𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum, don Allaah tambaya ce da ni:
Menene hukuncin mutumin da yake jan mutane limanci a sallah, amma a wajen ɗagowa daga ruku'u sai ya ce: ‘ALLAHU
AKBAR’ a maimakon ya ce: ‘SAMI'ALLAAHU LIMAN HAMIDAH.’ Sannan kuma menene
hukuncin faɗin:
‘SAMI'ALLAAHU LIMAN HAMIDAH’ a sallah?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
Da farko wajibi ne kowannenmu ya san cewa abin da
ya tabbata a Sunnah Sahihiya, kuma malamai suka yi ittifaaƙi a kansa shi ne:
Duk lokacin da liman ko mai Sallah shi kaɗai yake ɗagowa daga ruku'u sai ya ce: 'SAMI'ALLAAHU
LIMAN HAMIDAH'. Idan kuma ya daidaita a tsaye sai ya ce: 'RABBANAA LAKAL HAMD'
ko 'RABBANAA WA LAKAL HAMDU' ko 'ALLAAHUMMA RABBANAA LAKAL HAMDU' ko 'ALLAAHUMMA
RABBANAA WA LAKAL HAMDU.'
Amma game da mamu mai Sallah a bayan liman ne
malaman suka sha bamban. Kuma abin da ya fi bayyana, kuma ya fi zama daidai a
fahimtarmu daga cikin maganganunsu shi ne:
Shi ma dai yadda limaminsa ya yi haka zai yi,
watau ya faɗi
'SAMI'ALLAAHU LIMAN HAMIDAH' a lokacin ɗagowa, kuma ya faɗi 'RABBANAA WA LAKAL HAMDU' bayan ya gama ɗagowa. Saboda Hadisin Al-Bukhaariy wanda a
cikinsa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
صَلُّوا كَمَا رَأَيْتُمُونِي أَصَلِّي
Ku yi
Sallah kamar yadda kuka ganni ina yin sallar.
Kuma da wanda ya ce:
إِنّمَا جُعِلَ الْإِمَامُ لِيُؤْتَمَّ بِهِ
An sanya
Liman ne kaɗai
domin a yi koyi da shi.
Kuma amma game da hadisin da ya ce:
إِذَا قَالَ ألْإِمَامُ : (سَمِعَ اللهُ لَمَنْ حَمِدَهُ) فَقُولَوا : (رَبَّنَا وَلَكَ الْحَمْدُ)
Idan Liman ya ce: ' SAMI'ALLAAHU LIMAN HAMIDAH'
sai ku ce: 'RABBANAA WA LAKAL HAMDU'
Malamai irinsu Al-Imaam As-Suyuutiy a cikin
Al-Haawiy Lil Fataawiy sun nuna cewa, bai saɓa wa abin da ya gabata ba, saboda wasu
bayanai ingantattu da ya zo da su a can.
Game da hukuncin faɗin 'SAMI'ALLAAHU LIMAN HAMIDAH' kuwa, abin
da ya fi bayyana daga aganganun malamai shi ne: Shi wajibi ne, ko kuma Sunnah
Mu'akkadah domin hadisin da Al-Imaam Abu-Daawud ya riwaito daga hadisin mutumin
nan Mai Munana Sallarsa, inda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
ya umurce shi da faɗin
wannan zikirin a lokacin ɗagowa
daga ruku'u.
Don haka, limamin da ba ya faɗin wannan zikirin a lokacin ɗagowa daga ruku'u, kuma yake musanya shi
da wani zikirin daban, sai a ce ya kayar da wannan wajibi kenan daga cikin
sallarsa. Kuma dole a yi masa nasiha domin ya gyara.
Idan kuma ya ƙi yarda da nasihar, ya
cigaba da wannan ɓarnar,
to sallarsa tana iya ɓaci,
saboda wulaƙanta surar sallar da ya yi.
Wanda ya yi Sallah a bayan irin wannan limamin
sallarsa ta yi, matuƙar dai shi ya faɗi abin da yake daidai a lokacin ɗagowarsa da lokacin tsayuwarsa, saboda
hadisin da Al-Imaam Al-Bukhaariy ya riwaito cewa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
Suna yi muku limanci; to idan suka dace, duk kun
dace. Idan kuwa suka yi ba daidai ba, to kun dace, su kuma sun kauce wa daidai.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.