Alh. Abdu Dangunduwa Kagara Da Wakokinsa

    Kundin neman digiri na farko (b.a. Hausa) a ƙarƙashin sashen nazarin harsuna da al’adu, jimi’ar tarayya gusau, jihar zamfara, nigeria, AUGUSTA, 2023

    ALH. ABDU ƊANGUNDUWA KAGARA DA WAƙOƙINSA

    NA

    BABANGIDA AHMAD BARAU

     

    TABBATARWA

    Na tabba cewa, ni na rubuta wannan kudin bincike da kaina mai suna, ALH. ABDU ƊANGUNDUWA KAGARA DA WAƙOƙINSA . A karkashin jagorancin Dr. Musa Fadama Gummi. Duk bayanan da aka samo daga wata madogara to an Ambato madogarar a cikin matani da kuma manazarta, da aka ratayo. Babu wani sashe na wannan da aka water a wani wuri a matsayin kundin Digiri ko Diploma a cikin mujallu,

    AMINCEWA

    An amince da wannan kundin bimcike naBabangida Ahmad Barau (1710104008) a kan cewa, ya cika duk ƙa’idojin kammalawa da aka shimfiɗa dangane da neman takardar kammala digiri na farko (B.A. HAUSA) a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

     

    SADAUKARWA

    Na sadaukar da wannan kundi ga iyayena wato Malam Barau Abubakar da Mahaifiyata Malama Nana Firdausi Barau Abubakar Kagara.

    GODIYA

    Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai. Tsira da mincinSa su ƙara tabbata ga shugaban halitta manzon tsira Annabi Muhammadu (SAW) da iyalansa da sahabbansa. Ina ƙara gode wa Ubangiji (SWT) da ya ba ni damar kammala wannan kundi cikin nasara.

    ALHAMDULILLAH!

    Bayan haka ina miƙa godiya ta musamman ga jagoran wannan aikin,

    watau Dr. Musa Fadama Gummi a kan namijin ƙoƙarin da ya yi duk da tarin ayyuka da suke gabansa amma kuma ya jajirce wajen ganin cewa, aikin ya samu kammaluwa cikin nasara da kuma irin ingancin da ake buƙata aikin ya samu. Allah ya saka masa da mafificin alhkairinsa. Amin.

    Bayan haka, ina miƙa godiyata ga ilahirin Malaman Jami’ar Tarayya, Gusau musamman waɗanda suke a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu. Ina jinjina musu a kan ƙoƙarin da suka yi na ganin cewa, mun samu tarbiyya da ilimi ingantacce kuma nagartacce. Waɗannan Malaman kuwa su ne kamar haka: Prof. Aliyu Muhammad Bunza da Prof. Magaji Tsoho Yakawada da Prof. Muhammad Lawal Amin da Prof. Dumfawa Atiku da Prof. Ɗantumbishi Muhammad da Dr. Nazir Abbas Ibrahim da Dr. Adamu Rabi’u Bakura da Dr. Musa Fadama Gummi da Dr. Tahir Rabi’u Muhammad, da Malam Aliyu Rabi’u Ɗangulbi da Malam Musa Abdullahi da Malam Isa Sarkin Fada da Abu-ubaida Sani da Malam Muhammad Arabi da Malam Bashir Abdullahi da Malama Halima Kurawa. Da sauran ma’aikatan sashen Nazarin Harsuna da Al’adu na Jami’ar Tarayya Gusau. Ina godiya ga kowa da kowa.

    Haka kuma, ina godiya ga Malam Barau Abubakar da Mahaifiyata Malama Nana Firdausi Barau Abubakar Kagara. a kan goyon bayansu a gare ni da addu’oinsu da taimakonsu a kan dukkan abubuwan da ya shafi rayuwata, haƙiƙa ina matuƙar godiya, Allah ya saka musu da alheri. Bayan haka, ina godiya ga yan uwana musamman Dr. Lawal Musa Kagara da Malan Abubakar Sani Kagara da Hon. Sani Barau sa Shuaibu Barau Kagara ganin irin kulawar da suka bani ta hanrar shawarwari da abin hannunsu domin ganin wanannan yayi nasara. Haka kuma bazan taba mantawa da malan Danlami A Garba Morai shima duk da yana sashen Faransanci amma ya taka rawar gani ga gudum muwa da yake bahaushe ne mai kishin Harshen Hausa bias ga haka yayi daka domin ganin cewa ya taimaka.

     

    Tsakure

    Wannan kundi na bincike ya kunshi ma’anar waƙa ire-iren waƙa, Tarihin Alh. Abdu Ɗangunduwa Kagara da yadda ya fara koyon waƙoƙkinsa da kuma yadda yake shirya waƙoƙinsa da kuma nauoin waƙoƙkinsa da kayan da yake amfani dasu da kuma wasu daga cikin waƙoƙinsa.


     

    KUNSHIYA

    Tabbatarwa- - - - -ii

    Amincewa- - - - -iii

    Sadaukarwa- - - - -iv

    Godiya- - - - -v

    Tsakure- - - - -vii

    Kunshiya- - - - -viii

    BABI NA DAYA

    GABATARWA

    1.0    Shinfiɗa- - - - --1

    1.1. Manufar Bincike- - - --2

    1.2. Hasashen Bincike- - - --3

    1.3. Farfajiyar Bincike- - - --3

    1.4. Matsalolin Bincike- - - --4

    1.5.  Muhimmancin Bincike- - - -5

    1.6. Hanyoyin Gudanar Da Bincike- - --5

    1.7. Nadewa- - - - -6

     

    BABI NA BIYU

    BITAR AYUKKAN DA SU KA GABATA

    2.0  . Shinfiɗa- - - - --7

    2.1. Bitar ayukkan da suka gabata- - --7

    2.1.1. Bugaggun Littafai- - - --8

    2.1.2. Kundayen Bincike- - - 10

    2.2.Hujjar cigaba da bincike- - - 16

    2.3. Naɗewa- - - - -16

    BABI NA UKU

    FASHIN BAKI A KAN MA’ANONIN DA SUKA SHAFI TAKEN BINCIKE

    3.0. Shinfiɗa- - - - -17

    3.1. Ma’anar waƙa- - - - 17

    3.2. Ire – Iren waƙoƙin baka- - - 20

    3.2.1.Waƙoƙin Baka Na Yara- - - 20

    3.2.2. Waƙoƙin Baka Na  manyan Mata - - -21

    3.2.3. Waƙoƙin Yara Maza- - - -21

    3.2.4. Waƙoƙin Yan Mata- - - -22

    3.2.5 Waƙoƙin Daka - - - -23

    3.2.6. Waƙoƙin Reno- - - -24

    3.2.7 Waƙoƙin Daɓe- - - -25

    3.2.8 Waƙoƙin nika - - - -25

    3.2.9 Waƙoƙin Talla- - - -26

    3.2.10  Waƙoƙin Baka Na Cikin Labarai Da Tatsuniyoyi- 27

    3.2.11 Waƙoƙin Baka Masu Tafiya Da kaɗe-kaɗe- -27

    3.2.12 Waƙoƙin Jamaa- - - -28

    3.2.13 Waƙoƙin Maza- - - -28

    3.2.14 Waƙoƙin Sanaa- - - -29

    3.2.15 Waƙoƙin Fada- - - -29

    3.2.16 Waƙoƙin Bandariya- - - 30

    3.2.17 Waƙoƙin Shaawa- - - -30

    3.3  Nazarin Waƙar Baka- - - 31

    3.3.1. Hanyar Nazarin Waƙar Baka- - -31

    3.3.2. Salsalar Waƙa- - - -32

    3.3.3. Shekarar Da Makaɗi Ya Fara Waƙar- - 32

    3.3.4. Yawan Ɗiya a Waƙa - - - 33

    3.3.5. Tarihin Makaɗi a Taƙaice- - - 33

    3.3.6. Bayanin Wanda Aka Yi Wa Waƙa- - -33

    3.3.7. Turke Da Warwaransa- - - 34

    3.3.7.1. Muhallin Turke- - - -34

    3.3.7.2. Taƙaita Turke (Turke a gajarce) - - 34

    3.3.7.3. Warwara Da Tsattsefewar Turke- - 35

    3.3.7.4. Tubalan Ginin Turke- - - 36

    3.3.8. Awon Baka- - - - 36

    3.3.9. Yawan Layuka A Ɗa- - - -37

    3.3.10. Tsarin ɗan waƙa- - - -38

    3.3.11. Tsarin Rerawa- - - -39

    3.3.12. Takiɗi a ɗiyan waƙa- - - 40

    3.3.13. Ƙarin Murya - - - -41

    3.3.14. Amsa Amon Kari- - - -41

    3.3.14.1. Gidan Dara Na Kari- - - 41

    3.3.15. Salon Sarrafawa Da Adon Harshe- - 42

    3.3.16. Adon harshe- - - -43

    3.3.17. Zaɓen Kalmomi- - - -43

    3.3.18. Karin Harshen Waƙa- - - 44

    3.2.19.  Gini Jimla Da Tsarinta - - -45

    3.3.          Naɗewa- - - --45

    BABI NA HUDU

    ABDULLAHI DANGUNDUWA KAGARA DA WAKOKINSA

    4.0. Shinfiɗa- - - - -46

    4.1. Taƙaitaccen tarihin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara-47

    4.1.1. Ƙurciyarsa da Tasowarsa da Neman Iliminsa- -48

    4.1.2. Koyo da fara waƙoƙinsa- - --49

    4.1.3 Yaransa- - - --52

    4.1.4. Yawace - yawacansa- - --53

    4.1.5. Shirya Waƙoƙinsa- - - -54

    4.1.6. Kayan kiɗansa- - - -56

    4.1.7 Nau’oin waƙoƙinsa- - - -58

    4.1.8. Rasuwarsa- - - --62

    4.2. Matsayin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara a Tsakanin Mawaƙan Da da Na Yanzu- - - --63

    4.3. Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa- - -64

    4.4. Nazarin waƙoƙinsa- - - -65

    4.4.1. Turken Waƙoƙinsa- - - -65

    4.4.2. Zubi da Tsari waƙoƙinsa- - --68

    4.4.3. Turken waƙoƙinsa- - - -70

    4..4.4. Warwarar Turke- - - -72

    4.4.5. Salon Sarrafa Harshe- - --82

    4.4.6. Salon Amshi- - - --87

    4.4.7. Zubi Da Tsarin waƙoƙinsa- - - 90

    4.5. Naɗewa. - - - - 92

    BABI NA BIYAR

    SAKAMAKON BINCIKE

    5.0.Shinfiɗa- - - - 93

    5.1. Sakamakon Bincike- - - 93

    5.2. Shawarwari- - - - 95

    5.3. Naɗewa- - - - -96

    Mazarta - - - - -98

    BABI NA DAYA

    GABATARWA

    2.0    Shinfiɗa

    Nazari bisa ayyukkan adabin Hausa ya ginu ne ta hanyar yin tsokaci da tarke da fiɗa don a fito da armashi ko rashin armashin abin da ake nazari a kai. Nazari ne wanda yake duba adabi ta fuskar lugga da nahawu da yadda aka sarrafa harshe a cikinsa, da balaga da hikima. Haka kuma da fito da yadda halin zamantakewa da tattalin arziki da sha’anin addini da siyasa na al’umma suke ƙunshe a cikinsa da sauran manufifi da dangogin hikimomin da aka ɗora shi a kansu.

    Wannan binciken ya waiwayi wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Abdullahi Ɗangunduwa Kagara domin ya ba da haske da jagora ga fahimtar irin gudunmawa ta fasaha da hikima wadda Alh. Abdullahi Ɗangunduwa Kagara ya bayar don bunƙasa adabin Hausa. An yi ƙoƙari a ruwaito wasu daga cikin waƙoƙinsa, bisa taƙaitawa  domin a yi nazarin su. Acikin aikin an zo da aƙalla waƙoƙi daban daban guda uku kamar yadda muka faɗa cewa wasu daga ciki. Domin haka ne aka laƙaba wa kundin sunan Nazarin Wasu Daga Cikin Waƙoƙin Alh. Abdullahi Ɗangunduwa Kagara. Kusan a iya cewa wannan kundin yana daga cikin kundayen da za su iya taimakawa ɗalibbai da ma su shawar nazarin adabin Hausa.

    Shi dai wannan aiki ya zama fitila ne kawai, domin haka, ina kira ga dilibbai yan’uwana da masu shawar ganin harhsen Hausa ya ci gaba da mu tashi tsaye, mu daɗa kyautace wannan nazari.

    1.1. Manufar Bincike

              Manufar wannan bincike ita ce samar da wani kundi da zai gano jigogi da salailai na wasu daga cikin waƙoƙin Alh. Abdullahi Ɗangunduwa Kagara, tare da zayyana irin rawar da waƙoƙinsa ke takawa cikin, adabin Hausa. Nazari a kan waƙoƙin Noma ko kaɗan ba su kama ƙafar sauran takwarorinsu na waƙa ba, misali waƙoƙin sarauta wadanda har zuwa yau akwai masu ƙoƙarin nazari da bincike a kan wani abu daga cikinsu domin bunƙasa su, wannan  dole, shi ya sa muka ga ya dace mu yi wani ƙwaƙƙwarar nazari a kan wasu daga cikin waƙoƙin Alh. Abdullahi Ɗangunduwa Kagara, gwargwadon ikonmu. Bayan haka tabbas manufar wannan bincike ita ce taimakawa wajen raya adabin Hausa, da kuma bar ma na baya tarihi da abin koyi da ƙara harzuƙa su dan su tashi tsaye gadan-gadan domin ganin anci gaba da raya wannan adabi na Hausa.

    1.2. Hasashen Bincike

    Muna hasashen cewa, idan wannan aiki na bincike ya samu kammaluwa zai taimaka wajen haɓaka da raya harshen Hausa, dan haka ya sa mu muka zaɓi rubuta kundinmu game da nazari a kan wasu daga cikin waƙoƙin Alh. Abdullahi Ɗangunduwa Kagara. Domin waƙoƙin Hausa na da muhimmanci ƙwarai ga rayuwar Hausawa. Waƙa ta baka ko rubutacciya, kamar yadda muka sani tun ba yau ba, ita ce hanya mafi sauƙi da ake bi wajen isar da saƙo ga Jamaa.

    A ƙarshe, muna hasashen bincikenmu zai ba mu damar cika ƙaidoji da a ka gindaya  na neman takardar shaidar digiri (B.A. HAUSA) asashen Nazarin Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau.

    1.3. Farfajiyar Bincike

    Aikin binciken da za a gudanar ya shafi waƙoƙin baka na makaɗan Hausa. Saboda haka za a yi nazari ne a kan wasu daga cikin waƙoƙin Alh. Abdullahi Ɗangunduwa Kagara daga farko har karshen aikin.

    Haka kuma, aikin zai tsaya a farfajiyar jigogi da salai-lai waƙoƙinsa. Haka binciken zai zaƙulo Taƙaitaccen tarihin da kuma yadda yagudanar da rayuwar Alh. Abdullahi Dangunduwa Kagara, musamrnan yadda ya koyi sana’arsa ta waƙa da ire - iren waƙoƙinsa. Duk da kasancewar aiki zai gudana a fannin wasu waƙoƙinsa.na noma da kuma sarauta.

    1.4. Matsalolin Bincike

    Kamar yadda aka sani cewa babu wani aiki da za a gudanar ba tare da an ci karo da matsaloli ba nan da can, musamman a kan aikin bincike. Abdullahi Dangunduwa Kagara, ya yi fice a kan kawo cigaban harshen Hausa ta fannin adabin baka. Manazarta da masu bincike a kan harshen Hausa ba su mayar da hankali ba wajen bincike ko nazari a kan Abdullahi Dangunduwa Kagara da waƙoƙinsa. Kuma ko da an yi ba su yi yawa ba. Wannan ya sa na ci karo da matsaloli daban – daban a kan wannan  binciken.

    Ganin irin matsalolin da na fuskanta wajen wannan bincike, ya  ƙara ba ni ƙarfin guiwa ganin cewa manazarta ba su yi yawa ba wnnan fagen binciken. Dan haka wannan  aikin zai taimakama na tafe masu shaawar nazari a kan Alh.Abdullahi Dangunduwa Kagara da waƙoƙinsa. 

