Ko Da So… (Kashi na Ashirin da Biyar – 25)

Kamar wasa son uncle Mukhtar ya kama zuciyar Hafsah amma ta kasa ganewa. In tana zaune shi kadai take tunani. In ta na bacci mafarkan hirar su kawai take. Son shi ya ma ta kamun da ba za ta iy guduwa ba.

A karo na farko da ta aminta da cewar tana son burge shi ya sa yau ta ji tana so tayi kwalliya don ya yaba. Ya saba yaba yanayin fahimtar ta kuma hakan yana sanyaya mata zuciyarta. Yau so take yi ya yaba da kwalliyarta.

Hoda ta dauko ta shafa a fuskarta sannan ta nemi lipstick ta shafa. ba ta so tayi wata kwalliya me hayaniya ba kuma taso yau din ta fito yadda ta saba.

Ta kalli yatsunta ta ji tana sha’awar tayi musu lalle ko dan ya ce tayi kyau.

Tashi tayi ta debo littafan ta sannan ta bar dakin. Ko da ta fito ba kowa a falo hakan yasq ta nufi wurin fulawowin ta ajiye littafan ta sannan ta koma ciki don dauko madaidaiciyar carpet din da take shimfida musu. Ta duba ko ina ba ta ganta ba sai ta nufi dakin mummy. A hankali ta murda handle din taga mummy bacci take.

Sadaf sadaf ta shiga ta fara neman ta amma ba ta ganta ba.

“Me kike nema a nan duk kin hana ni bacci.” Ta tsinci muryar mummy kamar daga sama. Har fa minshari ta ji mummyn tana yi ya akayi ta ji motsinta.

“Mummy carpet din lesson din mu.” Ta fadi fuskarta ba yabo ba fallasa sai dai haka kawai ta ji wani nervousness yana lullube ta, ta fara wasa da yatsunta ganin yadda mummyn take kallonta.

Mummy ta mike zaune sannan ta daga labulen gefenta tana kurawa Fuskar Hafsah ido wadda tana gani tasan yau anyi mata kwaskwarima.

Mummy tayi kwafa ciki ciki sannan ta daga girarta. “Carpet din soyayya dai ko?”

Hafsah ta zaro ido. “Mummy…”

“Rufe min baki a nan! Wato kun mayar dani shashasha ke da babanki ko. Ya ce za a dakatar da lesson din amma cigaba ma kukayi ko? Toh daga yau na soke wani abu waishi lesson.”

Hafsah ta yarfa hannu. “Mummy carryover fa?”

Mummy ta danyi wata dariya da ba ta da alaka da nishadi sai dai ta nunawa Hafsah cewa ba ta isa ba. “ta zama spill over ma. Fice min a daki!”

Hafsah ta tsaya a wajen da take kamar an dasa ta. Ta kasa gane fushin mummy na menene da kuma dalilin da za ta ce ta soke lesson dinsu. Ita fa ba son shi take yi irin son soyyaya ba kawai tana son shi ne saboda yana da kirki kuma yana birge ta. Ta rasa abun cewa amma ta sani a zuciyarta cewa ba za ta fita daga dakin ba har sai ta fahimci wani abu.

“Mummy me nayi?”

Mummyn tayi tafi. “Tambaya ta ma kike yi me kikayi ko Hafsah?”

Hafsah ba ta gane ba. “Toh shi uncle Mukhtar din me yayi?” Ta tambaya tana ware idanuwa akan mummy wadda shock ma ya sa ta kasa magana.

“Mu…”

“Kinga fice min a daki kuma wallahi kar na ji labarin ya shigo min cikin gida. Ba ma wannan ba…” sai mummyn ta mike da sauri ta bude drawer kusa da ita ta dauko wani mayafi ta yafa. Ta ja hannun Hafsah ta kaita dakinta sannan ta janyo kofar tana huci.

Kai tsaye ta tafi gate ta sami me gadi. Ya russina ya gaisheta. “Wannan yaron, kar ka sake barinsa ya shigo min gida. Duk yadda zakayi, kayi amma kar nuna umarni ne daga mutanen gidam.”

