Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

Kundin Binciken Da Aka Gabatar Na Neman Digirin Farko, Ƙarƙashin Sashen Harsunan Najeriya Da Walwalar Harshe, Tsangayar Adamtaka, Jami'ar Sule Lamiɗo Kafin Hausa, Jihar Jigawa, Yuli, 2023. 

GUDUNMAWAR DAM ƊIN MUHAMMADU AYUBA, WAJEN BUNƘASA TATTALIN ARZUKI DA AL'ADUN GARIN KAZAURE.

NA 

YUSIF MUKHTAR
Yusifmukhtar24@yahoo.com
+234 (09) 037920843 

TABBATARWA

 Haƙiƙa na tabbata cewa, ni Yusif Mukhtar ni na rubuta wannan kundin bincike da kaina, mai suna: “Gudummawar Dam ɗin Muhammadu Ayuba wajen bunƙasa tattalin arzuki da Al'adun garin Kazaure”.

 A ƙarƙashin jagorancin Hon. Dr. Habibu Abdulƙadir Musawa. Duk bayanan da aka samo daga wata madogara, babu shakka na ambato madogarar a cikin matani ko kuma manazartar da aka kawo a ƙarshen wannan kundi. Babu wani ɓangare na wannan aiki da aka taɓa gabatarwa ko wallafawa a wani wuri, a matsayin kundin digiri ko na diploma ko na takardar shedar malanta ta ƙasa wato (NCE) ko kuma maƙalu da mujallu.

SHAFIN AMINCEWA

 Wannan kundi mai taken “Gudunmawar Dam ɗin Muhammadu Ayuba, wajen Bunƙasa tattalin arzuki da Al'adun garin Kazaure”. Ya sami damar karanta wa da duba wa, da samin amince wa a matsayin wani ɓangare na cika sharuɗɗa da ƙa’idar samun takardar shaidar kammala digiri na farko (B.A HAUSA). A tsangayar Adamtaka, sashen nazarin harsunan Najeriya da Al'adu, A Jami'ar Sule Lamiɗo da ke Kafin Hausa, jihar Jigawa.

SADAUKARWA

 Na sadaukar da wannan aiki ga abubuwan alfaharina kuma ababen koyina wato iyayena, Alh. Mal. Mukhtar Lawan Ɗankullu, da Malama Rabi'atu Musa. Sannan na sadaukar da wannan aiki ga ahalin "DARHO FAMILY". Da "HAJIYA "RABI'ATU FAMILY". Bayan haka na sadaukar da wannan aiki ga malamaina da kuma Duniyar ilimi, da sauran Jama'a, waɗanda Alƙalami bai sami damar dangwalar tawada, wajen rubuta sunayensu ba, su ne waɗanda suka sanya ni a hanya ingantacciya tun daga ƙuruciyata har zuwa wannan mataki da nike a yanzu.

GODIYA

 Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, masanin dukkan halittun sarari da na ɓoye. Dukkan yabo da godiya sun tabbata gare shi. Allah ka yi daɗin tsira ga fiyayyen halitta, shugaban dukkan manzanni kuma manzon ƙarshe, bawan Allah Annabi Muhammadu Ɗan Aminatu da Abdullahi, Sallallahu alaihi wa sallam! Godiya marar iyaka ga Allah (S.W.T), wanda ya ba ni dama da ikon karatu da kammala shi a Jami'a mai tarin albarka ta Sule Lamiɗo da ke garin Kafin Hausa, cikin jahar Jigawa, ya Allah! Ka sanya albarka a cikin wannan karatu na mu. Amin summa amin!

 Haƙiƙa yabon gwani ya zama tilas, saboda haka ina miƙa godiya ta musanman ga iyayena Alh. Mal. Mukhtar Lawan Adam da Marigayiya Hjy. Rabi'atu Musa Allah ya jaddada rahama amin da Dr. Ibrahim I. Ahmad Todarya bisa shawarwari da gudummawa tare da nuna ƙauna ta musamman a gare ni Allah ya ƙara ɗauka, haka kuma ina miƙa godiya ta musamman ga babbar yayata wato A'isha Mukhtar Lawan da sauran yayye na da ahalina, da kuma abokan arzuƙa a bisa irin gudunmawoyinsu a kaina Allah ya biya ku amin.

 Ba zan yi tuya in manta da albasa ba, wajen miƙa bangajiya da godiya marar misaltuwa ga jagoran da ya yi ƙoƙari matuƙa gaya, wajen sadaukar da lokacinsa da iliminsa, domin ganin an aje ƙwarya a gurbin da ya dace, ma'ana ayi aiki ingantacce, wato haziƙi fasihi Hon. Dr. Habibu Abdulƙadir, wanda shi ne ya yi min Jagoran wannan aiki, tun daga farko har zuwa ƙarshe na sami damar kammala wannan bincike cikin nasara. Allah ya ƙara ilimi da ɗaukaka ya ƙaro arziki marar yankewa da basira, Na gode Allah ya ƙara hasken makaranta, ya kawo ci gaba mai amfani. Allah ya saka masa da mafificin alheri, ya sa Aljanna Firdausi ce makoma a gare mu ranar gobe ƙiyama, Amin summa amin.

 Haka kuma ina miƙa godiya ta musamman ga shugaban wannan sashe na nazarin harsunan Najeriya da kimiyyar harshe na Jami'ar Sule Lamiɗo wato; Dr. Ma'azu Sa'adu Muhammad (Dr. Kudan). Wanda bisa jajircewa da amince wa da shawarwari da kyakkyawan jagorancinsa muka gudanar da wannan karatu na digirin farko. Allah ya ƙara buɗi da basira da ci gaba mai amfani.

 Sannan ina miƙa babbar godiya ta musamman ga Jajirtaccen malami haziƙi fasihi kuma adali wato; Malam Abdulƙadir Ginsau, wanda ya yi ƙoƙari matuƙa gaya wajen sadaukar da iliminsa da lokacinsa da sauran damammakin da yake da su, wajen ganin Albasa ta yi halin ruwa wato wannan aiki ya inganta. Allah ya ƙaro ɗaukaka da arziki marar yankewa Amin. Haka kuma ina miƙa godiya ta musamman ga sauran kafatanin malaman wannan sashe, irin su: Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, da Farfesa Isah Mukhtar, da Farfesa Muhammad Aminu Mu'azu, da Farfesa Usman Usaini Fagge, da Farfesa Salisu Garba Kargi, da Farfes Ibrahim Garba Satatima, da Dr. Ɗahiru Abdulƙadir Dr. Auwal Ado Aujara (Dr. A.A. Aujara) da Dr. Abdulmumini da Dr. Jamilu Muhammad da Malam Muhammad Sani Lawan, da Malam Hassan Sabo, da Malam Yusuf Nuhu Inuwa da Malama Halima Kurawa, da Sauran malaman Sashe baki ɗaya, waɗanda suka bayar da irin ta su gudummawar wajen karatu da shawarwarin da suka dace ɗalibi ya yi amfani da su wajen gudanar da karatu har ya kawo ƙarshe. Allah ya ƙara basira ya saka musu da alheri baki ɗaya.

 Haƙiƙa ɗan halak ba ya mantawa da alheri, ya zama tilas a gare ni na miƙa godiya ga Farfesa Yusufu Abdullahi Riɓaɗo da Farfesa Sani Lawan Taura da Farfesa Umar Saje, da Dr. Mustapha Hussaini Garun Gabas da Malama Hussaina Ibrahim Ringim, da Malam Izaddeen da sauran waɗanda Allah bai sa na ambaci sunayensu ba, na gode! Allah ya saka da alheri amin.

 Tabbas! Ba zan taɓa mantawa da abokan Karatuna ba, waɗanda muka fara gwagwarmayar karatu da su, tun daga farko har zuwa wannan lokaci ba, irin su: Adamu Sulaiman, da Umar Muhammad Ɗan-Asabe da Jazuli Nuhu Achilafiya da Aminu Ado Usman da Usman Sani da Usman Abdullahi, da Sayyida Habiba Abubakar Ibrahim B/Kd, ƴar uwa kuma Babbar Aminiya, da Tawakkaliyya Mukhtar da Bahijja Ibrahim Adamu da Maryam Aliyu Usman da Hafsat Lawan Tambari da sauran waɗanda ban ambaci sunayensu ba, haƙiƙa ina matuƙar alfahari da su.

 Godiya marar misaltuwa zuwa ga Hukumar masarautar Kazaure mai albarka a bisa gudunmawar da aka ba ni, wajen samar min da abubuwan da na ke buƙata daga gare ta, a yayin gudanar da wannan bincike, tabbas masarautar garin Kazaure ta haɗa ni da waɗanda suke da sani kan tarihi da harkokin da suka shafi garin Kazaure da kewaye, ba zan taɓa mantawa da wannan gudunmawa ba na gode! Allah ya saka da alheri ya ƙara wa sarki lafiya amin.

 A ƙarshe ina miƙa godiya zuwa ga Al'ummar garin Kafin Hausa da Jami'an tsaron Kafin Hausa, a bisa zama na lumana da mu ka yi da su na tsawon wani lokaci, mun zauna lafiya ba cuta ba cutarwa Allah ya saka da alheri, na gode!

TSAKURE

Wannan bincike mai taken "Gudunmawar Dam ɗin Muhammadu Ayuba wajen bunƙasa tattakin arziki da Al'adun garin Kazaure". An aiwatar da shi ne a bisa dalilin samar da rubutaccen kundi, mai ɗauke da tarihi da gudummawar Dam ɗin Muhammadu Ayuba ya bayar, wajen bunƙasa tattalin arziki da Al'adun garin Kazaure. Ganin cewar ayyukan da hannu ya kai gare su waɗanda magabata suka gudanar, a kan abubuwan da suka shafi garin Kazaure, ba su himmatu sosai ba a kan abun da ya shafi Dam ɗin Muhammadu Ayuba ba.

 Wannan shi ne ya bayar da damar himmatuwa domin aiwatar da wannann bincike, a kan Gudunmawar Dam ɗin Muhammadu Ayuba, domin fito da bayanai masu muhimmanci a kansa. Da kuma samar da abun karanta wa da nazari ga ɗalibai da kuma manazarta waɗanda suka haɗa da: Manazartan tarihi da al' adu, da sauran Jama'a masu sha'awar karance-karance.

 Domin haka manufar wannan bincike ita ce nazari akan Dam ɗin Muhammadu Ayuba, domin gano irin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa tattalin arzukin garin kazaure. Sannan yana daga cikin manufar wannan aikin, ƙoƙarin nuna fa'idar da Dam ɗin yake da ita ga rayuwar Al'ummar Kazaure da sauran Jama'ar Hausawa baki ɗaya, tare da nuna yadda Hausawan yau suke riƙon sakainar kashi da kayan tarihinsu da kyawawan al'adunsu na dauri. Sannan an yi ƙoƙarin nuna muhinmanci da fa'idar da Dam ɗin Muhammadu Ayuba yake da ita ga rayuwar mazauna garin Kazaure da sauran mutanen da suka kasance Hausawa.

Hanyoyin da aka bi yayin gudanar da wannan bincike, sun haɗa da: Ziyartar ɗakunan karatu na Jami'o'i da cibiyoyin bincike da masana tarihin garin Kazaure da ziyartar Dam ɗin domin gani da ido da kuma zanta wa da masu gudanar da sa'na'o'i a ciki da wajen Dam ɗin na Muhammadu Ayuba.

 Tabbas an tabbatar da abin da manazarta suke cewa "Sana'o'in gargajiyar Hausawa suna bunƙasa tattalin arzukin Al'umma, wanda daga cikin sana'o'in har suke yi wa wata kirari da cewa" Noma tushen arzuki". An kuma kawo bayanai akan ire-iren sana'o'in da ake gudanarwa a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba. Tare da bayyana gudunmawar su wajen bunƙasa tattalin arzukin garin Kazaure.

 

 

MAƘUNSHIYA

TABBATARWA----I

SHAFIN AMINCEWA----II

SADAUKARWA----III

GODIYA------IƁ

TSAKURE----ƁII

ƘUNSHIYA----IƊ

BABI NA ƊAYA.

GABATARWA

1.0 SHIMFIƊA----1

1.1 DALILAN BINCIKE----3

1.2 MANUFAR BINCIKE----4

1.3 MUHINMANCIN BINCIKE----5

1.4 FARFAJIYAR BINCIKE----7

1.5 TAMBAYOYIN BINCIKE----8

1.6 MA'ANAR MUHINMAN KALMOMI--9

 1.6.1 Gudunmawa----9

 1.6.2 Dam------9

 1.6.3 Muhammadu Ayuba----9 1.6.4 Bunƙasa----9

1.6.5 Tattalin arzuki----10

1.6.6 Garin Kazaure----10

1.7 NAƊEWA----10

BABI NA BIYU.

BITAR AYYUKAN MAGABATA

2.0 SHIMFIƊA----12

2.1 TAƘAITACCEN TARIHIN GARIN KAZAURE--13

2.2 TAƘAITACCEN TARIHIN MUHAMMADU AYUBA17

2.3 TAƘAITACCEN TARIHIN DAM ƊIN MUHAMMADU AYUBA20

2.4 MA'ANAR AL"ADA----23

 2.4.1 Rabe-raben Al'ada----26

 2.4 2 Muhinmancin Al'ada----28

 2.4.3 Sifofin Al'ada----29

2.5 MAKAMANTAN BINCIKE----30

 2.5.1 Bugaggun Litattafai ----31

 2.5 2 Kundayen Bincike----33

 2.5.3 Maƙalu----38

 2.5.4 Mujallu----41

 2.5.5 Takardun ƙara wa juna sani----43

 2.5.6 Jaridu ----46

2.7 NAƊEWA--49

BABI NA UKU

HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

3.0 SHIMFIƊA----50

3.1 LURA/SA-IDO----51

3.2 NAƊAR ZANTUKA----51

3.3 ƊAUKAR HOTUNA----52

3.4 TATTARO BAYANAI TA HANYAR RABA MATAMBAYIYA.52

3.5 TATTAUNAWA/ZANTAWA--53

3.6 TATTAKI----53

3.7 NAƊEWA----54

BABI NA HUƊU

GUNDARIN BINCIKE

4.0 SHIMFIƊA----55

4.1 GUDUNMAWAR DAM ƊIN MUHAMMADU AYUBA GA AL’UMMAR KAZAURE------55

4.2 GUDUNMAWAR DAM ƊIN DANGANE DA RAYA AL’ADUN GARGAJIYA NA BAHAUSHE ----57

 4.2.1 Sana'ar Su (kamun kifi)..----57

 4.2.2 Sana'ar Noma----63

 4.2.3 Sana'ar Fawa----70

 4.2.4 Sana'ar Ga-ruwa----73

 4.2.5 Sana'ar Wanki----74

 4.2.6 Sana'ar Kiwo----75

4.3 TASIRIN AL'ADUN SIHIRI DA SUKA SHAFI DAM ƊIN MUHAMMADU AYUBA----76

4.4 CAMFE-CAMFEN DA SUKA SHAFI DAM ƊIN MUHAMMADU AYUBA------78

4.5 TASIRIN SANA'O'I NA ZAMANI DA SUKE A DAM ƊIN MUHAMMADU AYUBA----79

4.6 NAƊEWA----81

BABI NA BIYAR.

KAMMALAWA

5.0 SHIMFIƊA----82

5.1 TAƘAITAWA----82

5.2 SAKAMAKON BINCIKE----84

5.3 SHAWARWARI----86

5.4 NAƊEWA----88

MANAZARTA------90

MUTANEN DA A KA TATTAUNA DA SU---.94

RATAYE NA 1, 2,

BABI NA ƊAYA

GABATARWA

1.0 SHIMFIƊA

 Wannan nazari an yi shi ne a kan; “Gudunmawar Dam ɗin Muhammadu Ayuba wajen bunƙasa tattalin arzuki da Al'adun garin Kazaure”, da kuma ta wace hanya Dam ɗin yake haɓaka tattalin arzukin da Al'adun garin Kazaure dangane da sana'o'in gargajiya na Bahaushe.

 Nazarin al'adun gargajiya kan iya taɓo dukkanin ɓangarorin rayuwar al'ummar Hausawa ta kowane fanni, kamar abincinsu, tufafinsu, muhallinsu, sarautunsu, sana'o'insu, magungunansu, bukukuwansu, sarautunsu, da sauransu. Kamar sauran al'ummomin Duniya, Hausawa al'umma ce da Allah ya sanya mata riƙon al'adunsu na gargajiya, da kuma yin amfani da su a dukkanin waje ko muhallin da suka tsinci kansu, kuma suna ba da ƙwazo da himma da ƙoƙari gami da jajircewa wajan ganin sun inganta su. Irin wannan ƙoƙari da ƙwazon ne ya sa ake samun sana'o'in gargajiya daban-daban, waɗanda suka haɗa da; Su (kamun-kifi) da Noma da Fawa, da Sassaƙa da Farauta da Ƙira da Wanzanci da Jima da Rini da Dukanci da Fatauci da Ɗinki da Saƙa da Ɗori da kuma uwa uba wato Malanta, kamar yadda masu fasahar baka kan ce; "ilimi jagoran rayuwa".

 Suna yin amfani da waɗannan nau'o'in sana'o'in wajan samar wa da kawunansu abubuwan biyan buƙatunsu na yau da kullum, kuma suna ba wa waɗannan sana'o'in muhimmanci matuƙa gaya. A wannan nazari an duba an tantance an ware tsakanin zare da abawa an zaƙuko wasu daga cikin sana'o'in gargajiya na zahirin Bahaushe wanda suke gudana a jiya da kuma yau a ciki da wajen Dam ɗin garin Kazaure na Muhammadu Ayuba (magajin gari) wanda tattalin arzuƙin garin Kazaure yake ɓunƙasa da kuma haɓaka ta dalilinsu, waɗannan sana'o'in sun haɗa da: Noma da Su (kamun-kifi) da Fawa da wankin tufafi da na motoci da babura da adon cikin gida da kuma sana'ar ga-ruwa da ake samu a rijiyoyin da aka gina a Dam ɗin wanda ake ɗibar ruwan ana shiga da shi lunguna da saƙo-saƙo kwararo da tudu na cikin garin Kazaure, gami da samar da wani yanayi mai kyau da ban sha'awa da Dam ɗin yake bayarwa wanda ya sanya ɗalibai da masu shirya finafinai suke ziyartar gurin domin inganta sana'arsu, da sauran sana'o'in Hausawa na gargajiya birjik kamar sana'ar Aski da Yankan farce da Saƙa da Rini da Jima da Faskare da makamantansu.

 Waɗannan sana'o'in sanannu ne kuma daɗaɗɗu ne a wajen al'ummar Hausawa, kayayyakin da ake samarwa ta hanyarsu suna da matuƙar tasiri da amfani ga al'ummar Hausawa kamar yadda nagartattun masana da manazarta irin su: Bunza (2006) da Sani (1986) da Rimmer (1948) da Garba (1999) da sauransu suka bayyana. A wannan babin ne za a yi bayanin wasu ginshiƙai kuma ƙashin bayan kowane irin bincike na ilimi, wanda in babu su to tabbas babu nagartaccen bincike, wato dalilin bincike da manufa gami da tambayoyin da binciken yake ɗauke da su har da iya farfajiyar da bincike ya gudana, domin Hausawa kan ce: "Dai-dai ruwa dai-dai tsaki", da sauran muhinman abubuwan da bincike na ilimi yake da su.

1.1 DALILAN BINCIKE

 Kamar yadda aka riga aka sani kowane abu da ake gudanarwa ko ake kan aiwatarwa a kwai dalilan aiwatar da shi. Saboda haka wannan bincike yana da dalilai masu tarin yawa wanda suka haɗa da;

  1. Dalili na farko da ya sanya wannan bincike shi ne; domin a samar da rubutaccen kundi mai ɗauke da gudunmawar da Dam ɗin muhammadu Ayuba ya bayar wajan bunƙasa tattalin arzuƙi da Al'adun garin Kazaure, ganin cewar ayyukan da hannu ya kai garesu wanda magabata suka aiwatar a kan wasu muhimman abubuwa na garin Kazaure, ba su himmatu sosai ba a kan abubuwan da suka shafi Dam ɗin, da kuma abubuwan da suke gudana a ciki da wajensa ba, wannan shi ne dalilin da ya ba da damar himmatuwa domin aiwatar da wannan bincike akan gudunmawar da Dam ɗin ya bayar wajen haɓaka tattalin arzuƙin garin kazaure tare da fito da bayanai a kansa a gargajiyance.
  2. Haka kuma daga cikin dalilan gudanar da wannan bincike akwai samun sahalewar kammala digiri na farko, kamar yadda doka ta ilimi ta tanada kafin a ba wa ɗalibi takardar shedar kammala digiri ya zama tilas a kansa ya yi rubutu akan wani batu mai muhinmanci domin bayar da muhimmiyar gudunmawa ga fannin ilimi.
  3. Wani dalilin na wannan bincike shi ne samar da muhimmi kuma nagartacce ingantaccen abun karantawa da nazari ga ɗalibai da kuma sauran manazarta waɗanda suka haɗa da; manazarta al'adu da tarihi da kuma sauran jama'a masu buƙata ko sha'awar karance-karance na ƙarawa kai ilimi da sauran dalilan da ba za a rasa ba.
  4. Na daga cikin dalilan gudanar da wannan bincike raya al'adun Hausawa da kuma la'akari da yadda suke wakana a ciki da wajen Dam ɗin muhammadu Ayuba (magajin gari) na garin kazaure domin taskance su da kuma adana su.
  5. Wani dalilin da ya sanya wannan nazari shi ne domin sanin irin abubuwan da suke da matuƙar muhinmanci ga rayuwar al'ummar garin Kazaure wanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin na Muhammadu Ayuba (Magajin-gari).
  6. Na daga cikin dalilan wannan bincike gano ta wace hanya Dam ɗin yake ba da muhinmiyar gudunmawa wajan haɓakar tattalin arzuƙin garin na Kazaure.