    1.5.  Muhimmancin Bincike

              Muhimmancin bincike shi ne zai daɗa fitowa tare da zaƙulo hikimomi da ke cikin waƙoƙin baka na Hausa. Ba wannan kaɗai ba, aikin zai daɗa faɗaɗa ayyuka adabi a matsayinsa na madubin al’umma. Aiki binciken zai taimaka wajen adanawa da kare waɗannan waƙoƙi masu ɗauke da tarin hikimomi daga salwanta, Salwantarsu kuwa ba ƙaramar hasara ba ce ga harshen da ma al’umma ta Hausawa. Dalili kuwa shi ne cewa waƙoƙin Alh. Abdullahi Dangunduwa Kagara, wani babban madubi ne na kallon rayuwar Hausawa.

    1.6. Hanyoyin Gudanar Da Bincike

    Hanyoyin da aka bi don gudanar da wannan bincike su ne :-

    1.      Ganawa da tattaunawa  da abokan sana’arsa ido-da- ido mai suna Hussaini Ɗanbaraka a Kagara

    2.      Haka kuma kamar  hira da mukayi da wani yaron Alh. Abdullahi Dangunduwa Kagara da ake kira Bashar Maidaura Kagara 085/02/2023 a gidansa da ke garin Kagara.

    3.       Sa’annan kuma an gana da wani yaronsa kuma mai yi ma sa banbaɗanci mai suna Namaimuna 06/3/2023.

    4.       da kuma hirar da muka yi da Babban  ɗansa wanda ya gade shi 27/3/2023.

    1.7. Nadewa

    Wannan babi wanda shine na farko a cikin tsarin wannan aiki an kawo abubuwa da dama wanda suke sune muhimman bayanai na shimfiɗa. Da farko an kawo gabatarwa da Shinfiɗa, Manufar Bincike, Hasashen Bincike, Farfajiyar Bincike, Matsalolin Bincike, Muhimmancin Bincike, Hanyoyin Gudanar Da Bincike da kuma Naɗewa.


    BABI NA BIYU

    BITAR AYUKKAN DA SU KA GABATA

    3.0  . Shinfiɗa

    Wannan babi ya bibiyi tarahin irin wannan nazarin ko kuma mai kama da shi wanda aka aiwatar domin raya adabin Hausa dangane da lokutta daban – daban. Wannan babi wanda shi ne na biyu a cikin tsarin wannan aiki za mu  kawo abubuwa wanda suke sune muhimman bayanai kamar haka ; Shinfiɗa bitar ayukkan da su ka gabata, hujjar cigaba da bincike,  da kuma naɗewa.

    2.1. Bitar ayukkan da suka gabata

    Hausawa na cewa “waiwaye adon tafiya” duk aikin da za a yi, ya kamata a yi bitar ayyukan masana da manazarta da su ke da alaƙa da wannan aiki ko su ka yi kama da shi, da nuna hanyar da su ku bambanta da wannan aiki. An nazarci kundaye, mujallu da kuma littattafai. Ayyukan da aka nazarta waɗanda ke da nasaba ko alaƙa da wannan aiki su ne:-

     

    2.1.1. Bugaggun Littafai

    Akwai wallafaffun littafai da dama masu alaƙa da wannan bincike waɗanda masana da manazarta da dama suka yi a baya. Daga cikin  littatafan akwai:-

    Yahaya, (2001: 289) a littafinsa mai suna “Salo Asirin waƙa” ya yi bayanin ma’anar salo a cikin waƙa. Sannan kuma ya bayyana muhimmancin salo, bayan wannan kuma ya yi bayani  kan sauran dabarun sarrafa harshe kamar, Jinsarwa, kamance, kinaya, zayyana da makamantansu. Wannan aiki na da dangantaka da nawa, sakamakon salo da za a kalla a cikin waƙoƙin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara da kuma kawo ma’anar shi salon.

    Bunza, (2009:45) a Lttafinsa mai suna “Narambaɗa” ya kawo tarihin Narambaɗa da ƙoƙarinsa, da fito da ma’anar Salo da ire – irensa. Da sauran abubuwan da ake iya samu cikin waƙa. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa duk da cewa kan Narambaɗa aka yi shi, amma tun da an kalli salo da ma’anarsa to ya na da alaƙa da nawa sosai da sosai saboda ya kawo tarihin Narambaɗa da ƙoƙarinsa, sai dai ni a kan nazarin wasu daga cikin waƙoƙin Alh. Abdullahi Ɗangunduwa Kagara aikina zai gudana.

    Gusau, S.M. (1986 16) Ya rubuta littafi mai suna “Jagoran Nazarin waƙar baka. A cikin littafin marubucin ya yi tsokaci a kan abubuwa da dama musamman waƙoƙin baka na gargajiya. Marubucin ya tattauna sosai da sosai a kan ire – iren waƙoƙin baka kuma ya yi ƙoƙarin rarrabe su zuwa rukuni rukuni inda ya kai kowane kaso a cikin rukunin da ya fi dacewa da shi. Ya tattauna a kan ma’anar waƙar baka, da karani da dai sauransu. Saboda haka, littafinsa da wannan kundin bincike suna da aalƙa da juna kasancewar su duka bangaren waƙoƙin baka na Hausa.

    Gusau, S.M. (2009: 285) Ya rubuta littafi mai suna “Diwanin waƙoƙin baka, zaɓaɓɓun  matanonin na waƙoƙin makaɗan baka na Hausa. Alaƙar wannan littafin da wannan kundinbincike ita ce dukkansu sun shafi waƙoƙin baka na Hausa. Gusau ya yi akan waƙoƙin baka na Hausa na maza da matagaba ɗaya shi kuma wannan binciken ya shafi waƙoƙin maza ne kawai kuma ko a maza ya shafi waƙoƙin Alh. Abdullahi Dangunduwa Kagara ne kawai.

    Gusau, S. M. (1995: 7) Ya rubuta littafi mai suna “Dubarun Nazarin Adabin Baka,” Shi wannan littafi ya waiwaiyi sassan hanyoyi da dubarun nazarin adabin Hausa daga makarantunsu mabanbanta ya fito da su a dunƙule don ya ba da haske da jagora ga fahimtar manyan matakan nazarin adabin baka na Hausa.Musamman ga ma su nazarin waƙoƙin makaɗan baka na Hausa. Alaƙar wannan littafin da wannan kundin bincike ita ce dukkansu sun shafi waƙoƙin baka na Hausa. Wannan binciken nawa ya shafi wasu daga cikin waƙoƙin Alh. Abdullahi Dangunduwa Kagara .

    2.1.2. Kundayen Bincike

    Mashi, (1982:32) A cikin kundin bincikensa na digiri na farko mai suna “Gudummuwar Hajiya Barmani Coge Mai Amada ga adabin Hausa” wanda aka gabatar a sashen fasaha da nazarin Al’amuran Musulunci, jami’ar Bayero, Kano.

    Ya yi bayani sosai a kan irin gudummuwar da Barmani Coge ta bayar a wajen bunƙasa adabi da harshen Hausa. Kundin bincikensa yana da alaƙa ta kusa da wannan kundin binciken ta fuskar waƙoƙin baka na Hausa. Mashi, ya yi a kan ɗaya daga cikin mata mawaƙan baka na Hausa wato mawaƙiya Saadatu Barmani Coge. A wannan kundin binciken kuma, an yi shi ne a kan Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara. Don haka suna da alaƙa da juna kasancewar dukkan su an yi nazari ne a kan mawaƙan baka na Hausa.

    Hadiza, (2007: 41) A cikin kundin bincikinta na neman digiri na farko mai suna “Waƙoƙi a Kan Mata” A cikin wannan kundin binciken, ta yi bayani cewa mata su ne suka fi yin amfani da waƙa domin isar da saƙo ko kuma domin nishaɗantatwa a tsakaninsu a cikin aikin nata ta bayyana ma’anar waƙar baka da ire- iren waƙoƙin baka na Hausa. Haka ta yi bayanin ire-iren mawaƙa inda ta nuna cewa a cikin mata akwai waɗanda suka shahara wajen isar da saƙonni a waƙoƙinsu zuwa ga jamaa. Hakazalika ta nuna yadda matsayin mace yake ga Bahaushe da kuma sharhin wasu daga cikin waƙoƙin mata.

    Garba Keku (1992:10) a kundinsa da ya rubuta a kan rayuwar Salisu Jankidɗi, ya yi tsokaci ne a kan waƙoƙin Salisu Jankiɗi, a inda aka yi bayanin asalinsa, haihuwarsa, ƙuruciyarsa da kuma tasowarsa, fara waƙarsa da kuma shahararsa. Haka kuma an yi bayani a kan sarakunan da ya yi zamani da su, da kuma sarautar da Sarkin Musulmi da ya naɗa shi.An kuma bayyana yadda yake shirya waƙoƙinsa tare da matsayin waƙoƙinsa ga wasu sauran waƙoƙi, sannan an yi bayanin shahararsa a wajen kida da kuma jigon waƙoƙinsa wadanda su ka ƙunshi yabo, zambo, habaici, zuga, da kirari da kuma salon waƙoƙinsa na mai-maitawa da aron kalmomi.

     Shi kuma Alhaji Lawal Faruku (1997:13) a kundin da ya rubuta a kan “Rayuwar Ƙwazo Bagega da Waƙoƙinsa”, nazarin waƙoƙin Ƙwazo Bagega aka yi,  a inda aka bayyana tarihinsa tun daga haihuwarsa har tsufansa. An bayyana yadda yake tsara waƙoƙinsa da jigogin waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa ta fuskar sarrafa harshe, daga ƙarshe aka kawo jerin wasu waƙoƙinsa.

    Yayin da Abdurrahaman da Ahmad na Baba Tsafe, da Attahiru Rufai Gwandu (1993:21) a kundinsu da suka rubuta akan rayuwar Sani Sabulu na Kanoma da waƙoƙinsa a inda aka bayyana tarihinsa tun daga haihuwarsa har tsufansa, an bayyana yadda yake tsara waƙoƙinsa da jigogin waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa ta fuskar sarrafa harshe. Daga ƙarshe aka kawo jerin wasu hikimominsa

     Har ila yau mun dubi wani kundi na Muhammad Y. Nasarawa da na Muhammad Khalid (1997: 23) mai taken “Nazari A Kan Alhaji Abdu Inka Bakura da waƙoƙinsa”. Anan ma an bayyana yadda yake tsara sana’arsa ta waƙa da jigogin waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa ta fuskar sarrafa harshe dagaƙkarshe aka yi fashin baki a kan waƙoƙinsa.

    Ashiru (2001: 48) kundin digiri na farko mai taken: “Jigon Kishi A Cikin Rubutattun Waƙoƙin Soyayya” wannan kundi ya yi tsokaci kan kishi da abin da ke haifar da kishi, tsakanin namiji da mace. Wannan aiki yana da alaa da nawa domin kishi jigo ne a cikin jigogin soyayya. Bayan haka kuma a waƙoƙin soyayya da za ayi nazari akwai jigon kishi, amma waƙoƙin wanɗanda Sadi Sidi Sharifai ya yi ne. Saboda haka wannan aiki ya sha bamban da nawa aikin.

    Muhammad. (2010:34) kundi mai taken “Kalaman Cikin Waƙoƙin Soyayya, Gaskiya ko Ruɗi  An yi wannan aiki ne don neman digirin farko a sashen koyar da Harsunan Nigeriya Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato. A cikin wannan aikin an yi ƙoƙarin bayyana irin rawar da marubuta da masu rera waƙoƙin soyayya na Hausa ke takawa, musamman wajen salo a cikin waƙoƙin. Shi ma wannan aiki yana da alaƙa da nawa tun da a kan wakokin soyayya ya gudana. Amma ni nawa ya sha bamban da shi, saboda a kan wakokin Alhaji Danbalade da waƙoƙinsa ne na Sarauta, Noma da kuma Dambe. zan yi shi.

    Umar, (2011:63) a cikin kundinsa na neman digirin farko a sashen Harsunan Nigeriya Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, mai taken “Salo da Sarrafa harshe a cikin waƙoƙin Ibrahim Aminu Dandago, na Aliyu Magatakarda Wamakko. A cikin wannan aiki, an yi ƙoƙarin fito da salailai daban – daban da ma’anar Salo da mahimmancinsa da Sauransu. Shi ma wannan aiki ya na da alaƙa da nawa ta fuskar salo kawai duk da cewa shima a kan waƙoƙin wani ya yi. Ni kuma a kan waƙoƙin Sarauta, Noma da Dambe nawa  aikin zai gudana, inda za a kalli jigoginsu da salailansu.

    Hamza, (2011:25) a kundinsa na neman digirin farko a sashen koyar da Harsunan Nigeriya Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, mai taken Salo da Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA). Aikin ya bayyana Salo da ire – irensa duk a cikin waƙoƙin Ala. Shi ma wannan ya yi tarayya da nawa aikin ta fuskar salo, sai dai shi wannan a kan waƙoƙin  ALA ya gudana, ni kuma nawa a kan wakokin Alhaji Danbalade Morai zai gudana.

    Bisa la’akari da ayyukan da suka gabata, na kundaye har zuwa littattafai, za a samu cewa ba wani aiki da ya yi daidai da nawa, saboda an yi wasu ayyuka a kan wasu mawaƙa daban, ko ma a kan wani abu da ya shafi Soyayya.

     Dan haka, ko da akwai wasu bambance- bambance a tsakanin su, wadannan makaɗa da Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara kaɗan ne, Saboda shi dai makadin ‘yan dambe ne kuma sana’ace ta maza. Amma Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara yana waƙoƙin. Sarauta da kuma fawa , duk da ya fi ba da ƙarfi ga waƙoƙin noma domin gare su ya yi fice har duniya ta san shi..

    Daga ƙarshe mun dubi wadannan ayukka ne domin mu ga yadda magabata suka gudanar da bincike da kuma abin da bincike ya ƙunsa da irin hanyoyin da ya kamata mai bincike ya bi da kuma kariyar harshe daga salwanta.

     

    2.3.Hujjar cigaba da bincike

    Za a ci gaba da wannan bincike ne, Sakamakon ba wani aiki da aka taɓa samu wanda aka aiwatar a kan wannan fasihi, duk da cewa an yi aiki a kan wasu daga cikin waƙoƙinsa , da dama,  amma ba a yi a kan Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ba.Kuma ko da har in an yi Ni nawa nazarin ya sha bamban da na sauran manazarta.

    2.3. Naɗewa

    Wannan babi a cikin sa ne aka kawo bitar ayukkan da su ka gabata, a inda a ka fara shi da  shimfiɗa, a ka yi tsokaci a kan wasu kundayen kammla karatu da Littafai na magabata, duk a cikinsa ne a ka kawo  hujjar cigaba da wanan binciken,  da kuma naɗewa.

     

     


     

    BABI NA UKU

    FASHIN BAKI A KAN MA’ANONIN DA SUKA SHAFI TAKEN BINCIKE

    3.0. Shinfiɗa

    A wannan babi, za a kawo ma’anonin waƙa daga bakin masana  da manazarta kamar yadda suka bayyana raayoyinsu daban-daban dangane da ma’anar waƙa da kuma sauran abubuwan da  suka shafe ta. Mawaƙan baka na Hausa maza da mata suna ba da gagarumar gudunmuwa wajen inganta harshen, domin yana ɗaya daga manyan rukunnai na raya al’adu da adabin ko wace al’umma ta duniya.

    Saboda haka, daga cikin abubuwan da za a tattauna a wnnan babin akwai ma’anar waƙa da kuma ire-iren waƙa tare da jawabin naɗewa a ƙarshen babin.

    3.1. Ma’anar waƙa

    Masana da dama sun yi ayukka daban-daban sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar waƙar baka ta Hausa da ma rubutacciyar waƙa kaɗan daga cikin su akwai:

     Ahmad, I. M. (1982: 36) acikin nazarinsa na kundin Digiri na biyu wanda ya yi a Jami’ar Bayero dake Kano, wanda zamu iya cewa duk sun haɗu kan cewa waƙa wata  maganar hikima ce. Tsara ta ake yi, ana zaɓen kalmomi da za a gina ta da su.

