Takarda da aka gabatar a taron ƙara wa juna ilimi na Ɗalibai masu karatun Digiri na Uku (PhD) a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, Satumba 04-09, 2023
Dalhatu Abubakar Zauro
+234 803 594 8260
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, Nigeria
Tsakure
Hausawa sun karfi addinin musulunci har suka fara maye
gurbin wasu al’adunsu da shi. Binciken ya gano addinin musulunci ya sauya
rayuwar mafi yawan Hausawa wajen canza al’adunsu na haihuwa don su yi daidai da
koyarwar addinin musulunci. An yi amfani da hanyoyin bincike na ayyukkan da aka
wallafa da waɗanda ba a wallafa ba. An kuma yi hira da malaman addini
da leƙa yanar gizo an kalato muhimman ayyukkan da ke da
muhimmanci. Takardar ta yi nasarar fitowa da tasirin addinin musulunci ga al’adun
haihuwar Hausawa guda goma sha uku (13).
Fitilun kalmomi: Al’ada, Haihuwa, Musulunci
1.0 Shimfiɗa
Kalmar haihuwa ta
samo asali ne daga uwa. Fitar wani rai daga cikin wani rai shi ake kira da
haihuwa. Ana haihuwa ko aihuwa ne bayan an yi aure. Hausawa kan ce “haihuwa
‘yar dangi”, ba dan ke ba da iri ya ƙare. Kowace al’umma
ta Hausawa tana da nata al’adu da suka bambanta daga wuri zuwa wuri dangane da
abin da ya shafi haihuwa. Wannan yana nufin al’adun da ake samu tun daga ɗaukar ciki har zuwa
yaye yaro ko yarinya. Ɓatan wata yana daya daga cikin alamomin da ake iya gane
mace ta sami ciki ko juna biyu kamar yadda ake kiransa. Haka kuma idan mace ta
sami ciki akan ganta tana yawan zubar yawu, ko harassuwa (Amai) da yawan kwana
da kwaɗayi. Duk waɗannan akan fassara su
da cewa mace ta sami ciki.
Idan mace ta sami ciki, iyayenta ko wasu nata
za su shiga kula da ita, da nema mata taimako don ta sauka lafiya. Za a kafa
mata wasu sharuɗɗa dangane da abin da
za ta ci. Haka kuma ba za a bari ta yi
wani abu da zai taɓi lafiyar jikinta ba.
Wasu na riƙe da al’adar idan ciki ya kai wata bakwai yarinya za ta
tafi gidansu, don ta haihu can. Wannan al’adar ake kira da goyon ciki.
Inda duk aka yi
haihuwa, akwai waɗansu zaunannun
al’adun da Hausawa ke gudanarwa da suka haɗa da:
·
Goyon ciki
·
Kayan ƙauri
·
Zanen suna
·
Jego
·
Gara
·
Reno
·
Yaye
·
Kaciya
da sauransu
A sakamakon shaƙuwa da
al’ummar Hausawa suka yi da addinin musulunci kuma musuluncin ya same su da
nasu al’adun da suka gada kaka da kakanni. Wannan bai hana su yin watsi da
dukkanin al’adun da suka saɓa koyarwar addininsu. Aikin zai yi ƙoƙarin
lalabo wasu daga cikin al’adun Hausawa da musulunci ya yi tasiri a kansu. Amma,
kafin nan zan soma da kawo taƙaitaccen
tarihin ƙasar Hausa da Hausawa da fayyace abin da ake nufi da
al’ada a mahangar masana, sai ƙarin haske kan
taƙaitaccen tarihin shigowar musulunci a ƙasar
Hausa.