1.2 MANUFAR BINCIKE

 Hausawa sukan ce " In ka ji gangami, da labari", haka kuma masu fasahar baka na cewa " Banza ba ta kai zomo kasuwa". A kowane lokaci mutum ba ya yin wani abu sai yana da manufar da yake son cimmawa, haka kuma wannan bincike yana ɗamfare ko tattare da nagartattun kuma fasihan manufofi da yake da buƙatar cimmawa, wasu daga cikinsu sun haɗa da:

 Babbar manufar wannan bincike ita ce; nazari gami da bincike mai zurfi a kan Dam ɗin Kazaure na Muhammadu Ayuba, tare da binciko abubuwan da suke a ciki da wajensa, da suka shafi gargajiyar Bahaushe.

 Sannan kuma yana ɗaya daga cikin manufar wannan bincike ko nazari, ƙoƙarin nuna fa'idar ko amfanin Dam ɗin na Muhammadu Ayuba da irin muhinmancin da yake bayarwa ga rayuwar mazauna garin Kazaure da kuma sauran al'ummar Hausawa baki ɗaya.

 Haka kuma wata manufar wannan bicike ita ce; nuna yadda wasu Hausawan dauri da kuma Hausawan yau suke riƙon sakainar kashi da nuna halin ko in kula da suke yi a kan muhinman abubuwan tarihinsu da kyawawan al'adunsu da sauran wasu manufofi daban-daban.

1.3 MUHIMMANCIN BINCIKE

 Kamar yadda masana suka bayyana muhinmanci kalma ce da ke nuni da daraja ko ƙima ko martaba gami da inganci, a kowane lokaci aka ce ana gudanar da bincike a fagen ilimi ba ya rasa nasaba ko ƙoƙarin binciko wani sabon al'amari, ko kuma gano yanayin yadda wani abu ya ke faruwa ko ake kan gudanar da shi. Saboda haka wannan bincike ya na da muhimmanci kamar haka:

  1. Wannan bincike yana da muhinmanci ga wasu daga cikin fagagen bincike na Hausa, musanman ta ɓangaren al'ada da kuma Adabi, ma'ana wannan bincike da ake gudanarwa yana da muhinmin muhinmanci ga fannin al'ada, domin binciken ya taimaka wajen gano al'adun Hausawa, irin su Noma da kiwo da fawa da su (kamun-kifi) da sauran al'adun da suke a ƙasar Hausa. Ta hanyar adana ko taskance irin waɗannan abubuwa na al'adu a cikin kundi, wanda yin hakan ne zai ba da matuƙar gudunmawa ga ƴan baya akan irin kyawawan al'adun magabata, waɗanda suka haɗar da sana'o'i da bukukuwa da sauran al'adun al'umma.
  2. Haka kuma wannan bincike yana da matuƙar muhinmanci a fannin Adabi, kamar yadda masana suka bayyana Adabi shi ne hoto ko madubi ko taswira da al'umma suke amfani da shi wajan duba yadda al'umma suka hinmatu wajan gudanar da dukkannin al'amuran rayuwarsu. Haka ma wannan bincike zai bayyana yadda Al'ummar garin Kazaure suka rinƙa gudanar da rayuwarsu a zamanin da ya shuɗe kafin samuwar Dam ɗin Muhammadu Ayuba, da kuma yadda suke gudanar da rayuwarsu bayan samuwar Dam ɗin.

Haka kuma wannan bincike shi ma zai kasance tamkar wani madubi ne da mutane za su runƙa dubawa domin su samu damar sanin yanayin yadda al'ummar garin kazaure suka runƙa gudanar da rayuwarsu a zamani ko lokacin da ya shuɗe da kuma yadda al'ummar garin kazaure suke gudanar da rayuwarsu a wannan lokaci.

Haka kuma wannan bincike yana da muhinmanci a fannin tarihi, domin bincike ne da ake a kan abun da ya ruga ya shuɗe tun zamani daɗaɗɗe ko makusanci da ya shuɗe da kuma kan abun da yake kan gudana yanzu, da kuma kirdadon abun da ake zaton zai iya wakana a nan gaba. Saboda haka wannan bincike ne da ake gudanar da shi a kan Dam ɗin garin Kazaure na Muhammadu Ayuba, tare da yin bincike game da abubuwan da suka wakana a dalilin samuwar Dam ɗin , gami da hasashen abin da ka iya faruwa a nan gaba, tare da yin himma wajen ganin an taskance su domin ƴan baya masu nazari wata rana su duba su karanta su ga yadda magabatansu suka yi ƙoƙarin tafiyar da rayuwarsu, wanda hakan na iya zama sanadiyar su jinjinawa magabatansu a bisa ƙoƙarin da suka yi.

  1. Haka kuma muhinmancin bincike ba ya ƙarewa face an bayyana hanyoyi da kuma yadda binciken zai taimakawa ɗalibai da masu bincike (manazarta) wajen yin nazari, domin zai kasance wata ragin hanya ce ga masu nazari akan abubuwan da suka shafi al'adun Hausawa, da kuma garuruwan Hausawa.

1.4 FARFAJIYAR BINCIKE

 Hausawa na cewa " Kowa da kiwon da ya ƙarɓeshi, maƙwafcin mai Akuya ya sai Kura". Yayin da wasu masu fasahar baka kan ce; " Kowa da muhallinsa, an ce da Jemage kifi yana gayyatar ka biki", ya ce " a gayawa kifin ya kawomin gayyatar da kansa zuwa da kai ya zarce saƙo". Wasu gwanayen azanci suka ce " Dai-dai ruwa, dai-dai tsaki". Wato komai da iyakarsa, wannan bincike an ƙuduri aniyar aiwatar da shi ne a ɓangaren al'ada wato fannin sana'o'i da kuma Adabi wato fannin tarihi. domin zaƙulo ko binciko irin gudunmawar da Dam ɗin garin Kazaure na Muhammadu Ayuba ya bayar wajan haɓaka tattalin arzuƙin garin Kazaure, saboda haka wannan aikin bai shafi kimiyyar harshe ba, bincike ne da ya shafi al'ada da tarihi. Farfajiyar wannan bincike iya fannin sana'o'in Hausawa da sauran al'adun Hausawa ya shafa, waɗanda suke gudana a garin Kazaure, kuma a cikin garin Kazauren bai shafi kasuwanni ko masarauta ko duwatsun garin Kazaure ba, bai kuma shafi ruwan Dam ɗin garin Kazaure na Arewa da garin ba wato Dam ɗin Ibrahim Saminu Turaki. Haka kuma bai shafi Dam ɗin yammacin garin Kazaure ba wato Dam ɗin Dambo Dam, kuma bai shafi Dam ɗin Karaf-tayi ba, ya shafi iya Dam ɗin dake kudancin garin Kazaure wato Dam ɗin Muhammadu Ayuba ( magajin-gari).

1.5 TAMBAYOYIN BINCIKE

 Sanannen abu ne cewa duk wani nazari ko bincike na ilimi yana da tambayoyi ko kuma hasashen da yake da buƙatar tabbatarwa ko samun amsoshi nagartattu kuma ingantattu da za su amsa tambayoyin da binciken yake ɗauke da su. Saboda haka wannan bincike ma ya shirya tsaf domin gano amsar wasu nagartattun tambayoyi da yake ɗauke da su, kamar haka:

  1. Shin wace irin gudunmawa Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure ya bayar wajen haɓakar tattalin arzuƙi a garin Kazaure ta fuskar sana'o'in Hausawa na gargajiya?
  2. Anya samuwar Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure ya samar da wani ci gaba ga tattalin arzuƙin Kazaure ta fannin sana'o'in gargajiyar Bahaushe?
  3. Ko Dam ɗin garin Kazaure na Muhammadu Ayuba ya na da wata fa'ida ga mutanen garin kazaure da kewayanta?
  4. Ko a kwai wani sihiri na Iskoki (Aljanu) a Dam ɗin garin Kazaure na Muhammadu Ayuba?
  5. Ko a kwai wasu camfe-camfe da ake yi game da Dam ɗin garin Kazaure na Muhammadu Ayuba?
  6. Wai da gaske ne samuwar Dam ɗin garin kazaure na Muhammadu Ayuba ya sanya ɗalibai da sauran jama'a na zuwa wajen domin nishaɗantarwa?

1.6 MA'ANAR MUHIMMAN KALMOMI

 Kamar yanda masu iya magana kan ce " Tarayya ita ke haifar da tsarin zaman jama'a a wuri ɗaya har wasu ke mulkar wasu", haka abin yake tarayya ita ke sanya shinkafa ta cika tukunya". Sanannen abu ne cewa gamayyar kalmomi ita ke sa su haɗu su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen bayar da wata muhinmiyar jumla mai ma'ana ko akasin haka, haka wannan Jumlar gamayyar wasu zaƙaƙuran kalmomi ce ta haifar da su, muhimman kalmomin su ne:

1.6.1 GUDUNMAWA:- Kalma ce da ke nuni da ƙoƙarin wani abu wajen kawo haɓaka ko akasin haka.

1.6.1 DAM:- Kalma ce da take nuna ruwa wanda ƙorama ta ke wucewa ta wajen, sai a tare shi ya zauna a wani wuri na musamman ya daina wucewa, akasin ruwa wanda yake tafiya yau da gobe wanda ake wa laƙabi da suna kogi.

1.6.3 MUHAMMADU AYUBA:- Ya na ɗaya daga cikin manyan mutane kuma manyan hakimai masu amana yardaddun sarkin Kazaure, wanda kuma shi ne ya gina Dam ɗin a lokacin yana kwamishinan ayyuka na Jahar Kano karkashin gwabna Audu Bako, wanda shugaban ƙasa na lokacin sunansa Yakubu Gawon.

1.6.4 BUNƘASA :- Kalma ce da take nuni da hauhawa ko haɓaka ko ci gaba na wani abu.

1.6.5 TATTALIN ARZUKI :- Kamar yadda masana suka bayyana kalmar tattalin arzuki ta na nuni da wani makami ko abu ko abubuwa masu muhinmanci na more rayuwar yau da kullum da kuma gudanar da rayuwa a tsakanin al'umma daban-daban (Bunza, 2006).

1.6.6 GARIN KAZAURE :- Yana ɗaya daga cikin garuruwan Hausawa masu tarihi da yake a cikin jahar Jigawa a Arewacin ƙasar Nijeriya.

1.8. NAƊEWA.

 Bisa duba da la'akari da bayanai da jawaban da suka gabata tun daga farkon wannan babi an fara ne akan wasu muhinman abubuwa kuma nagartattu ƙashin bayan kowane bincike na ilimi, kamar yadda masa suka zauna suka tattauna aka furzar gami da misayar yawu, yayin da wasu suka dangwali tawada wasu kuma suka taɓo Alli, amma duk daga ƙarshe dukkaninsu Dodo ɗaya su kai wa tsafi, ma'ana sakamako ɗaya suka fitar.

 Wanda kuma aka yi bayanin su ɗaya bayan ɗaya tun daga kan dalili ko batun da ya somi aiwatar da wannan bincike domin komai sai da dalili, haka kuma aka yi bayanin manufar da wannan bincike yake da ita kamar yadda duk wani batu na ilimi yana da manufarsa, aka kuma kawo muhiman tambayoyin da wannan bincike yake da buƙatar samun amsoshinsu, tare da kawo bayanin muhinmancin da wannan bincike yake da shi, har da kuma bayanin iya farfajiyar da wannan bincike yake da buƙatar gudana, sannan aka kawo ma'anonin muhinman kalmomin da suka haɗu suka gina wannan bincike. Yayin da a ƙarshe kuma aka kawo kammalawa kamar yadda sunnar kowane babi ce yayin da aka gama bayani a rufe babin da kammalawa.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SU KA GABATA

2.0 SHIMFIƊA.

Ƙwararru a fagen sarrafa harshe kan ce "Da na gaba ake gane zurfin ruwa, ko da na gaban wada ne", haka an tabbata cewa "Waiwaye adon tafiya", babu shakka ko tantama wannan magana ta da ce da abin da aka tattauna aka furzar a wannan babin, ma'ana a kowane abu da mutum zai yi yana da matuƙar amfani ya riƙa waiwaya wa baya domin duba yadda magabata suka gudanar da nasu aikin. Yin hakan tabbas zai taimaka wajen sanin yadda ya kamata ya gudanar da nasa aikin domin ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

 Haka kuma an yi ƙoƙari gami da jajircewa wajen bin diddigin ayyukan da suka gabata, wanda suke da alaƙa ta kai-tsaye da wannan bincike, daga cikin abubuwan da aka bibiya sun haɗa da: Bugaggun litattafai, da mujallu da jaridu da muƙalu gami da kundayen binciken da aka gabatar na kammala karatu tun daga matakin difuloma da takardar neman shedar malanta ta ƙasa wato (N.C.E.) har da digirin farko da na biyu da na uku kuma da takardun da aka gabatar a tarukan ƙarawa juna sani. An kuma yi ƙoƙarin zaƙulo gami da binciko hirarrakin da aka gabatar a kafafen yaɗa labarai da wasu ayyukan da aka samu a kafafen sadarwa (yanar gizo-gizo) gami da jajircewa wajan bibiyar ƙamusun Hausa da na Turanci. Dalilin hakan shi ne samun haske da madogara a kan yadda za a gudanar gami da inganta wannan bincike mai taken "Gudunmawar Dam ɗin Muhammadu Ayuba wajan haɓaƙa tattakin arzuƙin garin Kazaure".

2.1 TAƘAITACCEN TARIHIN GARIN KAZAURE

 Ƙasar kazaure tana daga arewacin Kano, kuma tana kudancin ƙasar Daura, daga yamma ta yi iyaka da ƙasar Katsina. Tana da murabba'in kilomita dubu da ɗari bakwai da tamanin (1780sƙ). Masarautar Kazaure ta ƙunshi ƙananan hukumomi kamar haka: Kazaure, Roni, Gwiwa, ƴankwashi. Ƙidayar farko da aka gabatar a ƙasar kazaure ta bayyana adadin yawan mutane kimanin dubu talatin da huɗu da ɗari da talatin da tara (34,139) a wancan gabataccen lokacin a shekarar 1908. A ƙidayar da aka gudanar ta shekarar 2006, al'ummar masarautar sun ƙaru izuwa dubu ɗari biyar da wani abu (500,000). Garin yana tsakanin duwatsu da ƙorama, a kewaye da garin akwai albarkatun ƙasa da tsirrai da fadamu, akwai gada wadda ta haɗa tsohon garin wato cikin gari da kanti. Kaso tamanin cikin ɗari na tattalin arzuƙin mutanen garin ya ta'allaƙa ne akan Noma, da Kiyo, da ƙananan sana'o'i irin su Rini da Jima da Ƙira da Saƙa, da Noman rani da na damuna. Sannan kuma Allah ya albarkaci garin da ƙananan masana'antu, kamar gidajen Burodi, da gidajen ruwa (pure water) da kuma gidajen abinci (restuarants) da makamantan su. Akwai wurare na musamman da aka tanada don gina manyan masana'antu a nan gaba.

 Abin da ƙasar ta mallaka na ƙarƙashin ƙasa, sun haɗa da; Duwatsu waɗanda za a iya sarrafawa zuwa "Merble tile", akwai kuma kanwa da farin dutsi da sauran su. Ci gaban da aka samu na hanyoyin kafafen yaɗa labarai da hanyoyin sadarwa da manyan tituna su ne suka ƙara wa kazaure ci gaba.

 Ƙasar kazaure ta kafu ne kamar yadda bayanai suka gabata a baya, sakamakon tasowar Ɗantunku daga Ɗambatta zuwa garin na Kazaure, domin faɗaɗa mulkinsa. Kafin zuwan sarkin Kazaure ta kasance ƙarƙashin mulkin sarkin Fulanin Ɗambatta, wato Ibrahim Ɗantunku, zuwan sarkin Kazaure yasa sarkin ya zama sarkin Kazaure tun daga shekarar 1780, ko da yake tarihi ya tabbatar da cewa "Ɗantunku ya ƙarɓo tutar jaddada musulunci daga wurin Shehu Usman Ɗanfodiyo a shekarar 1805.

 Da saukar sarkin a garin Kazaure, gidaje goma sha biyu aka fara kafawa, kuma ya umarci Ɗambo da ya gina masa ganuwar gari domin tsaro, kasancewar akwai masu kawo hari, amma a lokacin da a aka zo ginin ganuwar sai Ɗambo ya shigo da unguwar Haɓen tsohon kafi ciki. Wannan garin ya kafu sakamakon zaman Ɗantunku, bayan al'amura sun lafa ne Jama'a suka riƙa shigowa wannan gari daga wurare daban-daban, misali; ƙasar Katsina da Kano da kuma Faranshi (Nijer) Tun da garin ya kafu gida ɗaya ne yake mulki, ba a samu wani canji ba tun daga kan Ibrahim Ɗantunku har zuwa sarki Muhammadu Najib daga Ɗa sai jika ko ɗan jika. Akwai kirare-kiraren da ake wa garin, wasu daga cikinsu sun haɗa da;

v  Kazaure birnin Adamu,

Garin Fura wurin damu,

 Garin da ba a yunwa balle tsiya,

 Kazaure ta Dambo, kunu sai yaɗa,

 Kazaure kaɗan mai albarka.

 Kazaure tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Akwai hotuna da aka ɗauki wannan gari a can baya da kuma wannan zamani ga wasu ɗaga cikinsu sun haɗa da:

 

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

2.2 TAƘAITACCEN TARIHIN MUHAMMADU AYUBA

 An haifi Alh. muhammdu Ayuba a shekarar 1918 a unguwar Burji, cikin garin Kazaure ya fara karatunsa a garin kazaure a shekarar 1928-1935 a makarantar Elemantary, daga nan ya ci gaba da karatunsa a garin Kano a makarantar middle school, (Rumfa college) daga shekarar 1935-1940. Alh.

 Muhammadu Ayuba ya yi auran farko a ranar 9 mayu a shekarar 1942 ya auri Hajiya Laure, sun koma garin Kano da zama a yakasai bayan wasu shekaru ya ƙara aure na biyu wanda ya auri hajiya Zuwaira a matsayin matarsa ta biyu, bayan wasu shekaru ya ƙara aure na uku inda ya auri hajiya Sa'adatu, bayan wasu ƴan shekaru ya yi aure na huɗu inda ya auri hajiya Karima, ya haifi ƴaƴa biyu, sannan ƴarsa ta farko hajiya fatima ita ce wadda ta auri Alh. Shehu Adamu ɗan sarki Adamu sannan kuma shi ne Isan Kazaure (hakimi). Sai ɗan sa na biyu Alh Ibrahim, wanda ya yi sakatare na din-din-din na gwabnatin Jahar Jigawa, yanzu kuma ya gaji mahaifinsa an naɗa shi magajin garin Kazaure, kuma babban ɗan majalissar sarki. Muhammadu Ayuba yana da mata huɗu(4), ƴaƴa biyu (2) da jikoki 29.