    Gusau, S. M. (1984:47) Ya ce “Waƙa wata abu ce da ake shirya maganganu daki-daki cikin azanci da nuna ƙwarewar harshe.

    Yahaya, A.B. ( 2001: 56) Ya na cewa “Waƙa ita ce tsararriyar maganar hikima, da ta ƙunshi saƙo cikin zaɓaɓɓin kalmomi masu azanci, da aka auna don maganar ta reru, ba wai a yi faɗarta ba kawai”.

    Dangambo, A (.2017: 54).Waƙa wani salo ne da aka gina shi a kan tsarriyar ƙaida ta baiti, ɗango, rerawa, ƙari, (bahari), amsa-amo (ƙafiya) da sauran ƙaidojin da suka shafi dai-daita kalmomi, zaɓaɓɓu da ake amfani da su cikin jigogin da ba lallai ne haka suke a maganar baka ba.

    Umar, (1987: 64) Ya bayyana ma’anar waƙa da cewa “Waƙa ita ce nauin guduwoyin zance da ake kira ƙayyadajje, kuma ake rerawa da wani irin sautukan murya na musamman”

    Gusau, (1993: 45) Ya ce “Waƙa magana ce ta fasaha a cure wuri ɗaya a cikin tsari na musamman”.

    Sa’idu, (1981:76) Ya ce ”Waƙar baka ita ce wadda ake rerawa don jin daɗi, a ajiye ta aka a kuma yaɗa a baki”.Saboda haka a waƙar babu amsa amo na harafi kamar na rubutacciyar waƙa.

    Dangambo, (1982: 76)  Ya bayyana waƙa da cewa Waƙa wani saƙo ne da aka gina kan tsararriyar ƙaida ta baiti da ɗango da ake rerawa a kan ƙari da amsa amo da sauran ƙaidojin da suka shafi daidaita kalmomi 

    Muhammad, (1980: 68) Cewa ya yi “Waƙa Magana ce cikin sarrafarfiyar murya wadda ake rangaɗawa bisa wani tsari”.

    Idan muka yi la’akari da abin da masana suka faɗa dangane da ma’anar waƙa, za a iya cewa: waƙar baka wani zance ne na azanci wanda ake yi ta hanyar zaɓen kalmomi da lafuzza tare da daidaita sautin murya da zaɓen kalmomi waɗanda ake rerawa da fatar baki cikin sautin murya mai daɗi”.

     

    3.2. Ire – Iren waƙoƙin baka

    Farfesa Sa’idu M. G., (1983:92) ya ce “waƙoƙin baka na Hausa sun shiga koina a dukkan ɓangarorin rayuwar Bahaushe. Waƙar baka takan yi ruwa ta yi tsaki a duk inda ta ga Bahaushe ya jefa kafarsa. Kasancewar waƙoƙin baka suna da wannan halayya ta ratsa kowane zango na rayuwar Hausawa ya sa suka zama suna tafiya daidai da rayuwar yara ƙanana da matasa da kuma manyan mutane, maza ko mata. Za a iya karkasa wakokin baka na Hausa zuwa gida-gida kamar haka:

    3.2.1.Waƙoƙin Baka Na Yara

    Wannan nau’i na waƙoƙi ya ƙunshi sassan waƙe-waƙe da yawa waɗanda yara ‘yan maza da ‘yan mata suke gudanarwa da suka haɗa da waƙoƙin wasannin dandali da wasannin tashe da wasan kwaikwayo da bikin aure da sallar takuutaha da roƙon ruwa da sauransu. Ga wasu misalansu:

    Kai rawa kai malan kai rawa

    Dagemun nawa

    3.2.2. Waƙoƙin Baka Na  manyan Mata :

    Waƙoƙin baka na manyan mata su ne waƙoƙin da yawanci mata suke yin su a lokacin da suke aiwatar da wasu ayyukan gida. Manyan mata suna yin waƙoƙin a lokacin daka ko raino ko dabe ko nika ko wanke-wanke da sauran lokuta na gudanar da wasu hidimominsu na yau da kullum. Farfesa Sa’idu M. G., (1983) ya ce “waƙoƙin baka na Hausa.

    3.2.3. Waƙoƙin Yara Maza

    Waƙoƙin yara maza su ne waɗanda suke shiryawa a lokacin da suke wasansu na dandali. Irin waɗannan Waƙoƙi kan sami jagora mai bayarwa, sauran yara kuwa suna karɓawa, kamar a waƙar sha burburwa:

    Bayarwa:       Shaburburwa,

    Amshi:           Sha.

    Bayarwa:       Kowa ya bace,

    Amshi:           Sha.

    Bayarwa:       A sha shi da kulki,

    Amshi:           Sha.

    Bayarwa:       Kulkin kira,

    Amshi:           Sha.

    Bayarwa:       Ba na aro ba,

    Amshi:           Sha.

    Bayarwa:       Ku ba shi gidanai,

    Amshi:           Sha.

    Bayarwa:       Har ya kawo,

    Amshi:           Sha.

                                                 ( Gusau, S.M. (1983).

    3.2.4. Waƙoƙin Yan Mata

    Waƙoƙin yan mata su ma naui-naui ne, kuma su ne ake kira wakokin gaɗa ko na bojo. Su ma ‘yan mata suna gudanar da wasanninsu ne a dandali ko a wasu wurare na musamman kamar a wajen bikin aure ko bikin sallar takutaha ko lokacin rokon ruwa ko tashe a watan azumi da sauransu. Misalan waɗannan waƙoƙin akwai kamar haka:

     Waƙar Talle

    Bayarwa:                                                      Amshi:         

    Maina ya kone,                                             talle

    Ba da talle ba,                                               talle

    Jirkita mani,                                                  talle

    In ciwo kashi.          talle

    ( Gusau, S.M.., 1983)

     Waƙar Sabara:

    Bayarwa:                                                    Amshi:

    Na tai tsarince,                                           Sabara

    Magarya tai mani jar tsikara,                     Sabara

    lye, lye, lye                                                 Sabara

    Magarya ba haka nan akan yi ba,               Sabara

    lye, iye, iye,                                                Sabara                      

    ‘Yar bakin gulbi,                                        Sabara

    Ta yi liya-liya,                                            Sabara

    Ku yayyafa mata ruwa,                              Sabara

    Shaf, shaf, shaf,                                         Sabara

    Ka dauko naka ka tura daka,                      Sabara

    Ka dauko dan wani kai ta damfara  Sabara.  Forofesa Sa’idu M. G., (1983) ya ce “waƙoƙin baka na Hausa

    3.2.5 Waƙoƙin Daka :

    Waƙoƙin daka su ne waƙoƙi waɗanda mata suke yi lokacin da suke daka inda za su dinga gwama tabarya da turmi, sai su ba da sautin da ake kira lugude ko mama, misalin waƙar daka ita ce:

    Ana lugude ana mama,

    Cikin shigifa cikin soro,

    Mama ba habaici ce ba,

    Salon daka a haka nan,

    Ga macen da ba a so ta haihu,

    Ta haifi kwandamin da namiji,

    Shugaban daka shi ka daka,

    ‘Yan tanyo kissa su kai,

    Sukus-sukus sai su aje,

    Gidan Marafa kaji ka daka,

    Tarmani na izon wuta,

    Angula na kirba dawo.

                                              ( Gusau, S.M., 1983)

    3.2.6. Waƙoƙin Reno

    Waƙoƙin reno su ne waɗanda mata suke yi a lokacin da suke rainon yara suna yi musu tawai don su yi shiru su bar kuka a kwantar da hankalinsu a sanyaya musu rai. A cikin waƙoƙin akan faɗi nasabar yaro da ayyukan da ake yi a gidansu da yabon masoya da zambo da habaici ga maƙwabta in akwai su. Misali:

    Yi shiru bar kuka,

    Ku taho ku gane shi,

    Ku yo ziyara,

    Dan yaro sai dai a bi ka.

     Gusau, S.M., (1983)

    3.2.7 Waƙoƙin Daɓe

    Waƙoƙin dabe su ne waƙoƙin da manyan mata suke yi a lokacin da suke aikin daɓe. Yawanci waƙoƙin daɓe sukan ƙunshi bege da zambo da habaice-habaice da kalmomin batsa da na zage-zage da sauransu. Ga misali:

    Ina Lumu shege,

    Mai malmala ga munta,

    Kare bakin bahwade,

    Ya hana mu walawa.

                                                    (Gusau, S.M., 1983)

    3.2.8 Waƙoƙin Niƙa

    Waƙoƙin niƙa su ne waƙoƙin waɗanda mata suke yi lokacin da suke nikan tsaba a kan dutsen nika na gargajiya.Waƙoƙin sun ƙunshi begen miji ko wani masoyi ko habaici ga kishiyoyi ko uwar miji ko ta hanyar shagube ko ambaton juyayin nakuda da dai sauransu. Misali:  Waƙar Naƙuda:

    Wayyo naƙuda ta tashi,

    Ciwon naƙuda ya tashi,

    Kuma ciwon naƙuda ya motsa,

    Yau kam babu zama zaure,

    Wayyo inna ki cece ni,

    Da kis sha daɗinki,

    Shin wai ke tuna inna ta cece ki?

    Ko ko Ke tuna da baba ya cece ki?

    Wayyo naƙuda yar ziza,

    Ciwon naƙuda horo ne,

    Ko ko naƙuda hauka cc?

    (Gusau, S.M. 1983)

    3.2.9  Waƙoƙin Talla

    Waƙoƙin talla su ne waƙoƙi waɗanda ake yin su a lokacin da ake tallan wani abu. A cikinsu akan zuga sana’ar da ake tallar tare da fito da kwarjiinta ko amfaninta. Misali:

    Ku sai dawon gero da barkono,

    Furata da ‘yan yaji rankanɗam,

    Sai da nid daka nib burke,

    Harda gudajin nono.

      (Gusau, S.M. 1983)

     

    3.2.10  Waƙoƙin Baka Na Cikin Labarai Da Tatsuniyoyi

     Gusau, (1980) ya ce haka kuma akwai wasu ‘yan waƙe waƙe da ake sakawa a cikin labarai ko tatsuniyoyi don ƙara musu armashi ko jawo hankali da tunanin mai sauraro. Ga wani misali daga tatsuniyar Maɗaci da Yarinya:

    Yarinya: Maɗaci,

    Maɗacci ubana,

    Gare ka anka ban ni,

    Gare ka za ni tsira.

    Maɗaci: Ishunki, ishunki ɗiyata,

    Gare ni anka bakki,

    Gare ni za ki tsira,

    Mutum ɗari da goma,

    Manzo dai kan kai gida.

    (Gusau, S.M. 1980)

    3.2.11 Waƙoƙin Baka Masu Tafiya Da kaɗe-kaɗe

    Gusau, (1980) ya ce " waƙoƙin baka masu tafiya da kaɗe-kaɗe waƙoƙi ne waɗanda makaɗan baka suke shiryawa. Waƙoƙin makaɗan baka sun karkasu dangane da ire-iren makaɗan da ke aiwatar da su, ko ta hanyar kayan kiɗan da ake amfani da su ko kuma ta yanaye-yanayen waɗanda ake yi wa su. Waƙoƙin baka masu tafiya da kaɗe-kaɗe sun haɗa da:

    3.2.12 Waƙoƙin Jamaa

    Waƙoƙin jamaa su ne waƙoƙi waɗanda ake yi wa attajirai da ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a. Makaɗan da ke yin waƙoƙin jamaa suna da yawan gaske, sunayen wasu daga cikinsu sun haɗa da Mamman Shata da Danmaraya Jos da Abdu Karen Gusau da Mammalo Shata da Garba Supa da Shehu Ajilo da Sabo Saya-Saya da Musa Danba’u da Aliyu Gadanga da Haruna Uji da Hassan Wayam da Sani Dan’indo da sauransu. (Gusau, S.M.,1980)

    3.2.13 Waƙoƙin Maza

     Gusau, (1980).  ya kawo cewa waƙoƙin maza, waƙoƙi ne da ake yi wa wasu rukunin jama’a da suka haɗa da ‘yan dambe da ‘yan tauri da ‘yan kokawa, da ‘yan baura da sauransu. Daga cikin makaɗan wannan sashe akwai Kassu Zurmi da Alhaji Danbalade Morai da Muhammadu Bawa Dan’anace da Isa Danmakaho da Illon Kalgo da Muhammadu Gambu da makamantansu.

    3.2.14 Waƙoƙin Sanaa

    Waƙoƙin sanaa, waƙoƙi ne waɗanda ake yi wa masu sana’o’in gargajiya kamar wanzamai da mahauta (runji) da manoma da masunta da maƙera da majema da masaka da sauransu. Yawancin makaɗa na rukunin waƙoƙin maza su ne suke shirya waƙoƙi na rukunin waƙoƙin sanaa kamar Dananace da Alhaji Danbalade Morai. (Gusau, S.M.,1980)

    3.2.15 Waƙoƙin Fada

    Waƙoƙin fada waƙoƙi ne waɗanda ake shirya wa sarakuna da sarautunsu na gargajiya. Wasu daga cikin fitattun makaɗan fada sun haɗa da Ibrahim Gurso da Ibrahim Narambaɗa da Salihu Jankidi da Abubakar Akwara da Buda Dantanoma da Muhammadu Dodo Maitabshi da Musa Dankwairo da Abdu Inka Bakura da Aliyu Dandawo da Sani Dandawo da Alhaji Danbade Morai da sauransu.  (Gusau, S.M., 1980)

     

    3.2.16 Waƙoƙin Bandariya

    Waƙoƙin bandariya, waƙoƙi ne waɗanda ake aiwatarwa domin nishaɗantarwa da yi wa rai yayyafi. Daga cikin makaɗan ban dariya akwai ‘yan kama da ‘yan gambara da ‘yan galura da sauransu.  (Gusau, S.M., 1980)

    3.2.17 Waƙoƙin Shaawa

    Waƙoƙin sha’awa su ne waƙoƙin da ake shirya wa abubuwan da suka ba mutum shaawa ko suka ƙayatar da shi. Da wuya a ware makaɗi daya daga cikin makaɗan Hausa a ce waƙoƙin shaawa kawai yaƙe shiryawa, amma akwai wasu makaɗan da suke tsarma ire-iren waɗannan waƙoƙi jefi-jefi a cikin waƙoƙinsu  kamar Haruna Uji da Mamman Shata da Danmaraya Jos da Hassan Wayam da Sani Danindo da sauransu.  (Gusau, S.M.., 1980)

     A dunƙule, waƙoƙin baka na Hausa suna nan jibge kuma sun ratsa dukkan sassan rayuwar Hausawa ta fuskar zamantakewa da siyasar zama ko tattalin arziki ko addini ko ta hanyar al’adu ko wasanni da sauransu.

     

    3.3  Nazarin Waƙar Baka

    Waƙar baka aba ce wadda take buƙatar shiryawa da tsarawa , wato tsara batutuwa a samar da gangar jikinta cikin a zanci da hazaƙa da naƙaltar harshe da ake amfani da shi.

    Yahaya (1984) Ya ce “Waƙar baka maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke ƙunshe da wani saƙo da ke ɗauke da wasu kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma zaunannu”

    Dangambo, (1982) ya bayyana ma’anar waƙar baka kamar haka Waƙa wani furuci ne wato lafazi ko saƙo cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da dai-daita kalmomi cikin wani tsari ko ƙaida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi.

    3.3.1. Hanyar Nazarin Waƙar Baka

    A wannan sashe an harhaɗo, tsofaffin hanyoyin nazarin ne da kuma sababbin a tayar wannan hanyar ta nazarin waƙoƙin baka na Hausa. Wani abun ƙoƙari a nan shi ne matakan nazarin da ake yin amfani das u a wannan hanyar za su fi dacewa da waƙoƙin baka wadanda makaɗan baka suka aiwatar.

    A ƙarƙashin wannan hanyar ana buƙatar mai nazarin waƙar baka da ya fara gabatar da waƙar da ya ke yiwa sharhin yin bayani game da waƙar abubuwan kamar haka:

    3.3.2. Salsalar Waƙa

    Mai nazari zai bayyana ainihin sunan wanda ya yi waƙa da wanda ake yi wa ita, da abin da ake yi amfani da shi wajen kiɗan waƙar wato (abin kiɗa). Wato ana buƙatar mai nazari ya bayyana kayan kiɗan da makaɗi ke amfani da su, sannan ana son mai nazari ya bayyana hanyoyin da aka bi, ko ya bi ya sami waƙar ta zo hannunsa. Samar da waɗannan bayanai yana ƙara tabbatar da ainihin waƙar da ƙarfin ta da madogararta.