“Toh Hajiya in sha Allahu. Allah ya kara girma.” Ya fada yana jaddadawa har sai da mummy ta bar wurin.

Ta wuce ta inda Hafsah ta ajiye littafanta. Ta kallesu tayi tsaki sannan ta shige cikin gida.

***

Wasa wasa zazzabi ya kwantar da Mukhtar don tun da ya dawo daga aiki ranar juma’a ba inda ya sake fita. Kwance yake a kasan bargo yana jin yau da dama dama kamar zai iya fita. Ko kadan baya son yaki zuwa koyawa Hafsah karatun ta na yau.

Ya mike zaune yana ta gumi, kanshi yana ta sarawa kamar zai tsage gida biyu. Ya dafe kan nashi da hannu bibbiyu sannan ya koma yq kwanta.

Kwanaki shida ya ke yi kafin ya saka Hafsah a iso yaji wannan karan sun masa nisa. Yau din cike yake da kewarta gashi zazzabi yaki barin jikinsa. Ji yake kamar in ya tashi ya watsa ruwa zaiji dama dama ya leka. Ko bai samu nasarar yi mata karatu ba ya dai ganta ko dan zuciya da ruhinsa zasu samu nutsuwa. Domin a yanzu ko

ina ciwo yake masa.

Ya sake yunkurawa zai tashi. Inna ta daga labule ta shigo sannan ta yi sallama wadda da kyar ya amsa, hakan yana kara tabbatar masa da cewar ba zai iya fitar ba.

“Kaqi ka sha magani. Shi zazzabin nan naci ne dashi.” Innar ta fada tana mika masa kwanon hannunta. Ya leka yaga wani koren ruwa yaji kamar ya ture amma ganin yadda Inna take ta fama ya sa ya kafa kai ya sha kadan ya mika mata.

“Sannu.” Da kai ya amsa mata sannan ya koma luu ya kwanta jikinsa sam babu kwari. Innar ta kalle shi cile da tausayinsa sannan ta tashi ta fita tana jinjina irin kamun da zazzabin ya masa.

Ko da Inna ta fita, bacci ne ya dauke shi har lokacin zazzabin sam bai bar jikinsa ba. Kwana uku yana yawo da shi a jikinsa don kan shi ciwo yayi tayi a satin sai ya dauka kawai pressure aiki ne da hayaniyar yara. Ko panadol bai sha wa ciwon kan ba shiyasa zazzabin yayi masa mugun kamu har ya kwantar da shi.

Inna ta leko ta gan shi yana bacci. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta koma gaban wuta tana dama masa kunu da zai sha in ya tashi. Ta lura ba iya zazzabin bane yake damunsa. Akwai wani abu da yake boye mata. Ko an kore shi ne ba ta sani ba tun da gashi tun ranar Jumu’a ya kwanta, yau lahadi amma jiki yayi tsamari.

Sauki kawai take so yaji ta ga me yake damunsa a zuciya. Hakan ya sa ta fita wajen abokinsa me kemis ya zo bayan magariba ya ba shi magani da allura.

***

Kallon question paper din dake hannunta Hafsah tayi sannan ta soma amsa test din. Allah yaso tayi karatu irin yadda uncle Mukhtar ya koya mata. Ya gaya mata tun kafin a sanya lokacin test za ta dinga bin courses din tana karantawa don in lokaci yayi revision kawai zatayi.

Jiki ba kwari ta gama test din duk da ta iya komai amma ba ta ji wani farin ciki ba. Ko da ta fito ba ta tsaya jiran kowa ba ko direba ba ta kira ba ta hau bus. Har suka isa old site tana zaune tayi jigum abun tausayi.

Tsakanin jiya da yau yanayin ta ya chanja akan rashin ganin uncle Mukhtar kuma jin cewa bai zo ba jiya sam ya kara saka ta a damuwa. Ga mummy da gaba daya yau ko gaisuwarta ba ta amsa ba har sai da tayi ta naci sannan ta ce mata ta dawo lafiya.