1.1 Taƙaitaccen Tarihin Ƙasar Hausa da Hausawa
Ƙasar
Hausa tana daga cikin Nahiyar Afirka, a ɓangaren Afirka ta yamma, tsakanin Hamadar
sahara da dazuzzukan da ke gaɓar tekun Atalantika kuma ana kiran ƙasar Hausa da suna
Sudan ta yamma. Ƙasar Hausa wata farfajiya ce mai yalwar gaske wadda take
a shimfiɗe, tare da samun
gulabe da duwatsu da tsaunuka suka ratsa ta jifa-jifa. Ita wannan ƙasa ta ƙunshi garuruwa da
birane manya da ƙanana da suka haɗa da Daura da Gobir da Zazzau da Rano da
Garun gabas da Gaya da sauransu. Harshen Hausa shi ne wanda suke amfani da shi,
kuma shi ne babban jigo wanda ya haɗa dangantaka da kusanci tsakanin waɗannan garuruwa, sai
kuma harkokin kasuwanci da ciniki da saye da sayarwa. Mazauna ƙasar Hausa, kamar
sauran ƙabilun duniya, suna da fitattun al’adunsu da suka samo
tushe da asali tun ran gini, ran zane. Wasu daga cikin al’adun suna tattare da
bukukuwa da ake aiwatarwa don daɗa bayyana armashi.
Hausawa suna ganin
kansu ƙabila ne. Amma, Shaihin Malami Adamu Ngaski (1976) ya
bayyana Bahaushe da cewa mutumin da aka haifa ƙasar Hausa iyayensa
Hausawa ne, kakanninsa Hausawa ne, abincinsa da tufafinsa da mu’amalarsa duk
dai na Hausawa ne. Kuma ko da ɗan wata ƙabila ne in dai ya tashi da harshensa
na farko Hausa ne, to ya zama Bahaushe. Wato, haifaffen mai magana da harshen
Hausa da rayuwa irin ta Hausawa.
Bunza, (2006) cewa ya
yi “Hausawa dai mutane ne da suke zaune a ƙasar Hausa tun farko
sa’annan suna zuriya a cikinta har zuwa yau, kuma suna magana da harshen Hausa,
ba su da wani harshe in ba Hausa ba, duk al’adu da ɗabi’unsu irin na
Hausawa ne.
Shi kuwa Ahmed,
(1992) yana ganin “Hausawa mutane ne waɗanda harshensu shi ne Hausa, sa’annan
dukkanin al’adunsu da ɗabi’unsu na Hausawa ne, haka kuma addinin musulunci ya
yi cikakken tasiri a kansa”.
1.2 Ma’anar Al’ada
Ita dai Kalmar
“Al’ada” Balarabiyar kalma ce. Ma’ana daga harshen Larabci aka aro ta inda take
nufin abin da aka saba da shi. A lokacin da Hausawa suka aro ta sai suka bata
wata ma’ana ta daban. Don haka masana da dama sun kalli kalmar kuma sun bata
ma’ana daban-daban gwargwadon fahimtarsu. Alal misali:
Bunza, A. M. (2006)
ya ce “Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗan Adam tun daga haihuwarsa har zuwa
kabarinsa. A ko’ina mutum ya sami kansa duk wata ɗabi’a da ya tashi da ita tun farkon
rayuwa ya tarar a wurin da ya rayu, ko yake rayuwa, ita ce al’adarsa da za a yi
masa hukunci a kai. Babu wata al’umma da za ta rayu a doron ƙasa face tana da
al’adar da take bi, kuma da ita ake rarrabe ta da wata da ba ita ba”.
A ganin wasu masana,
Al’ada tana nufin tarsashin rayuwar mutane da abubuwan da rayuwa ta ƙunsa baki ɗaya. A taƙaice, abubuwan rayuwa
sun haɗa da:
i. Harshe iv. Mutuwa
ii. Addiniiiv.
Ƙawa
iii. Bukukuwaiiiv.
Sana’o’i
iv. Aure
v. Siyasa
v. Haihuwa
x. Rayuwar yau da gobe.
1.3 Taƙaitaccen Tarihin Shigowar Musulunci a Ƙasar Hausa
Addinin Musulunci shi ne miƙa wuya ga Allah
(S.W.T) baki ɗaya tare da kaɗaita shi da kuma
dogaro gare shi da yi masa ɗa’a da kuma tsarkake shi daga shirka. Addinin Musulunci
shi ne addinin da Allah Maɗaukakin Sarki ya aiko Annabi Muhammadu (S.A.W.) da shi
zuwa ga bayinsa a duniya baki ɗaya. (Bunza 2006).