    3.3.3. Shekarar Da Makaɗi Ya Fara Waƙar

    To ana buƙatar mai nazari ya faɗi shekarar da makaɗi ya fara rera wannan waƙa ya dace kuma a faɗi lokacin da ya yi ta, da kuma wurin da aka rera ta.

     

     

    3.3.4. Yawan Ɗiya a Waƙa

    Sannan yana da kyau a bayyana yawan ɗiya da waƙar ta ƙunsa, tare da tabbatar da cewa an yi laakari da mabanbanta lokuttan rerawarta, banbancin lokuttan rerawarta kan sa yawan ɗiya ya ƙaru ko ya ragu.

    3.3.5. Tarihin Makaɗi a Taƙaice

    Sanin taƙaitaccen tarihin makaɗi yana taimakawa ga fahimtar waƙoƙinsa. Ashe kenan yana da alfanu ga mai nazarin ya zo da dunƙulallen tarihin rayuwar makaɗin waƙar da zai yi wa sharhi.

    3.3.6. Bayanin Wanda Aka Yi Wa Waƙa

    Kafin a shiga nazarin gundarin waƙa, ya dace a zo da bayanai masu gamsarwa game da nasaba da tsakuren tarihin rayuwar wanda aka shirya wa waƙar. Wannan zai taimaka wajen fahimtar inda makaɗi ya dosa da gundarin saƙo ko saƙonnin da waƙar take ɗauke da su. Idan sha’awa ce ta ɗauki makaɗi ya yi wa wani abun da aka yi wa waƙar ta fito da halayensa da ɗabi’oinsa da sauran makamantan waɗannan bayanai.

     

    3.3.7. Turke Da Warwaransa

    Turke shi ne abin da waƙa ke Magana a kan sa wanda ya ratsa tat un daga farkonta har zuwa ƙarshenta wato dai turke shi ne ainihin manufar waƙa, wasu abubuwa da ake dubawa don ƙara fito da turke a waƙa sune

    3.3.7.1. Muhallin Turke

    Muhallin turke wani wuri ne ko wasu wurare da yawancin makaɗa ke bayyana takamaiman saƙon da waƙa ke ƙunshe da shi. Makaɗi yakan jefa saƙon waƙa ko wureren da aka bayyana gundarin saƙon waƙa.  

    Misali a cikin waƙar Danmaraya Jos ta Aure akwai inda yak e cewaJawabin aure zai yi.

    3.3.7.2. Taƙaita Turke (Turke a gajarce)

    A wannan ɓangare na taƙaita turke ana buƙatar fito da bayanan waƙar ne a taƙaice. A na iya ɗaukar ɗiyan waƙa rukuni rukuni a fito da muhimman abubuwan da suke magana a kai. Ga misali daga waƙar Danmaraya Jos ta Karen mota.

    Ɗa  na 1 – 2 Bayanin maƙasudin waƙar kuma inda aka bayyana muhallin turke.

    Ɗa na 3 Wasu halayen  Karen mota da siffofinsa

    Ɗa na 4 Rashin sa’ar Karen mota da yadda ya zama macuci.

    Ɗa na 5 – 19 Ci gaba da ambaton siffofi da halayen Karen mota.

    Ɗa na 20 Ssiddabarun da Karen mota ya ke yi idan wani abu ya auku a mota da fito da ƙwarewar makaɗin waƙar ta fuskar fahimtar sassan mota.

    3.3.7.3. Warwara Da Tsattsefewar Turke

    A nan mai nazari yana da babban aiki saboda a nan ne ake so ya tsattsefe bayanan da waƙa ta ƙunsa ya fito da su daki – daki za a yi sharhin waƙa na gaba ɗaya tare da fito da manyan da ƙananan saƙoninta. Sannan kuma a bayyana abubuwan da makaɗi ya kafa hujja da su a cikin waƙarsa

     

     

    3.3.7.4. Tubalan Ginin Turke

    Yawancin waƙoƙin baka, idan mai nazari ya duba zai tarar da an jajjefa wasu abubuwa a cikin su bayan manyan saƙonnin da su ke magana a kai waɗannan abubuwan da makaɗi ke sanyawa ƙari ne ga babban turke, kuma su ake kira tubalan ginin turke, kenan tubalan ginin turke na nufin wasu magangannu da aka bi aka ƙulla waƙa da su don ta ƙara tsawo amma ba su ne babbar manufar waƙar ba.

    Daga cikin abubuwan da za a iya kawowa a nan su ne:

    Ambaton addinin, asali ko nasaba, ƙaramcin kyauta, iya shugabanci, tsarin sarauta, jaruntaka, alfahari, ko ma kan tarihi, roƙo, zuga, kambamawa, zambo, yabo, da dai sauran abubuwa makamantan waɗannan.

    3.3.8. Awon Baka

    Shi wannan fagen nazari ne da ya shafi yadda makaɗi ke shirya waƙa a cikin zubin ɗiya da dabarun karin murya . A wannan ɓangaren ana duba zubin layuka da yawan ɗiyan waƙa da tsarin rerawa da karin murya da amsa amon kari da sauran abubuwan da suka shafi awon baka.

    3.3.9. Yawan Layuka A Ɗa

    Makaɗan baka suna da walwala ta musamman dangane da shirya layukan ɗiyan waƙoƙinsu. Wasu sukan tsara waƙoƙin ne nan take wato a lokacin da suke a wajen kiɗa, wasu kuma sukan shirya waƙoƙin ne tun daga gida layuka ba su ɗaukar yanayi bai ɗaya a tsarin ɗiyan waƙoƙin baka na Hausa. A kan shirya ma layi ɗaya ko biyu ko uku ko huɗu ko biyar koma fiye da haka a waƙa ɗaya. Domin haka a waƙa ɗaya akan samu ɗiyanta su zamanto masu ƙunshe da yawan layuka daban – dabban. Misali a cikin waƙar Ma su garin mazan gabas ta tsayayye ta sarkin Rafin Kurya Dambo wadda Ibrahim Naranbaɗa ya yi kamar haka:

    Jagora: Ai kurya ta Dambo ce Makauru yannan.

    Yan amshi: Zamfara babu Bagare kamarshi.

    Jagora : Ai da takobi da garkuwa da mashi.

    Yan amshi: Mai sulki Dambo na da yaƙi, kurya akwai mazan faɗa da arna.

     

     

    3.3.10. Tsarin ɗan waƙa

    Ɗiyan waƙa tamkar rassa ne na itaciya wadda ake fara hawowa daga gindin kuma a sauka ta kansa. A kowane “ɗa” za a sami “hawa” da sauka. Hawa shi ne wanda jagora ke fara yi sannan ‘yan amshinsa (‘yan karɓi) su tarbe shi su iyar da sauka. Haka kuma a wajen tsarin ɗan waƙa akwai ɗa) mai sauki akwai (ɗa) mai tsauri. Ga bayaninsu kamar haka.

    Misalin ɗan waƙa mai sauƙi shi ne

    Hawa= In an so ko in ba a so ba,

    Sauka = Mai abu dai shi adda abu nai,

    Haka a cikin waƙar Narambaɗa ta sarkin Kiyawa Abubakar Kaura Namoda.

    Bayan wannan kuma akwai saukar sauka

    Saukar sauka : wuri ne inda ma’ana ta ƙare kwata – kwata, wato wurin da ake gama sauke ma’ana musamman bayan “takiɗi” ko ajewa : Wuri ne inda ma’ana take numfasawa , ta ɓangaren tsari kuma ana amfani da waɗannan alamomin ne na ƙwayoyin sauti don fitar da shi a ɗan waƙa kamar haka:

    A – (2) amma banda (+) ana  ƙirga ƙarewar maana a cikin ƙaramin saƙo da su. Idan ma’ana ɗaya ce sai a ba ta alamar (A) idan aka ƙara samun wata maanar a ɗan waƙa sai ba ta alamar (B)  Haka dai za a yi ta yi har ƙananan ma’anonin su ƙare.

    3.3.11. Tsarin Rerawa

    Rerawa wani tsari ne inda makaɗi yake ɗan  ƙarin murya cikin ranji mai maana ya furta kalmomi ɗaya zuba cikin ɗiyan waƙoƙinsa

    Akwai wasu dabaru da ake amfani das u wajen fitar da tsarin rerawa na ɗiyan waƙoƙin baka, su ne kamar haka:

    -          Kaɗaita furucin jagora

    -          Karɓi furucin yan amshi

    -          Kulli wuri ne inda ake fara furta ƙaramin saƙo a ɗan waƙa

    -           Ƙari  wuri ne inda ake ƙarasa furta ƙaramin saƙo

    -          Tarbe wuri ne inda ‘yan amshi suke iyar da ma’ana ƙarama wadda jagora ya fara ta ɓangaren kulli

    -          Rakiya wuri ne inda ‘yan amshi suke maimaita ƙarin da suka riga su ka yi wa jagora zuwa wani ɗan lokaci

    -          Karɓeɓeniya dabara ce ta maimaita furucin ƙari da niyyar yi wa makaɗi rakiya

    -          Bayayyeniya wuri ne inda ake karɓe - karɓen ‘yan amshin za su dinga maimaita rera abinda duk jagora ya furta ba tare da canza ko kalma ɗaya ba

    3.3.12. Takiɗi a ɗiyan waƙa

    Takiɗi shi ne maimaita abu domin ƙara ƙarfafa shi sannan dalilin da ke sa makaɗi amfani da takiɗi shi ne: ƙarfafa nauyin ma.ana ko jaddada ƙaramin saƙo, domin ƙara fito da muhimmancinsa fili. Misali a cikin waƙar Bubakar sarki na Ma’azu,

    -          Gidan Shehu da Bello (waƙar sarkin taushi Katsina ta sarkin musulmi Abubakar na 111)

    -          Ƙulli = kakka sake a ramma,

    -          Ƙari = Sa’idu shirin ka ya yi ,

    -          Takiɗi ƙulli = kakka sa ke a ramma,

    -          Ƙari Sa’idu shirinka ya yi,

    3.3.13. Ƙarin Murya

    Ƙarin murya ko tsayuwar sadaru a ɗiyan waƙoƙin su ta fuskar ƙarin waƙar baka an fi jan gaba mai nauyi ko a ƙarwara ta kangaba maras nauyi wato gaba mai sauƙi . Gaba maras sauƙi wato gajeriya , ita ce wadda ta haɗa baƙi da wasali (BW) DA (BWW) wadda ake nunawa da alamomi kamar haka [ - ] ko  [ ! ].

    3.3.14. Amsa Amon Kari

    Amsa amon ƙari shi ne daidaitawar ƙari inda zai iya zamantowa bai ɗaya a gaɓoɓin ƙarshe wato madirar sauti na ƙarshe a saduwar ɗan waƙa.

    Amsa amon ƙari yana daidaita hawa da saukar murya a saduwar su ta fi jere bisa ƙaida. Amma alamomin da ake amfani da su wajen fitar da ƙari a waƙa. Ga su  kamar haka:

    3.3.14.1. Gidan Dara Na Kari

    Wannan wata hanya ce da ke nuna ƙari ta bin hawa da saukar murya a sadurun  ɗan waƙa  a fitar da gidan dara na ƙari ta amfani da gubabun ƙari da ginshiƙai. Awajen tantance wannan hanya zaa yi laakari da wannan abubuwan kamar haka.

    -          Ginshiƙi: shi ne gaba ɗaya na murya da za a iya wakilta da alama kamar haka [+]

    -          Ginshiƙin ƙari wuri ne da yake ɗaukar ginshiƙi ɗaya ko biyu . Idan gaɓa mai nauyi ce to ta an a matsayin ginshiƙi duga  biyu ne, amma a gurbi ɗaya. Misali {++}

    Idan, kuma gaɓa mai sauƙi ce wato marar nauyi tana a matsayin ginshiƙi ɗaya, Ciko wannan shi ne ƙunshiyar gurbi wanda zai iya zuwa gaɓa ɗaya mai nauyi ko gaɓa biyu marasa nauyi.

    3.3.15. Salon Sarrafawa Da Adon Harshe

    Dangane da salo masana sun bayar da ma’ana da dama . Dangambo (1981:23) Yan a ganin salo shi ne dabarun jawo hankali wajen isar da saƙo.

    Salo a waƙar baka kuma na nufin wata hanya wadda makaɗi ke kyautata zaren tunanensa, ya sarrafa shi cikin azanci dan ya cimma burinsa na isar da saƙo a waƙa.

    3.3.16. Adon harshe

    Adon harshe wata dabara ce wadda ake yi wa harshen waƙa kwalliya. Daga cikin dabarun da ake amfani da su don yi wa waƙoƙin baka ado akwai:

    -          Kamantawa

    -          Sinfantawa

    -          Jinsarwa

    -          Kinaya

    -          Alamtarwa

    -          Ƙarangiya

    3.3.17. Zaɓen Kalmomi

    A wannan fage mai nazari zai yi ƙoƙari ya fito da yadda makaɗi yake zaɓo kalmomi da yake zubawa a cikin ɗiyan waƙoƙinsa za a duba a gani, kalmomin nan tsofaffini ko sababbi ko ƙirƙirarru ko kuma ba ƙire ba waɗanda su ka shigo harshen Hausa daga wasu harsuna. Ga abin da suke so mai nazari ya fito da su a wannan ɓangaren.

    -          Tsofaffin kalmomi – kalmomin ƙarfafa ma’ana

    -          Ƙirƙirarrun kalmomi kalmomin sakaya zance

    -          Sababbin kalmomi – kalmomin sakaya ma’ana

    -          Baƙin kalmomi kalmomin amsa kama

    -          Kalmomin kambamawa – kalmomin nishaɗi

    3.3.18. Karin Harshen Waƙa

    Makaɗan baka suna aiwatar da waƙoƙi ne cikin kare Karen harshen Hausa da ake da su kamar Sakkwatanci da Gobiranci da Zamfarci da Katsinanci da Zazzaganci da kuma Kananci da dai sauransu.

    Dangane da nazarin Karin harshe a waƙa zaa iya duba waɗannan abubuwa :

    -          Nau’in Karin harshe

    -          Kalmomin fannu na Karin harshe

    -          Rambun kalmomi

    -          Yanayi furuci

    -          Yanayin ɗauri da sauransu. 

     

    3.3.19.  Gini Jimla Da Tsarinta

    Masana adabin waƙa sun nuna cewa lahirar waƙa akan ba makaɗi da mawaƙi dammar karya wata doka ta ginin ko tsarin jimla. Amma duk da haka, makaɗa da mawaƙa kan tsara jimloli dogaye da gajeru da kuma matsakaita.     

    3.4.          Naɗewa

    A cikin wannan babi mun fara gabatar da shine da taken fashin baki a kan ma’anonin da suka shafi taken bincike, domin kawa yadda siffar babin za ta kasance da kawo ra’ayoyin masana akan ma’anar waƙa kuma mun kawo Ire-Iren waƙoƙin Hausa da yadda ake aiwatar da su ackin al’ummar Hausawa tare da cikakken bayani da misalai na Ire-Iren waƙoƙin Hausa, haka kuma a wannan babi mun kawo mu ku hanyar nazarin waƙar baka.


     

    BABI NA HUDU

    ABDULLAHI DANGUNDUWA KAGARA DA WAKOKINSA

    4.0. Shinfiɗa

    A babi na hudu kuma za a kawo bayanai game da gundarin taken bincike. Wato, bayanai a kan Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara da wasu daga cikin waƙoƙinsa a inda muka fara da shinfiɗa game da taƙaitaccen tarihinsa, wato haihuwarsa, ƙurciyarsa da tasowarsa da kuma neman iliminsa. Haka an zo da bayanai dangane da koyo da fara waƙoƙinsa, da yaransa, da kuma  yawace yawacensa, da yadda yake shirya waƙoƙinsa, da  rasuwarsa, da matsayin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara a tsakanin mawaƙan da da na yanzu, da nauoin kayan kiɗansa, da kuma nau’oin waƙoƙinsa. Babin bai kamala ba sai da aka nazrci wasu daga cikin waƙoƙinsa, inda aka fayyace, jigon waƙoƙinsa tare da warwarar jigo. Haka an yi bayanai dangane da salon waƙar Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara, aka zo da bayanai dangane da salon sarrafa harshe, da  salon amshi, aka kuma yi bayani game da zubi da tsarin waƙoƙinsa daga ƙarshe kuma aka zo da naɗewa.  