 Alh. Muhammadu Ayuba ya yi aiki da ma'aikatar baitul-mali ta jahar kano daga shekarar 1940-1945. A tsakanin 1945-1946 ya halarci darasin kasuwanci, wanda ya sanya ya zamo babban mai kula da harkar kasuwancin arewacin Najeriya har zuwa 1949. Daga shekarar 1949 ya samu muƙamin magajin garin Kazaure, wanda kuma ya zamo yana ɗaya daga cikin manyan ƴan majalissar sarkin kazaure Alh Adamu, wanda aka naɗa shi a 1941, Allah ya yi masa rasuwa a shekarar 1968. A shekarar 1968 ya ci gaba da aiki da ɗansa, wato sarki Ibrahim Adamu, wanda shima Allah ya yi masa rasuwa a 1993, kuma aka naɗa ƙanensa Alh. Hussaini Adamu a 1993, Alh Muhammadu Ayuba ya yi aiki da sarki Hussaini Adamu a matsayin magajin garin Kazaure har zuwa shekarar 1999, Allah ya yi wa sarki Hussaini Adamu rasuwa, Muhammadu Ayuba ya ci gaba da aiki da ɗan sarki Hussaini Adamu mai suna Alh. Najib Hussaini Adamu wanda aka naɗa a 1999, sun yi aiki tare har zuwa lokacin da Allah (S.W.T) ya yi wa Alh. Muhammadu Ayuba (magajin garin Kazaure) a shekarar (2006).

 Kafin rasuwar alh. Muhammadh Ayuba a shekarar 1951 ya wakilci yankin sa a matsayin ɗan majalissar Jaha a shekarar 1956 da 1961. A shekarar 1962 Sir Ahmadu Bello sardaunan sokoto ya naɗa shi a matsayin kwamishinan lardin Borno. A shekarar 1967 aka ba shi muƙamin kwamishinan ayyuka na Jahar kano. Bayan ya fara aiki sai aka samu chanjin gwabnati wadda ta koma hannun mulkin Soja 29 yuli 1975, wanda ya yi sanadiyyar barin aikinsa ya dawo gida Kazaure ya ci gaba da aiki a fadar sarkin Kazaure. Alh. Muhammadu Ayuba (magajin garin kazaure) ya koma ya ci gaba da aiki a matsayin kwamishinan ayyuka na Jahar Kano, a ƙarƙashin sahalewar gwabnan Jahar Kano na lokacin wato; Audu Baƙo a ranar 26 yuli a shekarar 1967 a lokacin shugaban ƙasa Yakubu Gawon.

 Ayyukan da ya samar a lokacinsa na kwamishinan ayyuka. Alh. Muhammadu Ayuba ya yi ayyukan tituna da na ruwa da sauran ayyuka da dama wanda suka haɗa da: A lokacin mulkin Muhammadu Ayuba ya samar da ayyukan tituna da daman gaske a cikin jahar Kano wanda suka haɗa da: (1) Titunan Kunya zuwa Ɓaɓura zuwa Nijer mai tsawon mil (56). Wanda aka yi shi domin ɗaukar gyaɗa daga Ɓaɓura zuwa magarya cikin Nijer da kuma wanda daga kano zuwa Daura zuwa Jamhuriyar Nijer. (2) Titunan Kano zuwa Gwarzo zuwa Dayi (55 mil) wannan tituna har tsallakawa wata jaha suka yi wanda suke a yammacin jahar kano da suka haɗa da Funtuwa zuwa Yashi tsawon titin daga kano zuwa Dayi mil 64. (3) Titunan Kafi Mayaƙi zuwa Tudun Wada zuwa Jos mil (75) wanda an gama titunan a 1974. (4) Kachako zuwa Dutse zuwa Kiyawa, wannan tituna suna da ɓangare biyu da suka haɗa Gaya da Karnaya wanda nisan sa ya kai (mil 20). (5) Kano zuwa Haɗeja, wanda ya fara daga gabashin Kano zuwa arewacin kogin Haɗeja. (6) Gaya zuwa Kafin Hausa zuwa Haɗeja, wanda daga Haɗeja zuwa Kafin Hausa yana da tsayi mil 18. (7) Malam-madori zuwa Nguri, wanda yake da sukwaya mil 500-1000. (8) Ɗan Hassan zuwa Rano zuwa Rurum zuwa Dam ɗin Tiga zuwa Rano zuwa Kibiya zuwa Burum-Burum. da sauran su.

 Ayyukan ruwan da ya yi yana matsayin kwamishina. Alh. Muhammadu Ayuba ya yi ayyuka da dama lokacin yana matsayin kwamishinan ayyuka na jahar Kano, wanda suka haɗa da: (1) Dam ɗin Bagauda wanda yake a kano titin zariya, wanda aka fara a watan Augusta 1969, aka kuma gama shi a 1970. (2) Dam ɗin Tiga wanda aka fara a 1970 an gama shi a 1974, yana da mil 9 tsakaninsa da Dam ɗi Bagauda. (3) Ya gina ƙananan Dam guda biyu a Ƙaraye da Birnin-Kudu.(4) Ya gina Rizabuwa da tankunan ruwa a ɓangarorin Jahar Kano, kamar mutanan yankin Bichi, Badume, Dawakin-Tofa, Dawanau, Mil-tara, Ungwoggwo, Gwauron-Dutse, da sauransu. (5) Ya gina Tuƙa-tuƙa a ƙauyukan Jahar Kano, sannan ya gina Dam a garin Kazaure daga kudancin garin wanda ya samar da sauƙin wahalar ruwa da garin Kazaure yake fama da ita wanda sanadiyyar hakan aka masa laƙabi da Dam ɗin Muhammad Ayuba.

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

2.3TAƘAITACCEN TARIHIN DAM ƊIN MUHAMMADU AYUBA

 An gina Dam ɗin Muhammadu Ayuba a cikin shekarar 1974 a lokacin jahar Jigawa na haɗe da jahar Kano, a zamanin Muhammadu Ayuba yana (magajin gari) yana kuma riƙe da kujerar kwamishinan ayyuka na jahar Kano a ƙarƙashin gwabnatin mulkin Soja wanda kwamishinan ƴan sanda Alh. Audu Baƙo shi ne ke riƙe da kujerar gwabnatin jihar ta Kano, shugaban ƙasa kuma a lokacin Yakubu Gawon shike rike da kujerar.

 A wajen da aka gina Dam ɗin Fadamu ne a wajen, waɗannan fadamu suna samar da ƴaƴan itatuwa masu ban sha'awa, a kwai fadamu da yawa a wajen wanda suka haɗa da; Fadamar hukumar gidan sarki wadda ake mata laƙabi da cewa " Natiɓe Assoraty (N.A)", akwai kuma fadamar sarki ta shi shi kaɗai, sai kuma sauran fadamun al'ummar gari wanda Allah ya ba wa ikon mallaka a wajen. Babban dalilin da ya haddasa waɗannan fadamu su ne akwai wata ƙatuwar ƙorama wadda ta taso daga wawan Rafi wato yammacin garin Kazaure ta biyo ta wannan wajen da fadamun suke wanda hakan ne yasa itatuwa suke samun isasshen ruwa har suke fitar da ƴaƴan itatuwa masu rai da lafiya wannan ƙorama ba iya wajen da aka gina Dam ɗin Muhammadu Ayuba ba kaɗai ta tsaya, ta fita izuwa gabas da Dam ɗin inda ta ratsa dajin da ake kira da suna Kwari, a cikin wannan daji na kwari akwai wata ƙatuwar gonar sarki ta Dawa wadda wannan ƙorama ta rasta ta cikin ta, wannan ƙoramar ba iya nan ta tsaya ba har wasu ƙauyukan masarautar kazaure ta ruske daga cikin ƙauyukan akwai Gezoji da sauran ƙauyuka.

 Alokacin da aka gina wannan Dam babu isasshen ruwan amfani a garin Kazaure, mutanen gari na zuwa wajen wannan fadamu suna yin barruwan dabobi da sauran amfanin yau da kullum kasancewar wajen ba shi da wahalar tsatsatowar ruwa, da ka yi tono kaɗan kawai ruwa lafiyayye zai runƙa tsatsatowa sakamakon wannan ƙorama da take kawo ruwa, da wannan ruwa ake gudanar da wasu al'amuran amfanin yau da kullum har zuwa shekarar 1973 kafin a gina wannan Dam. Akwai wata ƙatuwar bishiyar Gawo a wajen Gadar da aka gina a lokacin Gabnatin, Gwabna Ibrahim Saminu Turaki (Turakin kazaure) wannan gada ita ce ta haɗa tsakanin cikin gari da kuma Kanti inda kasuwa da wasu harkokin kasuwanci suke, a dai-dai wajen da aka gina wannan gada ta Ibrahim saminu turaki wannan ƙatuwar Bishiyar ta Gawo take, wadda masana sun bayyana cewa a wannan lokaci a duk faɗin Nageriya babu bishiyar Gawon da ta kai wannan bishiya girma, amma zuwa wannan lokaci ba a sami wani hoto na wannan bishiya ba wanda aka ɗauka lokacin kafin a gina Dam ɗin. Yanzu haka wannan Dam yana nan ya bunƙasa har sana'o'i ake gudanarwa a ciki da wajensa wanda suke ba da muhimmiyar gudummawa wajen haɓakar tattalin arzuƙi a garin kazaure. Masu iya magana kan ce " Gani ya kori ji" saboda haka ga wasu daga cikin hutonan Dam ɗin muhammadu. ayuba na garin Kazaure domin ƙarin haske wajen fahimtar yadda Dam ɗin ya kasance;

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

2.4 MA'ANAR AL'ADA

 Haƙiƙa kusan kowace al'umma da take a faɗin duniya suna matuƙar tinƙaho da alfahari da al'adunsu na gargajiya wanda suka gada tun zamanin dauri, wato daga gun iyaye kaka da kakanni, waɗanda suka danganci hanyoyin aiwatar da lamuran rayuwarsu ta yau da kullum da kuma sauran al'amuran rayuwa. Shehunnan malamai masana da manazarta al'ada sun bayar da nagartattun ma'anoni dangane da ma'anar al'ada da kuma asalin kalmar al'ada da cewa; asalin kalmar al'ada ba Bahaushiyar kalma ba ce, hatsin bara ce, wato aro ta aka yi daga harshen Larabci.

 Masana al'adu irin su: Tukur da Adamu da wani (2000) da Bello (2015) da Maryam (2009) da Kargi (1993) da Bunza (2006) da sauran su, sun yi ƙoƙari gami da jajircewa wajen bayyana ma'anar al'ada tare da fashin baƙi.

 Muhammad (2020), cewa ya yi "Al'ada na nufin wata hanya ce wadda wata al'umma suka ɗaukarwa kan su, kuma suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum da ita. Tun daga addini da shugabanci da abinci da makwanci wato muhalli da bukukuwa da tufafi da magunguna da sauran su. Ahmad, (2001) ya ce "Al'ada na nufin hanyar da al'umma take gudanar da rayuwarta. Don haka al'ada ta haɗa da; ɗabi'a da ci gaba da hanyoyin sadarwa da duk wasu abubuwa da suka danganci rayuwar wannan al'umma".

 Abdulƙadir (2001) cewa ya yi "Al'ada tana da faɗin gaske, in da ta ƙunshi dukkannin abubuwan da ɗan Adam ke tafiyar da rayuwarsa a kai, tun daga farkon samuwarsa, har zuwa ƙarshen rayuwarsa da kuma mutuwarsa".

 Bunza (2006) ya ce " A luggar larabci kalmar al'ada na nufin wani abu da aka saba yi ko ya saba wakana, ko aka san da shi. A harshen Hausa, kalmomin da suka fi kusa da kalmar al'ada su ne kamar: "Sabo" da "gado" da "hali" da "sada" da "gargajiya". Ya ƙara cewa " Al'ada tana nufin dukkan rayuwar ɗan Adam tun daga haihuwarsa har zuwa ƙabarinsa". A ko ina mutum ya samu kansa duk wata ɗabi'a da ya tashi da ita tun farkon rayuwarsa ya tarar a wurin da ya rayu ko yake rayuwa, ita ce al'adarsa da za'a yi masa hukunci da ita, kuma babu wata al'umma da zata rayu a doron ƙasa, face tana da al'adar da take bi kuma da ita ake iya rarrabe ta da al'umma wadda ba ita ba".

 Ibrahim (1981) ya bayyana al'ada da cewa ita ce "Abubuwan da mutane suka saba gudanarwa a rayuwarsu ta duniya a kai, da yadda suke gudanar da al'amuran su da harkokinsu na yau da kullum". Adamu da tukur, (2000) sun bayyana al'ada da cewa: "Sababbiyar hanya ce domin tafiyar da rayuwar al'umma". Aikin Maryam, (2009) kuma an bayyana al'ada da cewa: "Al'ada na nufin rayuwar al'umma ana koyar da ita ana kuma koyanta, kafin zaman al'umma ya tabbata".

 Shi kuwa Bello (2015:10) ya ce : Al'ada a tafiye take da dukkannin harkoki da mu'amala ta rayuwar Bahaushe. Domin ta haɗa da muhallinsa da tarbiyyarsa, da tufafinsa, da auratayyarsa, da abincinsa da sauran su".

 Bunza, (2006) ya bayyana cewa " Kalmar al'ada aro ta aka yi daga Kalmar Larabci, aro ba wani sabon abu bane a harshen Hausa, wato daɗaɗɗen abu ne a tarihi". Galadanci da wasu, (1990/1992) sum bayyana al'ada da cewa " Ita ce hanyar rayuwa ta ɗan Adam, kowace al'umma tana da irin tata. Wannan hanyar rayuwar ta shafi yanayin zaman mutane da tunaninsu da imaninsu da duk wani abu da ya shafi rayuwarsu".

 Shi kuma Sani (1982) ya bayyana al'ada ta fuskoki uku rigis kamar haka:

1- Al'ada na nufin Haila, wato irin jini da mata ke yi wata-wata.

2- Al'ada na nufin bin wata hanya don yin maganin gargajiya misali; yin karatu da tofi ko turare ko zubar da jini wato ƙaho da sauran su.

3- Al'ada na nufin abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya da suke yi don zaman duniya."

Bargery (1834) ya ce "Al'ada na nufin ta'ada ko tabi'a ko tada ko tsabi'a". A wani ƙaulin kuma ya bayyana ma'anar al'ada da cewa " Ita ce ɗabi'a halayya ko kuma hanya".

 

 2.4.1 RABE-RABEN AL'ADA

 Shahararrun malamai manazarta da masana al'ada sun yi nazari na kininiya a ciki da wajen al'ada, inda suka yi ittifaƙi akan za a iya raba al'ada zuwa gida biyu kamar haka:

1- Al'adar da ake iya gani da ido (material culture), wadda ta ƙunshi abinci da tufafi da gine-gine, da magunguna da bukukuwa da wasanni da sauran su.

2- Al'ada da ba a iya ganinta da ido (non-material culture), wadda ta ƙunshi; imani da ɗabi'a da tarbiyya, da kunya, da sauran su.

 Muhammad (2021) cewa ya yi " Al'adun Hausawa ana kasafta su ne gida biyu, akwai waɗanda suka shafi imani, wato jiyau waɗanda jin su ake kuma a yi imani da su ba tare da ganinsu ko iya taɓa su ba. Sannan kuma akwai al'ada ganau ita kuma saɓanin al'ada jiyau ce, ita ana iya ganinta harma a iya taɓa ta waɗannan sun haɗar da; cimaka da kayan amfani da gine-gine da bukukuwa da sauran su".

 Bunza (2006) cewa ya yi Al'ada ta fuskar yanayi ana iya kasa al'ada zuwa gida uku; wadda ake aiwatarwa da gaɓoɓi da wadda ake furtawa da baki da kuma wadda ake ƙudurtawa a zuci ta zama aƙida". Ya ƙara da cewa " muhimmancin al'ada ne yasa duk al'ummar duniya take da ta ta al'adar da take tafiyar da rayuwarta a kai. Kuma muhimmanci al'ada yasa ake samun sababbin al'adu a doron ƙasa. Abu ne da ba zai yi wu ba a rayu a doron ƙasa ba tare da al'ada ba".

 Ubali (2021) ya ce "Al'ada ana iya raba ta gida biyu, wato al'ada jiyau da al'ada ganau. Al'ada jiyau ita ce wacce ba a gani sai dai kawai a ji, kamar; kishi da zalunci da rowa da kyauta, da faɗa da zumunci da sauran su. Ita kuma al'ada ganau ta shafi duk abin da za a iya gani kuma a taɓo shi, irin waɗannan al'adu sun haɗa da; gine-gine da tufafi da bukukuwa da abinci da sarautu da magunguna da sauran su.

 Ginsau (2018) ya labarta mana ra'ayoyin masana da manazarta dangane da rabe-raben al'ada irin su: Taykor (1871) Yahaya da Ɗangambo (1980) da Garba (2012) sun raba al'ada zuwa gida uku kamar haka:

1- (Material culture) Al'ada wadda ta shafi kayayyakin amfani irinsu suturu da gine-gine da abincinsu da kayan ƙere-ƙere da sassaƙe-sassaƙe da sauran su.

2- (Idiological culture) Al'ada wadda ta shafi addini, wato yanayin addinai da yadda ake bauta da iliminsu da imaninsu da kuma halayyarsu.

3- (Social culture) Al'ada wadda ta jiɓanci yanayin bukukuwan al'umma, kamar aure da suna da bikin sarautu da wasanni da makamantansu.

 Garba (2012) ya yi aikinsa ya kasa al'ada zuwa gida huɗu kamar haka:

1- Al'adar da ta shafi tsarin zaman Jama'a, kamar dangantaka da masarauta da kuma sana'o'i (Noma da Su da Kiwo da Fawa da Sassaƙa).

2- Al'adar da ta shafi kayayyakin amfani na al'umma da yadda suke samar da su, da kuma yadda ake amfani da su.

3- Al'ada da ta shafi aƙida, wadda ta haɗa da addini. Ko da yake an samu saɓanin ra'ayi a wannan wasu na ganin kamata ya yi a haɗa ta da ta farko, wato tsarin zaman iyali.

4- Al'adar da ta shafi fasaha, wannan ta haɗa da zane-zane da rubutu.

Ɗangambo da wani (1980) sun kasa al'ada zuwa gida uku kamar haka:

1- Tatsarin zaman jama'a, kamar abin da ya shafi shugabanci da iyali da malanta da maƙwabtaka da sarauta da tarbiyyar jama'a zumunta da sauran su.

2- Hanyoyin gudanar da rayuwa, kamar abinci da tufafi zane-zane da sauran su.

3- Bukukuwa, kamar na aure da suna da taku-taha, kacici-kacici da bikin sallah da sauran su.

2.4.2 MUHIMMANCIN AL'ADA

 Gamayyar masana da tarin manazarta al'ada sun tattauna sun furzar sun bayyana muhimmancin da al'ada ta ƙunsa a rayuwar al'umma wajan gudanar da al'amuran yau da kullum. daga cikinsu akwai:

 Uba (2010) A hirar da ya yi da gidan rediyo Dala F.M. ya bayyana muhimmancin da al'adun Hausawa suke da su, inda ya bayyana cewa: Ta fuskar tarbiyya da girmama na gaba al'ada tana da matuƙar muhimmanci domin duk inda ka samu ɗan Bahaushe za ka tarar yana girmama na gaban shi, duk lalacewarsa ba lallai ne ya yi faɗa da ubansa ba, kuma ba lallai bane ya rumbaci mace a tantagayyar idon jama'a ba.

 Hassan (2013) shi kuma cewa ya yi “Muhimmancin al'ada ne yasa ake iya tantance kyawawan ɗabi'u da kuma munanan ɗabi'u, haka kuma muhimmancin al'ada ne yasa ake tantance ƙabila da wata ƙabilar".

 Ƙudan (2018) ya bayyana muhimmancin al'ada da cewa "Hanya ce ta gudanar da rayuwa wadda ta ƙunshi ɗabi'un mutane tun daga haihuwa har izuwa mutuwa".

 Y ahaya (1981) ya ce " muhimmancin da al'ada take da shi yasa dukkan hanyoyin gudanar da rayuwar al'umma suke ƙunshe a cikin al'adunsu".

2.4.3 SIFOFIN AL'ADA

 Babu shakka masana da manazarta da kuma tarin manazarta sun sha ɗauki ba daɗi wajen jajircewa da kuma juriya wajen ganin an binciko sifofi ko alamomin al'ada, wanda daga cikinsu akwai; Taylor (1871) Kargi (2012) Kuta (2013:1) da Almajiri (2010) da William (2005:24) Chukuɗi (2005:20) da Adamu (2012:44) da Umar (2009:39) da Murdock (1930) da Herskoɓit (1995) da kuma Centre for the study of institution (CSI) (1970:11) Sun bayyana wasu alamomi ko sifofi da al'ada ta ƙunsa kamar haka:

1- Al'ada kan canza: Ɗan Adam al'adarsa da ya gada wajan iyaye da kakanni ko ya saba yana gudanar da ita yau da gobe, Ɗan Adam na iya yin hijira zuwa wasu wurare masu wani yanayi kamar zafi ko sanyi, kuma ya jure zamansa a can. Haka kuma yakan yi watsi da wasu daga cikin al'adunsu ya rungumi wasu sababbi domin samun damar gudanar da wasu da rayuwa cikin sauƙi da salama.

2- Al'ada aba ce da take da karɓuwa ga akasarin al'umma da ta shafa. Galibi al'umma na aiwatar da wata al'ada ba tare da nuna kyama ko guje mata ko tsangwama ba. Kamar yin kaciya ga ƴaƴa mata da kuma haihuwa (samun ɗa) kafin gudanar da aure da sauran su.

3- Al'ada tana ƙunshe da alamomi da suka ƙeɓanta ga al'ummar wasu al'ummomi ne da kan iya jiɓantar sadarwa, waɗanda ke da nuni da al'adar wata al'umma ta musamman. misali tsagar gado, yanayin gine-gine, yanayin sanya tufafi da kuma alamomin tutocin ƙasashe ko wata al'umma ta daban.

4- Al'ada koyanta ake. Mutane kan koyi al'ada ne, ba halittarsu ake da ita ba, akan haifi ɗan Adam da wasu buƙatu kamar yunwa da ƙishi da tsiraici amma yadda zai yi ya kawar da su sai ya koya daga al'adar mutanen da yake kewaye da su.

2.5 MAKAMANTAN BINCIKE

 Kalmar kamanci kalma ce da ke nuni da wani abu mai sifa ko alama iri ɗaya da wani abun, sanannen abu ne cewa kusan dukkan al'amuran da mutun yake gudanarwa ko yake shirin aiwatarwa ba a rasa wani ko wasu magabata da suka yi makamancin sa, ko kuma irin sa. Saboda haka a wannan binciken ma an yi ɗamarar bibiyar ire-iren ayyukan da suka gabata daga guraren masana da manazarta waɗanda suka gabatar masu kamanceceniya da wannan binciken da ake kan gudanarwa, kamar haka:

2.5.1 BUGAGGUN LITATTAFAI

 Akwai wallafaffun ko bugaggun litattafai da dama masu alaƙa da wannan bincike. Daga cikin wallafaffun litattafan akwai:

 Muhammad, M.S. (2019) a littafinsa mai suna " Sana'a Sa a". A wannan littafin an yi bayanin sana'o'in gargajiya na Hausawa kamar: Noma da kiwo da saƙa da fatauci da sauran su. Alaƙar wannan littafi da wannan bincike ita ce ta fuskar sana'o'in gargajiya na Hausawa. Amma sun bambanta domin wannan binciken an yi shi ne a kan sana'o'in Hausawa na gargajiya, amma iya waɗanda su ke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure.

 Gusau, (2012) a littafinsa mai suna "Bukukuwan Hausawa" ya yi nazari ne a kan sana'o'in Hausawa daban-daban kama daga Fatauci da Gini, da Noma da Wanzanci da sauransu. Wannan littafi yana da alaƙa da wannan binciken ta fuskar sana'o'in Hausawa. Amma duk da haka suna da bambanci da wannan bincike, domin an yi shi ne a kan sana'o'in Hausawa na gargajiya wanda suke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure.

 Durumin Iya, M.A (2006). Littafi mai taken; "Tasirin Kimiyya da Ƙere-ƙeren Zamani a kan Sana'o'in Hausawa na Gargajiya. A wannan littafi an kawo bayanan wasu sana'o'in gargajiya na Hausawa kamar: Su da fatauci da noma da kiwo da jima da sauran su. Alaƙar wannan littafi da wannan Bincike ita ce ta fuskar sana'o'in Hausawa na gargajiya. Amma su na da bambanci saboda wannan binciken za a yi shi ne akan sana'o'in gargajiya na Hausawa amma iya wanɗanda suke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure.

 Garba, C.Y (1991). Littafi mai suna " Sana'o'in Gargajiya a ƙasar Hausa". A cikin wannan littafi an kawo bayanin wasu sana'o'in gargajiya na Hausawa, kamar: Noma da jima da fawa da jima da sauran su. Alaƙar wannan Bincike da ake kan gudanarwa da wannan littafi ita ce, ta fuskar sana'o'in Hausawa na gargajiya. Amma sun bambanta domin wannan binciken an yi shi ne a kan sana'o'in Hausawa na gargajiya, amma iya waɗanda su ke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure.

 Rimmer, E.M da wasu (1984). Littafi mai suna "Zaman Mutum da Sana'ar sa". A wannan littafi an yi bayanin wasu sana'o'i na Hausawa kamar; kiwo da noma su (kamun kifi) da sauran su. Wannan littafin yana da alaƙa ta kai tsaye da wannan Bincike ta fuskar sana'o'in Hausawa na gargajiya, amma iya wanɗanda suke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure.

 Alhasan, da wasu (1982) a cikin littafinsu mai suna " Zaman Hausawa". Marubutan sun yi ƙoƙarin kawo wasu sana'o'in Hausawa waɗanda suka haɗa da: Noma da Ƙira da Fawa da Farauta da Kiwo da Saƙa da Kaɗi da sauran su. Aikinsu yana da alaƙa da wannan bincike, domin ya shafi sana'o'in Hausawa na gargajiya. Abin da ya bambanta su shi ne; sun yi aikinsu ne a kan sana'o'in Hausawa na gargajiya gaba ɗaya. Wannan bincike kuma ya shafi sana'o'in Hausawa na gargajiya amma iya wanɗanda suke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure.

 East, (1968) a cikin littafinsa mai suna; "Labaru na Da da na Yanzu". Ya kawo tarihin fitattun sana'o'in Hausawa na gargajiya kamar Noma da kiwo da su da fatauci tare da bayanansu. Alaƙar wannan littafi da wannan aiki ita ce ta fuskar sana'o'in Hausawa na gargajiya. Amma suna da bambanci, yayin da wannan Binciken ya kalli sana'o'in Hausawa na gargajiya, amma iya wanɗanda suke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure.

 Maɗauci I. (1963). Littafi mai suna "Al'adun Hausawa". A wannan littafi an yi bayanin Al'adun Hausawa ciki harda waɗanda suke wakana a cikin sana'o'in gargajiya na Hausawa kamar Al'adun manoma da masunta da makiyaya da sauran makamantansu. Alaƙar wannan bincike da wannan littafi ita ce ta fuskar sana'o'in gargajiya na Hausawa. Amma sun bambanta domin wannan binciken an yi shi ne akan sana'o'in Hausawa na gargajiya, amma iya waɗanda su ke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure.

2.5.2 KUNDAYEN BINCIKE

 Kundayen Bincike na nufin wata gudummawa ce da ɗaliban gaba da sakadare ke rubutawa domin neman takardar shedar kammala karatunsu, tun daga matakin Dufuloma da neman takardar shedar malanta ta ƙasa wato (N.C.E) har da Digiri tun daga na farko har zuwa na uku. Saboda haka a lokacin da ake kan gudanar da wannan bincike an leƙo wasu daga cikin kundayen magabata masu alaƙa ta kai tsaye da wannan bincike da ake kan gudanarwa, kamar haka:

 Ginsau, A. (2018). Kundin Digiri na biyu, mai taken: "Nazarin Jirwayen Wasu Kayayyakin Sana'o'i A Karin Maganar Hausa". Wanda aka gabatar a sashen nazarin harsunan Najeriya da na Afirka, na Jami'ar Ahmadu Bello da ke zaria. Alaƙar wannan kundi da binciken da ake gudanarwa ita ce; ta fuskar sana'o'in gargajiya, amma sun bambanta domin wannan binciken an yi shi ne a kan sana'o'in gargajiya na Hausawa amma iya waɗanda su ke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba.

 Yusuf, S. (2017). kundin Digiri na ɗaya mai taken "Al'adun hawan Sallah a Masarautar Kazaure". Sashen nazarin Harsunan Najeriya da na Afirka, na Jami'ar Sule Lamiɗo ta Kafin Hausa Jahar Jigawa. A cikin wannan kundi an kawo tarihin garin Kazaure da yanayin yadda al'adun hawan sallah babba da ƙarama ke gudana a cikin garin na Kazaure. Alaƙar wannan kundi da wannan bincike ita ce ta fuskar wasu al'ada kuma ya kawo tarihin garin Kazaure a cikin kundin. Amma sun bambanta da wannan bincike, domin wannan binciken bai shafi al'adun hawan sallah ba, iya sana'o'in Hausawa na gargajiya wanda suke wakana a ciki da gefen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure ya shafa.

 Ibrahim, U. ( 2012). Kundin digiri na biyu mai taken: Tasirin Haye a kan sana'o'in Hausawa na gargajiya. Wanda aka gabatar a sashen nazarin Harsunan Najeriya da Afirka na Jami'ar Bayero Kano. Wannan kundi ya kawo bayanin wasu Sana'o'in gargajiya na Hausawa kamar haka; Noma Fawa da makamantansu. Alaƙar wannan bincike da wannan kundi ita ce ta fuskar sana'o'in gargajiya na Hausawa. Amma sun bambanta domin wannan bincike da ake aiwatarwa iya sana'o'in gargajiya na Bahaushe wanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba ya shafa.

 Ɓatagarawa, S.A. (2010). Kundin Digiti na biyu mai taken: "Nason wasu Al'adu a kan na Hausawa mazauna Lokoja". Wanda aka gabatar a sashen nazarin Harsunan Najeriya da Afirka na Jami'ar Bayero Kano. A wannan kundin an yi bayanin nason wasu Al'adu na Hausawa kamar wajen bukukuwan Aure da makantantansu. Alaƙar wannan kundi da binciken da ake aiwatarwa ita ce, dukkaninsu suna magana a kan Al'adun Hausawa. Amma sun bambanta domin an taƙaita wannan bincike a kan iya sana'o'in gargajiya na Bahaushe wanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba.

 Bunza, D.B. (2004). Kundin Digiri na ɗaya mai taken " Noma da yadda ake gudanar da shi". Sashen koyar da harsunan Najeriya na Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato". A wannan kundi an yi bayanin mene ne Noma da yadda ake gudanar da Noman. Alaƙar wannan bincike da wannan kundi ita ce ta fuskar Noma, domin Noma yana ɗaya daga cikin sana'o'in Hausawa na gargajiya wanɗanda suke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure. Amma sun bambanta da wannan kundi domin shi ya yi aikinsa a kan noma gaba ɗaya, shi kuma wannan bincike da ake kan gudanarwa iya noman da ake gudanarwa a gefen Dam ɗin Muhammadu Ayuba

 Hassan, A. (1998) Kundin digiri ɗaya, mai taken: "Matsayin Sana'o'in Gargajiya wajen Bunƙasa tattalin arzukin Najeriya". A wannan kundi an yi bayanin sana'o'in gargajiya da irin gudummawar da suke bayarwa, wajen bunƙasa tattalin arzukin Najeriya. Alaƙar wannan kundi da wannan bincike ita ce ta fuskar sana'o'in gargajiya da kuma tattalin arzuki, domin wannan binciken an yi shi ne a kan sana'o'in gargajiya na Hausawa wanda ta dalilinsu tattakin arzukin garin Kazaure ke haɓaka. Amma sun bambanta domin wannan bincike ya taƙaita ne a kan iya sana'o'in gargajiya na Hausawa waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba.

 Yaro, A. (1994). Kundin Digiri na biyu mai taken: " Jirwayen Al'adun Hausawa a kan Fulanin Yola". Wanda aka gabatar a sashen nazarin Harsunan Najeriya da Afirka na Jami'ar Bayero Kano. A wannan kundi an yi bayanin wasu daga cikin al'adun da ke cikin sana'o'in gargajiya na Hausawa kamar Noma da kiwo da sauran su. Alaƙar wannan kundi da wannan bincike ita ce ta fuskar Al'ada, domin dukkansu suna ƙoƙarin nuna al'adun Hausawa wajen gudanar da rayuwa. Amma su na da bambanci domin wannan binciken ya taƙaita ne a kan Sana'o'i da Al'adun da ke cikin sana'o'in gargajiya na Bahaushe wanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba.

 Aminu, M. (1991). Kundin digiri na ɗaya mai taken: Tasirin zuwan Turawa akan sana'o'in gargajiya na ƙasar Hausa. Wanda aka gabatar a sashen nazarin Harsunan Najeriya da Afirka na Jami'ar Bayero Kano. A wannan kundi an kawo wasu daga cikin sana'o'in gargajiya na Bahaushe da irin tasirin da Turawa su ka yi akan sana'o'in na gargajiyar Bahaushe. Alaƙar wannan kundi da binciken da ake gabatarwa ita ce ta fuskar sana'o'in gargajiyar Hausawa. Amma sun bambanta yayin da wannan binciken ya taƙaita akan iya sana'o'in gargajiya na Hausawa waɗanda su ke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure kaɗai ya shafa.

 Kafin Hausa, A.A. (1983). Kundin Digiri na biyu mai taken " Nazarin wasu zaɓaɓɓun Bukukuwan al'adun gargajiya na shekara a Arewa maso yammacin kano". Wanda aka gabatar a sashen koyar da Harsunan Najeriya da na Afirka na Jamai'ar Ahmadu Bello Zariya. Wannan kundi yana da alaƙa da wannan bincike domin an kawo sana'o'in gargajiya na Hausawa da al'adunsu. Amma suna da bambanci da wannan Binciken da aka gudanar, domin wannan binciken iya sana'o'in Hausawa na gargajiya wanɗanda suke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure, waɗanda ta dalilinsu tattalin arzuƙin garin Kazaure ya haɓaka.

 Idi, A. (1982). Kundin Digirin farko, mai taken " Bukukuwan Al'adun gargajiya a ƙasar Kano da Sakkwato". Sashen Nazarin harsunan Najeriya na Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo. Wannan kundi yana da alaƙa ta kai tsaye da wannan bincike da ake gudanarwa, domin yana magana a kan bukukuwan al'adun gargajiya a ƙasar sakkwato, kuma ya taɓo ire-iren sana'o'in Hausawa na gargajiya kamar; kiwo da noma da fatauci da sauran su, da al'adun da suke tattare da su. Wannan alaƙar ce ta ƙullu a tsakaninsu, domin wannan binciken ma an yi shi ne a kan sana'o'in Hausawa na gargajiya. Sai dai sun bambanta, domin wannan binciken iya sana'o'in Hausawa na gargajiya wanɗanda suke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure ya shafa, yayin da shi ya yi aikinsa a kan wasu daga cikin sana'o'in Hausawa na gargajiya na garin sakkwato.

2.5.3 MAƘALU

 Gobir, Y. A. A maƙalarsa mai taken: "Harshe da tsaron ƙasa: (makamin Harshe da Al'ada ga jami'an tsaron iyakokin Nijar da Najeriya: Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa, don girmama wa ga shehun malami masanin Harsunan Duniya, marigayi farfesa Muhammad Hambali Junju, a fadar mai martaba Sultan na Yamai a Jamhuriyyar Nijar. Daga laraba 19 zuwa juma'a 21 ga watan fabrairu, 2014. A wannan maƙala an yi bayanin wasu daga cikin al'adun da jami'an tsaron iyakokin Najeriya da Nijar suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu da sauran makamantansu. Wannan maƙala ta na da alaƙa da binciken da ake aiwatarwa, domin duk suna magana ne a kan al'adun Hausawa, sai dai sun bambanta domin shi a kan al'adun jami'an tsaro ya rubuta maƙalarsa, wannan kuma akan al'adu da sana'o'in gargajiya na Hausawa, waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba ya shafa.

 Bunza, A.M. "Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani, na ƙasa da ƙasa na kwanaki biyu kan: "Taɓarɓarewar Al'adun Hausawa A Yau". Da hukumar gidan tarihi ta jihar Katsina ta shirya, tare da haɗin gwiwar sashen koyar da Harsunan Najeriya, Jami'ar Umaru Musa Ƴar'aduwa Katsina, a ranakun 25 da 26 na watan yuni, 2013 a babban ɗakin taron Jami'ar. A wannan maƙala an yi bayanin ma'anoni dangane da Al'ummar Hausawa da al'adun Hausawa, an yi bayanin al'adun Hausawa kafin zuwan turawan mishan da bayan zuwan turawan mishan. Alaƙar da ke tsakanin wannan maƙala da binciken da ake yi ita ce; dukkaninsu suna magana ne a kan Al'ada, kuma suna nuna ire-iren al'adun na Hausawa. Amma suna da bambanci, domin wannan bincike iya al'adun da suke gudana a cikin sana'o'in gargajiya na Hausawa waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba ya shafa.

 Bunza, D.B. ( 2013). Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa mai taken; "Zama da maɗaukin Kanwa, ke sa farin kai: Nason baƙin al'adu cikin al'adun Aure na Hausawa". A sashen nazarin Harsunan Najeriya, na Jami'ar Umaru Musa Ƴar'aduwa Katsina. A wannan maƙala an yi bayanin ma'anoni dangane da al'ada an kuma nuna yanayin yadda wasu baƙin al'adu suka yi naso a cikin al'adun aure na Hausawa. Alaƙar da ke tsakanin wannan maƙala da binciken da ake yi ita ce; dukkaninsu suna magana ne akan Al'ada, kuma su na nuna ire-iren al'adun gargajiya na Hausawa. Amma suna da bambanci, domin wannan binciken bai shafi al'adun Aure ba. iya al'adun da suke gudana a cikin sana'o'in gargajiya na Hausawa waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuna ya shafa.

 Yakasai, (2011). A cikin maƙalarsa mai taken: Al'adun Auren Zawarawa a ƙasar Hausa". A cikin maƙalar ya kawo ma'anar al'ada da ma'anar kalmar aure. Haka kuma an kawo bayanin wace ce Zawara? Da kuma bayanin al'adun neman auren Bazawara da bambanci tsakanin neman auren Bazawara da na Budurwa, duk dai a cikin wannan maƙalar. Wannan maƙala tana da alaƙa da binciken da ake aiwatarwa, domin duk ana magana ne a kan al'adun Hausawa, sai dai sun bambanta domin shi akan al'adun aure ya rubuta maƙalarsa, wannan kuma a kan al'adu da sana'o'in gargajiya na Hausawa, waɗanda su ke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba ya shafa.

 Gusau, (2010). A cikin Maƙalarsa mai taken" Al'adun Hausawa a cikin Makarantun Allo: Nazari a kan wasu al'adu da suka danganci karatu da zamantakewa a cikin makarantun Allo". A cikin maƙalar ya yi gabatarwa in da ya bayyana cewa "Hausawa Al'umma ce mai tarin al'adu da yawa". Ya kawo ma'anar Al'ada da makarantar Allo. Duk a cikin takardar ya yi bayanin al'adun karatun Bahaushe da makamantansu. Wannan maƙala tana da alaƙa da wannan bincike, saboda duk ana magana ne akan al'adun Hausawa, da yadda suke wakana a cikin rayuwa. Sai dai sun bambanta domin shi wannan bincike iya al'adu da sana'o'in gargajiya na Hausawa, waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba ya shafa.

2.5.4 MUJALLU

 Almajiri, T. S. (2012). "Zamantakewar Hausawa matasa a ƙarƙashin shirin gama-Duniya". A cikin mujalla mai suna: "Journal of African Languages: Jami'ar Ahmadu Bello Zaria. A cikin wannan maƙala an nuna yanayin zamantakewar Hausawa. Alaƙar wannan mujalla da binciken da ake kan aiwatarwa ita ce ta fuskar al'ada domin zamantakewa ta haɗa da dukkanin hanyoyin da ake bi wajen tafiyar da rayuwa kama daga kan sana'o'i da magunguna da muhallai da makamantansu na al'umma wajen gudanar da zamantakewar rayuwa. Amma suna da bambanci domin shi ya rubuta maƙalarsa ne a kan zamantakewar Hausawa, wannan bincike kuma ya shafi iya sana'o'in gargajiya na Hausawa waɗanda suke gudana a cikin da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba, waɗanda al'ummar garin Kazaure ke aiwatarwa domin kyautata zamantakewa a tsakaninsu.

 Murtala, G. Y. (2011). Ya yi rubutu a kan "Al'adun Auren Zawarawa a ƙasar Hausa". A cikin mujalla mai suna: "Algaita Journal of current reserch in Hausa studies. Ta Jami'ar Bayero. A cikin wannan mujalla an yi bayanin al'ada da ire-iren al'ada kamar Aure, da bayanin Al'adu akan auren Zawarawa. Alaƙar wanna mujalla da binciken da ake yi ita ce, dukkaninsu su na magana ne akan Al'ada, kuma suna nuna ire-iren al'adun gargajiya na Hausawa. Amma suna da bambanci, domin wannan binciken bai shafi al'adun Aure ba. iya al'adun da suke gudana a cikin sana'o'in gargajiya na Hausawa, waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba ya shafa.

