𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Jirginmu zai tashi da ƙarfe
6: 30pm na yamma ne, ko zan iya yin sallar Maghrib da Isha’i? Yaya zan yi sallar Isha’in: A qasaru ko sallar zaman gari? Ko zan
iya yin sallar Farilla a bayan wanda yake yin sallar nafila?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
1. Ana yin kowace sallah ce kawai idan lokacinta
ya yi. Don haka, sallar Maghriba ba zakuyita ba sai a bayan rana ta faɗa, ko dai a gida kafin ku fito zuwa tasha
ko kuma a tasha kafin tashin jirgin. Sallar Isha’i ita ma sai idan lokacin ta
ya yi, a lokacin da shafaƙi (ruɗa-kuyangi)
a yamma ya ɓace.
2. Ana yin sallar qasaru ce kawai idan an fara
tafiya. Don haka idan a cikin gari tashar jirgin ta ke, to ba za a ce kun fara
tafiyar ba a lokacin. Idan kuwa ba a cikin gari ta ke ba, to za ku iya yin
sallar Maghriba da Isha’a a farko lokacin Maghriba a tashar, idan kun samu hali
yi kafin tashin jirginku. Idan kuwa ba ku samu hali ba, sai ku bari har sai kun
sauka daga baya, sai ku haɗa
sallolin biyu a lokacin sallar Isha’in.
3. Yin sallah a cikin jam’i ga maza wajibi ne a
maganar da ta fi inganci a wurin malamai. Don haka ya halatta kowane mai sallah
ya yi koyi da kowane limami a cikin kowace irin sallah, a fahimtar waɗansu malaman. Suka ce: Musulmi zai iya yin
sallar Azahar a bayan limamin da yake yin sallar La’asar haka kuma akasi, saboda
mashahuriyar maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:
وَإِنَّمَا لِكُلِّ امْرِئٍ مَا نَوَى
Kuma kowane mutum yana da irin niyyarsa ne.
Kamar yadda kuma suka ce: Yana iya yin sallar
Maghriba a bayan limamin da yake yin Ishaa’i, ya yi sallama daga raka’a ta uku,
kuma ya miƙe ya samu raka’arsa
ta farko a bayan limamin.
Wannan shi ne fahimtar malamai irin su Ibn Hazm
Az-Zaahiriy (Rahimahul Laah)
Haka kuma mai farilla ya yi sallah a bayan mai
nafila ma ya halatta, saboda dalilai sahihai kamar waɗannan:
1. Limancin sallar Isha’i da Sahabi Mu’azu Bn
Jabal (Radiyal Laahu Anhu) ya riƙa yi wa mutanen unguwarsu a bayan ya yi sallar a
bayan Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a cikin masallacinsa.
(Sahih Al-Bukhaariy: 700; Sahih Muslim: 465)
Watau shi yana yin nafila, su kuma suna yin
farilla. Kuma in da ba daidai ya yi ba da kuwa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ya hana shi, irin yadda ya hana shi tsawaita musu karatun
sallar.
2. Sannan kuma ga limancin sallar tsoro da Annabi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi, inda ya yi raka’a biyu tare da
jama’ar farko, kuma ya sake yin raka’o’i biyu da jama’a ta biyu. (Sahih
An-Nasaa’iy: 836)
Abu ne sananne kuwa cewa ba a yin sallar farilla
guda ɗaya a
rana ɗaya
sau biyu. Don haka na ƙarshen suna matsayin nafila a wurinsa, su kuma
suna yin farilla.
Allaah ya ganar da mu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy,
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.