    4.1. Taƙaitaccen tarihin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara

    An haifi Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara a garin Kagara, ƙaramar hukumar Talata Mafara a cikin jihar Zamfara, Nijeriya. Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara an haifeshi a shekara ta alif ɗari tara da sittin da shidda (1966). Sunansa na yanka Abdullahi, wanda ake masa laƙabi da Dangunduwa ya tashi a cikin gidan makaɗa, saboda makaɗi ne Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ya yi gadon kiɗan ne daga mahaifinsa wato Ibrahim, wanda makaɗin Tama da fawa, ya na kuma amfani da kayan kiɗa kamar  kalangu.

    Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ana yi masa wannan laƙabi ne na Dangunduwa  tun yana ɗan yaro lokain da ba ya da baki idan yana jin yunwa sai ya ce a ba shi (gunduwa da wule) ma’anar gunduwa shi ne abinci wule kuwa miya. Ta nan ne wannan laƙabi ya samo asali tun ya na yaro. 

    Fahimtar wannan ba zai kammala ba, ba tare da anbi diddigin tarihin mahaifinsa ba. Mahaifinsa (Ibrahim) shi dai makaɗin kalangu, kuma mawaƙi ne mai hazaƙa da son mutane, ya na kuma da ƙoƙarin zagaye domin tafiyar sanaarsa ta kiɗa da waƙa (waƙar baka) kamar irin waƙar fawa da ta noma ko tama.[1]

    4.1.1. Ƙurciyarsa da Tasowarsa da Neman Iliminsa

    Kamar yadda muka yi fira da wani malami kuma dattijo kusan ɗan shekara saba’in zuwa tamanin mai suna malam Zakari Kagara kuma ƙanen wanda ya koyar da Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ilimin addinin musulunci ya bayyana mana cewa, kamar yadda  al’adar Bahaushe take, idan aka haifi yaro ya tasa ya kai lokacin ƙurciya, babansa yana kai shi makarantar allo domin neman ilimin addinin Musulunci. Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara mahaifinsa ya kai shi makarantar allo ta wani malami mai suna malam Muhammadu domin samun ilimin addini. A sha’anin waƙa kuwa, da Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ake zagayawa duk in da aka je, domin yin amshin waƙa, ta haka ne ya bi mahaifinsa ana waƙa yana amshi, har ma wata rana yana yi masa ƙari a cikin waƙarsa. Tun daga nan mahaifinnasa ya ga cewa shi yaro ne mai fahinta da kuma fasaha.

    4.1.2. Koyo da fara waƙoƙinsa

     Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara, ya koyi waƙa ne ga mahaifinsa ta hanyar bin sa sau da ƙafa har zuwa lokacin da Allah ya sa mahaifinsa ya tuba ya bar waƙa. Bayan mahaifinsa ya tuba ya bar waƙa, sai ya koma yana bin wani makaɗin ‘yan mata ko da yake ba wannan sana’a ya koya ba a wajen Abdullahi Bayan ya yi biyar Abdullahi ya kuma yi biyar ƙanen ubansa wanda ake kira Muhammadu Dan’inna, shi ma Amadu Danbaƙi tare da Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara suka yi biyar Ibahim watau mahaifin Danguduwa Kagara.[2]

     To kamar yadda muka faɗa tun da farko cewa Abdullahi Dangunduwa Kagara mutun ne mai basira mai hazaƙa, haka suka cigaba ya na biyar ƙanen babansa Muhammadu Dan.inna, suna kiɗa da waƙa tare. A wannan lokaci, Ɗangunduwa ne tauraro a wajen waƙoƙin. A kan haka Abdullahi Dangunduwa Kagara yana nan yana biyar ƙanen babansa shi ma sai Allah ya yi masa rasuwa. Ta haka ne Alhaji ya zama mai gidan kansa.[3]

    Waƙoƙinsa Na farko

    Waƙar da ya fara aiwatarwa da kansa ta farko ita ce ta fidda shi waje wato waƙar noma ta Alhaji Amadu Morai, kamar haka:-

    Alhaji Amadu ginshiƙin dutse ,

    Tunkuɗa ba ta kasheka ɗan Mamman,

    Za mu kai mai kiɗa can garin Morai,

    Ya ci gwabron maza ya buwai daji,

     

     

    Wannan ita ce waƙar da Danguduwa Kagara ya fara ta farko, da ya yi wa wani manomi Alhaji Amadu Morai. Haka kuma ya yi waƙoƙin fawa da dama, waɗanda suka ba shi damar zama makaɗin waƙoƙin baka, duk da kasancewar abin da ya gada ga mahaifnsa shi ne kiɗan fawa da kuma kidan noma.

    Bayan ga kiɗan noma yana kuma kiɗan fawa. Bisa  al' adar Bahaushe mun san cewa wancan lokaci ko babbar  Sallah ko kuma in aka yi wani naɗin sarkin fawa. To su waɗannan mutane masu sana'ar fawa suna da nasu makaɗi na kansu, kamar dai yadda mafi yawan sana'oin Hausawa suke da su. Ita ma sana'ar fawa ta na da muhimmanci ƙwarai da gaske,  ga rayuwar Bahaushe don hka tana da nata makaɗa na daban.

    Dangunduwa Kagara a fagen waƙa ko ina ya na iya tattaɓawa, ya yi ma sarkin fawa waƙa da sauran maƙarrabansa, a inda yake waƙe sarkin fawa Abu Kagara kamar haka:-

    Sa maza su ji tsoron nama,

    Abu Danmiko ka bugi tozon nagge,

    Ba gari nama Abu Danmiko,

    Ya Allah shi riƙama mahauta.

     

    Kamar dai yadda muka gani cikin bayanin cewa Dangunduwa Kagara, ra'ayi ne kawai ya sa ya koma makaɗin sarauta, duk da ya yi fice sosai ga waƙoƙin sarauta.

    Waƙar Sarauta

    Waƙarsa ta farko daya fara yi ta sarauta, ita ce wadda ya yiwa Banagan  Morai Alhaji Abdulmali a inda yake cewa :

    “Kai adda Morai riƙa

    Allah ya baka Morai riƙa ta da kyau

    Malikki ɗan Muh’d Macciɗo,

    Malikki ɗan Abu Banaga,

    Ɗan Farinruwa ɗan Danau,

    Garnaƙaƙi bari tsoron maza,

    Na Abu Morai, Ɗanmusa.

     

     

     

    Wannan ita ce waƙa ta farko da Dangunduwa Kagara ya fara yi ma wani basarake. Wannan shi ne dan takaitaccen bayanin yadda Dangunduwa ya koyi sana'arsa ta waƙa. Duk a cikin waƙoƙinsa na farko akwai wata waƙa ta sarkin Morai inda ya fara ta ne kai tsaye:-

    "Ya hana gwangwani gwauron Majikira ƙansaƙin Danau,

    Alhaji Banaga na jekada Allah kai dai ya zaɓa,

    Da girmanai ya hau na malam,

    Da halin girma zai sauka

    Ya hana gwangwani gwauron Majikira ƙansaƙin Danau

    4.1.3 Yaransa

    A wannan fagen za mu kawo bayanai dangane da yaransa kuma abokanan sana’arsa ta kiɗa da waƙa.Ya zama dole idan ana zancen makaɗa Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara a yi zancen yaransa, domin su ne masu taimaka masa wajen fito da waƙarsa. Saboda da yawa za ka ji a cikin wasu waƙoƙinsa idan ya faɗi gindin waƙa, ba zai ƙara cewa komai ba sai dai ya rinƙa yin shiru, su ko suna cigaba da waƙar har ƙarshenta, kamar yadda a waɗansu waƙoƙin su kuma yaransa idan suka yi amshi ɗaya a farko ba su ƙara cewa komai har sai ƙarshenta ayi amshi ɗaya, wannan yana faruwa ne domin mafi yawan waƙoƙinsa kamar bayanin wani abu ne da ya faru yake yi. Kuma ga jerinsu kamar haka :

    1.      Muhammmadu Ɗanbaraka - Makaɗi

    2.      Hussaini Abdullahi Maidiki - Makaɗi

    3.      Shehu Abdullahi Dangunduwa - Makaɗi

    4.      Sa’idu Tsauni - Makaɗi

    5.      Ummaru Ɗanauta Ɗan amshi

    6.      Mustapha Abdullahi - Ɗan amshi

    7.      Haruna Muhammadu Jatau - Ɗan amshi

    8.      Muhammadu Nagido - Ɗan amshi

    9.      Abdullahi Ƙwazo Mai kwazakke

    4.1.4. Yawace - yawacansa

    Kamar yadda muka yi bayani can baya cewa Abdullahi Dangunduwa Kagara mutun ne haziƙi a fagen waƙar Hausa. Abdullahi Dangunduwa tun farko da shi ake zagayawa ana yawace – yawace a duk inda aka je, domin yin amshin waƙa, ta haka ne ma Abdullahi Dangunduwa ya bi mahaifinsa ana waƙa yana amshi, har ma wata rana yana yi masa ƙari a cikin waƙarsa. Bincike ya nuna cewa, dangane da yawace-yawace wajen yin waƙa. duk faɗin tsofuwar jihar Arewa Maso Yamma wadda ta haɗa Sakkwato, da Kabi, da Zamfara, da lardin Neja  har a sauran garuruwan arewacin Nijeriya da kudaccinta, ba inda bai ƙafa ba a wajen yawon kiɗa da waƙa. Abdullahi Dangunduwa ya yi yawace – yawace domin isar da sana’arsa ta waƙa, wanda aka shaida mana cewa a wajen yawace – yawacansa na waƙa har wani masoyinsa ya biya masa kujerar hajji, bayan alhairan da yake samu wajen aiwatar sana’arsa ta waƙa.

    4.1.5. Shirya Waƙoƙinsa

    A kowane al’amari ko fanni, ana samun maɗaukaka da na ƙasa-ƙasa, saboda bambancin da Allah ya yi tsakanin bayinsa, haka ma a wajen makiɗa ana samun irin wannan banbanci domin wasu makiɗa sukan tsaya ne da su da yaransu ('yan amshi) tun a gida su shirya irin waƙar da za su je su yi ma wani mutun wanda suke son su yi wa waƙa. Irin su: Alhaji Musa Danƙwairo Maradun da Alhaji Aliyu Dandawo da sauransu domin su makiɗa ne na sarauta da ke son su zo waje su burge, ko dai wanda suka yi wa kiɗan ko jama’a. Amma shi Danbalade Morai mun sani cewa makaɗin maza ne sannan kamar yadda bayani ya gabata cewa shi ba wai ra’ayi da shawa ya sa yake kiɗa da waƙa ba a' a gadon abinsa ya yi wajen mahaifinsa.

    To a takaice dai, Abdullahi Dangunduwa Kagara shi makaɗin shawa ne tun lokacin da ya fara sana'ar, har lokacin da Allah ya amshi abinsa, saboda haka ba ya shirya komai na waƙa tsakaninsa da jama'arsa watau (makiɗa da 'yanamshi) domin idan an tafi daji ko fagen kiɗa, suna  amfani da duk wanda suke da shawar yi wa waƙa, ko wanene ko an san shi ko ba' a san shi ba, misali waƙar wani gwarzonsa da ya yi wa waƙa.

    Mai suna "Haruna Sarkin noman Mayanci. Wannan wani bawan Allah ne da Abdullahi Dangunduwa ya ji labarinsa ya yi masa waƙa kurum ba don ya san shi ba, sai bayan shekara biyu da yi masa waƙar sannan ya je ya kai ma sa ziyara.

    Wannan waƙar ga ta kamar haka:

    "Sarkin noma mai hana aikin gona ya kwan,

    Matsa a gama manyan makasa sabra Ɗan Abu,

    Haruna Ɗanbau barker ka da yaƙin tausar yama,

    Sarkin noma mai hana aikin gona ya kwan,

    Matsa a gama manyan makasa sabra Ɗan Abu,

    Gabas ga Mayanci ba ku da daji ko ɗankaɗan,

    Sarkin noman yamma ga titi ya kau da shi,

    Haruna Ɗanmani, daure ka yi min kyautar isa,

    Ni dai na san ba ka da ruwa ko yar kaɗan”.

     

    Wannan ita ce waƙar  da Abdullahi Dangunduwa Kagara ya yi wa sarkin noman Mayanci tun kafin su haɗu. Akwai  ire-iren waƙoƙin da yawa domin makaɗin tama bai san irin mazan da zai haɗu da su ba sai an je fagen  tama, amma tsayawa a shirya wata waƙa kafin a fita bai ko taso ba.

    4.1.6. Kayan kiɗansa

    Kayan kiɗan sun danganta da irin kiɗan da mai kiɗa ke aiwatarwa, saboda haka da yake Abdullahi Dangunduwa Kagara ya keɓanta ga masu sana'ar fawa da tama da kuma Sarauta, a halin yanzu, kayan kiɗan fawa da noma  da kuma sarauta yake amfani da su. Daga da baya ya fara waƙar sarauta, sai ya sami kotso. Kamar yadda bayani ya gabata cewa Abdullahi Dangunduwa Kagara, kiɗan sarauta ba gadonsa ya yi ba daga baya ne da ya ga ya  shahara fagen waƙa har ya yi wa Sarkin Morai Banaga Abdul malik Muhammadu waƙa, daga nan sai Sarkin Morai na yanzu wato Banaga Abdul malik Muhammadu  sai ya ga cewa ya kamata ya canza tafashe sai ya saya masa kotso domin ya riƙa amfani da shi wajen kiɗan sarauta.  Kalangu da kwazakke wajen kiɗan fawa da noma.Ga kayan kamar haka :

    1.      Kalangu

    Alh. Abdu Dangunduwa Kagara Da Wakokinsa

    2.      Kotso

    Alh. Abdu Dangunduwa Kagara Da Wakokinsa

    3.      Kwazakke

    Alh. Abdu Dangunduwa Kagara Da Wakokinsa

    4.1.7 Nau’oin waƙoƙinsa

    Kamar dai yadda ya zo cikin bayani cewa Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara mutum ne haziƙi da fasaha, kuma ya shahara akan waƙoƙin Hausa, kuma ya yi  waƙoƙi daban-daban; iri-iri, kala-kala ire-iren waƙoƙinsa su ne kamar haka:-

    Waƙar Fawa

    Su kuma dai waɗannan waƙoƙi na fawa su na zuga mahauci komahauta su yi bajin ta da sibiri, irin na shan Gumba ko kuma  kamun "Sa" ko su dubi sa ya faɗi a yanka shi, da sauran waɗan su abubuwa na nuna bajin ta, da kuma nuna kwarewa ga sauran runji, da bada shawa ga wanda ke kallo ko saurare, muna iya ganin wasu misallan wadannan waƙoƙi kamar haka :-

    “Sai na kai kiɗa gidan sarkin fawa Ummaru,

    kai ash shugaban mayanka shanu kaf ƙasar Kagara,

    Dawo Ummaru ‘yanrujji ai sun san da ba su yi

    In dai Ummaru ya yi magana ban san mai iya tayar mai ba,

    Ai ga wani saunan sakin fawa,

    Shi bai yanka bai alheri,

    Sai in sun yi ya dauki kwashi”

     

    Waƙar Noma

     

    Waɗannan waƙoƙi ana yin su ne domin a cusa ƙwazo da karsashi a zuciyar manoma su motsa, su -girgije, su duƙufa ga noma. A cikin waƙar wani sarkin noma Lawali Anka,. Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara yana cewa :

                           « Lawali na Abu sarkin noma,

    Allah mai san Anka in ga Lawali na Abu sarkin noma,

    Lawali ko ana fari ya fi gaban kakare,

    Lawali ka noma ɗari ka kuma noma dubu don mun gani ».