Adaidaita sahu ta hau ta fada masa address din makarantar. In ba ta je ba, ba za ta iya bacci ba. Kawai so take ta ji ko lafiya lau yake har ma yaki zuwa jiya.

Tana isa ta ciro kudi ta sallami me adidaitar wanda ko chanji ba ta karba ba tayi cikin school din. Kujerar su ta je taga baya nan. Ta kalli time taga one ma ba ta yi ba. Watakila yana class ta ayyana a ranta sannan ta shiga staff room tana gaida malaman da ta tarar.

Sama sama ta ji ana cewa baida lafiya.

“Kuma gashi ba ni da wata number din shi bayan wannan balle mu tambayi address dinsa. He really looks sick.” Uncle Mas’ud ya fada wanda shi yafi kusanci da shi. Dayar malamar ta girgiza kanta.

“Allah sarki. Allah ya ba shi lafiya.”

Hafsah tana jin haka ta matsa kusa da fara’arta ta karfin hali ta tambaya.

“Uncle Mukhtar ne ba lafiya wallahi. ya zo da safe amma sai sick leave principal ya bashi.”

Taji kamar ba gaske ba. Hafsah ta sake kallonsa taga dai maganar da ya fada bai wai gizo ko mafarki take yi ba. Take ta ji kafafuwanta sunyi mata nauyi.

Da kyar tayi musu sallama ta tafi. Tana isa dakinta itama zazzabin ya rufe ta. Taja bargo tana rawar dari hawaye masu zafi suna zuba daga idanta. Allah sarki uncle Mukhtar. Ashe bai da lafiya. Ko waye zai kula dashi? Ko waye zai ce masa sannu?

Tunaninsa kala kala ya cika mata kai. ba ta ankara ba itama zazzabi mai zafi ya rufe ta. Dukkan sassan jikinta ya dauki zafi da ciwon kewar uncle Mukhtar.

**

Ko da ya koma gida allurar aka sake mishi hakan ya sa yaji dama dama. Sune zaune a tsakar gida shi da Inna ta gyara zama. “Ince dai komai lafiya a wajen aikin?”

Mukhtar ya matsar da kwanon abincin da ko rabi bai ci ba ya ce, “lafiya lau inna. Sun ma ce na huta na kwana biyu sannan na dawo.”

Ta kalle shi ta ji alamar ba karya yake mata ba. “Toh Allah ya kara sauki.”

Mukhtar ya amsa da ameen sannan ya mike ya tafi dakinsa. Ya kwanta yana jin wani irin sanyi da emptiness yana eloping dinsa. Zazzabin ya sauka.

Jikin da sauki. Amma zuciyarsa da ruhinsa cikw suke da ciwo. Ciwon so. Ko shakka baya yi.

Son ta yake yi. Kuma son ya mishi wata iriyar damka. Ko kadan zuciyarsa ba ta mishi adalci ba. Ko kadan bayajin zai iya jarumtar cinye wannan yakin da zuciyarsa ta ballo masa. Ya juya, sai yaji kamar muryar Hafsah a kunnensa.

“Uncle Mukhtar, ina kewarka.” Ya san ba gaskiya bane. Ya furta a hankali.

“Zuciya da ruhi suna kukan rashin jinki Hafsah.” Ya furta.

Juwairiyya ta zaro ido cike da tsoro sannan ta karasa inda yake ta kwallawa Inna kira.

“Wallahi sambatu yake yi. Innalillahi, Inna cewa fa nayi Yaya Mukhtar ya jiki amma yake kirana da Hafsah… mun shiga uku! Allah ya sa ba aljanu bane.”

Inna ta ja ta tsaya, tabbas ta san akwai wani abu a kasa. Zuciyarta ta yi missing beat. Maimakon ta shiga dakin sai taja da baya ta koma tana alhinin wannan jarabawa da ta kama Mukhtar.

Tasan ba zazzabi ne kawai ba.

Ciwon so ya kama shi!

**

Rubutawa

Aeshakhabir

Fadimafayau

Soyayya
Credit: LuckyTD

Post a Comment

0 Comments