Shika-shikan
Musulunci su ne: Shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu (S.A.W.) Ma’aikin Allah ne,
tsai da sallah da ba da zakka sai kuma ziyarar ɗakin ka’aba a Makka domin aikin hajji
ga mai iko. Ana samun wannan a zuciya da kuma aikace ga kowane ne, to, nan take
sunansa yake rikiɗa ya zama Musulmi. Kuma
ya zama ana ƙirga shi a cikin al’ummar Musulmi.
Yana da
wuya a tantance lokacin da addinin musulunci ya shigo cikin al’ummar Hausawa.
Amma, a ƙalla za a iya cewa lalle kafin ƙarni na goma sha ɗaya akwai musulmi da
kuma al’adun addinin musulunci a harkokin al’ummar Hausawa.
Haka
nan kuma an tabbatar da cewa akwai hanyoyi biyu da addinin musulunci ya shigo
cikin wannan ƙasa.
Hanyar
farko ita ce wadda kusan dukkan masana tarihi suka yarda da ita wannan hanya
kuwa ita ce ta hulɗar cinikayya tsakanin
ƙasashen
Afirka ta yamma da ƙasashen Afirka ta Arewa wanda ake kira da suna Magrib.
Hausawa na cikin irin al’ummomin da suka shahara wajen wannan harka ta
cinikayya. Masana tarihi sukan yi bayanin lawalan nan da suka haɗa Afirka ta Arewa da
ta yamma. Dalilin wannan hulɗa ne aka samu cuɗanya tsakanin Larabawa musulmi da kuma
Hausawa matsafarta. Wannan cuɗanya kuwa ita ta
haddasa Hausawa suka karɓi musulunci da kuma
kawo shi ƙasar Hausa.
Hanya
ta biyu kuwa ita ce wadda baƙi musulmi suka yi ɗawainiyar yaɗa addinin musulunci.
Waɗannan baƙi kuwa su ne
Wangarawa.
Da
farko dai sun iso ƙasar Hausa cikin ƙarni na goma sha huɗu ƙarƙashin jagorancin
Shaykh Abdur Rahman Zaite. Wannan shugaban Wangarawa ya fito daga Mali ne da
niyyar zuwa aikin hajji tare da jama’arsa waɗanda a ƙalla sun haura mutum
dubu uku.
Wasunsu
sun zauna ƙasar Gobir wasunsu kuma ƙasar Azben, sannan
wasunsu sun barbazu Katsina da ƙasashenta da kuma Kano da ƙasashenta.
A duk
waɗannan garuruwa da
suka zauna sun fi yin hulɗa da Sarakunan waɗannan garuruwa.Watau,
sun fara musuluntar da Sarakunan, sannan su kuma Sarakunan suka musuluntar da
mutanensu. Misali a Kano Wangarawan sun iso lokacin Sarki Yaji ne. yayin da
suka musuluntar da shi Sarkin shi kuma ya umurci mutanensa da su rungumi
addinin musuluncin. Ya tsayar masu da salloli biyar na kowace rana. Haka nan suka
yi ta yi a duk wuraren nan da suka zauna.
Muhammadu
bin Abdul Karim al-maghili shi ma ya iso Kano amma, zamanin Sarki Muhammadu
Rumfa wanda ya yi yayinsa daga 1463 zuwa 1499. Al-Maghili ya ziyarci wurare da
dama a ƙasar Hausa bayan zamansa a Kano. Ya zauna a Gao da
Katsina. A Kano ne ya sa aka sare wata bishiya inda ake yi maguzanci. A
maimakonta ya sa aka gina hasumiya da masallaci.
Al-Maghili
ya yi aiyuka da yawa. Misali shi ya wallafa littafi mai bayanin yadda za a
gudanar da harkokin gwamnati. Wannan aiki Sarki Muhammadu Rumfa ne ya buƙace shi da ya yi.
Kamar
yadda aka ambata tun farko musulmi masana da yawa sun zauna ƙasar Hausa yawancinsu
kuwa zuwa aikin hajji ne sanadin zamansu a ƙasar Hausar. Wasu ma
labarin ƙasar Hausa suka ji sannan suka yi wa ƙasar tsinke suka zo
da niyyar ba da tasu gudummowar don kyautata addini musulunci da yaɗa shi.
