Salamar bako, da kaya bisa kai ne dauke
Tafe da sako a kumshi nay tufke
Bayanay ne kan zamani mai yanayi da fatake
Gami da yana mai nade da bayanai tufke
Allah na roka ya bani ikon rubuta baituka na take
Babu ratse ko batun kauce da yanke
Za ni dau duk nay bayanay na su take
Don warware wasu kulle kulle a sake
Da daura yan uwa nawa hanya mike
Hanyar da za tay nuni da goben mu take
Ma'ana dai hanya ta tsirar mu yanke
Na dau zamani za na fara baya ni a ta kai ce
Amfani sa kamar ace gona ce a misalce
Sharrin sa ka dauki ciyawa a kwatance
Zamani ke saka barin masar a uzurce
Don ka ishe dan uwanka a Uganda takaice
Cikin kanka nin lokaci kaji an iso fujuance
Kay zumunci ga karin shekaru da ladaan ka jirace
Duk wadan ga alkairai ne na zamani na zayyano su rubuce
Zamani ke saka barin al'adu ma su kyawon zance
Canjin shiga da aski marar kyawon gani a misalce
Sauyin zamani ke sanadin kauce ma manya a makance
Ita ko yanar gizo wato Internet a nufi na
Y'a ce gurin zamani iya sani na
Dan sauyin zamani ne da dalilin samuwarta kani na
A kwai ilimi kunshe cikin ta dan uwa ka tunana
Dau wayar ka ta Hannu daurata ma'auni ka auna
Ta hada ka da na nesa kunnuwan ka su jiya na
Ka tura soko ga kasuwanci tabbatace na amfana
Ka duba makalay da jaridu cikin nazari na
Sai ka hankaltu da masu zamba ka san abin gudu na
Da masu yin karya da cuta duk dai matsala na
Dan uwana say ka hankaltu da su ni a nufi na
Wanga bayani na yi ne don fadakarwa
Ga yan uwa na zamanin ga mai rikitar wa
Don gujewa yin asara a yau da gobe abin kokawa
Don mu tsira a duniyar ga abin gujewa
Gami da rabauta ran rabe wa
Nai amfani da kafar sadarwa dan isarwa
Da wan ga soko nawa abin dubawa
Ga yan uwa nawa abin yabawa
Sha biyu na watan tara kuy jiyawa
Shekara ta dubu biyu sai ashirin ga ukku kai hadawa
Nai godiya gun rabbi sarki mai iyawa
Mustapha Kalmalo
12/09/2023
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.