 Waya, Z. I. (2008). "Hausawa da Al'adunsu, dangane da aikin Hajji". Mujalla mai suna "Algaita Journal of current reserch in Hausa studies. Nubember 5. Ɓol. 1. Ta jami'ar Bayero Kano. A cikin wannan mujalla an bayyana su wane ne Hausawa da kuma Al'adun Hausawa kamar Sana'o'in da muhallai da makamantansu. Alaƙar wannan mujalla da binciken da ake yi ita ce, dukkaninsu suna magana ne akan Al'ada, kuma suna nuna ire-iren al'adun gargajiya na Hausawa. Amma suna da bambanci, domin wannan binciken ya taƙaita ne akan iya al'adun da suke gudana a cikin sana'o'in gargajiya na Hausawa waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba ya shafa.

 Aminu, L. A. (2006). Ya yi rubutu a kan "Tattalin arzukin Al'umma: Nazarin Sana'o'i da kasuwancin Hausawa". A cikin wata "Journal" mai suna "Algaita" ta Jami'ar Bayero da ke Kano. A cikin wannan mujalla an yi bayanin mene ne tattalin arzuki da ire-iren sana'o'i na kasuwannin Hausawa kamar sana'ar fawa da fatauci da noma da makamantansu. Wannan maƙala ta na da alaƙa da binciken da ake aiwatarwa, domin duk suna magana ne a kan tattalin arzuki da al'adun Hausawa, sai dai sun bambanta domin shi a kan tattalin arzuki ya rubuta maƙalarsa, wannan binciken kuma a kan al'adu da sana'o'in gargajiya na Hausawa, waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba wanda ta dalilin su tattalin arzukin garin Kazaure ke haɓaka.

 Usman B. B. (1981). "Kiɗan Sana'ar Ƙira Don Zuga Maƙera". A cikin mujalla mai suna " Journal of African Languages". Wadda aka gabatar a sashen nazarin Harsunan najeriya na Jami'ar Ahmadu Bello: Zariya. A cikin wannan mujalla an yi Bayanin ɗaya daga cikin sana'o'in gargajiya na Bahaushe, wato sana'ar ƙira da ire-iren al'adun maƙera yayin da aka zuga su ta hanyar ƙiɗa musu taken maƙera. Alaƙar wannan bincike da wannan mujalla ita ce ta fuskar al'adu da sana'o'i'n gargajiya na Hausawa. Amma sun bambanta domin shi ya yi aikinsa ne akan ɗaya daga cikin sana'o'in gargajiya na Hausawa, wannan bincike kuma ya shafi iya sana'o'in gargajiya na Hausawa waɗanda suke gudana a cikin da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba.

2.5.5 TAKARDUN ƘARA WA JUNA SANI

 Gobir, Y.A. "Tsofaffin Al'adun Hausawa a cikin waƙoƙin na Narambaɗa". Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani, a sashen nazarin Harsunan Najeriya da Afirka na Jami'ar Bayero Kano. Daga ranar 15 zuwa 17 na watan satumba, 2019. A cikin wannan takarda an yi bayanin wasu daga cikin tsofaffin al'adun Hausawa na cikin waƙoƙin Narambaɗa kama daga kan sana'o'i da muhallai da makamantansu. Alaƙar wannan takarda da wannan bincike ita ce ta fuskar al'ada, domin dukkaninsu suna magana akan al'adun Hausawa. Sai dai suna da bambanci domin shi ya yi aikinsa ne a kan al'adun Hausawa na cikin waƙoƙin marigayin mawaƙi wato Ibrahim Narambaɗa, yayin da wannan bincike kuma za a yi shi ne akan sana'o'in gargajiya na Hausawa, waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba.

 Gobir, Y. A. "Da Abin mu aka Gan Mu: "Darussan Haɗin kai daga Al'adun Hausawa". Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani. A Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, 1 zuwa 3 na watan maris 2015. A sashen "Faculty of Art and Islamic studies. Wannan takarda ta yi bayani mai gamsarwa a kan al'adun Hausawa da hanyoyin haɗin kai, na al'adun Hausawa. Alaƙar wannan takarda da wannan bincike ita ce ta fuskar al'ada, domin dukkaninsu suna magana a kan al'adun Hausawa. Sai dai suna da bambanci domin shi ya yi aikinsa ne a kan haɗin kai na al'adun Hausawa, wannan bincike kuma an yi shi ne akan al'adun Hausawa ta fuskar sana'o'in gargajiya na Hausawa, waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba.

 "The Hausa Peole, Language and History: Past, Present and Future". Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa na farko. Wanda sashen nazarin harsunan Najeria, Jami'ar Kaduna ta shirya daga ranar 22 zuwa 25 na watan Maris 2015. A wannan takarda an yi bayanin cewa Hausawa Al'umma ce da ta dogara da kanta wajen samar da; hanyoyin arzikinta, ya kara da cewa "Ba a san Hausawa da ragwanci ko kasala ba, tun asali sukan tashi tsaye tsayin daka wajen samarwa da kawunansu abubuwan buƙata da sauran su". Wannan takarda tana da alaƙa ta kai tsaye da binciken da ake gudanar wa, domin ta yi bayani a kan tattalin arzukin Al'ummar Hausawa wanda yake samuwa ta hanyoyi da dama, kama daga kan sana'o'i da sauran su. Sai dai suna da Bambanci domin wannan aiki ya shafi iya sana'o'in gargajiya na Hausawa ne, waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba. Waɗanda ta dalilinsu tattalin arzukin garin Kazaure ke bunƙasa ta dalilinsu.

 Gobir, Y. A. "Iska a Tunanin Bahaushe a ƙarni na 21". Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa akan; "Harshe da Adabi da Al'adun Hausawa". A cibiyar nazarin Harsunan Najeriya, Jami'ar Bayero Kano, daga ranar litinin 14 zuwa Laraba 16 na watan Janairu, 2013. Alaƙar wannan takarda da wannan bincike ita ce ta fuskar al'ada, domin dukkaninsu suna magana a kan al'adun Hausawa. Sai dai suna da bambanci domin shi ya yi aikinsa ne akan al'ada ta fuskar "ISKA". Wannan bincike kuma an yi shi ne a kan al'ada ta fukar sana'o'in gargajiya na Hausawa, waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba.

 Umar, M. B. (1983). A Wannan takarda an yi bayanin abubuwa da yawa, daga ciki an taɓo; ma'ana ta tattalin arzuki da dangoginsa. Bayan haka kuma an yi magana akan sana'o'i, wanda ƙarƙashin haka ne ya zayyano, sana'o'in gargajiya na Hausawa harda sassaƙa wanda ya nuna, cewa noma shi ne wanda gidan kowa akwai shi. Alaƙar wannan takarda da wannan bincike ita ce ta fuskar al'ada, domin dukkaninsu suna magana a kan al'adun Hausawa. Sai dai suna da bambanci domin shi ya yi aikinsa ne a kan tattalin arzuki, wannan bincike kuma an yi shi ne a kan sana'o'in gargajiya na Hausawa, waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba. Waɗanda ta dalilinsu tattalin arzukin garin Kazaure ke haɓaka ta dalilinsu.

2.5.6 JARIDU

A Jaridar BBC Hausa wadda aka wallafa a ranar 14 ga watan Fabrairu na shekarar 2022. Jaridar ta yi bayanin yadda wani matashi ke fafutukar bayyana musu alfanunta tare da jawo hankalin matasa ƴan uwansa domin shiga harkar noma a Najeriya. In da aka zaɓi matashi ɗan ƙasa da shekara 30 a matsayin shugaban ƙungiyar matasa ta Najeriya, mai suna NYFN.

 NYFN wata ƙungiya ce da take ayyukanta a kan harkokin kasuwancin noma dan baiwa matasa damar morar damarmakin da ke cikin harkokin noma.

 Haƙiƙa wannan jarida ta na da alaƙa ta kai tsaye da binciken da a ke aiwatarwa, domin noma ya na ɗaya daga cikin sana'o'in gargajiya na Hausawa. Amma suna da bambanci domin wannan binciken iya sana'ar noma wanda yake faruwa a gefen Dam ɗin Muhammadu Ayuba ya shafa.

 A Jaridar Aminiya wadda aka wallafa a ranar 06 ga watan maris na shekarar 2022. A Jaridar an bayyana yadda wani Bature ya haska yadda ya ke siyo ɗanyen nama ya wanke shi da ɗanyen kwai, ya haɗa shi da madara ya runƙa ci ɗanye ba tare da an dafa ko soyawa ba. Jaridar ta ce " Baturen ya bayyana hakan a shafinsa na Instagram mai adireshin @rawmeaedperiment, sun ce "Baturen da ke cin ɗanyen naman ya bayyana cewa yana cin ɗanyen naman ne, domin neman tsawon rai inda ya shafe kwanaki 78 a jere ya na cin ɗanyen naman".

 Alaƙar da ke tsakanin wannan binciken da wannan jarida ita ce, ta fuskar ɗanyen nama, domin galibi ɗanyen nama na samuwa ne ta dalilin masu gudanar da sana'ar fawa, wadda tana ɗaya daga cikin sana'o'in gargajiya na Hausawa. Amma sun bambanta, domin shi wannan binciken ya taƙaita ne a kan iya sana'ar fawa wadda take gudana a garin Kazaure.

 A Jaridar BBC Hausa wadda aka wallafa a ranar 11 ga watan Augusta na shekarar 2022. A jaridar an bayyana cewa "Matan da ba sa cin nama za su iya fuskantar yiwuwar karyewar kwankwaso a nan gaba". In da suka ƙara da cewa " masu binciken sun riƙa bin rayuwar mata 26,000 na tsawon shekaru 20. Masu binciken sun yi nazari a kan rukunin mata masu shekaru 35 zuwa 69. Jagoran wannan binciken mai suna James webster ne ya ce "Matan da ba sa cin nama na iya rasa sinadaran inganta lafiyar ƙashi da tsokar ƙashi, lamarin da ke haifar da haɗarin karaya.

 Wannan jarida tana da alaƙa da binciken da ake gudanarwa domin ta yi magana ne a kan nama, wanda galibi masu sana'ar fawa ne ke samar da shi ga Al'umma. Amma suna da bambanci da wannan bincike, domin shi wannan binciken ya taƙaita ne a kan sana'ar fawa wadda take gudana a garin Kazaure

 A Jaridar Aminiya wata sanarwa da ƙungiyar matasan Kano ta bayar, zuwa ga gwabnatin jihar Kano mai taken "Ƙungiyar matasan kano Adɓocacy Organisation ". A ranar 20 ga watan Augusta 2020. A cikin bayanin da Jaridar ta wallafa ta ce "Ƙungiyar matasan sun bayyana irin gudunmawar da masu sana'ar Ga-ruwa ke bayarwa ga Al'umma, saboda haka suna bawa gwabnatin Kano shawarar ka da a hana masu sana'ar gudanar da sana'arsu a lokacin kullen da ake yi, domin hana yaɗuwar cutar Coɓid 19. Amma kafin hakan gwabnati ta kula da masu gudanar da sana'ar wajen bin dokokin hana yaɗa cutar ga Al'umma a yayin da suke jigilar ruwan ga Al'umma.

 Babu shakka wannan jarida tana da alaƙa ta kai tsaye da wannan binciken domin ta yi magana ne a kan sana'ar ga-ruwa wadda tana ɗaya daga cikin sana'o'in Hausawa na gargajiya. Amma suna da bambanci domin wannan binciken iya sana'ar ga-ruwa wadda ta ke faruwa a ciki da gefen Dam ɗin Muhammadu Ayuba ta shafa.

 A Jaridar BBC Hausa wadda aka wallafa a ranar 7 ga watan satumba na shekarar 2019, a jaridar an bayyana muhinmancin cin nama ga Ɗan Adam. An kuma yi bayanin cewa " Waɗanda basa cin nama suna fuskantar barazanar kamuwa da cutar mutuwar ɓarin jiki da ciwon zuciya. Sun bayyana hakan ne a lokacin da ƙasar Birtaniya ta bayyana sakamakon gwaje-gwajen da ta shafe shekaru 18 ta na yi akan mutane 48,000.

 Wannan jarida tana da alaƙa da binciken da ake gudanarwa domin ta yi magana a kan nama, wanda galibi masu sana'ar fawa ne ke samar da shi ga Al'umma. Amma suna da bambanci da wannan bincike, domin shi wannan binciken ya taƙaita ne a kan sana'ar fawa wadda take gudana a garin Kazaure.

2. 7 NAƊEWA

 Wannan babin ya yi waiwaye a kan ayyukan da suka gabata daga wajan masana da manazarta, musamman ma waɗanda suke da alaƙa ta kusa da wannan aikin. Haka kuma an yi bitar abubuwan da suka gabata ne a akan wallafaffun litattafai. Haka kuma an duba kundayen bincike tun daga na matakin Dufuloma da na (N.C.E) har da na digirin farko da na biyu har da na uku gami da duba ingantattun takardun da aka gabatar a tarukan ƙara wa juna sani. Bayan haka waiwayen bai tsaya iya nan ba har kafafen yaɗa labarai da yanar Gizo-gizo an bibiya kuma hakan ya ba da muhinmiyar gudummawa wajen bayar da ƙarin haske akan yanayin yadda yakamata a gudanar da wannan bincike mai taken "Gudummawar Dam ɗin Muhammadu Ayuba wajen haɓaka tattalin arzuƙin garin Kazaure". Kuma Alhamdulillahi an samu nasarar yin hakan cikin sahalewar ubangiji Allah (S.W.T).

 

 

 

 

BABI NA UKU

HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

3.0 SHIMFIƊA.

 Dabarun tattara bayanai su ne ginshiƙai kuma ƙashin bayan kowane irin bincike, matuƙar ana buƙatar samun ingantattu kuma jajirtattun bayanai ko hujjoji da za su dace da wannan bincike da ake gudanarwa. Matuƙar dai ana son sakamakon ya inganta, babu shakka samar da bayanai da hujjoji ingantattu ko fasihai ita ce hanya mafi muhinmanci ga kowane irin bincike. Akwai dabarun tattaro bayanai da daman gaske birjik, kuma ana samar da dabarun ne bisa lura ko la'akari da irin binciken da ake kan gudanarwa ko matsalar da take cikin nazarin domin ganin an fitar da Jaki daga duma, wajen samun amsar tambayoyin da binciken yake ɗauke da su ko hasashen da binciken yake da muradin tabbatarwa.

Don haka wannan aiki ya nazarci hanyoyi da kuma irin sana'o'in da suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin garin Kazaure na Muhammadu Ayuba (Magajin gari) wajen bayar da gudummawa ga haɓakar tattalin arzuƙin garin Kazaure. Domin ganin an samu nasarar hakan, binciken ya yi amfani da dabarun tattara bayanai kamar; lura/sa-ido ta kai tsaye da hira ko zantawa da mutane waɗanda wannan binciken ya shafa. Bayan haka kuma an yi amfani da hanyar naɗar zantukansu lokacin da suke gudanar da al'amuransu, da kuma ɗaukar hirarrakin da aka yi da su yayin gudanar da wannan bincike, gami da tattaki ƙafa-da-ƙafa domin samun nasarar gudanar da wannan bincike .

 3.1 LURA / SA-IDO.

 Haƙiƙa yayin gudanar da wannan bincike an yi amfani da dabarar sa-ido da kuma lura da yanayin yadda al'amura suke faruwa a ciki da wajen Dam ɗin na Muhammadu Ayuba, wanda suka haɗa da sana'o'in da suke faruwa a tantagaryar cikin ruwa, kamar sana'ar: Su (kamun kifi) da waɗanda suke faruwa a gefen Dam ɗin kamar Noma, (noman rani da na damuna) da Kiwo, da Wanki da Guga da kuma masu Ga-ruwa (masu ɗiban ruwan sayarwa) da Mahauta (Barunje/Rundawa) da ma wasu masu amfani da wannan ruwa wajen gudanar da sana'arsu kamar shirya finafinai da kuma masu yawon buɗe idanu da ɗalibai masu nazari da sauran su. A yayin gudanar da al'amuransu za a lura da yanda suke harkokinsu da kuma irin abubuwan da suke shiga suna fita a cikin al'amuran nasu, a inda an yi hakan ne wasu da saninsu wasu kuma ba da saninsu ba ko umarninsu, an yi hakan ne ba don wata manufa ba sai dan domin ganin an samu bayanai ingantattu kuma nagartattu kamar yadda masu iya magana kan ce " Zuwa da kai, ya zarce saƙo", haka kuma mun ƙara tabbata cewa; "Gani ya kori ji".

3.2 NAƊAR ZANTUKA

 Tabbas wannan dabara tana ɗaya daga cikin hanyoyin da aka yi amfani da su wajen samun nagartattun bayanai, lokacin da ake gudanar da wannan nazari an naɗi muryoyin masu alaƙa ta kai tsaye da wannan bincike, a inda aka yi amfani da Rukoda, da wayar hannu (salula). Sannan daga baya aka zauna aka nutsu domin yin bitar abubuwan da aka naɗa domin tace bayanan da suke da gurbi a wannan bincike da kuma ajiye wanda ake ganin ba su da muhalli a wannan bincike.

 3.3 ƊAUKAR HOTUNA

 Masu iya magana kan ce "Gani ya kori ji". A yayin gudanar da wannan nazari babu shakka an gaskata wannan zance, domin an yi ƙoƙari gami da jajircewa tare da zage dantse wajen ganin an ɗauki hotunan wasu daga cikin abubuwan da wannan bincike ya shafa. Domin mai bincike ko nazari a kan wannan bincike zai ƙara fahimtar abubuwa a zahiri, a inda aka yi amfani da na'urar zamani irin su, kyamara (Camera) wajen ɗaukar hotuna. Haka kuma an yi amfani da nau'o'in kyamarori wanda zamani ya zo da su, kamar kyamarar wayar hannu, da kuma kyamarar ɗaukar hoto gami da kyamarar ɗaukar hoton abubuwa daga sararin samaniya (flight camera) wato kyamara mai ƙirar jirgin sama, duk domin ganin an samu nasarar abun da ake da buƙata game da wannan bincike.

3.4 TATTARO BAYANAI TA HANYAR RABA MATAMBAYIYA.

 Matambayiya tana nufin mutum ya tsara/hirya jadawalin wasu tambayoyi a rubuce bisa wani abin ko abubuwan rubutu, kamar takarda ko fata ko ganye da makamantan su, da nufin a rabawa mutane/al'umma da nufin su karanta ko a karanta musu su kuma ba da amsar tambayoyin da suke ɗamfare bisa abun rubutu. Babu shakka wannan ma wata hanya ce wacce aka yi amfani a ita a wannan bincike a inda aka shirya matambayiya aka yi kwafin kimanin guda ɗari uku da hamsin (350), kuma aka rabawa masu alaƙa da wannan bincike aka kuma tsaya suka karanta suka cike amsar da hannayensu, wasu kuma aka karanta musu suka faɗi amsar da suke ganin ita ce ta dace da amsar matambayiyar aka cike musu dai-dai da ra'ayinsu. Daga baya aka tattara matambayiyar domin dubawa a gano amsoshin abubuwan da ake buƙata, ta hanyar amfani da amsoshin kaso mafi rinjaye daga cikin waɗanda suka cike matambayiyar domin ganin an ware tsakanin zare da abawa.

3.5 TATTAUNAWA/ ZANTAWA

 A wannan bincike an yi hira da mutanan da aka tabbatar da samun ingantattun bayanai ko jawabai daga gare su. Musamman masana tarihi da kuma waɗanda suke da ruwa da tsaki wajan sanin tarihin garin Kazaure da abubuwan da suke a cikin sa. Sannan kuma an tattauna da masu gudanar da sana'o'in gargajiya na Hausawa a gefen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure.

3.6 TATTAKI

 Hausawa na cewa " Zuwa da kai, ya zarce saƙo!" Haka ma a wannan bincike an yi tattaki ƙafa da ƙafa zuwa Dam ɗin domin samun nagartattun bayanai kamar yadda masu salon magana kan ce "Gani ya kori ji!".

 Wata hanyar da aka yi amfani da ita, ita ce ziyartar ɗakunan karatu, domin laluba gami da binciko bayanan da aka wallafa a cikin mujallu da muƙalu da jaridu da takardun ƙarawa juna sani, har da wasu daga cikin bugaggun litattafai waɗanda suke da alaƙa da wannan bincike.

 Haka kuma an yi amfani da hanyar tattara bayanai daga cikin kundayen binciken da magabata suka gabatar a manyan cibiyoyin ilimi, kamar Jami'o'i da kwalejoji da sauran cibiyoyin bincike daban-daban.

 Bayan haka an bibiyi gidajen adana tarihi da al'adu da suke a garin Kano da kaduna domin samun wasu daga cikin adanannun bayanai a kan garin Kazaure. Bibiyar waɗannan hanyoyin za su bayar da gagarumar gudunmawa matuƙa-gaya, wajan samu gami da tace ingantattu da sahihan bayanan da suka zama matakan da aka tattaka tun daga farko har zuwa ƙarshen wannan bincike, wanda aka samu nasarar gudanar da binciken yadda ya kamata.