     

    Dama Hausawa ba abin da suke so irin wannan kiɗa na noma, ka san halin Bahaushe mazauni karkara ga kiɗa irin na noma domin ba ya da wata sana’a da ta wuce noma. Kamar sauran waƙoƙin noma su ma sun ƙunshi jigon yabo, zuga misali a cikin wata waƙa yana cewa:

     

    “Ga wagga ƙasa duk mai riƙa kalme ya san da kai,

    Gabas da yamma ga Mayanci ba su da daji ko ɗan kaɗan

    Sarkin noman yamma ga kwalta ya sassabe,

    Na Ɗan mani barkarka da yaƙin noman hatsi,

    Na Ɗan mani barkarka da yaƙin noman gyaɗa”.

     

     

     

    Waƙar Sarauta

    Waƙoƙin sarauta, galibin su sun keɓanta ga wasu jinsin mutane a cikin al'ummar Hausawa waɗanda suka ƙunshi sarakuna ko 'yan sarki, ko kuma duk wani wanda sarki ya ke naɗawa ya zama wani shugaba a cikin al'umma. Waɗannan rukunan mutane ne ake yi wa waƙa irin ta sarakuna. Waƙar sarakuna keɓantacciya ce, ba kowa ake yi wa ita ba sai irin su sarakuna da hakimai da ‘ya’yan sarakai. Waƙoƙin sarakuna ana yin su ne domin cusa yabo da zuga ga zukatan sarakuna. Waƙoƙin suna ƙunshe da jigon yabo,
    zugi kwazo da kumaƙauna misali a cikin wata waƙa ta sarkin Anka  waton  maimartaba Sarkin Zamfara Attahiru,  makaɗa Ɗangunduwa yana cewa:-

    Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta 

    Bai yarda a rammai ba, ba takura jan zaki,

    Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta

    Alhaji Ɗan Ummmaru giwa ba kikan kula da tarkoba,

    Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta,

    Maigima mai Kadandaɓa mai BirninTudu da Janbaƙo,

     

    a.       

     

     

    4.1.8. Rasuwarsa

    Kamar yadda bayanai su ka zo daban – daban dangane da Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara, tun daga haifuwarsa har zuwa ƙurciyarsa da yadda ya gudanar da rayuwarsa. Abin da aka sani ne cewa kowace rayuwa za ta ɗanɗana mutuwa, haka Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ya rasu ranar Litanin 16 / 10 / 2015. Ya bar mata ɗaya da ‘ya ‘ya  kamar

    i. Muhammadu

    ii. Hussaini,

     iii.Ya’u,

    iv.Ummaru,

     v. Sa’idu,  

    vi.Nana Fiddausi.

    Bayan rasuwarsa, ɗansa Muhammadu shi ya gade shi kuma shi ke jagoranci aiwatar da wannan sana’ar ta waƙa kamar yadda babansa, watau Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ya gada ga mahaifinsa Ibrahim.

    4.2. Matsayin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara a Tsakanin Mawaƙan Da da Na Yanzu

    Kamar yadda yakan kasance kowane mutun bai rasa abokanan hulɗa duk fannin da yake gudanar da harkokinsa na sana'arsa. Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara shi ma yana da dangantaka da wasu makaɗa da mawaƙa kamar haka:-

    Alhaji Abdullahi Xangunduwa yana da alaƙa makusanciya da wasu abokan sana’arsa. Daga ciki akwai Alhaji Danbalade Morai. Shahararren makaɗin fawa / dambe da noma da kuma sarauta a cikin ƙasar Talata Mafara da Ƙwazo Bagega da Abamu Maradun, mai kiɗan 'yandambe, da Ibrahim Dangulbi, da Musa Ɗangulbi da Muhammadu Maiturare Wababe. A cikin duk waɗannan makaɗa, dangantakar da ke tsakaninsa da makaɗa Alhaji Danbalade Morai ta fi ƙarfi sosai dalilin kusanci da ke tsakanin garuruwan da su ke zaune. Ko da yaushe sukan haɗu. Hasali ma, sukan ziyarar junansu koyaushe. Hasali ma duk abin da za su yi, sukan shawarci junansu.

     A wani ƙauli, cewa aka yi Alhaji Danbalade Morai ne ya fara shawartar Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara da ya kai ma sarkin Morai waƙa. Bincike ya tabbatar da cewa daga baya sun ɗan sami takin saƙa tsakaninsu. Ana kyautata zaton cewa ganin ɗaukakar da Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ya samu inda har aka saya masa kayan kiɗan sarauta ne ya sa dangantaka tsakaninsu ta yi tsami. Idan kuwa muka koma wajen mawaƙan yanzu Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ba ya da wata dangantaka a tsakaninsa da mawaƙan yanzu domin bai yi wata cikakkiyar hulɗa da su ba.

    4.3. Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa

    Kamar dai yadda ya zo cikin bayani cewa Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara mutum ne haziƙi mai fasaha, kuma ya shahara akan waƙoƙin Hausa, kuma ya yi  waƙoƙi daban-daban; iri-iri, kala-kala ga wasu daga cikin waƙoƙinsa su ne kamar haka:-

    Waƙarsa da ya yi wa sarkin Mayanchi Sabon gari Ƙashimu ga ta kamar haka:-

     

    "Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

    Sabon gari Ƙashiu,

    Allah babban mutum ya yi ka,

    Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

    Sabon gari Ƙashiu,

    Na Anaruwa ƙara gyaran faɗa,

     

    4.4. Nazarin waƙoƙinsa

    A cikin wannan nazarinwasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara, zai kasance sharhi kan waɗansu waƙoƙi da muka zabo a cikin waƙoƙinsa. Wannan sharhi zai shafi jigon waƙoƙinsa, warwarar jigo, salo waƙoƙinsa, salon sarrafa harshe, salon armashi da zubi da tsari waƙoƙinsa.

    Daga farko za mu fara da sharhi akan waƙar  sarkin Anka  waton  Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru, in da ya ke cewa :

    4.4.1. Turken Waƙoƙinsa

    Kamar yadda muka sani jigo a cikin waƙoƙin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara, shima abin da waƙar ta ke tafe da shi ko kuma abin da waƙar ta ke son ta isar ga alumma. Saboda haka ita wannan waƙa jigonta shi ne zuga, watau a inda yake cewa:

    "  Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta »

    Bai yadda a rammaiba, ba takura jan zaki,

    Alhaji Ɗan Ummmaru giwa ba kikan kula da tarkoba,

    Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta,

    Maigima maikadandaɓa maibirnin tudu da Janbaƙo »

     

     Idan muka duba a cikin wannan waƙa daga baiti na ɗaya har zuwz na biyu, a nan jigon ya nuna mana cewa sarkin Anka  waton  Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru wani shahararren sarki ne wanda bai yarda da wasa ba, kuma ba a kai masa reni sannan kuma ya bayyana shi sarkin Anka  waton  Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru da cewa idan baya nan sarakuna suna yadda sukaso, amma idan sun ganai duk sunzan kamar ba sarakuna ba,. Dan haka Dangunduwa Kagara ke kiransa da cewa:-

    Bai yadda a rammaiba, ba takura jan zaki »

     

    A cikin wannan waƙa, Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ya na nuna mana cewa ko shakka babu, Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru da gaskiya yake yin mulminsa ba da wasa yake yi ba.

    Bayan haka, duk a cikin waƙar Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru ya fito mana dawani jigo na nuna bajin ta, da Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru ya yi haka kuma ya bayyana mana shi dai Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru duk yawan da ya bamu labarin jaruntakar shi idan an fito fagen fama, dangane da haka sai a dubi wannan baiti:-

    "  Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta »

     

              A nan makaɗa Abdullahi Dangunduwa Kagara ya na sun ya bayyana mana irin jaruntakarsa, da kuma nuna sadaukantaka da bajinta da Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru yake da ita.

    Salon waƙar

             To a cikin wannan waƙa ta Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru, Makaɗa ya fara wannan waƙa ta Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru kai tsaye ba tare da budewa da komi ba ita wannan waƙa Dangunduwa Kagara ya fara tane da:-

                  "  Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta »

     

    Haka kuma ya kara da salon danbantarwa ya na cewa:-


       "
    Alhaji Ɗan Ummmaru giwa ba kikan kula da tarkoba"

     

          Bayan haka, ya yi amfani da salon siffantawa a ya yin da ya siffanta, shi wannan shahararren dan damben da cewa:-

     " ba takura jan zaki".

     

     

    A nan in muka duba, Dangunduwa ya kamanta wannan shahararren basarake da wannan baitin, domin ya na nuna ma duniya cewa wannan basarake shi sadaukin sarki ne.

             Bayan haka Abdullahi Dangunduwa Kagara ko shakka ba bu ya yi amfani da salon yabo kamar haka:-

    Idan muka yi la' akari da wani baiti a cikin wannan waƙa, wurin day a ke nuna cewa a lokacin day a na aikin gomnati ya kawo wurai – rai daban – daban inda ya yi aiki  Abdullahi Dangunduwa Kagara ya na cewa “kowa ya yaba da aikinsa”

           Bayan haka, kuma cikin wannan waƙa Abdullahi Dangunduwa Kagara ya yi amfani da salon aron kalmomi, musamman daga harshen larabci har dai in muka yi la’akari da wannan baiti da ke biye :

                             ‘Ya Allahu Rabbana ba ni abinda zan faɗa,

       Kar yanduniya su rena ni’.

     

    Ko shakka ba bu idan muka dubi wannan baiti za muga cewa gaskiya ne Abdullahi Dangunduwa Kagara ya yi amfani da salon aron kalmomi domin wannan kalma ta Allahu da Rabbana duk ya aro su ne daga harshen larabci.

    4.4.2. Zubi da Tsari waƙoƙinsa

    Ita wannan waƙar Abdullahi Dangunduwa Kagara ya fara ta ne kai tsaye tare da nuni zuwa ga ‘yan sarki ya na cewa: -

    «  Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta »

     

     Haka kuma wannan mawaƙi Abdullahi Dangunduwa Kagara ya kuma tsara waƙarsa ne acikin baiti biyu-biyu, sannan yan mai maita wasu daga cikin baitocin bayan haka yan amshi su na yi mashi ƙari.

    Idan muka yi la'akari da bayanin da ya gabata da kuma yadda muka yi bayani tun farko cikin nazarin waƙar Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru, na kawo zubin baitocin waƙoƙin baka ya sha bambam dana rubutatun waƙoƙin domin a cikin waƙoƙin baka za mu tarar da cewa akwai layi biyu - biyu ne, dan haka wanda ya ke a rubutattu ba haka abin ya ke ba sai dai idan waƙa mai ɗango biyu-biyu zai kasance kowane baiti yana da waɗannan ɗangwayen wato biyu ko uku ko hudu ko kuma biyar.

    Haka zalika a cikin wannan waƙar Dangunduwa ya fara kai tsaye da kiran sunan basaraken, yana cewa :

    Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta 

     

    Bayan  haka wannan mawaƙin ya tsara wakarsa ne acikin baiti biyu-biyu, sannan ya na marmaita wasu daga cikin baitocin, bayan haka ‘yan amshi suna yi mashi ƙari.

              Zubin layukkan baitocin waƙar baka ya sha bamban da rubutacciyar waƙa, domin kuwa a cikin waƙar baka ana iya samun baiti mai dangi daya (gwaron dango) ko baiti mai dango biyu (tagwai ko mai dango uku). (yar uku) ko hudu (tarbi’i) ko kuma biyar (tahamisa) har ma fiye da haka ana samu a cikin waƙoƙin baka. Amma ita waƙar da muke nazari, tana da layukka da zuwa biyu a matayin dango guda misali, 1, 2.

    4.4.3. Turken waƙoƙinsa

    Kamar yadda bayani ya gabata cewa duk waƙoƙin Alhaji Dangunduwa Kagara ba su wuce Muhimman turke guda biyu ba, watau zuga da turken yabo, to shi wannan jigon yabo shi ma kamar yadda jigon zuga ya kasu kashi biyu shima ya kasu kashi biyu, domin akwai yabon na musamman watau na Alheri da ake yi masa sannan akwai yabo irin na koɗawa watau irin wanda ya ke aiwatarwa  ga mutanensa watau ‘runji, manoma ko sarauta.

    Misali kamar yadda za mu gani a cikin wasu waƙoƙin fawa na Alhaji Dangunduwa Kagara , turken kamar yadda muka sani cewa turke a cikin waƙoƙin shi ne abin da waƙar take tafe da shi ko kuma abin da waƙar take son ta isar ga al'umma. Saboda haka ita wannnan waƙa turken shi ne zuga, watau a inda ya ke cewa:-

    "Sai na kai kiɗa gidan sarkin fawa Ummaru, kai ar shugaban mayanka shanu kaf ƙasar Kagara,

    Dawo Ummaru ‘yan runji ai sun sanda ba su yi

    Ida Ummaru ya yi magana ban san mai iya tayar mai ba,

    Ai ga wani saunan sakin fawa,

    Shi bai yanka bai alheri,

    Sai in sunyi ya ɗauki kwashi”

     

           Idan muka duba a cikin wannan waƙa daga ɗa na biyu har zuwa na uku, a nan jigon ya nuna mana cewa sarkin fawa Ummaru wani shahararren barunje ne wanda bai yarda da wasa ba, kuma ba a kai masa reni sannan kuma ya bayyana shi sarkin fawa Ummaru da cewa”idan Ummaru ya yi magana ban san mai iya tayar mai ba. Dan haka Dangunduwa Kagara ke kiransa da cewa:-

    Ummaru ‘yanrujji ai sun sanda ba su yi

     

    A cikin wannan waƙa, Dangunduwa Kagara ya na nuna mana cewa ko shakka babu, Sarkin Fawa Ummaru da gaskiya yake yin wannan sarauta ba da wasa yake yi ba.

    Bayan haka, duk a cikin waƙar Dangunduwa Kagara ya fito mana da wani zambo, dangane da haka sai a dubi wannan baiti:-

    " Ai ga wani saunan sarkin fawa,

       Shi bai yanka bai alheri,

       Sai in sun yi ya ɗauki kwashi”

     

              A nan Dangunduwa Kagara yana son ya bayyana mana irin lalacewa da kuma nuna komawar baya da wani sarkin fawa ya yi a fagen sana’arsa ta fawa.

    4..4.4. Warwarar Turke

    Jigo shi ne wani muhimmin saƙon da mawaƙi yake son isarwa a cikin waƙarsa, watau manufar ko maƙasudin waƙar. (Gusau, S.M. 1989).

    Shi ma Dokta Tanimu Yar’aduwa a cikin littafensa yana cewa turke shi ne ginshiƙin waƙa don kuwa duk waƙar da ta kasance ba ta da turke to ba waƙa ba ce. Akwai masana adabi ko masu nazarin waƙa sun yi laakari da fito da wasu hanyoyin nazarin waƙa wajen nazarin turke :

    1. Hanya ta farko ita ce ka gano jigon wajen sauraron da kake yi, watau mene ne saƙon mawaƙin.

    2. Hanya ta biyu ita ce bayan ka gano abin da mawaƙi yake nufi a waƙarsa sai ka yi ƙoƙarin bayyana turken mawaƙin.

    3. Hanya ta uku ita ce wanda maisauraro zai warware turkenn ko feɗe turken mawaƙi.

    Turken Zuga

     Kamar yadda muka sani cewa turke a cikin waƙoƙin baka kamar ta makaɗa Dangunduwa Kagara shi ne abin da waƙar ta ke tafe da shi ko kuma abin da waƙar take son ta isar ga al'umma. Saboda haka ita wannnan waƙa turkenta shi ne zuga, watau a inda yake cewa a cikin waƙarsa ta noma:-

                            "Lawali na Abu Sarkin noma,

    Allah mai san Anka inga Lawali na Abu Sarkin noma,

    Lawali ko ana fari ya fi gaban kakare,

    Lawali ka noma ɗari ka kuma noma dubu don mun gani ».

                        Ga wagga ƙasa duk mai riƙa kalme ya san da kai,

    Gabas da yamma ga hanya ba su da daji ko ɗan     kaɗan

    Sarkin noman yamma ga kwalta ya sassabe,

    Na Ɗan mani barkerka da yaƙin noman hatse,

    Na Ɗan mani barkerka da yaƙin noman gyaɗa”.