A dalilin zaman irin waɗannan mutane a ƙasar Hausa an samu wuraren karatu da kuma shahararrun malamai wurare daban-daban na ƙasar Hausa. Ɗaya daga cikin irin waɗannan shahararrun malaman kuwa akwai Wali Ɗan Marina wanda ya yi zamaninsa ne a Birnin Katsina. Ya yi aiyuka da yawa watau aiyuka na rubuce-rubuce da kuma koyarwa[1].
1.4 Tasirin Musulunci a Al’adun Haihuwa a Ƙasar
Hausa
Addinin musulunci
warayyen addini ne da ke tafiya daidai da lokaci, haɗuwar Hausawa da
musulunci ya haska masu fitila da suka hangi gabansu har ma suka waiwayo baya,
don kallon wasu al’adun haihuwa da ke da kurakuran da aka daɗe ana gudanar da su.
A nan za a yi ƙoƙarin fito da al’adun da yadda musulunci ya yi tasiri
kansu.
Hausawa suna da nau’o’in al’adun haihuwa sun
fi a ƙirga, sai dai akwai waɗanda ake yi gabanin haihuwa, akwai na lokacin
da haihuwar, sai kuma waɗanda ake gudanarwa
bayan an haihu.
1.4.1 Tanade-Tanaden Naƙuda
A lokacin da cikin mace ya kai wata tara
wato, lokacin haihuwarta ke nan, daga nan ciyon naƙuda zai kamata. Za ta
dinga jin raɗaɗi, ko azaba kala-kala
wata mara, wata ƙugu wata ƙafa, wata baya kowa da irin yadda zai
zo masa. Wani lokaci in abu ya yi tsanani wata sai an yi mata tiyata, wata ma
sai ta rasa ranta duk ta dalilin naƙuda.
A yau sakamakon
tasirin addinin musulunci akwai abubuwan da Bahaushe ke amfani da su lokacin da
mace take naƙuda irin su, tanade-tanaden abubuwan da za a sha domin a
sami saukin haihuwa, kamar rubutu da kuma magungunan musulunci.
1.4.2 Yin Guɗa In An Haihu
Guɗa ita ce babbar
shaidar da Bahaushe ke gane an sami ƙaruwa, ma’ana an
sauka lafiya. Domin da ka ji guɗa tau komai ya daidaita. Haka kuma Bahaushe ya tabbatar
da cewa duk lokacin da ka ji mata na guɗa to, abin farin ciki ya samu. Wannan guɗar tamkar shela ce,
cewa ga irin abin da aka haifa, idon aka ji an yi guɗa sau uku to, mace ce
aka haifa, in kuwa sau huɗu aka yi, namiji ne
aka samu.
Yau a sanadiyyar
karantarwar addinin musulunci da tasirin da ya yi ga al’ummar Hausawa, an daina
yin guɗa in an sami ƙaruwa. Musulunci ya
yi hani ga mace ta yi ihu ko kururuwa har wasu da ba muharramanta ba su ji
muryarta. Wannan ne babban dalilin da ya sa al’adar ta zama tarihi a ƙasar Hausa.
1.4.3 Yin Huɗuba Ga Kunnen Jinjiri (Kiran Sallah da Iƙama)
A ƙasar Hausa can baya,
in an sami ƙaruwa ta haihuwa kakanni da arwanka (ungozoma) ke ta
shige da fice da abin da aka haifa. A yi masa ƙulle-ƙullen kandaye da
layu. Suna yin wannan ne wai don neman tsari da kariya daga miyagun abubuwa. A
wasu lokuttan ma mahaifin jinjiri har dai in haihuwar farin ce yana iya kwanaki
bai sa abin da aka haifi ga ido ba saboda kunya.
“Musulunci mai daɗi”, saboda koyarwar
addini da an yi wa Bahaushe haihuwa abu na farko bayan wanka da ake yi wa abin
da aka haifa namiji ko mace, shi ne a yi masa kiran sallah a kunnensa na dama
da iƙama a kunnensa na hagu. Abin da aka fi so, uba ya yi wa
yaronsa da kansa kamar yadda addinin musulunci ya koyar
1.4.4 Ruwan Zamzam ko Dabino a Matsayin Abincin Farko Ga
Jinjiri
Bahaushe yana matuƙar girmama al’adarsa
da ya gada kaka da kakanni. A ƙasar Hausa inda aka fito da an haifi jariri
ko jaririya, abu na farko da ake ba shi kafin nono shi ne ruwa har dai kafin
nonon uwar ya kawo.
A yau soboda koyarwar
addinin musulunci, Hausawa sun karkata wajen gudanar da abubuwan da addini ya karantar.
Mafi yawan Hausawa suna tanadar ruwan zamzam su aje da ciki ya kai lokacin
haihuwa (wata tara), da an sauka lafiya, don a fara baa bin da aka haifa kafin
komai. Wasu kuwa dabino suke nemowa a tauna a saka a bakin jariri ko jaririyar
da aka haifa kafin komai. Ana son su zama abu na farko da ya fara faɗawa cikin jinjirin,
kafin nonon uwa.
1.4.5 Al’adar Lugude
Lugude wani azanci ne
da mata kan yi a lokacin da aka sami wani abin farin ciki, haihuwa ko aure ko
wani abu makamancin haka. Akan yi lugude ne da Turmi da Taɓarya ta hanyar amfani
da salon magana, a yi ta habaici da arashi ga wasu.
Tasirin musulunci ya
sa Hausawa sun gano wannan taron babu wani alheri a ciki sai dai haddasa fitina
da ƙyamar
juna.
1.4.6 Zaɓen Suna
Addinin Musulunci ya
yi horo da a zaɓa wa abin da aka
Haifa suna mai kyau da ma’ana cikakka, wannan dalili ne ya sa ake zaɓar sunayen Annabawa
ko sahabbai ga ‘ya’ya maza, su kuma mata ana zaɓar masu sunayen matan Annabawa ko na
Sahabbai ko sunayen ‘ya’yansu. Ire-ren waɗannan sunaye su ne Hausawa suke kira da
sunayen yanka, wato, sunayen da aka samu bayan shigowar addinin musulunci[2].
Ga misalan ire-iren sunayen kamar haka:
i.
Sunayen
Annabawa. Misali: Adamu, Nuhu, Idris, Salihu, Ibrahim da sauransu.
ii.
Sunayen
Sahabbai. Misali: Abubakar, Umar, Usmanu, Aliyu da sauransu.
iii.
Sunayen
Waliyyai. Misali: Abdulqadir, Ahmadu Tijjani, Ahmadu Rufa’i da sauransu.
iv.
Sunayen
Matan Annabawa. Misali: Aminatu, Faɗimatu, Maryamu, Zainabu da sauransu.
v.
Sunayen
Mala’iku. Misali: Jibrilu, Mika’ilu, Rilwanu da sauransu.
1.4.7 Sunayen Al’ada a Matsayin Sunan Yanka
Hausawa kafin zuwan
addinin musulunci ƙasar Hausa, idan aka sami ƙaruwa ta yaro ko
yarinya, ana raɗa wa abin da aka
haifa suna ne ta la’akari da lokaci ko yanayi da aka yi haihuwa. A mafi
yawancin lokuta, ire-iren waɗannan sunaye kakanni ne suke zaɓar sunaye. Daga cikin
ire-iren sunayen da Hausawa suke amfani da sun a gargajiya akwai:
i.
Sunayen
da suka danganci yanayin shekara. Misali:
-
Anaruwa
ko Mairuwa: Yaron da aka haifa a lokacin da ake ruwan sama
-
Damina:
Yaron da aka haifa da damina
-
Nomau:
Yaron da aka haifa a lokacin da ake yin noma da sauransu.
ii.
Sunayen
da suka danganci yawan ‘ya’ya wurin wadda ta haihu. Misali:
-
Mati
ko Tanko ko Namata: Sunaye ne waɗanda ake kiran yaron da aka haifa bayan an
haifi mata uku ko fiye da haka.
-
Auta:
Sunan da ake raɗa wa yaro ko yarinya
waɗanda bayan an haife
su ba a ƙara haihuwar wani ba.
iii.
Sunayen
da suka danganci watannin jinjiri a ciki. Misali:
-
Shekarau:
Ana raɗa wa yaron da ya
shekara a ciki
-
Shekara:
Suna ne da ake raɗa wa yarinyar da ta
shekara a ciki ba a haife ta ba.
