𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Matar aure ce ta yi zina, daga
baya kuma ta tuba, kuma ta nemi mijinta ya yafe mata. To tambaya ita ce: (1)
Yaya hukuncin aurensu? (2) Taubatun Nasuuhah na iya kankare mata zunubanta duk
da ba a yi mata haddi ba? (3) Menene matsayin mijin da ya cigaba da zama da ita
bayan ya yafe mata, domin wai ya rufa mata asiri kuma don kar ’ya’yansu su
tozartu? (4) Menene matsayin abin da mijin ya yi a mahangar shari’a?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Da farko dai Ubnagiji Ta’aala ya ce:
ٱلزَّانِی لَا یَنكِحُ إِلَّا زَانِیَةً أَوۡ مُشۡرِكَةࣰ وَٱلزَّانِیَةُ لَا یَنكِحُهَاۤ إِلَّا زَانٍ أَوۡ مُشۡرِكࣱۚ وَحُرِّمَ ذَ ٰلِكَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِینَ
Mazinaci ba ya yin aure sai da mazinaciya ko
mushirika, ita kuma mazinaciya babu mai auren ta sai dai mazinaci ko mushiriki,
kuma an haramta hakan ga muminai. (Surah An-Nuur: 3).
Saboda dalilin wannan ayar da makamantanta ne
malamai suka yarda cewa: Ba ya halatta a ɗaura aure da mazinaci ko mazinaciya, haka ma a
tsakanin su kansu mazinatan har sai sun tuba, kuma sai matar ta gama istibra’i.
Amma idan a bayan an ƙulla auren ne wani daga
cikinsu ya afka cikin wannan masifar ta zina, to a nan malamai suna ganin auren
bai warware ba saboda hakan. Sai dai idan su ma’auratan ne da kansu suka warware shi,
kamar idan mijin ya saki matar, ko kuma idan ita ta zaɓi rabuwa da shi.
Idan kuma suka zaɓi su cigaba da zama tare, to wajibi ne su
nisanci saduwa da juna har sai matar ta yi istibra’in da zai nuna cewa babu
komai a cikin mahaifarta bayan zinar da ta yi.
Tuba ta-gaskiya (Taubatun Nasuuhah) ta isa ta kankare
kowane irin zunubi, in Shã Allãh. Kuma haddi yana zama wajibi ne a lokacin da
maganar ta kai gaban alƙalin musulunci. Amma kafin nan, ba za a ce wajibi
ne sai mai laifi ya kai kansa don a tsayar masa ba.
Cigaba da zama da matar da mijin ya yi daidai ne,
bai yi laifi ba a shari’ance. Kamar dai yadda ita ma matar take iya haƙurin
cigaba da zama da shi idan shi ne aka samu da laifin.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.