     

           Idan muka duba a cikin wannan waƙa daga saɗara ta uku har zuwa ta shida, a nan turken ya nuna mana cewa Lawali wani shahararren manomi ne wanda bai yarda da wasa ba, kuma ba a kai masa reni sannan kuma ya bayyana shi Lawali da cewa Lawali ko ana fari ya fi gaban kakare, Dangunduwa Kagara ke kiransa da cewa:-

    “Na Ɗan mani barkakka da yaƙin noman hatsi,

     Na Ɗan mani barkakka da yaƙin noman gyaɗa”.

     

    A cikin wannan waƙa, Dangunduwa Kagara yana nuna mana cewa ko shakka babu, Lawali da gaskiya yake yin wannan sana’a ba da wasa yake yi ba.

    Bayan haka, duk a cikin waƙar, Dangunduwa Kagara ya fito mana da wani turke na nuna bajinta, da Lawali ya yi haka kuma ya bayyana mana shi dai Lawali duk yawan da ya ba mu labarin jaruntakar shi idan an fito fagen fama, dangane da haka sai a dubi wannan ɗa:-

    "Na Ɗan mani barkakka da yaƙin noman hatsi,

     Na Ɗan mani barkakka da yaƙin noman gyaɗa”.

     

              A nan Abdullahi Dangunduwa Kagara yana son ya bayyana mana irin jaruntakarsa, da kuma nuna bajinta da Na Ɗanmani yake da ita, idan an fito fagen fama.

    Haka kuma Abdullahi Dangunduwa Kagara cikin waƙarsa ta Sarkin Mayanchi, ya fito mana da wani turke

    Idan muka duba wannan waƙar za mu ga cewa turken wannan waƙar ya fito ne a cikin ɗa na bakwai. A nan ya nuna mana cewa, Sarkin Mayanchi wani shahararran Sarki ne, wanda Abdullahi Dangunduwa Kagara ya fito mana da turken Juriya ga wannan basarake wato Sarkin Mayanchi inda yake cewa:

    "Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

    Sabon gari Ƙasimu,

    Allah babban mutum ya yi ka,

    Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

    Sabon gari Ƙasimu,

    Na Anaruwa ƙara gyaran faɗ

    Tsare aiki cikin gaskiya

    Duk mai aikin cikin gaskiya

    Yana samun rabon duniya

    Yana samun rabon lahira

    Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

    Sabon gari Ƙasimu,

    Allah babban mutum ya yi ka.

     

     

     

    A cikin wannan ɗa, Abdullahi Dangunduwa Kagara ya nuna mana cewa Sarkin Mayanchi, Shahararren sarki ne mai gaskiya, saboda zamansa buwayayye sai dai kallo domin duk yadda ka yi ba za iya ba shi cin hanci ya yi rashin gaskiya ba kamar yadda mawaƙin ya nuna mana cewa,                   Tsare aiki cikin gaskiya,

    Duk mai aikin cikin gaskiya "

    To kaga wani ɗan ya nuna mana cewa mai gaskiya ne, duk abin da ka yi sai dai ka gaji ka barshi wuri nai.

    Idan muka yi la'akari da bayanin da ya gabata a nan za mu iya cewa wadannan waƙoƙin na Abdullahi Dangunduwa Kagara na da muhimmin saƙo, wannan saƙon kuwa nau'i - nau' ne daga cikinsu akwai babban saƙon da ya haifar da a aiwatar da su daga cikinsa akwai saƙon zuga watau. turken zuga ke nan san nan akwai saƙon yabo watau turken yabo kenan, dan haka turken zuga shi ne babban turken waƙoƙin Abdullahi Dangunduwa Kagara saboda. Kasancewar mashahuri a wajen kiɗa, Abdullahi Dangunduwa Kagara na tabbatar mana da cewa dama shi turken waƙoƙinsa zuga da yabo, domin a cikin waƙarsa ta Banagan Morai watau Alhaji Abdulmalik, akwai inda yake rerawa da bakinsa cewa:-

    "Banaga Ubanƙasa mai kwana da martaba,

      Dandanau na Bubakar,

      Banaga Ubanƙasa gumbar tsakkuwa,

      Wai wawa da yagguma,

      Haure nan yakkatse "

     

            Saboda haka idan muka dubi wannan gutsiren waƙa ta Abdullahi Dangunduwa Kagara za mu fahimci cewa wannan zuga ne ya ke yi tsakanin sa da wani.

        Haka a cikin wannan waƙa har yanzu Abdullahi Dangunduwa Kagara na cewa:-

    Ni ka hadawa bani rabawa

     Duk wadannan ire-ire zuga ne waton.zuga sarki, shi da wasu kalmomi domin ya firgice ya ba shi kyauta, ko wani abu mai kama da haka. Kamar yana haɗa shi da wasu ‘yan sarki ko kuma wasu talakkawa da sauransu, haka kuma wannan zugin yana sa sarki ya ƙara shiri. Misali a cikin waƙar da Abdullahi Dangunduwa Kagara ya yi ta  Musa Narabi ta noma akwai inda yake cewa :-

    Sai dare yana daji gonatai,

    dawo na Rabi mai kalme wa kilba".

     

    Shi kuma Jikin sa ya yi kaf da zan-zana sai ya fara kirari kamar haka:-

    "Kai Abdu mai kidin Noma,

    Wai na ji kana yabon kanen su Tafarki,

    To gobe in muka game wurin noma,

    Rannan sai anyi ba dare ba rana,

    In bani ba Abdu kanan su Tafarki,

    Rannan in ba a sha ga Gyamdama ta watse,

    Ko yaggiya ta tsuke ke shi”.

     

    A takaice irin wannan zuga a tsakanin sarakuna ko manoma yana da yawa, sai dai mu kawo irin waɗanda muke iya kawowa.

    Turken Habaici

    Habaici wanda ya ke tamkar zagin kasuwa ne wani jigo ne wanda makaɗa Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ke amfani da shi a cikin waƙoƙinsa domin ya adanta waƙarsa ko ya yi suka ga wani mutum zuwa ga wadansu manoma ko wadansu mutane na daban. Haka kuma ya kan yi amfani da shi domin ya isar da wani saƙo ga sarki ko wanda ya kewa waƙa. Misali a cikin waƙarsa ta sarki Morai Banaga Abdulmalik in da ya ke cewa:-

    ai ga wani yasha kashi,

    ya iske tumaki kwance,

    sai yace ku wadanga ina kwana ku".

     

                Haka kuma cikin waƙarsa da yawa wannan basaraken in da ya ke cewa:-

    Wai wawa da yagguma,

      Haurenan yakkatse ".

     

     

    A cikin duk kan waɗannan misalai guda biyu da mu ka zai yano zamu ga cewa makaɗa Abdu Dangunduwa shi na habaici ga wadansu jama'a, haka kuma shi na da kyau a san cewa shi habaici ya babban ta da zambo , domin ba'a fadin siffar mutum ko sunan shi, sai dai a yi zagin kasuwa kowa ya doka don kai ne.

     

    Turken juriya.

    Haka kuma Abdu Dangunduwa ya yi amfani da turken juriya. Watau anan ana nuna ainihin karfin halin mutun wajen jurewa wahala ko wace iri ce da kuma nu na cewa idan wani ya sami kansa cikin wannan wahala to ba shakka ba zai yi raki ba. Misali a cikin waƙar da Abdu Dangunduwa ya yi inda ya ke cewa:-

                              "Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

                          Sabon gari Ƙashimu,

                          Allah babban mutum ya yi ka,

                          Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

                          Sabon gari Ƙashiu,

                          Na Anaruwa ƙara gyaran faɗa »

     

    Turken zambo

     

    Haka kuma Abdu Dangunduwa Kagara ya yi amfani da turken zambo. Zambo shi ne munana mutum KO kuma muzanta shi, misali a cikin waƙar Abdu Dangunduwa Yana cewa:-

    Dan sarki yakoma kamar mata Yana shapa

    hoda da jan baki yara suna cewa koya tafu

     

    Idan muka yi la'akari da wandannan ɗiyan za mu ga cewa ko shakka babu Abdu Dangunduwa ya yi zambo ne ga wasu maƙiyan  wannan basaraken domin ya ƙara rage mu su darajja a idon jama'a domin shi wannan basaraken ya kara harzuƙa kuma darajarsa da ƙara fitowa a idan mutane.

    Turken Yabo

               Kamar yadda bayani ya gabata cewa duk waƙoƙin Alhaji Abdu Dangunduwa ba su wuce Muhimman turke guda biyu ba, watau zugi da turken yabo, to shi wannan turke na yabo shi ma kamar yadda turken zuga ya kasu kashi biyu shi ma ya kasu kashi biyu, domin akwai yabon na musamman watau na Alheri da ake yi masa sannan akwai yabo irin na koɗawa watau irin wanda yake aiwatarwa  ga mutanensa watau  manoma ko sarauta.

    Yabon alhairi

    Shi wannan turken na yabo da Abdu Dangunduwa ke amfani da shi wajen yabon mutanen da ke taimaka masa saboda nuna gamsuwar su da irin abin da yake yi kamar a cikin waƙarsa ta Banagan Morai ya kawo irin su Maudaci da Direban sarki da Bunun Morai, da sauransu.

    Turken Yabo Irin Na Koɗawa

       Kamar yadda muka bayyana baya cewa akwai turken yabo irin na koɗawa watau, yabo ne da ake amfani da wasu kalmomi irin waɗan da su sarakuna ko manoma suke son a rinƙa kiransu da su ko wani aiki wanda za a yabe su da shi a ce su suka yi shi ko da ko ba su aikata shi ba. Misali,  irin waɗannan kalmomi sun fara ne tun daga sunayensu misali za ka ji sunnan su kamar haka: zaki, gwarzo, toron giwa da dai sausansu

    To dai kamar yadda sunayen nan na su yake to a kuIlun haka suke son a rinƙa yabon da ire-ire wadannan ababe misali idan ka dubi waƙar babban gwarzonsa watau yabo kamar inda ya ke cewa:-

    "Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

     Saban gari Ƙasimu »

     

    Kai abin sai dai kurum domin idan ka dubi irin wannan yabo ka san cewa daban ne da irin wanda Alhaji Abdu Dangunduwa ya ke wa su mutanen Mayanchi da dai sauransu. Inda yake cewa :

    «  Mutan Mayanchi muna godiya zay yawa,

     Domin kun yo abin a yaba ».

    Saboda haka irin waɗannan kalaman da ya ke amfani da su ga sarakuna ba irin sa ne ya ke yi wa mutanen da ke bashi alheri ba amma dai duk yabo ne.

    4.4.5. Salon Waƙoƙin Alhaji Abdu Dangunduwa

    Ma’anar Salo:

    Wata hanya ce ko dabara ce da mawaƙa ko marubucin waƙa ke bi domin ya isar da saƙo ga masu saurarensa.

    Ire-iren salai-lan da yake amfani da su, game gari ga duk wani mawaƙi ko marubuci shi ne salon siffantawa wani naui ne na salo wanda mawaƙi ke amfani da shi ya siffanta wani abu da ka ganshi ka ce ai wannan ne. A ƙarƙashin wannan akwai salo daban-daban misali salo kamanci, salon kinaya salon jinsarwa, salon alamtarwa da sauransu. (Gusau, S. M..1984).

             Saboda haka Alhaji Abdu Dangunduwa ya fi amfani da salon jinsarwa a cikin waƙoƙinsa. Salon jinsarwa: shi ne wani nou’i na salon siffantawa wanda ke nufin daukar darajar wani a ɗaro wa wani wato kamar ka ɗauki darajar mutum ka ba dabba, ko ta tabba ka ba mutum.To shi jinsarwa saƙo ne wanda ya kasu gida? (uku) kamar haka:-

    1.      Matumtarwa

    2.      Dabbantarwa

    3.      Abuntarwa

               A cikin waƙarsa wanda ya yi wa Maimartaba Sarkin Zamfara ya yi amfani da salon kambamawa in da ya ke cewa:-

    « Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta,

     Ba takura jan Zaki »

     

             Haka kuma Alhaji Abdu Dangunduwa ya yi amfani da salon dabbantawa a cikin waƙarsa ta Mai martaba Sarkin Anka a  inda yake cewa:-

     "Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta,

     Ba takura jan Zaki 

     

     

    Sannan Alhaji Abdu Dangunduwa a cikin waƙarsa da ya yi wa Banagan Morai ya yi amfani da wasu salailai na domin ya mutunta ko isar da saƙo ko ya  fito da ma'anar waƙar  domin ta yi armashi ga mai sauraro ga ta kamar haka:-

                           "Na Anaruwa ƙara gyaran faɗ

                               Tsare aiki cikin gaskiya

                            Duk mai aikin cikin gaskiya    

                            Yana samun rabon duniya

                            Yana samun rabon lahira".

     

    Waɗannan ire-ire salailai da Alhaji Abdu Dangunduwa ke amfani da su mun saurare su ne da kaɗan kaɗan a cikin kasusuwa da muka saurara, da kuma wasu al’umma na kusa da shi.. Haka idan aka duba za a fahimci cewa Alhaji Abdu Dangunduwa Yana amfani da salon mai-maitawa a cikin waƙoƙinsa misali kamar a cikin waƙar inda ya ke cewa:-

    “Ya Na samun rabon duniya

      Ya na samun rabon lahira

     

    “Ya Na samun rabon duniya

      Ya na samun rabon lahira

     

        

     

     

     Haka zalika, a cikin waƙar "Sarkin fawa" watau sarkin fawan da ya fara yi wa waƙa akwai inda yake amfani da irin wannan salo na maimaitawa inda yake cewa:-

    Kai ɗan asalin fawa dodo,

     Kai ɗan asalin fawa dodo"

    da sauransu.

     

    A nan za mu kalli nau’oin salo a nazarin adabin hausa kamar haka :

    1. Salo sassauka ko miƙaƙƙen salo, wananan shi ne salo mai saukin fahimta wanda mai sauraro zai fahimci mawaƙi a kan abin da yake son isar da saƙo. Shi ne mawaƙi ya yi amfani da kalmomin Hausa sassauƙa.

    2. Salon tafiyar kura ko kwan- gaba kwan- baya ko salo maganar mata, shi wannan salo shi ne wanda mawaƙi zai sarrafa waƙarsa ta hanyar sai yana ba maisauraro labari kai tsayi sai kuma ya yanke ya dawo baya ko kuma ya kawo wani abu sabo shi wannan salo yana ba mai sauraro ciwon kai ko rashin fahimtar saƙo cikin sauki.

    3. Salo mai armashi da nashaɗantarwa, wannan salo shi ne wanda mawaƙi zai kawo nishaɗi da burgewa, wannan salo shi ne wanda zai sa mai sauraro ya yi ta sauraron waƙa harƙarshenta. Shi ne mai sa nishaɗi da bandariya ga mai sauraro.

    4. Salo kwarjanta harshe, shi wannan salo shi ne wanda ya ke ƙara kwarjinin harshe ga maisauraro in da mawaƙi zai riƙa kawo karin magana da habaicida sauransu.

    5. Salon ɗanmagori acikin wannan salo ne mawaƙi ya ke wasa kansa da kansa ko kuma ya wasa tauraronsa kafin ya haɗu da abokin gaba da dai sauransu.

    6. A kwai salo kashe jiki shi irin wannan salo, shi ne salon da mawaƙi zai yi ta kawo abubuwan alajabi ko ma su bantsoro, ko tausayi wadan da za su sa mai sauraro jikinsa ya mutu ko tsoro ma ya kamashi.

    7. Salon waskiya ko kauceya, wanana salo shi ne wanda mawaƙi zai yi amfani da dubaru dan ya kaucewa haɗarin da zai faɗa ko kuma ya kaucewa jin kunya, duk acikin wannan salo ne mawaƙi zai yi ƙoƙarin kaucewa irin haɗarin da ya shiga tun farkon waƙarsa.

    8. Salon jinsarwa shi ne wani nau’i na salon siffantawawanda ke nufin daukar darajar wani a dorawa wani wato kamar ka ɗauki darajar mutum ka ba dabba, ko darajar dabba ka ba mutum. Misali ; Mutmtarwa, Dabbantarwa da Abutarwa.