Duk waɗannan sunayen dama
sauran ire-irensu, a da Hausawa na amfani da su ne a matsayin raɗaɗɗun sunaye a ƙasar Hausa, ya yi
hani da amfani da su. Duk da haka wasu Hausawa na saka sunayen bayan na
musulunci a matsayin laƙabi.
1.4.8 Walima da Raɗa Suna a Kwana Na Bakwai
Shari’ar addinin
musulunci ta yi horo ga mabiya da su roƙi Allah, Maigirma da ɗaukaka, ga dukkan
abubuwan da suke buƙata ta hanyar yin addu’o’i. Wannan dalili ne ya sa idan
aka haihu ake yi wa abin da aka Haifa addu’a don roƙon Allah, Maigirma da
ɗaukaka, ya tsare shi
daga dukkan sharri, ya kuma zama mai amfani ga kansa da kuma sauran al’umma.
A rana ta bakwai da
haihuwa wasu na gayyatar ‘yan uwa da abokan arziki don yin taron addua’ar raɗin suna don a raɗa suna ga abin da aka
Haifa namiji ko mace. Daga cikin Hausawa musulmai mabiya Ɗariƙar Qadiriyya da
Tijjaniyya da ‘yan uwa musulmi, suna gayyatar ‘yan uwa da abokan arziki don yin
taron addu’ar raɗin suna.
Masu wannan ra’ayin
na taron addu’ar raɗin suna a rana ta
bakwai da haihuwa sun kafa hujja ne da cewa, yin irin wannan taro mustahabbi
ne, sun bayyana cewa akwai Hadisin Annabi tsira da aminci su tabbata a gare
shi, wanda ya bayyana cewa, idan aka yi masu haihuwa ku ciyar da al’umma da
abinci, kuma ku shayar da su da abu na halak (Al-Malik, 1913:224) a cikin Sallau,
(2013)
1.4.9 Raɗa Suna a Masallaci
Ga al’ada Bahaushe
idan matarsa ta haihu yakan tara mutane domin a yi buki na al’ada da ake yin kaɗae-kaɗe da
bushe-bushe. Akan yi dafe-dafen abinci kala-kala, har da su masoshi da daman
kaji da sauransu. A raba goro, a yi wa abin da aka haifa addu’o’i, a kira sunan
da aka raɗa wa yaro
ko yarinya, maba ya sanar wa jama’ar da ke wajen.
A yau saboda tasirin
musulunci mafi yawan Hausawa sun bar waccan al’adar. A maimakon hakan, in ranar
suna ta zo, masallaci ake zuwa bayan sallar Asuba. A sanar da liman cewa an yi
wa wane haihuwa yau ce kwana ta bakwai, ana neman addu’a. An sanya wa abin da
aka haifa suna wane ko wance. Daga nan sai liman ya yi jagorancin yi wa abin da
aka haifa addu’a, sai kowa ya wuce abinsa.
Masu wannan ra’ayin
na addu’a a masallaci ba a yin taron raɗa suna. Sun kafa hujjarsu da cewa, Annabin
Muhammadu Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai yi taron addu’ar raɗa suna ga ‘ya’yansa
ko jikokinsa ba, haka kuma sahabbansa ma ba su yi ba.
1.4.10 Yin Sheda ko Tsagar Gado
Tsaga wata alama ce
da Hausawa da wasu ƙabilu na sassa daban-daban da ke cikin Nahiyar Afirka da
ma wasu sassan Duniya ke yi da aska a fuska ko ɓangare na jiki, don a bambanta wata ƙabila da wata ko
mutanen wata Daula da wata, ko dangi da dangi, ko zuri’a ko don riƙon al’adu ko kuma don
yin kwalliya.
Da yawan Hausawa sun
daɗe da gano wannan
tsagar ba addini ba ce, al’ada ce kawai da son rai da ta’assubanci. Shi kuwa
musulunci ya yi hani ga duk wani abu da ke janyo ta’assubanci ko ɓangaranci a cikin
al’umma.
1.4.11 Shayar da Jinjiri Nonon Uwa da Yaye
A ƙasar Hausa kafin
bayyana addinin musulunci, wasu iyaye suna da al’adar ƙyamar shayar da abin
da suka haifa nono kamar yadda ya kamata, har dai kar a ce maka haifuwar farin.
