“Sabbin kaya za su iso nan da sati daya saboda haka ya kamata muyi clearance sales don mu rabu da tsofaffin.” Hajiya Hadiza, mahaifiyar Hafsah ta gayawa me kula da boutique din nata.
Matashiyar ta amsa. Sannan ta dora da, “how many percent off, ma?”
Hajiya Hadiza
ta danyi shiru tana ajiye biron hannunta. “Zan yi lissafi.”
Da haka ta ci
gaba da dudduba kayan tana jotting din abun da ya kusa karewa da abun da ya fi
yawa. Taku take daidai tana jin dadin nasarar da ta samu a kan kasuwancin nata.
Duk abun da ta saka a gaba ba ta kyale shi sai ta cimma nasara.
Kiran waya ne
ya katse mata tunani ya sa ta dubi wayar sannan ta tabe baki kafin ta dauka.
“Lafiya, ina
boutique ne. Toh shike nan.” Ta fadi sannan ta kashe wayar ta jefa ta cikin
jaka. Abun da aka fada ya sa ta juya za ta tafi don anyi mata ba zata. Matar
uncle din Hafsah ce ta haihu shi ne maman Hidaya ta kira ta fada mata suje
barka anjima.
“Wani abu ya
taso min. Zan shigo da safe.” Ta fadawa Saratu sannan ta fice tana nufar motar
ta tare da tunanin wacce irin shiga zatayi. ba ta son shigar da za ta jawo mata
raini.
**
Babban gida ne
sosai da ban garori da dama. Ko da mummy ta faka motar ta a harabar gidan sai
da ta tsaya tana tunanin ko ta yi kyau ko batayi ba. Karshe dai ta hakura ta
cire mukullin sannan ta fito. Kofar ban garen Amina me jegon ta yi tana taku a
hankali. Tana budewa sanyin kamshin turaren wuta ya bugi hancinta.
Ta kalli
corridor din da za ta kaita main parlor din taga yadda aka yi masa ado da
frames kala kala. Ga runner carpet nan har karshe. Ta cire takalmin ta ta saka
a rack din da aka ajiye a wurin.
Sama sama take
jin hirar su har ta karasa da sallamar ta. Cike da takama da nuna ita ma ta isa
ta samu wajen zama sannan suka fara gaisawa da mutanen wurin. Dukkan su dai
facaloli ne.
Maman Hidaya
ta kalle ta ta murmusa. “Hadiza leshin ki ya yi kyau wallahi.” Kanta ya
kumbura, amma sai ta basar kamar ba wani abu ne mai muhimmanci ba ta ce,
“Kuma kawai na
siya ne randomly saboda shan iska.”
Ta kyalla ta
kalli leshin jikin Amina taga babba ne sama da nata. Haushi ya cika ta wato ita
Amina za ta nunawa sutura. Ai kuwa dai babu abun da mijinta ya fi nata.
“Yayi kyau
kuwa.” Aminar ta fada itama tana yabawa. Hajiya Hadiza ta yi yake tana ganin
kamar magana kawai Aminar take so ta yaba mata.
Ta dan kau da
kai sannan ta ce, “ina babyn?”
“Yara sun
dauka. Ai ita kam wannan yayyin ta sune iyayenta.” Suka kwashe da dariya.
Maman Hidaya ta
ce, “toh abunka da kalan hanji.” Aka sake yin dariya. Amina ta maze duk da ba
ta dauka da komai ba. Tun da ta samu cikin ake nata tsiya kala kala wai ta
tsufa. Da farko ma taso ta cire likitan ya ce mata babu wani risks sosai.
“Daga ita na
kulle dai balle a samu nayi.” Ta fadi sannan suka shiga wata hirar daban.
***
Ganin a kwana
biyu Bilkisu tana ta boye matsalar da take ciki ya saka Hafsah yanke shawarar
take gidansu. Ko da ta shirya za ta tafi mummy ba ta ce komai ba hakan ya sa ta
ji dadi ta kama gabanta.
A dukkan
tsananin mummy ba ta takura mata idan wajen Hidaya za ta je ko wajen Bilkisu.
