

    Usaina – ‘yar tagwayen da aka haifa daga É—angaren mace.

    Dangane da sunayen gargajiya kuma Hausawa sun ci gaba da amfani da sunaye na da, amma ban da irinsu Maigiya da Shagiya da Ramau da Taroro, waɗannan sai Maguzawa kawai suke amfani da su. Haka kuma, Musulunci ya sa Hausawa sun ƙara ƙago waɗansu sababbin sunaye irin na gargajiya. Ga misalin irin sunayen da Hausawa suke amfani da su bayan Musulunci a matsayin sunayen kakanni, ko sunayen rana kamar haka:

    1.      Dogara (Na dogara ga Allah)

    2.      Alabura (Allah ya bari)

    3.      Nabara (Na bar wa Allah)

    4.      Dangana (Na dangana ga Allah)

    5.      Bawa (Bawan Allah)

    6.      Barmini (Allah ya bar mini)

    Sunayen yara maza da aka haifa bayan an yi ta haihuwa suna mutuwa (‘yan wabi).

    1.      Sadau     – yaron ko yarinya da aka haifa bayan mace ta koma É—akin mijinta.

    2.      Sodangi – Yaro ko yarinyar da aka haifa bayan iyayensa sun dawo cikin dangi, ko a lokacin da dangi suka taru don yin wani sha’ani.

    3.      Korau   – yaron da aka sa wa sunan wani mutum, amma ba a daÉ—e ba sai mutumin ya mutu.

    4.      Wada/Dawada/Maiwada/ÆŠanyalwa – yaron da aka haife shi lokacin wadata ko kuma wanda iyayensa suka sami wadata bayan haihuwarsa.

    5.      Tawada/Yalwa/goshi – yarinyar da aka haifa lokacin wadata ko kuma aka sami wadata bayan haihuwarta.

    6.      MaikuÉ—i – yaro ko yarinyar da iyaye suka sami kuÉ—i ranar haihuwarta, ko kuma waÉ—anda aka haifa ranar Talata.

    7.      Sallau/Nasalla/Maisalla/Tasalla/Tasalluwa – yarinya ko yaron da aka haifa lokacin salla.

    8.      Labaran/ÆŠanazumi/Azumi – yarinyar da aka haifa a watan azumin watan Ramalana.

    9.      Ladan/Maisalla/Mai salati – yaron da aka haifa lokacin da ladan yake kiran salla.

    10.   Gambo – yaro ko yarinyar da aka haifa bayan haihuwar ‘yan tagwaye.

    11.   Kadarko – yaro ko yarinyar da aka haifa a tsakanin haihuwar ‘yan tagwaye.

    12.   Gwamma (Gwamma ita da babu) Hakama (Haka ma ina so) – yarinyar da aka haifa bayan an sa ran haihuwar namiji.

    13.   Bakuso –  yaro ko yarinyar da aka haifa bayan an saki uwarsa ko uwarta.

    14.  Yawale – yaron da aka haifa a hanyar zuwa Makka.

    15.   Yabi – yarinyar da aka haifa a hanyar zuwa Makka.

    16.   Talle – (Tallafin marayun Allah) – yaro ko yarinyar da uwarsa ta mutu a wurin haihuwarsa ko bayan haihuwarsa kaÉ—an.

    17.   Alhaji/Baita – yaron da aka haife shi a lokacin shagalin salla babba.

    18.   Hajiya/Kyauta (kyautar Allah) – yaro ko yarinyar da aka haifa bayan uwarsa ko ubansa sun fitar da rai da samun haihuwa.

    19.   Tunau/ÆŠantune – yaron da aka haifa bayan uwarsa ko ubansa sun fitar da rai za su kuma samu haihuwa.

    20.   Tune – yarinyar da aka haifa bayan uwarsa ko ubanta sun fitar da rai za su kuma samun haihuwa.

    21.   Makwashi – yaron da bora ta haifa.

    22.   Kilishi – yaro ko yarinyar da aka haifa bayan an ci sarauta.

    23.   Dawai – yaron da aka haifa bayan kome (mace ta dawo É—akin mijinta).

    24.   Dawo – yarinyar da aka haifa bayan kome.

    25.   Sharubutu – yaro ko yarinyar da uwarsa ta sha rubutu da yawa kafin ta haife shi.

    26.   Sutura/Mairiga – yarinyar da aka haifa da rigar haihuwa.

    Sunayen Ranakun Mako

    Kafin zuwan Musulunci kusan in ban da su “yau, gobe, jibi, citta, jiya da shekaranjiya Hausawa basu da sunayen ranaku, sai dai su kira kowace rana da sunan garin da kasuwarsa take ci a wannan rana. Misali, ranar ÆŠanbatta, ranar Ma’aduwa, ranar Bakori, ranar MaÆ™arfi da sauransu. Da Musulunci ya zo, sai ya kawo musu sunayen ranakun mako kamar:

    1.      Assibit  – Asabar

    2.      Al-Ahd  – Lahadi

    3.      Al-thnain  – Litinin

    4.      Al-thulatha’a – Talata

    5.      Al-Arba’a   – Laraba

    6.      Al-Khamis   – Alhamis

    7.      Al-juma’at – Juma’a

    Daga waɗannan sunaye ne Hausawa suka ƙago sunayen da za su sa wa yaron da aka haifa a waɗannan ranaku kamar haka:

    1.      ÆŠanasabe/ÆŠan’asibi – yaron da aka haifa ranar Asabar.

    2.      ÆŠanladi/Lado/Nalado – sunayen yara maza da aka haifa ranar Lahadi.

    3.      Ladi/Ladidi/Ladingo/Ladigo – sunayen yara mata da aka haifa ranar Lahadi.

    4.      ÆŠanliti/ÆŠantani/Liti – sunayen yara maza da aka haifa ranar Linitin.

    5.      Tanin/Liti – sunayen yara mata da aka haifa ranar Linitin.

    6.       ÆŠantala/ÆŠantata/tatu/Maitala/Maitalata – sunayen yara maza da aka haifa ranar Talata.

    7.      Talatuwa/Talatu/Tatu/Lantu – sunayen yara mata da aka haifa ranar Talata.

    8.      Bala/Balarabe/ÆŠanbala/ÆŠanlarai – sunayen yara maza da aka haifa ranar Laraba.

    9.      Larai/Balaraba/Laraba/Balarabiya/Tabawa – sunayen yara mata da aka haifa ranar Laraba.

    10.   ÆŠanlami/Na Lami – sunayen yara maza da aka haifa ranar Alhamis.

    11.  Lami/Laminde/Lamisuwa – sunayen yara mata da aka haifa ranar Alhamis.

    12.   Jume/Jumare/Wajume/ÆŠanjuma/ÆŠanjimmai/Na-Jimmai – sunayen yara maza da aka haifa ranar Jumu’a.

    13.   Juma/Jummai/Aljumma – sunayen yara mata da aka haifa ranar Jumu’a.

    Gwargwadon hali, waɗannan su ne misalan sunayen da ake kiran Hausawa da su bayan shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa da suka danganci ranakun mako.

    5.0 NaÉ—ewa

    Tun kafin bayyanar addinin Musulunci a Æ™asar Hausa. Al’ummar Hausawa suna da sunayen da suke sanyawa ‘ya’yansu ta hanyar dubin lokaci da yanayi ko halin da aka yi haihuwar ko dai wani dalili na daban, su sanya wa abin haihuwar suna. Da addinin Musulunci ya shigo Æ™asar Hausa, sai ya sauya waÉ—annan sunayen na Maguzanci zuwa na Musulunci ta hanyar inganta su da Æ™ara masu yawa kan tsarin koyarwarsa. Kan haka, wannan bincike mai taken “Tasirin Addinin Musulunci Kan Sunayen Hausawa na Gargajiya” ya cimma burinsa gwargwado, ya yi Æ™oÆ™arin sanin al’ummar Hausawa da Æ™asarsu, sai kuma taÆ™aita bayani kan addinin Hausawa na gargajiya, da na Musulunci da kuma kawo sunayen Hausawa na gargajiya gwargwadon hali. Sai kuma uwa-uba hasashen aikin da ya shafi tasirin addinin Musulunci kan sunayen Hausawa na gargajiya inda binciken ya zayyana su dalla-dalla tare da misalai ingantattu.

    Sakamakon Bincike

    Bayan gabatar da Æ™umshiyar wannan bincike a taÆ™aice, ba zan naÉ—e wannan ‘yar takarda ba, sai na É—an yi tsokaci kan wasu abubuwa da wannan binciken ya gano kamar haka:

    1.      Binciken ya yi Æ™oÆ™arin gano tasirin addinin Musulunci kan sunayen Hausawa na gargajiya ta fuskoki da dama.

    2.      Binciken ya kuma yi Æ™oÆ™arin gano dangantakar al’ummar Hausawa da Larabawa da ma sauran maÆ™wabta malamai wanda dalilin su ne Bahaushe ya karÉ—i Musulunci har ya sauya suna daga “Bamaguje” zuwa “Bahaushe”.

    3.      Haka kuma, dalilin addinin Musulunci ya sauya sunayen Bahaushe na haihuwa ta la’akari da lokaci da yanayi da rana, ya ba shi sunayen Musulunci ta É—angarori daban-daban.