    9. Salon kambamawa shi ne wanda mawaƙi ke amfani domin ya kambama wanda ya ke wa waƙa don ya yi abinda bai isa ya yi ba. Dokta Tanimu Yaraduwa.Adabin Hausa, acikin laccassa ya fada a Bayero Kano.2/4/2008.

    4.4.6. Salon Sarrafa Harshe

    Da farko zamu kalli ma’anar salon sarrafa harshe.To salon sarrafa harshe dai masana sun yi rubuce – rubuce akan ma’anar salon sarrafa harshe, a nazarin adabin Hausa. Shi ma wani masanin adabin Hausa mai suna Isah Muktar wanda ya rubuta ma’anar salon sarrafa harshe a cikin littafensa mai suna Jagoran nazarin salon ƙagaggun labarai a 2002.Yana cewa Salon sarrafa harshe wani fage ne na more zaƙi, ko kwalliya da mawaƙi ko marubuci yake ɗauke da  su yadda za su ba da zantukka masu ma’ana da shawa da hikima  a cikin waƙarsa.

    Acikin salon sarrafa harshe Alhaji Abdu Dangunduwa yake sarrafa harsheta hanyar jujjuya kalmomi, a cikin jimloli masu sauƙin fahimta, a inda yake yin amfani da kalmomi sassauƙa domin ya kaucewa tsofaffin kalmomi sannan kuma idan zai taƙaita sai kuma ya taƙaita cikin sababbin kalmomi.

    Misali a cikin waƙarsa ta Sabon Garin Mayanchi inda yake cewa:

    " Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

    Sabon gari Ƙasimu,

    Allah babban mutum ya yi ka,

    Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

    Sabon gari Ƙasimu,

    Na Anaruwa ƙara gyaran faɗa".

     

    Duk a cikin salon sarrafa harshe ne Alhaji Abdu Dangunduwa Kagara yake ƙoƙarin adanta waƙarsa, watau ya yi kwalliya wajen waƙarsa, ta yadda yake amfani da kalaman jawo hankali ga mai saurarnsa ta hanyar luggar harshe misali: kamar su salon kamantawa, salon mutuntawa, salon dabbatarwa da ƙarangiya. Haka kuma tattare da adan harshe Alhaji Abdu Dangunduwa Kagara, ya yi ta amfani da kawo karin magana domin waƙarsa ta yi armashi ga mai sauraro , daga cikin adan da Alhaji Abdu  Dangunduwa Kagara ya fi amfani da su su ne salon kamantawa, salon mutuntawa, salon dabbatarwa.

    4.4.7. Salon Amshi

    Ya za ma dole idan ana zancen makaɗa Alhaji Abdu Dangunduwa Kagara a yi zancen ‘yan amshi, domin su ne masu taimaka masa wajen fito da waƙarsa. Saboda da yawa za ka ji a cikin wasu waƙoƙinsa idan ya faɗi kan waƙar ba zai ƙara cewa komai bas ai dai ya rinƙa yi musu shara su ko suna cigaba da waƙar harƙarshenta, kamar yadda a waɗansu waƙoƙin su kuma yanamshin idan su ka yi amshi ɗaya a farko ba su ƙara cewa komai harsai ƙarshenta ayi amshi ɗaya, wannan yana faruwa ne domin mafi yawan waƙoƙinsa kamar bayanin wani abu ne da ya faru yake yi.

    Misali a cikin waƙarsa ta Sarkin Mayanchi inda yake cewa:

    " Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

    Sabon gari Ƙashimu,

    Allah babban mutum ya yi ka,

    Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,

    Sabon gari Ƙashiu,

    Na Anaruwa ƙara gyaran faɗa".

     

    Haka a cikin waƙar da ya wa "Sa'idu Dan mutanen Wasagu" yana cewa:-

               "Alhaji Dan Ummaru Giwa ba ki kan kula da tarkoba".

     

    Idan muka saurari misalinmu na farko za mu ji cewa ‘yan amshi da suka yi amshi ɗaya a farko ba su ƙara cewa komai har sai ƙarshenta duk kalamansa ne har sai ƙarshenta su ka karba, wannan ya faruwa ne domin kamar bayani ne yake na wani abu da ya faru yake yi. Haka kuma, idan muka saurari misalinmu na biyu za mu ji cewa ‘yan amshi ne suke ta amshi tun  a farko da ya yi musu shara bai ƙara cewa komai har sai ƙarshenta duk kalamansu  ne har sai ƙarshenta su ka karba baki ɗaya. Waɗannan su ne misalan salon amshinwaƙoƙin.

    4.4.8. Zubi Da Tsarin waƙoƙinsa

    Wata hanya ce ko dabara ce da mawaƙa ko marubucin waƙa ke bi domin ya tsara waƙarsa akan wasu layukka na fasaha yandaya, biyu, uku ko fiye da haka. Domin ya isar da saƙonsa cikin sauƙi. Misali :  

     Ita wannan waƙar Dangunduwa Kagara ya fara ta ne kai tsaye tare da nuni zuwa ga ‘yan sarki ya na cewa: -

    « Ga wani ya fito biɗar sarauta bai samu ba,

    Can nigga nai da ɗankwashe ya na biɗar burgu,

    Tona hannuya rame tona hannuwa kogo,

    Bari kububuwa ta sare shi,

     

           Haka kuma wannan mawaƙi Dangunduwa Kagara ya kuma tsara waƙarsa ne acikin baiti biyu-biyu, sannan yan mai maita wasu daga cikin baitocin bayan haka yan amshi su na yi mashi ƙari.

          Idan muka yi la'akari da bayanin daya gabata da kuma yadda mukayi bayani tun farko cikin nazarin waƙar Maimartaba Sarkin Zamfaran Anka, na kawo zubin baitocin waƙoƙin baka ya sha bambam dana rubutatun waƙoƙin domin a cikin waƙoƙin baka za mu tarar da cewa akwai layi biyu - biyu ne, dan haka wanda ya ke a rubutattu ba haka abin ya ke ba sai dai idan waƙa mai ɗango biyu-biyu zai kasance kowane baiti ya na da waɗannan ɗangwayen wato biyu ko uku ko hudu ko kuma biyar.

           Haka zalika a cikin wannan waƙa Dangunduwa Kagara ya fara kaitsaye da kiran Sarkin Zamfaran Anka, ya na cewa :

    “Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta”

     

     

    Bayan haka wannan mawaƙi (Dangunduwa Kagara) ya tsara wakarsa ne acikin baiti biyu-biyu, sannan ya na marmaita wasu daga cikin baitocin, bayan haka yanamshi su na yi mashi ƙari.

              Zubin layukkan baitocin waƙar baka ya sha bamba da rubucciyar waƙa, domin kuwa a cikin waƙar baka ana iya samun baiti mai dangi daya (gwaron dango) ko baiti mai dango biyu (tagwai ko mai dango uku). (yar uku) ko hudu (tarbii) ko kuma biyar (tahamisa) harma fiye da haka ana samu a cikin waƙoƙin baka. Amma ita waƙar da muke nazari, ta na da layukka da zuwa biyu a matayin ɗango guda misali 1,2.

     

     

    4.5. Naɗewa.

    A wannan babi mun fara gabatar da shi ne.Inda aaka kawo bayanai game da gundarin taken bincike. Wato, fashin baƙi a kan Dangunduwa Kagara da waƙoƙinsa a inda mu ka fara da shinfiɗa,Tarihin Dangunduwa Kagara, Haihuwarsa, ƙurciyarsa da Tasowarsa da Neman iliminsa, Koyo da fara  waƙoƙinsa, Yaransa, Yawace yawacensa, Shirya waƙoƙinsa, Rasuwarsa, Matsayin Dangunduwa Kagara a tsakanin mawaƙan Da da na yanzu, Kayan kiɗansa, Nau’oin waƙoƙinsa, Wasu daga cikin waƙoƙinsa, Nazarin waƙoƙinsa, Jigon waƙoƙinsa, Warwarar jigo, Salon waƙar Dangunduwa Kagara, Salon Sarrafa Harshe, Salon Amshi, Zubi Da Tsarin waƙoƙinsa da kuma Naɗewa.  

     

     

     

     

     


     

    BABI NA BIYAR

    SAKAMAKON BINCIKE

    6.0.Shinfiɗa

    Kamar yadda za mu gani a cikin wannan babi na biyar shi ne babin ƙarshe a wannan bincike da aka gabatar. Za mu  gabatar da shinfiɗa, sakamakon bincike, shawarwari, naɗewa da kuma manazarta

    5.1. Sakamakon Bincike

    A wannan bincike an koro bayanai acikin sassauƙar hausa yadda mai karatu ko mai nazarin hausa zai iya karantawa ya fahimmci abinda wannan binkike yake tafe da shi na Nazarin wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara, Sakamakon wannan bincike shi ne bincike tare gano jigogi da salailai na wasu daga cikin waƙoƙinsa musamman a kan waƙoƙin fawa, nomad a kuma sarauta, tare da zayyana irin rawar da waƙoƙinsa ke takawa cikin, adabin Hausa.

    Bayan haka tabbas sakamakon wannan bincike shi ne taimakawa wajen raya adabin Hausa, da kuma barma na baya tarihi da abin koyi da ƙara harzukasu kan su tashi tsaye gadan-gadan domin ganin anci gaba da raya wannan adabi na Hausa.

     Ko shakka babu, muna hasashen cewa kammaluwar wannan aiki zai taimaka wajen raya harshen Hausa dan haka ya sa muka zaɓi rubuta kundinmu a kan nazarin nazarin wasu daga cikin  wakokin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara .

    Ba shakka a sakamakon wannan aiki, waƙoƙin Hausa na da babban muhimmanci kwarai ga rayuwar Hausawa. Waƙa ta baka ko rubutatta, kamar yadda muka sani tun ba yau ba, ita ce hanya mafi sauki da ake bi wajen isar da saƙo ga Jamaa.

    Babban sakamakon shine Kasancewar waƙoƙin baka na Hausa, ya ƙara ba mu shaawa da ƙwarin gwiwa na yin wannan bincike, domin mu bayyana hikima da haziƙancin da ke ga Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara.

    Muna hasashen cewa wannan kundi ne domin ya zama kundin tara bayanai ya kuma zama silar cusa sha’awar nazarin harshen hausa, ko shakka babu; muna da ƙwararan dalilai da ya sa muka zaɓi rubuta kundinmu a kan nazarin wasu daga ciki waƙoƙin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara.

    5.2. Shawarwari

    Dangane da wannan bincike da aka aiwatar, shawarwarin da nazarin zai bayar sun ta’allaƙa ne kai tsaye ga marubuta da manazarta da kuma masu sauraro da makaranta waƙoƙin baka na Hausa tare da makarantun da ake nazarin harshen hausa a kowane mataki, da kafofin watsa labarai da kuma iyaye ko masu kula da shaanin tarbiyar masu tasowa.

    Haƙiƙanin gaskiya, da marubuta da masu sauraro da ma su nazarin waƙoƙin baka za su iya amfani da iliminsu da hikimar da Allah ya hore musu, su dawo rakiyar waƙoƙin da suka shafi shaanin duniya da ake yi domin samun dukiya, su koma kan na fadakar da mutane da tarbiyyantar da su da an samu kyakkyawan ci gaba a cikin al’umma. Babban abin da za’a lura da shi shine, waƙoƙin a lokuttan baya masu dauke da manufofin waɗanda da su ne ake amfani da su domin madubin rayuwa, sun sha babban da na yanzu.

    5.3. Naɗewa

    Kamar yadda aka ga sunan wannan aiki «Nazarin wasu daga cikin waƙoƙinsa Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara », wannan babi shine babin da aka naɗe tabarmar binciken, wato babin ƙarshe a wannan bincike da aka gabatar. An tantauna sakamakon binciken da aka yi da irin nasarori da aka samu. Sannan kuma an yi duba zuwa ga shawarwarin da za su taimaka ga ci gaban aikin da kuma amfanin al’umma.

      A babi na farko a cikin tsarin wannan aiki an kawo abubuwa da dama wanda suke sune muhimman bayanai na shimfida. Da farko an kawo gabatarwa da shinfiɗa, manufar bincike, hasashen bincike, farfajiyar bincike, matsalolin bincike, muhimmancin bincike, hanyoyin gudanar da bincike da kuma naɗewa.

    Babi na biyu kuwa, wanda shine na biyu a cikin tsarin wannan aiki an  kawo abubuwa wanda suke su ne muhimman bayanai kamar haka ; Shinfiɗa bitar ayukkan da su ka gabata, hujjar cigaba da bincike,  da kuma naeɗewa.

    Shi kuwa babi na uku Kamar yadda za mu gani a cikin wannan babi na uku shi ne, wanda aka kawo fashin baƙi a kan maanonin da suka shafi taken bincike a inda aka fara da shinfiɗa, ma’anar waƙa, ire iren waƙa, ma’anar jigo da ire-irensa, zubi da tsari da kuma ma’anar salo da ire-irensa tare da cikakken misalai sai kuma naɗewa.

    Babi na hudu kuwa wanda nan ne zuciyar aikin. Kamar yadda muka gani a cikin wannan babi na hudu shi ne, fashin baƙi a kan wasu daga cikin waƙoƙinsa Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara  a inda aka fara da shinfiɗa, Takaitaccen Tarihin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara, waƙoƙin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara, waƙarsa ta Fawa, waƙarsa ta Noma, waƙarsa ta Sarauta, da kuma naɗewa.

    Daga ƙarshe a wannan bincike da aka gabatar, an gabatar da shinfiɗa da bayani akan  sakamakon bincike da kuma gabatar da shawarwari,sai muka  nadewa da kuma kawo manazarta wannan bincike

     


     

    MANAZARTA

    Alhaji Lwal Faruku (1997) rayuwar ƙwazo Bagega da Waƙokinsa, a kundin daya rubuta.

    Abdurrahman da Ahmad na Baba Tsafe, da Attahiru Rufai Gwandu (1993) raruwar Sani Sabulu na kanoma da Waƙokinsa a kudin su da sukarubuta

    A cikin kaset muka ciro Waƙoƙkin Danbareade Morai, da mu kayi amfani da su wajen gudanar da wannan aikin.

    A cikin Littafen Fulani Empire muka samu Takaitaccen tarihin garin Morai a shafi na 928 don nemen ƙarin bayani.

    Ashiru (2001) kudin digiri na farko mai taken: “Jigon kishi a cikin rubutattun waƙoƙin soyayyah.

    Firar mu da Babban Abokinsa kuma Malaminsa Muhammadu Sa’aban Morai 29/3/2020.

    Garba Keku (1992) rayuwar Salisu Jankiddi. Kudinsa da ya rubuta.

    Gusau, S.M. (1993). Jagoran Nazarin waƙoƙin Baka. Kaduna. Fisbas Media Services.

    Gusau, S. M. (1984) Nazarin Zababbun waƙoƙin Baka na Hausa Kano Jamiar Bayero.

    Gusau, S. M. (1989). Tsokaci A kan Waƙar Sahibi, Kano Jamiar Bayero.

    Dan Gambo, A. (2017). http.//m. facebook, com permalink.

    Dokta Tanimu Yar’aduwa. (1982) A cikin Nazarinsa na Kundin Digiri na Biyu wanda yay a A Kano: jamiar Bayero.

    Faru D. L (1997) Kwazo bagega da Waƙoƙkin sa, kudin N.C.E a Sashen Hausa SSCCE Sakwato.

    Muhammad Y. Nsarawa da na Muhammad Khalid (1997) Nazari a kan Alhaji Abdu-inka Bakura da Wakokinsa.

    Lawal, (20140) salon sarrafe harshe a cikin kagaggun Labaran Hausa nazari daga littafin Za-i-naka a kudinsa na neman digiri na farko a jamiar Usmanu Danfodiyo Sakkwato.



    An samu wannan bayani ne daga bakin wani dattijo maisuna Namaimuna kuma mabanbaɗansa a ranar 29/06/2023.

    An sami wannan bayani ne a wurin wani dattijo mai suna Mayau wanda maƙwancin Ɗangunduwa ne. An yi hira shi ranar Talata, 29/06/2023.

      Daidai da tushen bayani na 2.

    www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.