𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam Dan Allah a ba mu shawara
na kariya daga aljanu, ko sihiri da sauransu, kuma Wanda aka yi wa sihiri na
rashin aure me ya kamata ya yi? Ko na yawon banza?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam. Ina roqon Allah ya warware ma
kowa matsalarsa, ƴar uwa yana daga cikin hanyoyin kariya daga sihiri
kafin afkuwarsa:
1. Jin tsoron Allah da aikata dukkan wajiban da
Shari'a ta wajabta.
2. Nisantar dukkan abubuwan da Allah ya haramta,
da kuma tuba daga munanan ayyukan da mutum ya aikata.
3. Yawaita yin karatun Alqur'ani mai girma a
kullum, ta yadda zai zama mutum kusan koyaushe zai zama cikin tsarki.
4. Kyautata yin addu'o'i na neman tsari, da yin
sauran azkár waɗanda
shari'a ta aminta da yin su, kamar su:
بِسْمِ اللَّهِ الذِّي لاَ يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الأَرْضِ وَلاَ فِي السَمَاءِ وَهُوَ السَّمٍيعُ العَلِيمُ.
A riqa karantawa sau uku a duk safiya da yammaci.
Duba Abu Dawud 5088.
Da Karanta ayatul Kursiyyi a bayan idar da kowace
sallah, da karanta ta a safiya da yammaci, da kuma lokacin barci. Da karanta
Qulhuwallahu Ahad, da Qul'a'uzu Birabbil Falaq, da Qul'a'uzubirabbin Nás. Sau
uku a duk safiya da yammaci da lokacin barci. Da yin duk sauran zikirori da
suka tabbata a Alqur'ani da Sunnah, kamar addu'ar shiga gida da na fita gida,
da na shiga bayi da na fita, da na kwanciya barci da na tashi daga barci, da
sauransu.
5. Karyawa da dabino guda bakwai kafin a ci komai
a kowace safiya idan an sami dama, kamar yadda Annabi ﷺ ya tabbatar cewa duk wanda ya yi hakan
wata cuta ta dafi ko sihiri ba za ta same shi ba. Amma ita ruwayar Muslim ta ce
dabinon Madina ne, kawai dai idan ba a sami na Madinan ba a yi amfani da wadda
ake da shi.
Duba Bukhariy 5445. Muslim 2047.
In Allah ya so idan mutum ya lizimci waɗannan abubuwa cutarwar mai cutarwa ba za
ta taɓa
samun sa ba, sai dai abin da Allah ya qaddara masa na jarabawa, Allah ya kare
mu.
YADDA AKE WARWARE SIHIRI
Yana da kyau a sani cewa; ba a warware sihiri ta
hanyar sihiri, yin hakan haramun ne. Amma akwai hanyoyi guda huɗu ingantattu da Musulunci ya tanadar na
warware sihiri amma za mu taqaita ne ga nau'i biyu kamar haka:
1. Ciro sihirin da ɓata shi idan an gano inda yake ta hanyar
da shari'a ta halasta, wannan na daga cikin babbar hanyar yi wa wanda aka yi ma
sihiri magani.
2. Yin Ruq’ya da shari'a ta yarda da shi, wannan
shi ma yana da sigogi uku, amma za a taqaita a siga ɗaya, saboda kada rubutun ya yi yawa, ga
shi kamar haka:
A sami busassun ganyen magarya kore guda bakwai,
idan babu a sami ɗanyu,
sai a daka shi ya zama gari, daga nan sai a sami ruwa tsaftatacce kimanin wanda
zai isa wanka, sai a zuba a cikin magaryar da aka daka ɗin, daga nan sai a yi isti'aza a karanta
waɗannan ayoyi a ciki:
1. Ayatul Kursiyyi, (ita ce aya ta 255 a suratul
Baqara).
اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ
2. Sai a karanta aya ta 117 zuwa ta 122 na suratul
A'araf.
وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ ۖ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ {١١٧} فَوَقَعَ الْحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ {١١٨} فَغُلِبُوا هُنَالِكَ وَانْقَلَبُوا صَاغِرِينَ {١١٩} وَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سَاجِدِينَ {١٢٠} قَالُوا آمَنَّا بِرَبِّ الْعَالَمِينَ {١٢١} رَبِّ مُوسَىٰ وَهَارُونَ {١٢٢}
3. Sai a karanta aya ta 79 zuwa ta 82 na suratu
Yunus.
وَقَالَ فِرْعَوْنُ ائْتُونِي بِكُلِّ سَاحِرٍ عَلِيمٍ {٧٩} فَلَمَّا جَاءَ السَّحَرَةُ قَالَ لَهُمْ مُوسَىٰ أَلْقُوا مَا أَنْتُمْ مُلْقُونَ {٨٠} فَلَمَّا أَلْقَوْا قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئْت…
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.