A yayin da ake samun wasu iyayen kuma suna wuce shekara biyu suna shayarwa.
Da Hausawa suka karɓi musulunci, sai ga
Ubangiji Maɗaukakin Sarki da
kansa yana cewa:
“Yayensa a cikin shekara biyu” (Qur’an Suratul Luquman)
A mafi rinjayen
bayanin malaman addini, sun tsoratar game da wuce shekara biyu ana shayar da
jinjiri nono. Har suna ganin duk yaron da ya wuce shekara biyu yana shan nono,
to, lalle zai zama “wawa”. Sun faɗakar da iyaye irin muhimmancin shan nono uwa
da bayanin irin cutukan da yake hana wa yaɗuwa a ciki jikin jinjiri.
1.4.12 Kiran Sunan Ɗan Fari
A da can mata suna kunyar ɗan fari wasu ma har zuwa na uku. Duk yadda ka
yi da Bahaushiyar da ke da shekaru aƙalla hamsin da haihuwa, ba za ta kira sunan
danta ko ‘yarta ta farko ba. Mafi akasari ko da wani abun halaka zai same su ba
za su hana ba har dai in cikin jama’a ne, wai abin kunya ne gunsu.
Musulunci mai daɗi, yau a ƙasar Hausa wannan al’adar ta zama tarihi, saboda tasirin koyarwar
addini.
1.4.13
Bikin Kaciya:
A da, ba a yi wa yaro
guda kaciya. A maimakon haka, akan tara yara ne sa’o’in juna sannan a musu
kaciya lokaci guda. Sarkin aska shi ke jagorancin kaciyar yaran. Za a gina rami
a cikin zaure ko shigifa sannan a tanadi bagaruwa wanda ake amfani da ita wajen
tsai da jini. A wancan lokaci, Hausawa sun mayar da irin wannan hidima ta
kaciya a matsayin biki da ake tara jama’a a yi ta yin abubuwa na al’ada. Amma,
a yanzu tuni Hausawa sun watsar da irin wannan al’ada ta kaciyar yara lokaci
guda.
Musulunci ya yi
bayanin cewa idan an haifi yaro har ya kai shekara shida zuwa bakwai, sai a yi
masa kaciya. Kaciya ita ce yanke fatar saman zakarin yaro da aska ko wani abu
na musamman. Musulunci yana la’akari da wannan guri da aka yanke wajen
hukuntawa ta shari’a. misali musulunci ya wajabta wa duk wanda ya ɓatar da gurbin yankan
kaciyarsa a farjin mace ya yi wankan janaba.[3]
1.5 Sakamakon Bincike
Kowane bincike da aka
gudanar na ilmi daga ƙarshe akwai buƙatar ya warware zare
da abawa na babbar manufar gudanar das hi, wane sakamako ne bibciken ya samar?
Yin wannan da sa a ƙara fito da abubuwa fili, don haskawa ga na baya. Ga wasu
daga cikin sakamakon wannan binciken kamar haka:
1.
Aikin ya gano tasirin musulunci ne ya sauya
al’adun Bahaushe na haihuwa zuwa yin huɗuba ga
kunnen jinjiri da an gama masa wanka, wato, kiran sallah a kunnen dama da iƙama a kunnen hagu.
2.
Bahaushe ya daina yin guɗa in an haihu, saboda babu shi a musulunci.
3.
Binciken ya fito da dalilan da suka ja
wa Hausawa layi wajen barin amfani da sunayen al’ada a matsayin sunan yanka.
4.
Aikin ya kuma gano har yau akwai
Hausawa da ke taron raɗa suna na kwana bakwai, sai dai wasu, a masallaci bayan
sallar asuba suke yi.
5.
Al’adar sheda ko tsagar gado ta zama
tarihi a wajen Hausawa, a sakamakon tasirin addinin musulunci.
6.
Binciken ya gano akwai al’adun haihuwa
da tasirin musulunci ya shafe labarinsu, akwai waɗanda
musulunci ya yi wa gyaran fuska, akwai kuma waɗanda
suka yi daidai da na musulunci.
