1. Salamun a kan
wanga sako na kaya,
Da ni Muda an dakara
min a baya,
Na zancen kawayen da
ke yin hamayya,
Makwaftan ga Nijar da Najeriya.
2. Tasha ta ta Sunna
ta sa nai rubutu,
Na nusar da 'yan
al'umata batattu,
Gudun kar a maishe da
bayi matattu,
Musulmai mazauna na
jamhuriya.
3. Akan wanga zance
na juyi na mulki,
Da ke so ya jawo
dalili na yaki,
Tsakanin masoya
mazauna na yanki,
Aminanga Nijar da
Najeriya.
4. Ina wanda ke ji da
kunnen basira,
Matso duk bayanin da
zan yo ka tara,
Alakar da tsantsar
abota ta haura,
Tsakaninmu tilas
zaman lafiya.
5. Da Nijar da
Najeriya ai guda ne,
Kawai ‘yan’uwa ne da
yayu da kanne,
Alakar mahaifa da
nonon uwa ne,
Uban ma guda ne cikin
nahiya.
6. Da yarenmu tilo
muke kasuwanci,
Wajen cinikayya da
hirar zumunci,
Da zakinsa yayyenmu
ke yin zawarci,
Abin kayatarwa cikin
kwalliya.
7. Dalilin hakan ne
muke auratayya,
Tsakanin surukkai ko
sam ba hamayya,
Ga mai son mu yo
hargitsi ya ji kunya,
Ba zai nassara ba a
nan duniya.
8. Da Nijar da
Najeriya babu bare,
Bakake a fata muna
nan a tare,
Mu kyale bayanin
wadancan farare,
Na yankin kasa ko
batun nahiya.
9. Kamar yadda su
basu son mu bakake,
Hadin kanmu ma dole
zai sa su yake,
Dalilin ko in mun
hade za mu mike,
Mu zamto kamar
tsintsiya bai daya.
10. Tufafinmu na lura
shi ma guda ne,
Abincinmu ya shafi
dangin tuwo ne,
Matsa gefe can mai
fadin wane-wane,
Halin nan hali ne
abin kushiya.
11. Ku ban kunnuwa
kunga Nijar kasata,
Da Najeriya gun bison
cibiyata,
Musulminmu Allahu Yai
mana gata,
Zama tare sai an rike
yafiya.
12. Musulmi yaso duk
musulmi na gaske,
Batun bangaranci ya
bar tanke-tanke,
Mu tattaru domin mu
tayar da garke,
Mu zam masu iko cikin
duniya.
13. Idan da ace za ku
dau shawarata,
Da Nijar da Najeriya
har makota,
A koma guda dai ƙasa mai nagarta,
Kamar yadda Turai
suke tutiya.
14. Kasashe da dama
akai harhadawa,
Sukai yo Amerika
domin kwarewa,
A yau kunga ikonsu
yai tsallakawa,
Siyasarsu ta mamaye
duniya.
15. Idan zamu gane mu
dau namu yare,
Mu maishe shi harshen
kasashenmu dore,
A ofis cikin
mankarantu wurare,
Mu watsar da yare na
hauragiya.
16. Farance da
Turanci waye ya samu?
Kayo naka nai nawa
shi ke raba mu,
Idan da suna so mu
amfani kanmu,
Baza ma a faro ba
wannan tsiya.
17. Iyayen kwarai
basu cuta a kan mu,
Faransa da Ingila ku
ne idon mu,
Idan ma akwai mai
nufin kuntata mu,
Da karfinku ku sai ku
mai tankiya.
18. A hannunku ne ma
lagon ‘yan Afirka,
Idan kunka so sai
kasa tai yi mika,
Idan kunka ce a a ko
babu shakka,
Akwai damuwa ba zaman lafiya.
19. Ku yarje mu zauna
kalau mu dukanmu,
Mu more ku more cikin
arzikinmu,
Idan kunki to Rabbana
ya ishema,
A da ma da shi mu muke fariya.
20. Aboki taho gani
zo rungume ni,
Ka dube ni dube ka
mun yo kamanni,
Ku dan tausaya kanmu
ku shugabanni,
Ku yarje mu zauna zaman lafiya.
By:
Mahmud Ahmad Musa (Mahmudul Khalam) +234 902 019 4569
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.