    4.      Binciken ya waiwayi sunayen Bahaushe na gargajiya ya kwatanta su da na shi, ya É—ebe tsaki da tsakuwa ya fitar da gari don ya gyara wasu sunaye ya daidaita su da na shi, ya zubar da na zubar wa irin sunan “Shagiya” da “Kumatu” da sauransu.

    Manazarta

    Alti, K.M. (2012). “Wasu Dabarun Gargajiya na Kawar da Talauci A Birnin Katsina. Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa). Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu ÆŠanfodiyo.

    Amfani, A.H. (2011). “Hausa da Hausawa da Kuma Ƙasar Hausa Jiya Da Yau”Takardar Da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani, Assembly Hall Ahmadu Bello University, Main Campus Zaria, Kaduna State.

    Aliyu, A.Y. (1973). “Asalin Hausa” A Cikin Littafin Makon Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.

    Augie, A.R. Da Wasu (1991). Nazari a Kan Tarihin Al’ummar Ƙasar Zuru Gabanin Kafa Mulkin Mallaka Na Turawa. Ƙungiyar Raya Ci Gaban Ƙasar Zuru (ZED).

    Bunza, A.M. (1990). “HayaÆ™i Fidda Na Kogo: Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa”. Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa) Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

    Bunza, A.M. (2008). “Gadon FeÉ—e Al’ada”. Jerin Littafan Cibiyar Nazarin Al’adun Hausawa, Lagos: Tiwal.

    Bunza, A.M. (1995). “Magungunan Hausa a Rubuce: Nazarin Ayyukan Malamin Tsibbu”. Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa) Juzu’i na ÆŠaya. Kano: Jami’ar Bayero.

    Gobir, Y.A. (2002). “Iskoki a Idon ‘yan Bori da Masu RuÆ™iyya”. Kundin Digiri na Biyu (M.A.Hausa) Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu ÆŠanfodiyo.

    Gobir, Y.A. (2013). Tasirin Iskoki Ga Cutuka da Magungunan Hausawa. Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa) Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu ÆŠanfodiyo.

    Gobir, Y.A. (2023). Laccar Kwas Hau: 933 Mai Taken. “Hausa Culture and Islam” Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu ÆŠanfodiyo.

    Ibrahim, Y.Y. da Wasu (1986). “Jagoran Nazarin Hausa”. Northern Nigeria Publishin Company Zaria.

    Magaji, A. (1989). “Gudummuwa a Kan ƘoÆ™arin da Ake Yi Na Samar Da Cikakken Tarihin Hausawa da Harshensu” MaÆ™ala, Kano: Takardar da Aka Gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Magaji, A. (2002). “Wasu Al’adun Hausawa da Yanaye-Yanayensu a Ƙasar Hausa”. Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa) Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci. Kano: Jami’ar Bayero.

    Nafisa, M.G. (2014). “Kutsen BaÆ™in Al’adu Cikin Hidimar Aure a Sakkwato” (M.A. Hausa) Kundin Digri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu ÆŠanfodiyo.

    Sama’ila, A.K. (2019). “Al’adun da Addinin Musulunci ya hana Aikatawa, Kuma Ake yi a Wasu Masarautun Ƙasar Hausa”, Takardar da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani, Kwalejin Share Fage da Karatu Mai Zurfi Yelwa-Yauri.

    Safana, B.Y. (2001). Maguzawa Lezumawan (Babban kada) Gudummuwar Safana a Jihar Katsina. Kundin Digiri na Farko (B.A. Hausa) Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu ÆŠanfodiyo.

    Sallau, B.A.S. (2009). “Sana’ar Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani Jiya da Yau”. Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa) Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

    Tahar, M.A. (1990). “Siddabaru a Ƙasar Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa”. Kundin Digiri na Biyu. (M.A. Hausa). Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

    Tukur, A. (2015). “Sana’ar SaÆ™a a Ƙasar Hausa”. Kundin Digiri na Farko. Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

    Umar, M. (2015). “Zumuntar Tsafe-Tsafen Hausawa da Dakarkari (M.A. Hausa). Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu ÆŠanfodiyo.

    Umar, M. (2017). “Tasirin Zuwan Turawa Æ™asar Hausa”. Takardar Da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Ilimi. Kwalejin Share Fade Da Ilimi Mai Zurfi Yelwa-Yauri.

    Wushishi, B.J. (1998). “Dangantakar Magani Da Wasu Sana’o’in Hausawa Na Gargajiya”. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu ÆŠanfodiyo.

    Waziri, M. (2013). “Tasirin Sarautun Hausawa a kan Ƙabilar Kare-Kare da Sayawa”. Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa). Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu ÆŠanfodiyo.

    Zaruma, (1983). A Culture Magazine of Sokoto State.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.