 3.7 NAƊEWA.

 Bisa duba da la'akari da bayanan da suka gabata a wannan babi na hanyoyin da aka yi amfani da su yayin gudanar da wannan bincike, babu shakka an yi amfani da hanyoyi da daman gaske domin samun nagartattun bayanai, wasu daga cikin hanyoyin sun haɗa da; lura/sa-ido ta kai tsaye na yadda al'amura ke gudana. Haka kuma an yi tattaki ƙafa-da-ƙafa domin Hausawa kan ce "Zuwa da kai ya zarce zaƙo", bayan haka an yi amfani da kyamarori domin ɗaukar hotunan wasu daga cikin abubuwan dake faruwa, an kuma yi amfani da hanyar naɗar zantuka domin naɗar bayanai alokacin da ake tattaunawa da masu alaƙa ta kai tsaye da wannan bincike, sai kuma amfani da hanyar raba matambayiya domin samun ingantattun amsoshin da suka dace da wannan bincike, kuma waɗannan hanyoyi sun taimaka ƙwarai wajen samun kyawawan bayanai da hujjojin da suka dace da wannan bincike.

 

 

 

BABI NA HUƊU

GUNDARIN BINCIKE

4.0 SHIMFIƊA

 A wannan babi mai taken babi na huɗu (4) wato babin gundarin bincike, a nan ne za a yi bayani dalla-dalla a kan sakamakon da wannan binciken ya gano dangane da sana'o'in gargajiya na Hausawa, waɗanda suke wakana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba (magajin gari) na cikin garin Kazaure. Waɗanda tattalin arzukin garin Kazaure ke haɓaka ta dalilin samuwar Dam ɗin.

4.1 GUDUNMAWAR DAM ƊIN MUHAMMADU AYUBA GA AL'UMMAR GARIN KAZAURE

 Garin Kazaure, gari ne mai daɗaɗɗen tarihi wanda ya shafe ɗaruruwan shekaru masu tarin yawa da kafuwa. A shekarun baya garin Kazaure ya sha fama da mastalar rashin wadataccen ruwan gudanar da harkokin yau da kullum, waɗanda al'ummar wannan gari na Kazaure ke buƙata wajen tafiyar da harkokin rayuwarsu cikin salama, kamar, abubuwan da suka shafi gine-gine da al'adu da sarautu da magunguna da tufafi da kuma sana'o'in gargajiyar Hausawa, kamar; Fawa da Jima da Noma da Kiwo da Su ( kamun kifi) da sauran makamantansu. Masana tarihin wannan gari sun tabbatar da cewa samuwar Dam ɗin Muhammadu Ayuba ya kawo muhinmiyar gudummawa a garin Kazaure wajen samarwa da al'ummar wannan gari wadataccen ruwan gudanar harkokin rayuwar yau da kullum.

 Tarihi ya nuna cewa kafin samuwar Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin kazaure, al'ummar wannan garin matsalar wadataccen ruwan da take fama da ita ya samu ne sanadiyyar rashin isassun rijiyoyi da sauran hanyoyin samuwar ruwa mai tsafta. Masana tarihin wannan garin sun ce "Kafin samuwar Dam ɗin Rijiyoyi ake amfani da su wajen samun ruwan gudanar da harkokin rayuwar yau da kullum a wannan gari, wanda yawan rijiyoyin daga baya sai ya yi wa al'ummar garin Kazaure ƙaranci sosai, kama daga haifaffu da sauran baƙin da suke shigowa daga sassa daban-daban zuwa wannan gari, kamar mutanen Jahar Kano da Katsina da waɗanda suke shigowa daga Faranshi (Nijer) da dai makamantansu.

 Waɗannan dalilai suna daga cikin abubuwan da suka haifar da matsalar wadataccen ruwan amfanin yau da kullum, amma daga lokacin da wani kwamishinan Ayyuka na Jahar Kano wato Muhammadu Ayuba da ya yi zamani alokacin ya gina katafaren Dam a tsakiyar wannan gari na Kazaure, a dai-dai wajen da wasu fadamu suke na hukumar gidan sarki da sauran al'ummar wannan gari, waɗanda suka samu a sanadiyyar wata ƙorama da take tasowa daga garin Karaftayi zuwa wannan waje. Sai al'ummar wannan gari suka fita daga matsalar rashin wadataccen ruwan da suke fama da ita tsawon wani lokaci, daga samuwar Dam ɗin sana'o'in gargajiya na Hausawa suka fara samuwa a cikin Dam ɗin kamar sana'ar Su (kamun kifi) da kuma wajensa kamar Noma da wanki da guga da samuwar wasu sababbin rijiyoyi waɗanda masu sana'ar Garuwa suke ɗibar ruwan suna shiga da shi saƙuna da lunguna da kwararo na wannan garin, a sanadiyyar hakan aka samu damar gudanar da sana'o'in gargajiyar Bahaushe cikin salama a cikin wannan gari. Tun daga sana'ar Fawa da Jima da Rini da Kiwo da sauran ƙananun sana'o'i kamar soya kifi da da gasa nama da masu soye-soye irinsu sayar da ƙosai da Awara da kambu da kuma dafe-dafe kamar masu dafa abincin sayarwa da makamantansu. Waɗannan sana'o'in babu shakka sun bayar da gagarumar gudummawa wajen haɓaka tattalin arzukin garin Kazaure tun daga lokacin samuwar Dam ɗin har zuwa wannan lokaci.

4.2. GUDUNMAWAR DAM ƊIN DANGANE DA RAYA AL'ADUN GARGAJIYA NA BAHAUSHE

 Masu fasahar baka kan ce " Abin nema ya samu, matar Falke ta haifi ɗan Jaki". Babu shakka samuwar Dam ɗin garin Kazaure na Muhammadu Ayuba ya ba da gagarumar gudummawa wajen raya al'adun gargajiyar Bahaushe. Kafin samuwar Dam ɗin mutanen garin Kazaure su na fama da ƙarancin wuraren gudanar da wasu sana'o'in na su, wasu kuma su na son farawa amma rashin samun wajen gudanarwa ya dakatar da su, kamar masu son yin sana'ar Su (kamun kifi) amma ba su da wadataccen ruwa ko isasshen ruwan yin sana'ar, da masu buƙatar yin Noman rani amma ba su da isasshen wajen yin Noman rani.

 Daga lokacin da Muhammadu Ayuba ya gina Dam a garin Kazaure sana'o'i n gargajiyar Bahaushe da al'adun cikinsu suka ci gaba da haɓaka, tun daga wancan lokaci har zuwa wannan lokaci, kuma suna ba da muhinmiyar gudummawa wajen haɓakar tattalin arzukin garin kazaure. Wasu daga cikin sana'o'i da al'adun da suka haɓaka a dalilin samuwar Dam ɗin sun haɗa da:

4.2.1 Sana'ar Su (kamun kifi)

 Sana'ar Su (kamun kifi) ita ce sana'ar kamun kifi da sauran namun cikin ruwa. Akan shiga ruwa ko dai kai tsaye a yi amfani da hannu ko kuma ta hanyar amfani da wani abu domin kama kifi a ci ko a sayar. Wannan sana'a ta kamun kifi tana ɗaya daga cikin daɗaɗɗun sana'o'in gargajiya na Hausawa. Mai yin wannan sana'a ana kiran shi "masunci", idan suna da yawa "masunta". Ana gudanar da sana'ar kamun kifi a cikin kogi da tafki da ƙorama da gulbi da Dam da sauran guraren wucewa da kuma taruwar ruwa. Babu shakka wannan sana'a ta Su (kamun kifi) ta na gudana a cikin wannan Dam ɗin na Muhammadu Ayuba, yayin da ake amfani da ruwan Dam ɗin wajen gudanar da harkokin wannan sana'a. Kafin samuwar Dam ɗin akwai masu gudanar da wannan sana'a ta Su a garin Kazaure amma ba su da yawa sosai sanadiyyar rashin Dam a cikin garin, waɗannan mutane su na tafiya gefen garin Kazaure, wato ƙauyukan da suke da ruwa domin gudanar da wannan sana'a, daga cikin ƙauyukan akwai; Dam ɗin Karaftayi na ƙauyen da ke yamma maso kudu da garin kazaure sai Dam ɗin Dambo Dam na yamma maso Arewa da garin kazaure.

 A lokacin da mai girma hakimi wato kwamishinan ayyuka na jahar kano Muhammadu Ayuba, ya gina wannan Dam ɗin a shekarar 1974 domin ragewa al'ummarsa matsalar rashin ruwan da take fama da shi wajen gudanar da harkokin rayuwar yau da kullum. Babu shakka masu sana'ar su kakarsu ta yanke saƙa ma'ana nesa ta zo kusa, wahalar tafiya wasu ƙauyuka don gudanar da sana'arsu ta zo ƙarshe. Domin kuwa mafi yawancinsu sun ci gaba da sana'arsu a cikin wannan Dam, haka kuma su ka ci gaba da sana'arsu cikin annashuwa da walwala, domin irin alhairan da suke samu a cikin wannan Dam. Wasu mutanen kuwa sun je sun koyi sana'ar su (kamun kifi) a ruwan domin samun abubuwan buƙata na yau da kullum, domin gudanar da rayuwa, kuma Allah ya ba wa waɗannan masu sana'a haɗin kai da tallafawa junansu wajen gudanar da sana'o'insu. Kuma suna da ƙungiya ta su mai zaman kanta suna da wakilai da shuwagabanni da doka da ƙa'ida, a yanzu haka shugaban wannan ƙungiya ta masu sana'ar kamun kifi a cikin ruwan Dam ɗin Muhammadu Ayuba, sunan shi Lawan Yahaya (Ɗanjawo).

 Akwai ire-iren masu kamun kifi sama da kala biyar da masu sana'ar Su (kamun kifi) ke gudanarwa a wannan Dam ɗin kuma ko wane kalar kamun kifi da akwai irin masu aiwatar da shi a wannan Dam ɗin, ire-iren kamun kifin su ne kamar haka:

v  Akwai masu kamun kifaye a kan kwale-kwale da raga ma'ana da kalli, suna tafiya akan kwale-kwale a saman ruwa suna bin kalli suna kama kifaye.

v  Akwai masu kamun kifaye akan kwale-kwale masu watsa Birgi/bargi suna tafiya a saman ruwa suna watsa birgi suna kamun kifaye.

v  Da kuma masu kama kifaye a kan kwale-kwale masu watsa abinci kamar hatsi ko garin dawa ko masara sai su watsa birgi dai-dai wajen da kifayen suka taru suna cin abincin da suka watsa suna kama kifayen.

v  Akwai masu kamun kifaye daga ƙasa suna zagayawa wauraren da ba su cika zurfi ba, suna watsa abinci bayan kifayen sun taru suna cin abincin sai su jefa birgi su kama kifayen.

v  Akwai masu kamun kifaye ta hanyar haƙa mali a gefen ruwan suna zuba gero sai bayan tsayin wani lokaci bayan kifayen sun shiga cin abincin sai su kama kifayen.

v  Akwai masu kamun kifaye daga kan gorar-ruwa suna tafiya a saman ruwa bisa gorar-ruwa suna kama kifaye.

 Dukkanninsu ire-iren waɗannan masu kamun kifayen suna samar wa da ɗaruruwan mutane kifayen da suke buƙata a ciki garin Kazaure da wajenta, domin har daga wasu garuruwan na wajen Kazaure suna zuwa suna sayen kifaye a wajensu, kuma da kuɗaɗen kamun kifayen suke ciyar da kawunansu da iyalansu da sauran harkokin rayuwarsu na yau da kullum.

 Kimanin mutanen da ke kamun kifi a wannan Dam ɗin na Muhammadu Ayuba sun kai adadin mutane ɗari da tamanin da biyu (182) kamar yadda shugaban ƙungiyar masu sana'ar su (kamun kifi) ɗin ya bayyana a yayin zantawa da shi, kuma sana'ar ta kamun kifi tana ɗaya daga cikin sana'o'in gargajiya na Hausawa wanda tattalin arzukin garin Kazaure ke haɓaka ta dalilinsu, akwai sana'o'i masu yawa da suke samuwa a cikin garin Kazaure ta dalilin masu kama kifaye a Dam ɗin Muhammadu Ayuba, wasu daga cikinsu su sun haɗa da:

v  Akwai masu soya kifaye ƙanana da matsakaita (ramso), suna sayarwa.

v  Akwai masu soya kifaye manya ( Gammo-gammo da yanka-yanka), suna sayarwa..

v  Akwai masu dafa kifaye suna yi mishi miya suna sayarwa ( Dafge).

v  Akwai masu dafa kifaye suna yi mishi miya suna sayarwa ana ɗorawa a saman abinci.

v  Akwai masu yin dambu da shi suna ƙullawa a leda suna sayarwa ana masa laƙabi da suna dambun kifi.

 Muhinman kayan aikin da masu sana'ar kamun kifi suke amfani da su wajen kama kifaye a Dam ɗin Muhammadu Ayuba sun haɗa da:

  1. ƘUGIYA: Ana kafa ta a cikin ruwa a saƙala wani abu da kifi zai ci a jikinta, sai a baza ta acikin wani yanki na ruwan da ake son kama kifin a ciki.
  2. MALI: Abu ne da ake yin sa da itace da raga ta zare. Ana tsoma shi a cikin ruwa, idan kifaye suka shiga ciki sai a fito da shi a kwashe.
  3. KALLI: Shi ma dai kamar sauran kayan kamun kifi ya ke, wato raga ce ta zare ake kafewa a cikin ruwa, sai aja ta zuwa wani gefen idan kifaye suka taru a ciki sai a fito da su a kwashe.
  4. BIRGI/BARGI: Raga ce da zare ake yinta, wacce ake cin bakinta da dalma. Shi kuma birgi watsa shi ake yi a cikin ruwa, sai dalmar ta shiga cikin yashi ta kafe. Duk kifin da ya shiga ciki ba ya iya fita, idan suka taru a ciki, sai a janye shi zuwa gaɓar ruwa ko a saka cikin kwale-kwale a firfito da su a adana.
  5. FATSA: Fatsa ƙugiya ce guda ɗaya, ko biyu ake ɗaurewa a jikin sanda sai a saƙala wani abincin da kifi ya ke so, da zarar ya haɗiye wannan abinci sai ƙugiyar ta maƙale masa wuya sai a fisgo da ƙarfi a wullo shi wajen ruwa a kama.
  6. DALLA: Ita ma dalla raga ce ta zare, wacce ake riƙe gafe da gafen sai mutane su ratsa cikin ruwan su na ja. Duk kifin da su ka tokare shi to ba zai iya fita ba, bayan zuwa wani lokaci su fito da ita wajen ruwan sai su ciccire kifin.
  7. KOMA/HOMA: Ita kuma koma jaka ce ta raga da ake yi wa ƙaton baki riɓi biyu ake yin ta. Ana riƙe kowace ɗaya da hannu ɗaya, idan aka shiga ruwa da ita sai a riƙa tafiya can kuma sai a haɗe bakin ta a fitar da ita waje a kwashe kifayen da ke ciki.
  8. GORA: Ita kuma gora hawa kan ta ake yi ana iyo a cikin ruwa domin zuwa gurin da aka haƙa mali ko birgi ko makamantansu.
  9. KWALE-KWALE: Hawa ake kan shi ana sufuri a cikin ruwa.
  10. WUƘA: Ana amfani da ita wajen yanke kalli ko bargi ko mali idan ya harɗe yaƙi warwaruwa. Waɗannan sune wasu daga cikin muhinman kayan aikin kamun kifi, ga hotunan wasu daga ciki domin bayar da ƙarin haske ga mai nazari:

 

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

4.2.2 SANA'AR NOMA

 Noma sana'a ce a ƙasar Hausa, (Maɗauci da Isa da Daura, 1968), ana wa noma kallon cewa ita ce sana'ar da ta fi kowace sana'a muhimmanci, wacce idan babu ita rayuwar ma sam-sam ba za ta yiwu ba. Yakasai (1988). Sana'a ce da kusan kowane gida ake yinta musanman a karkara. Sana'a ce da ta girmi kowace sana'a a ƙasar Hausa, dama Duniya baki ɗaya. Saboda wannan dalilin ne ma yasa ake yi wa sana'ar kirari da cewa; "Na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo Duniya kai ya tarar". Asalin wannan sana'a yana komawa tun farkon samun halitta a doron wannan Duniya. Wato saukowar Annabi Adamu da Nana Hauwa'u cikin Duniya (Durumin iya, 2006). Alhassan da Musa da Zarruk(1982), sun bayyana noma a matsayin tonon ƙasa a fitar da amfaninta ta hanyar zafe ta, da zankaɗe ta, da yin shuke-shuke a bayanta.

 Sana'ar noma tana ɗaya daga cikin sana'o'in gargajiyar Bahaushe waɗanda suke gudana a bakin Dam ɗin Muhammadu Ayuba, kuma wannan sana'a ta noma babu shakka tana ba da gagarumar gudummawa wajen kyautatuwar rayuwar manoman, da kuma sauran al'ummar garin Kazaure. Domin tana samar musu da abubuwan biyan buƙatunsu da na iyalansu da kawunansu domin mafi yawan manoman da ke yin noma a bakin Dam ɗin da Allah suka dogara da ita suka dogara, da ita suke ci su sha da tufafi da muhalli da kula da lafiyar rayuwarsu da ta iyalansu. Musanman ma manoman da suke gudanar da noman rani da na damuna a wajen, ma'ana idan su ka kwashe abin da suka noma da rani, idan damuna ta kawo kai sai su shuka kayan noman damuna a wajen. Noman da ake gudanarwa a wannan waje ya kasu kashi biyu, kamar haka:

v  AKWAI NOMAN RANI: Noman rani noma ne amma an fi noma kayan miya da sauran makamantansu. Haka kuma abubuwan da aka fi shukawa da rani a Dam ɗin Muhammadu Ayuba suna da daman gaske. Wasu daga cikinsu sun haɗa da: Noman Tumatur da Albasa da na Kabeji da na kankana da na dankali da masara da Attaruhu da tattasai da yakuwa da kuɓewa da kabewa da gyaɗa da Barkono da Gurji da Citta da sauran makamantansu. Waɗannan kayayyakin amfanin noman rani ne da ake samarwa a bakin Dam ɗin Muhammadu Ayuba, kuma suna ba da gudummawa matuƙa gaya ga al'ummar garin Kazaure da ma wasun su, wajen gudanar da harkokin rayuwa na yau da kullum.

Haka kuma akwai ƙananan sana'o'in Hausawa na gargajiya waɗanda suke gudana a cikin garin Kazaure sanadiyyar wannan noman na rani da ake gudanarwa a garin Kazaure . ire-iren sana'o'in su ne kamar haka:

Ø  Akwai masu sayar da kayan miya a cikin garin Kazaure, wasu suna kasa kayan miyan a bakin tituna suna sayarwa, wasu kuma suna talla gida-gida suna sayarwa.

Ø  Akwai masu sayar da kayan yaji, kamar Citta da Albasa da sauransu.

Ø  Akwai masu sayar da ganyayyaki kamar: Kabeji da Salak da Lansir da Yakuwa da sauran su.

Ø  Akwai masu sayar da Gurji tare da ƙuli, a yayyanka shi a faranti a na haɗawa da ƙuli ana kwaɗawa.

Ø  Akwai masu sayan ɗanyun kayan miya suna yankawa, idan sun bushe su ɗauka su kai kudancin najeriya su sayar da sauransu.

Ø  Akwai masu sayar da Rogo dafaffe.

v  AKWAI KUMA MASU NOMAN DAMUNA: Akwai mutanen da su ke noman damuna a bakin Dam ɗin wasu bayan sun kwashe kayan amfanin ranin idan damuna ta zo, saboda ruwan da yake shigowa yana da yawa, sai su shuka Shinkafa da Alkama da Masara da sauran makamantansu, kuma suna yin amfani da su wajen ci da shayar da kawunansu da iyalansu da sauran buƙatun yau da kullum. Kamar dai noman rani akwai ƙananan sana'o'i da suke gudana a cikin garin Kazaure sanadiyyar wannan noman na damuna da ake yi a bakin Dam ɗin kamar haka:

Ø  Akwai masu yin Funkasau su na sayarwa.

Ø  Akwai masu sayar da dafaffen abinci kamar Shinkafa da Wake da sauransu.

 Waɗannan sana'o'in babu shakka samuwar Dam ɗin Muhammadu Ayuba ya ba da gudummawa wajen samuwar su, kuma suna ba da muhimmiyar gudummawa wajen haɓaka tattalin arzukin garin Kazaure. Waɗannan manoma suna da Ƙungiya ta su mai zaman kanta, kuma sun yi mata rijista a ofishin ƙaramar hukumar Kazaure da na Ƴansanda, su na da shugabannin da suke jagorantar wannan ƙungiya, sunan shugaban ƙungiyar Lawan Musa suna da mutane aƙalla mutum ɗari biyar da sittin a rubuce (560) a rubuce kamar yanda shugaban ƙungiyar ya shaida yayin zantawa da shi.

 Akwai kuma hotunan ire-iren abubuwan da ake nomawa a bakin Dam ɗin da suka haɗa da:

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

  Akwai kayayyakin aikin noma da ake amfani da su a wajen yin noma a bakin Dam ɗin Muhammadu Ayuba, kamar su:

1.      Fartanya: Fartanya ita ce babban makami ko kayan aikin gudanar da sana'ar noma, ta na da matuƙar muhimmanci a wannan sanaa. Da ita ake bi kunya-kunya ana sare dukkan wata ciyawar da ba a buƙata a gona. Fartanya kala uku ce: hauya, dungura ƙota da kuma fartanya.

2.      Sungumi: Shi ne makamin da ake amfani da shi wajen saran shuka; wato da shi ake sara ramin da za a yi shuka. Yana da baki irin na magirbi, sai dai ƙotarsa doguwa ce wacce takusan tsayin mutum.

3.      Magirbi: Magirbi da shi ake sassabe, da kuma girbin kayan amfanin gona kamar irin su dawa, gero, maiwa, da sauran dangoginsu waɗanda suke yin dogon kara a tsaye.

4.      Gatari: Gatari shi ne makamin da ake amfani da shi wajen sare icen da ya girma a gona don samun filin gona.

5.      Adda: Makami ce da ake amfani da ita wajen sara. Akan sare itatuwa ko ciyawa da ita, haka nan ma akan yi girbi da ita.

6.      Lauje: Ana amfani da lauje wajen shuci, wato yankan ciyawar da ke da tsayi. Sannan kuma da shi ake yankan shinkafa, alkama, da sauransu.

7.      Wuƙa: Ana amfani da wuƙa wajen yankan kayan amfani da suka haɗa da kuɓewa, yankan kan gero bayan an girbe, yankan kaba, da sauransu.

8.      Garma/Galma: Ana amfani da garma ko galma wajen yin huɗa.

9.      Ashasha: Nau’i ce ta garma da ake amfani da ita wajen noma ta hanyar rage girman kunya, ita takan burkuce kwarin kunya ne, sannan kuma ta rage faɗin kunyar, ta yadda mai aiki zai ji sauƙin gudanar da noma. A wasu guraren ma sai dai kawai ya ɗaga ciyawar ya karkaɗe ƙasar jikinta.

10.  Manjagara: Da shi ake sharar gona. Bayan an sassabe tushiya da sauran abubuwan da ba a so a lokacin rani kafin faɗuwar damina, to kuma sai a saka manjagara a share sararin gonar a ƙone.

11.  Igiya: Igiya ma ɗaya ce daga cikin kayan aikin gona wacce ake amfani da ita wajen ɗaure kayan amfanin gona da aka girba, kamar damin dawa, gero, da sauransu.

Waɗannan su ne wasu daga cikin muhimman ire-iren kayan aikin noma na rani da na damuna ga hotunan wasu daga ciki domin bayar da ƙarin haske ga mai nazari:

 

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

 4.2.3 Sana'ar Fawa

 Sana’ar fawa na ɗaya daga cikin tsofaffin sana’o’in ƙasar Hausa. Sanaa ce da ake yanka dabbobi domin a sayar da namansu ga mabuƙata. Wanda ke aiwatar da wannan sanaa shi ake kira Mahauci ko Barunje idan suna da yawa kuma mahauta ko Rundawa. Alhassan, Musa, da Zarruƙ (1982). Cewa suka yi ana kiran wannan sana’a da suna ‘Rudanci’. Sana'ar fawa tana ɗaya daga cikin sana'o'in gargajiya na Hausawa, wadda take gudana a bakin ruwan Dam ɗin Muhammadu Ayuba, Musamman ma a shekarun baya lokacin da ba a samu wadatuwar ruwan Burtsatse da na fanfuna ba. A shekarun baya masu wannan sana'a suna amfani da ruwan Dam ɗin wajen tafiyar da harkokin sana'arsu ta fawa, kasancewar garin ba shi da wani wadataccen ruwan amfani yau da kulkum face ruwan Dam ɗin, da shi suke yin amfani wajen fiɗar dabbobi idan sun yanka dabbobin da shi suke amfani wajen dafa naman da shi suke dukkannin amfani wajen sarrafa naman su sayar.

A yanzu haka mahautar garin Kazaure tana cikin kasuwar garin na Kazaure daga gabashin kasuwar wato bakin Dam ɗin na Muhammadu Ayuba daga yamma. A shekarun baya suna ɗibar ruwan Dam ɗin cikin sauƙi suna amfani da shi. Masu gudanar da wannan sana'a ta fawa a garin Kazaure suna da ƙungiya ta su ta mahauta, kuma suna da shuwagabannin da suke jagorantar ƙungiyar wajen tallafawa da hukunta masu laifi, sunan shugaban ƙungiyar masu sana'ar fawa na garin Kazaure Auduwa Ibrahim (sarkin fawa) shi yake yanke hukunci da sanya doka, kuma shi yake jagorantar masu sana'ar fawa na Kazaure a fadar sarkin Kazaure. Masu wannan sana'a a yanzu haka wasu suna amfani da ruwan Dam ɗin na Muhammadu Ayuba, wasu kuma suna amfani da ruwan Burtsatse (tuƙa-tuƙa) ko na fanfo wajen sarrafa naman dabbobin da suka yanka, sakamakon wadatar ruwa wanda hukuma da gwabnati ta samar a yanzu.   

 Saboda haka a bisa dalilin samuwar Dam ɗin masu gudanar da wannan sana'a, suna samar da abubuwa da daman gaske kamar Ɗanyen nama da Tsire da Balangu da Yaɗi da Naman kayan ciki da Kilishi da sauran makamantan su. Suna samarwa da al'ummar Kazaure naman ta da komaɗa da mayar da yawu, akwai ƙananan sana'o'in da suke gudana a cikin garin Kazaure ta sanadiyyar naman da masu sana'ar fawa suke samarwa kamar haka:

v  Akwai masu sayan ɗanyen naman suna dafawa su sayar a dafe.

v  Akwai masu sayen ɗanyen naman suna dafawa suna sayarwa a saman abinci.

v  Akwai ma su sayar da soyayyen nama ko Dambu.

v  Akwai masu sayen fata. Akan babbake ta a cire gashin a yi ganda ko ragadada da ita, ko kuma a sayar da ita ga masu sana’ar jima.

v  Akwai masu sayen Kai da Ƙafa. Ana dafa su a sayar.

Akwai muhimman kayan aikin da masu sanar fawa su ke amfani da su a garin Kazaure wajen gudanar da sana'ar su ta fawa kamar haka:

  1. Wuƙa: da ita ake yanka dukkan abin da ake da buƙatar yankawa tun daga ita kanta dabbar, zuwa feɗe ta, har zuwa yanka naman.
  2. Jantaɗi: Da shi ake wasa wuƙa ko gatari.
  3. Gatari: Ana sara ƙashi mai tauri da shi.
  4. Gungume: Shi ma ice ne mai kauri da ake ɗora ƙashi a kai a daddatsa shi.Daro: A cikinsa ake wanke nama, sannan kuma bayan an gasa naman kamar balangu sai a sake zuba shi a ciki.
  5. Tire: A cikinsa ake ɗora tsire ko kilishi.
  6. Takarda: Da ita ake naɗe naman.
  7. Leda: Ana zuba nama a cikinta.

 Ga hotunan wasu daga cikin abubuwan da masu sana'ar fawa na garin kazaure ke samarwa ta hanyar amfani da ruwan Dam ɗin Muhammadu Ayuba.

Nama

4.2.4 Sana'ar Ga-ruwa

 Sana'ar garuwa sana'a ce da ake amfani da Baro/Kura da Jarkoki wajen ɗibar ruwa daga bakin Dam ɗin Muhammadu Ayuba ana shiga da shi cikin lunguna da saƙuna na garin Kazaure. Domin samarwa da al'ummar garin Kazaure ruwan biyan buƙatun yau da kullum. Masu yin wannan sana'a suna ɗibar ruwa a dai-dai kofar unguwar ganguli, suna ajiye barukansu a bakin titi, yayin da ake amfani da injinan da aka ajiye a bakin Dam ɗin domin janyo ruwan Dam ɗin, ga masu sana'ar garuwa zuwa bakin titin kofar garin ganguli. Kasancewar akwai gangara mai tsawo daga bakin titin zuwa bakin Dam ɗin. Akwai mutanen da suka sayi injina da fayif-fayif mai tsawo suna janyo ruwan Dam ɗin suna ɗurawa masu sana'ar garuwa su kuma suna biyan kuɗi naira ashirin (20) a kowace baro ɗaya da aka cika, su kuma suna shiga cikin gari su na sayarwa.

 Akwai rijiyoyi da aka gina a bakin Dam ɗin waɗanda idan rani ya yi ruwan Dam ɗin ya ja baya, ana tsotso ruwa daga cikin rijiyoyin ana zubawa masu sana'ar garuwa suna biya, sannan su je su sayar. Masu wannan sana'a ba iya gidaje kawai suke sayarwa da ruwansu ba har da masu sana'ar Fawa suke kai wa mahauta da sauran waurare daban-daban, kama daga wuraren masu yin bulon ƙasa da na sumunti da sauran su. Wannan sana'a ba shakka tana ba da muhimmiyar gudummawa wajen gudanar da harkokin rayuwar al'ummar Kazaure, kuma tana ba da gudummawa wajen bunƙasa tattalin arzukin garin Kazaure.

 Masu yin wannan sana'a ba su da wata ƙungiya, amma suna zaune cikin salama, ma'ana babu hayaniya a tsakaninsu, suna ganin mutuncin junansu musamman waɗanda suka fi daɗewa a wajen.

4.2.5 Sana'ar Wanki.

Sana'ar wanki da guga sana'a ce da ake gudanarwa a bakin Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure, wajen wanke kayayyaki na tufafi da na kwalliyar cikin gida da abubuwan hawa da makamantansu. Masu gudanar da sana'ar wanki bakin Dam ɗin Muhammadu Ayuba suna da yawa, domin kalar wankin da ake yi a bakin Dam ɗin sun kasu kamar haka:

v  Akwai masu sana'ar wanki da guga: Waɗannan rukunin masu wanki ne da suke wankin kayan sawa, waɗanda suka haɗa da: Riga/Taguwa da wando da jamfa/babbar riga da zannuwa da mayafai shijabai gyaluluwa da labulaye da barguna da makamantansu.

v   Akwai masu sana'ar wankin motoci: Waɗannan rukunin masu wanki ne da suke wankin motoci manya da ƙanana.

v  Akwai masu sana'ar wankin Babura: Su kuma rukunin waɗannan mutanen suna wanke babura na hawa da makamantansu.

 Masu gudanar da wannan sana'a ta wanki a bakin Dam ɗin Muhammadu Ayuba, suna ba da muhimmiyar gudunmawa ga al'ummar kazaure wajen haɓakar tattalin arzukin garin Kazaure. Akwai mutane da dama a bakin Dam ɗin waɗanda suke yin wanki waɗanda yawan su zai kai adadin mutane saba'in da biyar (75), da sauran wasu na musanman kasancewar ba su da ƙungiya, ba za a iya tabbatar da iyaka yawansu ba.

4.2.6 Sana'ar Kiwo.

 Kiwo na ɗaya daga cikin sana’o’in ƙasar Hausa na dauri. Sanaa ce da ake gudanar da ita tun daga cikin gidaje har ya zuwa ruga da Fulani makiyaya kan yi. Babu wani gida da ba a kiwo a ƙasar Hausa (Alhassan, Musa, da Zarruƙ, 1982), sannan sana’a ce da ba gadonta ake yi ba (Zarruƙ, Kafin-Hausa, da Al-hassan, 1987). Akwai masu gudanar da kiwon dabbobi a garin Kazaure da makiyaya wato masu yawon kiwo zuwa waje-waje, suna amfani da ruwan Dam ɗin Muhammadu Ayuba wajen yi wa dabbobinsu barruwa da ruwan Dam ɗin. Akwai manoman da suke samarwa da waɗannan rukunin makiwatan ciyawu a bakin Dam ɗin, waɗanda suke sayar musu da sauran amfanin gonarsu, bayan sun gama ɗebe ƴaƴan su kuma masu kiwon su zuba dabbobinsu su cinye sauran amfanin da ke tsaye kamar ciyawar Attaruhu da tattasai da tumatur da ganyen dankali da karan masara da na dawa da makamantansu. Akwai kuma manoma da suke bin bakin iyakun gonakin noman da suke a Dam ɗin Muhammadu Ayuba suna yin kiwon dabbobinsu. Akwai masu zuwa gonakin daga cikin gari suna siyan ciyawa kamar ganyen dankali suna zuwa su ciyar da abubuwan da suke kiwo, kamar; Awaki da tumaki da shanu da sauransu.

 Waɗannan makiwatan suna yin kiwo a gonakin da ke yamma da gabas da arewacin Dam ɗin wajen ciyar da dabbobinsu abubuwan da suke buƙata idan sun gama kiwon suna yi musu barruwa da ruwan Dam ɗin. Kuma suna samarwa da al'ummar Kazaure dabbobin da suke buƙata kamar mahauta da sauran al'ummar gari, masu buƙatar dabbobin da za su yanka a wajaje kamar sallah babbah da ƙarama da bikin suna ko na aure ko na sauka da sauran su. Kuma suna ba da muhinmiyar gudummawa wajen haɓakar tattalin arzukin garin Kazaure.

4.3 TASIRIN AL'ADUN SIHIRI DA YA SHAFI DAM ƊIN MUHAMMADU AYUBA.

 Masana tarihin garin Kazaure da masu gudanar da sana'o'in gargajiya a bakin Dam ɗin Muhammadu Ayuba sun bayyana wasu daga cikin al'adun da ake aiwatarwa a ciki da wajen Dam ɗin da su ka haɗa da:

v  Akwai masana tarihin da suka tabbatar da cewa "Wasu lokutan musamman idan ruwan damuna ya shiga Dam ɗin ma'ana ya cika da sabon ruwa, a na samun wani ɓangare na ruwan Dam ɗin yana jujjuyawa a waje ɗaya kamar faɗin bakin rijiya". Mutane sukan taru su runƙa kallo suna cewa " Aljanu/Iskoki ne ke yin wasa da ruwan, amma yanzu bai cika faruwa ba amma masana sun tabbatar da yiwuwar hakan.

v  Akwai sihirin da Masunta ( kamun kifi) suke amfani da shi wajen shirya ƴaƴansu da kawunansu yayin farawa ko gudanar da wannan sana'a a cikin Dam ɗin Muhammadu Ayuba kamar haka: Wasu suna ɗinkawa ƴaƴansu guru ko guraye su ɗaura a ƙugu ko dantse, domin tsaron kai daga wasu haɗarurruka kamar yadda wani masunci mai suna Kaɗo dogon dare ya shaida yayin zantawa da shi. Ya ce "lokacin da za a fara zuwa da shi yin su cikin Dam ɗin baban shi ne ya ba shi gurun ya ce "duk sanda zai yi su ya ɗaura shi kafin ya shiga cikin ruwan Dam ɗin.

v   Akwai yara da suke gudanar da al'adar wasan iyo idan damuna ta kankama, suna zuwa kan gadar da ta ratsa Dam ɗin suna hawa suna faɗawa, ɗaya bayan ɗaya, sannan sai a duba wanda ya fi saurin iyo wajen fitowa wanda ya riga fitowa shi ake ba wa kyauta sai na biyu da na uku, ana gudanar da wannan wasan ne a wasu ranakun mako idan damuna ta yi nisa. Ga ire-iren Hotunan da aka ɗauka lokacin da yaran ke wasan iyon kafin yanzu da aka hana:

 

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure


v  Akwai manoman da suka bayyana cewa sukan yi wa gonakinsu wasu ƴan binne-binne yayin da suka shuka amfani, domin tsari daga maɓannatan dabbobi da makiyaya da ɓarayi, domin duk wanda ya shiga ya yi ɓanna ko sata da wuya ya fita daga gonar ba a kama shi ba".

4.4 CAMFE-CAMFEN DA SUKA SHAFI DAM ƊIN MUHAMMADU AYUBA.

Akwai camfe-camfen da ake yi dangane da Dam ɗin Muhammadu Ayuba, kamar yadda wasu mutane suka yarda kuma suke gudun aikatawa ko furtawa daga cikin camfe-camfen akwai masu cewa:

Ø  Akwai masu da'awar cewa duk ɗan sarkin da ya kuskura ya sake shiga cikin Dam ɗin na Muhammadu Ayuba da nufin yin wanka sai ya ci shi, ma'ana sai ya rasa ransa (ya mutu) suna yin wannan camfin ne sanadiyyar mutuwar ɗan sarki Ibrahim. Yayin da ya shiga wanka a shekarun da suka shuɗe bayan sun shiga wanka tare da sauran mutane.

Ø  Akwai makiyayan da suke cewa "Duk shekarar da dabbobin makiwaci suka fara shiga cikin gonakin bakin Dam ɗin Muhammadu Ayuba guda uku (3), su ka yi kiwo to duk yunwar da za a yi da rani, dabbobin shi ba za su kamu da yunwa ba".

Ø  Akwai masu camfin da suke cewa "Shiga cikin ruwa kamun kifi ka na cin gasasshe ko dafaffen kifi na kawo rashin sa'a wajen kamun kifaye a Dam ɗin", shugaban masu kamun kifi ne ya shaida wannan camfi duk da ya ce " wasu sun yarda da camfin, yayin da wasu kuma ba su yarda ba".

4.5 TASIRIN SANA'O'I, NA ZAMANI, DA SUKE A DAM ƊIN MUHAMMADU AYUBA.

 Masu fasahar baka kan ce "Zamani, mai yayi". Wasu kuma suka ce: "Zamani, abokin tafiya". haka kuma wasu suka ƙara da cewa: "Sarki goma, zamani goma". Babu shakka zuwan zamani ya yi tasiri a Dam ɗin Muhammadu Ayuba, dalili shi ne masu shirya finafinai suna zuwa wannan Dam ɗin, domin shirya harkokinsu na fim, yayin da dandazon al'umma sukan halarci Dam ɗin. Sana'ar fim sana'a ce wadda zamani ya kawo wadda ake amfani da na'urar zamani wajen ɗaukar hotuna da bidiyo kana daga baya a gyara a runƙa sayarwa jama'a suna saya suna gani domin nishaɗantarwa ko wa'azantarwa ko gargaɗi da sauransu. Akwai ire-iren masu harkar finafinai da ɗaukar hotuna da dama da suke halartar Dam ɗin kamar haka:

v  Akwai masu zuwa daga Kano suna ɗaukar finafinai a gefe da kuma kan Dam ɗin wasu daga kan gadar da ta ratsa ta kan Dam ɗin wadda ta haɗa cikin gari da kanti, da sauran su.

v  Akwai masu zuwa daga garuruwa da dama suna zuwa suna shirya harkokinsu na finafinai.

v  Akwai masu shirya finafinai waɗanda suke a cikin garin Kazaure suma suna zuwa suna shirya finafinai a Dam ɗin.

 Ga wasu daga cikin hotunan ire-iren masu ziyartar wannan Dam ɗin domin mai nazari ko masu nazari su ƙara samun haske:

 

Gudunmawar Dam Din Muhammadu Ayuba, Wajen Bunkasa Tattalin Arzuki Da Al'adun Garin Kazaure

4.6 NAƊEWA.

 A wannan babin an yi bayani dalla-dalla dangane da gundarin sakamakon da wannan bincike ya gano, yayin da aka kawo bayanai akan abubuwan da suke faruwa a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure, waɗanda ta sanadiyyar su tattalin arzukin garin Kazaure ke haɓaka. Waɗannan hanyoyin sun haɗa da; ta hanyar sana'o'in gargajiyar Bahaushe, kamar sana'ar Su (kamun kifi) da Noma da Kiwo, da sana'ar wanki da ga-ruwa da sauran makamantansu. Haka kuma an kawo al'adun da suka shafi sihiri da camfe-camfen da suka shafi Dam ɗin gami da tasirin sana'o'in zamani da suka shafi Dam ɗin. Daga ƙarshe kuma aka rufe babin da Kammalawa.

 

BABI NA BIYAR

KAMMALAWA

5.0 SHIMFIƊA

 Masu iya magana kan ce " Komin nisan dare, gari zai waye!". A wannan babi mai laƙabin babi na biyar, wato babin kammalawa wanda kuma shi ne babi na ƙarshe a wannan bincike. A nan ne aka kammala wannan bincike tare naɗe wannan bincike gaba ɗayansa. A wannan babi an yi ƙoƙari gami da jajircewa wajen taƙaita bayani a kan binciken tare da fito da bayanin sakamakon da binciken ya samo, sannan a bayar da shawarwari ga gwabnati da masu ruwa da tsaki da masu son nazari anan gaba. Yayin da a ƙarshe kuma an kammala aikin baki ɗaya.

