Ticker

Zan Iya Auren Mai Sana'ar Studio

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ina tambaya a kan mai neman auren ’yar uwata: Yana sana’ar studio ne inda mawaƙa suke zuwa su rera waƙoƙinsu, a gyara musu, daga baya kuma a fitar a riƙa sayarwa. Shi ne muke tambaya: Ko ya halatta a ba shi aurenta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Sana’ar waƙa dai haram ce a mafi ingancin bayanin da malaman Sunnah suka yi, kamar yadda muka ambata a amsar Tambaya da ta gabata. Duk kuwa da ƙoƙarin da waɗansu suke yi na mayar da ita halal a wannan zamanin, tare da koyar da ita ga yara da matasa da nuna cewa wai wata baiwa ce Allaah ya yi musu!

A asali buɗe studio a karan kansa kamar buɗe gidan TV ne da rediyo da makamantan hakan, ana iya yin amfani da shi domin alkhairi kuma ana iya amfani da shi domin sharri. Don haka ba za a ɗauke shi mummunan abu ba sai idan ta hanyar sharri ne ake amfani da shi, kamar irin aikin da aka ambata a cikin tambayar. Domin a nan ana ƙirga shi a matsayin taimako ne a kan waƙar da hukuncinta ya gabata. Allaah Taaala ya ce:

وَتَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَلَا تَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَ ٰ⁠نِۚ

Kuma ku taimaki juna a kan alkhairi da ƙarin taƙawa, kuma kar ku taimaki juna a kan zunubi da ƙetare haddi. (Surah Al-Maaidah: 2).

Sai dai ko in waƙoƙin da suke gyarawa a wurin waɗanda suka halatta ne, ba irin waɗanda shari’a ta hana kuma ta yi tsawa a kai ba ne, kamar yadda muka yi ishara a kan hakan a amsar tambayar da muka yi ishara gare ta a baya.

Amma game da siffofin wanda ake bai wa aure Annabi (Sallal Laahu ’Alaihi wa Alihi wa Sallam) ya ce:

إِذَا أَتَاكُمْ مَنْ تَرْضَوْنَ دِينَهُ وَخُلُقَهُ فَزَوِّجُوهُ

Idan wanda kuka yarda da addininsa da ɗabi’unsa ya zo muku, to ku aurar masa. (Sahih At-Tirmiziy: 886).

Abin lura a nan shi ne:

Bai taƙaita siffar wanda za a bai wa auren a kan addini kaɗai ko ɗabi’u kaɗai ba, sai da ya haɗe: Addini da Ɗabiu a tare. Don haka wanda ya rasa ɗaya bai dace a aura masa musulmar kirki ba.

Abin nufi da addini a nan kuma shi ne: Addinin da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya koyar kuma ya rasu ya bar Sahabbai (Radiyal Laahu Anhu) a kan sa. Ba addinin ’yan bidi’a da na ’yan al’ada da sauran na ’yan bin son rai da sha’awoyin zuciya ba.

Haka su ma al’adu ko ɗabi’u abin nufi da su a nan su ne: Ɗabiu ko halaye waɗanda Sahihin Addinin Musulunci ya koyar, har kuma magabatan wannan al’ummar (Sahabbai da Tabi’ai) suka gudanar da rayuwarsu a kansu. Amma ba al’adun son zuciya da sha’awar rai na lalatattun mutane, ’yan duniya a ƙarshen zamani ba.

Don haka wanda yake rayuwa a kan irin wannan sana’ar bai dace a ba shi auren yarinya musulma saliha ta-gari ba, sai dai idan ita ma irinsa ce. Allaah Ta’aala ya ce:

لۡخَبِیثَـٰتُ لِلۡخَبِیثِینَ وَٱلۡخَبِیثُونَ لِلۡخَبِیثَـٰتِۖ وَٱلطَّیِّبَـٰتُ لِلطَّیِّبِینَ وَٱلطَّیِّبُونَ لِلطَّیِّبَـٰتِۚ

Miyagun mata na miyagun maza ne, kuma miyagun maza na miyagun mata ne. Haka kuma kyawawan mata na kyawawan maza ne, kuma kyawawan maza na kyawawan mata ne. (Surah An-Nuur: 26).

Allaah ya ƙara mana fahimta.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments