𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam, wai menene matsayin mijin da ya ƙaurace
wa matarsa tsawon watanni biyar saboda sun samu saɓani? Bayan sun shirya kuma bai dawo gare
ta ba, sai daga baya kawai ta ji wai zai yi aure! Wai matar za ta iya neman
mijin ya sake ta? Ba ta yi laifi ba ga haka?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Ba ki faɗi menene saɓanin ba balle a san ko ƙauracewar tana kan ƙa’ida ko kuwa a’a.
Amma dai a ƙa’ida miji ba ya ƙaurace wa shimfiɗar matarsa sama da watanni huɗu. Duk wanda ya yi rantsuwa a kan hakan,
watau ya yi: Ilaa’i , to alƙalin musulunci zai dakatar da shi bayan watanni huɗu: Ko dai ya dawo ya ci gaba da saduwa da
matarsa ko kuma ya sake ta, kamar yadda Ayar Suratul Baqarah ta nuna.
Maganar neman saki kuwa, kamata ya yi ta yi
taka-tsantsan. Kar ya zama zafin kishi ya ɗauke ta ga yin hakan, ta tsaya ta yi
nazari mai kyau, kuma ta yi shawara da iyayenta: Su kira taro a zauna a
tsakaninsu da manyansa domin a samu mafita. Allaah ya ce:
إِن يُّرِيدَا إِصْلَاحاً يُوَفِّقِ اللهُ بَيْنَهُمَا
Idan dai sulhu suke nema to kuwa Allaah zai sanya
dacewa a tsakaninsu.
Sannan kuma a tuna cewa: Me yiwuwa akwai ’ya’ya a
tsakaninsu. Wa zai yi mata tarbiyyarsu yadda ya dace in ta fita ta bar su a
gidan? Yana da kyau a yi tunani mai zurfi a kan wannan.
Shi dai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) cewa ya yi:
أَيُّمَا امْرَأَةٍ سَأَلَتْ زَوْجَهَا طَلاَقًا فِى غَيْرِ مَا بَأْسٍ فَحَرَامٌ عَلَيْهَا رَائِحَةُ الْجَنَّة
Duk matar da ta nemi mijinta ya sake ta ba tare da
wani dalili ba, to kuwa ko ƙanshin Aljannah ba za ta ji ba.
WALLAHU
A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.