5.1 TAƘAITAWA

 Wannan nazari ya gudana ne a bisa tsarin da kowane bincike na ilimi ke gudana wato babi-babi, a inda aka tsara binciken cikin babuka har guda biyar. A cikin babi na ɗaya, wannan bincike ya fara ne da gabatar da aiki, domin nuna alƙiɓlarsa, sannan aka yi bayani a kan muhimmai kuma ƙashin bayan kowane irin bincike na ilimi. Waɗannan muhimman abubuwa sun haɗa da; dalilan bincike da manufar bincike, gami da muhimmancin bincike, har da tambayoyin da binciken ya ke ɗauke da su, tare da iya farfajiyar da binciken zai gudana, gami da ma'anar muhimman kalmomin da suka haɗu suka ba da taken wannan bincike. Sannan aka yi jawabin kammalawa a ƙarahen babin.

 A babi na biyu kuwa, an yi bita a kan gabatattun ayyukan da magabata suka gabatar a cibiyoyin ilimi, mabambanta an yi hakan ne domin ganin wannan bincike ya samu madogara wato tudun dafawa. A cikin babi na biyun ne aka bayyana fahimtar magabata waɗanda aka binciko ayyukansu cikin litattafai da kundayen bincike da muƙalu da mujallu da sauran makamantansu. Sannan kuma an kawo su ne tare da bayanin kanun muhinman batutuwan da suka jiɓanci wannan bincike. Muhinman batutuwan da aka kawo a babi na biyun sun haɗa da; ma'anar al'ada da rabe-rabenta da sifofinta da muhimmancinta ga al'umma. Haka kuma an kawo taƙaitaccen tarihin garin Kazaure tare da taƙaitaccen tarihin Dam ɗin Muhammadu Ayuba, sannan aka kawo makamantan bincike, waɗanda su ke da alaƙa ta kai tsaye da wannan bincike, daga ƙarshe kuma aka rufe babin da kammalawa. A babi na uku bayan an gama gabatar da abin da babin ya ƙunsa, sai aka kawo hanyoyin da aka yi amfani da su wajen gudanar da wannan bincike, kama daga kan; lura/sa-ido da naɗar zantuka gami da ɗaukar hotuna. Sannan kuma an kawo hanyar amfani da matambayiya domin samun sahihan bayanai da tattaki da aka yi ƙafa da ƙafa zuwa wajen waɗanda binciken ya shafa, sannan aka rufe babin da kammalawa. A babi na huɗu kuwa wato wajen bayani dalla-dalla akan abin da binciken ya gudana, an kawo gudummawar Dam ɗin Muhammadu Ayuba ga al'ummar Kazaure, waɗanda suka faru ta hanyoyi da dama kamar; gudummawar Dam ɗin dangane da raya al'adun gargajiya na Bahaushe. Kama daga amfani da ruwan Dam ɗin wajen gudanar da sana'ar su (kamun-kifi).

 Haka kuma an kawo bayanin wajen gudanar da sana'ar noma da sana'ar Fawa, gami da sana'ar ga-ruwa, tare yin sana'ar wanki da kiwo. Aka kuma kawo bayani a kan tasirin al'adun sihiri da ya shafi Dam ɗin, da camfe-camfen da suka shafi Dam ɗin, har da tasirin zamani wajen gudanar da sana'o'i na zamani da su ka shafi Dam ɗin, a ƙarshe kuma an rufe babin da kammalawa. A cikin wannan babi na biyar kuma a nan ne aka bayyana sakamakon da binciken ya gano, gami da bayar da shawarwari waɗanda binciken ke kalkon sun dace a bi su, domin haɓaka harkokin ilimi da bincike gaba, musamman ga ma'abota binciken gami da ɗalibai. Daga ƙarshe kuma aka kamala aikin tare da kawo manazarta.

5.2 SAKAMAKON BINCIKE.

 Nagartattun masana da manazarta sun bayyana cewa " Al'ada ado ce abar alfahari da tinƙaho ga mai ita ko masu ita, har akan ga gazawar al'ummar da ba ta rike al'adunta na gargajiya ba. Hasalima ba kasafai al'umma take ci gaba ba, in har ta yi watsi ko ruƙon sakainar kashi da al'adunta na dauri ta rungumi baƙi. Saboda haka wannan bincike ya binciko tare da gano cewa, lallai sana'o'in gargajiya na Hausawa, suna da matuƙar tasiri da muhinmancin gaske ga rayuwar al'ummar Hausawa. Kuma sana'o'in suna samarwa da al'ummar Hausawa abubuwan biyan buƙatun kansu da na waninsu domin tafiyar da harkokin rayuwarsu ta yau da kullum abubuwan more rayuwa.

 Wannan bincike ya fito da wasu ɗaiɗaikun sana'o'in gargajiya na Hausawa waɗanda su ke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammafu Ayuba, waɗanda ta sanadiyyar su tattalin arzikin garin Kazaure ke haɓaka. Kuma binciken ya gano cewa yin hakan zai taimaka wajen sake tunasar da Hausawa irin sana'o'insu da kuma amfaninsu, waɗanda suka gada a gun iyaye da kakanni. Haka kuma binciken ya gano ashe akwai sana'o'in gargajiya na Hausawa waɗanda suke gudana a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba, sannan har wasu ƙananan sana'o'in na gargajiyar Hausawa da suke faruwa a cikin garin Kazaure aka bayyana kamar; sana'ar soya kifi ko dafa kifi ta dalilin samuwar masu sana'ar kamun kifi. Da samuwar masu tallar rogo dafaffe ko aunanne da sayar da masara dafaffiya ko aunanniya da dankali da kankana da gyaɗa da ƙursa da kuɓewa da yakuwa, da kayan miya irin su tumatur da albasa da tattasai da sauransu, duk ta sanadin samun sana'ar noma a bakin Dam ɗin. Haka kuma an samu damar gudanar da sana'ar abinci da yin sana'ar fawa da sayar da ƙosai da awara da doya, duk ta dalilin samuwar masu sana'ar ga-ruwa waɗanda suke ɗibar ruwa a Dam ɗin na Muhammadu Ayuba.

 A ƙarshe binciken ya gano cewa duk lokacin da aka samu sauyin yanayi ko rayuwa, musamman ma ta fusakar amfani da kayayyakin amfanin yau da kullum, al'umma kan himmatu wajen inganta kayansu na gargajiya, domin su tafi dai-dai da zamani. Wasu kuma kan yi watsi da nasu kayan, su rungimi baƙi. A wannan binciken kuma an gano wasu al'adun sihiri da camfe-camfen da suka shafi Dam ɗin garin Kazaure na Muhammadu Ayuba, waɗanda wasu mutane ke aikatawa ko gujewa wajen gudanar da harkokinsu na rayuwa a ciki da wajen Dam ɗin. A wannan binciken an gano cewa lallai zuwan zamani ya yi tasiri a jikin wannan Dam domin an samu masu sana'ar shirya finafinai na yin tattaki zuwa Dam ɗin domin inganta sana'arsu.

5.3 SHAWARWARI.

 Masu fasahar baka kan ce " Ba a rasa nono, a riga". Yayin da wasu kuma suka ce "Shawara ɗaukar ɗaki". Wasu suka ce "Mai shawara aikinsa ba ya ɓaci, sai dai asirinsa ba ya rufuwa babu shakka wannan batu haka yake, domin kuwa wannan bincike yana da tarin shawarwari waɗanda idan aka samu nasarar yin amfani da su, za a samu ci gaba wajen ciyar da harkokin ilimi gaba. Ba tare da yin karo da wasu matsaloli masu yawa ba.

Bayan haka binciken yana da shawarwari da suke da muhinmanci a kan yadda yakamata abi domin inganta sana'o'in gargajiya na Hausawa, musanman ma a cikin garin Kazaure. Saboda yana da kyau hukumomin kula da bunƙasa al'adun gargajiya na Hausawa, su ɗauki nauyin binciko ire-iren sana'o'in Hausawa na gargajiya a koya wa al'umma maza da mata manya da yara domin inganta tattalin arzuki, wajen samar da abubuwan biyan buƙatun yau da kullum. Musanman ma ganin cewar; wasu daga cikin Hausawan yanzu suna watsi ko ruƙon sakainar kashi da kyawawan al'adunsu na gargajiya.

 Haka kuma yana da kyau masu ruwa da tsaki na garin Kazaure su ba wa mahukunta shawarwarin da suka dace wajen kula da inganta masu gudanar da sana'o'in gargajiya a ciki da wajen Dam ɗin Muhammad Ayuba. Sannan ya kamata mahukunta da masu hannu da shuni su yi wa Dam ɗin yasa domin inganta shi da kawar da shi daga barazanar ƙafewa, domin gudun lalacewarsa kan iya janyo wa wasu al'umma asarar wajen yin sana'o'insu, wanda hakan kan iya janyo lalacewar tattalin arzukin garin Kazaure.

 Bayan haka wannan bincike ya na kira ga gwabnati da ƴan kasuwa da su ɗauki nauyin inganta irin waɗannan sana'o'in na gargajiyar Bahaushe da kuma ɗaukar nauyin adana yadda ake aiwatar da irin sana'o'in ta hanyar amfani da na'urorin zamani, ta yadda za a rinƙa sayar wa baƙi na nesa ko ƴan yawon buɗe idanu da masu sha'awa abubuwan da aka samar daga sana'o'in gargajiyar, domin ƙara samun kuɗin shiga. Sannan kuma za a ƙara samun abin kallo a gidajen Hausawa da wasu al'ummomin, wanda yin hakan zai ƙara sa Hausawa musanman yara da matasa su ƙara sanin ƙima da daraja da sana'o'insu na gargajiya suke da su, tare da irin kayayyakin da suke samarwa da hannunsu. Ma'ana yanda suke samar da abubuwan amfani ga al'umma.

 Hakan zai taimaka wajen kawar da hankalin al'ummar Hausawa wajen rungumar sana'o'in zamani da suke shigowa, waɗanda suke ƙoƙarin danne na gargajiyar Hausawa, haka kuma gwabnati yana da kyau ta ware wasu ranaku a duk shekara ko bayan wasu shekaru, wanda cikinsu za a runƙa nuna irin abubuwan da sana'o'in gargajiya na Hausawa ke samarwa. Haka kuma a buɗe sababbin gidajen kallo na kayayyakin da ake samu daga sana'o'in gargajiya na Hausawa domin jawo hankalin matasa da baƙi sosai, saboda su iya ganin halaye na musamman na al'adun ƙasar Hausa.

 Haka zalika yana da kyau gwabnati da masu hannu da shuni su ware wasu ranaku domin yin bukukuwan gargajiya na Hausawa, a gayyato gwanaye a fannoni daban-daban na sana'o'in Hausawa, domin nuna irin fasaharsu wajen bukukuwan sana'o'in gargajiya.

 Yin hakan zai taimaka wajen haɓakar sana'o'in gargajiya na Hausawa a faɗin Duniya, wanda hakan kan iya kasancewa ta hanyar ɗauƙar bidiyoyi da hotuna da bayar da kayayyakin kyauta ga baƙi na ƙasashen waje, tare da sayar musu da kayan cikin farashi mai sauƙi.

 5.4 NAƊEWA.

 Sanannen abu ne cewa, kowace al'umma tana da al'adunta, tun kafin haihuwar ɗan Adam da kuma bayan haihuwarsa, har da bayan mutuwarsa, akwai al'adun da ake gudanarwa, kamar yadda shehun malami (Bunza,2006) ya bayyana. Haka kuma nazari wani katafaren fanni ne bunƙasasshe mai muhinmanci ga rayuwar al'umma. Saboda ta hanyar nazari ne ake lalubo tare da gano muhinman abubuwa da dama, waɗanda ba don nazari ba ba za a fahimci amfaninsu ba, ko da an fahimta wasu an yi watsi da su. Wannan nazari ya gudana ne a ciki da wajen Dam ɗin Muhammadu Ayuba na garin Kazaure, domin lalubo ire-iren sana'o'in gargajiya na Hausawa, wanda ta dalilinsu tattalin arzukin garin Kazaure ke haɓaka.

 Hakan kan ƙara nusar da al'ummar garin Kazaure wajen himmatuwa da kula da wannan Dam ɗin domin sanin amfanin da yake da shi, ga rayuwarsu tare da sanar da waɗanda basu san amfaninshi da muhinmancinshi a garin Kazaure ba. Haka kuma a wannan babin an taƙaita abubuwan da wannan bincike ya ƙunsa tun daga farko har ƙarshe, an yi bayanin sakamakon da binciken ya zaƙulo, aka kuma bada shawarwari da ake ganin sun dace ta hanyar amfani da sakamakon da binciken ya gano, yayin da aƙarshe aka kammala wannan bincike, tare da ba wa ƴan baya giɓin ɗorawa daga inda wannan bincike ya tsaya idan buƙatar hakan ta taso.

 

MANAZARTA

Alhassan, H. da wasu, (1982). "Zaman Hausawa". Bugu na Biyu. Zaria:Northern

 Nigerian Publishing Company.

Aminu, L. A. (2006). "Tattalin arzukin Al'umma: Nazarin Sana'o'in da

Kasuwancin Hausawa". Algaita Journal of Current reserch, Bayero

 Uniɓersity Kano.

Aminu, M. (1991). "Tasirin Zuwan Turawa a kan Sana'o'in Gargajiya na Ƙasar

 Hausa". Kundin Digiri na ɗaya. Sashen Nazarin Harsunan Najeriya da

 Al'adu. Jami'ar Bayero Kano.

Bargery, G.P (1993). "Hausa-English Dictionary and English-Hausa

 Ɓoɓabulary": Ahmadu Bello Uniɓersity Zaria. Opp 973. (2015). "Tasirin

Al'adun Hausawa na Gargajiya A Ilorin". (unpublished M.A Thesis) Zaria:

 Department of Nigerian and African Languages and Cultures. Ahmadu

 Bello Uniɓersity.

Bunza, A. M. (2006). "Gadon Feɗe Al'ada". Lagos; Tiwel Nigerian Limited.

Bunza, D. B. (2004) "Noma da Yadda ake Gudanar da Shi". Kundin Digiri na

 ɗaya. Sashen Nazarin Harsunan Najeriya da Al'adu. Jami'ar Usmanu

 Ɗanfodiyo Sakkwato.

Dokaji, A. (1958). "Kano Ta Dabo Ci gari". NNPC, Zaria.

Durumin Iya, M. A. (2006). "Tasirin Kimiyya da Ƙare-ƙaren Zamani a kan

 Sana'o'in Hausawa na Gargajiya". KABS Printing Serɓices (Nig),

 Durumin iya, Kano, Nigeria.

Furniss, G. (1996). "Prose Poetry and Popular Culture". SOAS. International

 African Library.

Galadanchi, M.M da wasu, (1992). "Hausa Don Ƙananan Makarantun

            Sakandare". Littafi na Biyu, Ibadan: Longman Nigerian PLC.

Garba, C. Y. (1991). "Sana'o'in Gargajiya A ƙasar Hausa". Baraka Press and

 Publishers Limited Kaduna.

Hassan, A. (1988). "Matsayin Sana'o'in Gargajiya Wajen Bunƙasa tattalin arzukin

 Najeriya". Kundin Digiri na ɗaya. Sashen Nazarin Harsunan Najeriya da

 Al'adu. Jami'ar Bayero Kano.

Ibrahim, U. (2012). "Haye a Sana'o'in Hausawa na Gargajiya". Language,

 Literaturr and Culture, Festschrift In Hornour of Professor Abdulhamid

 Abubakar. Department of Language and Linguistics; Uniɓersity of

Maiduguri.

Idi, A. (1972). "Bukukuwan Al'adun Gargajiya A Ƙasar Kano da Sakkwato".

 Kundin Digiri na ɗaya. Sashen Nazarin Harsunan Najeriya da Al'adu.

 Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

Kim, U. (2001)."Culture Science and Indigenous, Psychologist Intergrated

            Analysis in the Matsumoto(ed). Hand book of Culture and psychology".

 Oɗford: Oɗford Uniɓersity Press.

Kroecher, A. L. Kluckhohn, C. (1952). "Culture: A Critical Reɓiew of Concept

 and Definition". Cambridge. M. A. Read body Measum.

Maɗauci, da wasu (1968). "Hausa Customs". NNPC. Zaria: Opp 50-63.

Madauci, I. (1963). "Al'adun Hausawa". Northern Nigerian Publication Company

 (NNPC) Zaria.

 Muahmmad, M. S. (2019). "Sana'a Sa'a". Gado Da Masu Communication. No 51

 Ƙaraye Road, Kasuwar sati, Badarawa Kaduna.

Muhammad, K. K. (1981). "Sana'ar Ƙwarya A Ƙasar Hausa". Kundin Digiri na

 ɗaya. Sashen Nazarin Harsunan Najeriya da Al'adu. Jami'ar Bayero Kano.

Nasidi, Y. & Bello, S. (1991). "Culture Economy & Natural Deɓelopment".

 National Council For Arts & Culture. Lagos.

Oneil, D. (2006). "Cultural Anthropology Introrials". Behaɓioral Science

 Department, palornor colleges. San Marco. California, Retrieɓed.

Rimmer, E. M. da wasu, (1948). "Zaman Mutum da Sana'arsa". Zaria; Northern

 Nigeria Ltd.

Sallau, B.A. (2012). "Matsayin Sana'o'in Hausa Jiya Da Yau". Ƙalubale Ga

 Mazajen Zamani: Companion of Hausa cikin Hausa: A Festschrift in

 Honour of Ɗalhatu Muhammad: Zaria. Ahmadu Bello Uniɓersity, press.

Sani, D. (1986). "Sassaƙa A Ƙasar Hausa". Kundin Digiri na ɗaya. Sashen

 Nazarin Harsunan Najeriya da Al'adu. Jami'ar Bayero Kano.

Sulaiman. A. H. (1993). "Faɗaɗawar Sana'o'in Gargajiya A Zamanance". Kundin

 Digiri na ɗaya. Sashen Nazarin Harsunan Najeriya da Al'adu. Jami'ar

 Bayero Kano.

Ubali, M. L. (2021). "Tsakure Cikin Al'adun Hausawa da Adabin Gargajiya".

            Kano: Gidan Dabino Publiahers.

Umar, M. B. (1980). "Dangantakar Adabi da Al'adun Gagajiya". Zaria: Hausa

 Publication Centre Mangwaro Babajo.

Yunusa, Y. (1977). "Hausa A Duƙule". Zaria: Kamfanin Buga Litattafai na

 Arewa.

Yusuf, S. (2017). "Al'adun Hawan Sallah A Masarautar Kazaure". Kundin Digiri

            na ɗaya. Sashen Nazarin Harsunan Najeriya da Al'adu. Jami'ar Sule

 Lamiɗo; Kafin Hausa.

www.amsoshi.com

www.rumbumilimi.com.ng

www.academiɗ.ng

www.degeljounal.org

 

 

RATAYE NA ƊAYA (1)

MUTANEN DA AKA TATTAUNA DA SU.

 

Kazaure, Y. M. (2022). Hira da " Dr. Sadisu Mustapha Yaro". Masanin tarihin

 ƙasar Kazaure da kewaye". Ɗan shekara (50). Ranar 07/04/2022.

Kazaure, Y. M. (2022). Hira da "Rabi'u Mai Nasara". Marubucin Littafin;

 Tarihin Masarautar Kazaure daga 1770 Zuwa 2018. Ɗan shekara

 (52). Ranar 11/04/2022.

Kazaure, Y. M. (2022). Hira da "Auduwa Ibrahim, Sarkin Fawa". Ɗan shekara

 (55). Ranar 03/05/2022.

Kazaure, Y. M. (2022). Hira da " Mustapha Ɗan Leko, Sarkin Noma". Ɗan

 shekara (55). Ranar 19/05/2022.

Kazaure, Y. M. (2022). Hira da " Lawan Yahaya Ɗan Jawo". Shugaban masu

 Kamun Kifi a Dam ɗin Muhammadu Ayuba. Ɗan shekara (50).

 Ranar 04/06/2022.

Kazaure, Y. M. (2022). Hira da "Hassan M. Yusuf, mai Ba da Umarni a

 masana'antar Finafinai ta Kazaure". Ɗan shekara (33). Ranar

 23/06/2022.

Kazaure, Y. M. (2022). Hira da "Abubakar Nasiru, mai wanki da guga". Ɗan

  shekara (40). Ranar 25/06/2022.

Kazaure, Y. M. (2022). Hira da " Yahaya Ɗan Ga-ruwa". Ɗan shekara (40). Ranar 28/06/2022.

Post a Comment

0 Comments