1.6 Naɗewa
Ma’anar Bahaushe ba
za ta ciki ba in har ba a danganta shi da addinin musulunci ba, dalili kuwa shi
ne kusan kashi tasa’in cikin ɗari na Hausawa musulmai ne. Addinin musulunci tattare
yake da sharuɗɗa da dokoki da ke
takon saƙa da al’adunsa na gargajiya. Al’adun Hausawa na daga
cikin muhimman al’adu da Bahaushe ke gudanarwa, sai dai tasirin musulunci ya
taka rawar gani, a wajen shafe labarin wasu al’adun haihuwa a ƙasar Hausa. Wasu
al’adun kuwa bugi-sa-bugi-taiki suke masu, akwai kuma wasu da suka yi “tangam” ɗaurin zanen Bara’a.
Manazarta
Abdullahi, I. S. S. (2008). Jiya ba Yau ba:
Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa.
Kundin Digiri na Uku Wanda aka Gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Abdullahi, M. (1997). “Bukukuwan Musulunci a
Garin Maidahini a Ƙaramar Hukumar Mulki ta Bunza.” Kundin Digiri na Farko
Wanda aka Gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Adamu, A.D
(2002).Tarihin Baƙin Al’adaun Auren Hausawa
a cikin Kwantarora; Research project Depertment of Hausa, F.C.Kwantagora
Adamu, M. T.
(1988). Aure da Buki a Ƙasar Hausa. Kano: Ɗan sarkin Kura Publishers Ltd.
Ado, A.
(2015). Al’adun Hausawa da Canje-Canje da Ake Samu, Canje-canje a Cikin
Bukukuwa. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Katsina: jami’ar Umaru Musa
Yar’aduwa.
Ahmad, S.Y
(1988).Verbal Honorific In Hausa
Associologistics Analysis;
Aisha, B.L
(1990).Islamic Student for Senior
Secondary School Mawallfa;
Alhassan, H.
da Wasu (1982).Zaman Hausawa; Islamic
publication Bareau,
Baba, M.
(2012) Bukukuwan Hausawa Na Musulunci, Sokoto: Takardar da Aka Gabatar a Ajin
Babban Digiri Na Biyu. Usman Ɗanfodiyo university.
Bello, Y.W
(2002).Hausawa Da Al’adunsu; Muƙalar Tsangayar
Harsuna, Sashen Nazarin Harshen Hausa, F.C.E Kantagora.
Bunza, A.M. (2005). “Booruqiyya”: (Tazarar
Bori da Ruqiyya a Idon Manazarta). Takardar taron qara wa juna sani, CSNL,
Jami’ar Bayero, Kano.
Bunza, A.M
(2008).Gadon Feɗe Al’ada; Lagos, tiwal Nigeria; C&A Printed, Lagos
Gusau, G.U (2012). Bukukuwan
Hausawa; Gusau 01-faith prints.
Hassan, B. Y. (2013). Nason Baƙin Al’adu Kan Al’adun
Aure Da Haihuwa Da Mutuwa Na Hausawa. Muƙalar da aka Gabatar a
Taron ƙara wa Juna Sanin a ƙasa a Sashen Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Ummaru Musa ‘Yar’Aduwa.
Hassan, B. Y. (2013). Nason Baƙin Al’adu Kan Al’adun
Aure da Haihuwa Da Mutuwa Na Hausawa, Muƙalar da aka Gabatar a
Taron ƙara wa Juna Sanin a ƙasa a Sashen Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Ummaru Musa ‘Yar’aduwa.
Muhammad, T. A. (1998). Aure Da Buki A Ƙasar Hausa. Kano: Ɗan Sarkin Kura
Publishers Ltd.
Sa’id, B. Edita
(2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello
University Press.
Sallau, B.A (2013). Raɗa Suna Jiya Da Yau.
Cikin: Himma Jurnal o Hausa Studies. Department of Nigerian Languages. Katsina:
Umaru Musa Yar’adua University.
Umar, Y.B (2012) Tsaga a Matsayin Maganin
Bahaushe. Sokoto: Takardar da Aka Gabatar a Ajin Babban Digiri Na Biyu. Usman
Danfodiyo University.
Yahaya, I.Y
(2002), Darussan Hausa Don makarantun
Sakandare littafi na II;
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.