Ta yarda dasu da mu’amalar su da Hafsah din.
Tana isa gidan
ta yi sa’a ba ta tarar da kowa ba ta wuce dakin Bilkisu. A kwance ta same ta ta
kurawa sama ido hawaye nata fita daga idanunta a gefe kuma wayar ta tana ta
ringing.
Hafsah ta yi
sallama sannan ta zauna gefen ta ta daga wayar taga Tariq ne.
“Ki barshi
kawai.”
Bilkisun ta
fada tana tura bakin haushin sa da ta kasa boyewa. Hafsah kuwa daukar wayar
kawai ta yi ta ce masa ya zo yanzu. Tana sauke wayar, Bilkisu ta kalle ta ta
fashe da kuka.
Muryarta na karyewa
ta shiga bawa Hafsah labarin yadda sukayi. Ko da ta gama maimakon ta ji Hafsah
ta fara rarrashinta, dariya ta mata.
“Ke yanzu abun
da kike wa kuka ke nan?”
Bilkisu ta
juya. “Kema ba carryover kika gama yiwa zazzabi ba.”
“Bakiga yadda
ta yi mishi bane and he didn’t stop her.”
Hafsah ta ce,
“yo ke babu class ma sam a lamarin ki. Nice ke ta ruwan sanyi zan rama. Amma
duk ba wannan ba gaskiya Tariq bai kyauta ba.”
Bilkisun ta
gyada kai. “Toh kin gani. Yanzu ya zan yi.”
Hafsah ta yi
shiru sannan ta yi tafi. “Ina da wani tsari amma gaskiya sai kin goge hawayen
nan. Kuma ji be ki. Je ki yi wanka mu shiga kitchen.” Kamar mutum me rimot haka
ta tashi ta fada wanka, ba ta jima ba ta fito.
Sai da ta
daura robe a jikinta sannan Hafsah ta ce, “zabo kaya kala biyu muje mu tambayi
Ya Iftee wannan ya fi dacewa ki saka.” Bilkisu ta kalle ta alamun ba ta amince
da plan din ba.
Hafsah ta
tashi da kanta ta nemo kayan sannan taja ta har dakin Ya Iftee. Sukai sa’a tana
zaune tana zana jagira da alama fita zatayi.
“Hi Ya Iftee!
Dama Tariq ne zai zo shi ne muke so ki taya mu zaban kayan da ya fi kyau.”
Hafsah ta daga mata kayan. Tana kallo Ya Iftee ta ba ta rai amma ta basar.
“Eh Ya Iftee.
Wanne zan sa? ya ce na mishi kwalliya.” Ta sake tabe baki tana tunanin yadda
zatayi.
“Ke yanzu
saurayin kike wa wannan rawar jikin?” Ta tambaya tana yatsina fuskarta saboda
ta kasa boye bacin ranta.
Hafsah ta yi
kwafa ciki ciki. Kamar Bilkisun ba zatayi magana ba ta ce, “Ni ba komai bane a
wajena. We love each other so much.”
Hafsah ta ji dadin
amsar ta ce ita suke jira ta yi musu zabi. Tsabar takaici ma ya sa ta kasa
magana har sai da suka gaji suka bar dakin. Suna fita ta yi wurgi da jagirar
tana tsaki me cin rai. Ta tashi bazar bazar ta nufi bandaki inda zatayi ihu ba
tare da an jiyo ta ba.
Ko da suka
koma daki, ajiye kayan sukayi sannan suka tafa. “Kinga fuskarta kuwa?”
Hafsah ta ce,
“ai haka akeyi daman. Ke in kika zauna ranki ne zai baci.” Suka dara sannan
suka tafi kitchen.
Meatpie kawai
sukayi sai zobo da suka dafa. Sanda Bilkisu ta gama kwalliya sannan Tariq ya
iso.
Tare suka fito
fuskarta dauke da fara’ar da Hafsah ta ce mata ta makala. Suka zauna sannan
suka gaishe shi.
“Kawarki ta
guje ni. Na rasa dalili.”
Hafsah ta
kalli Bilkisu alamun ba ta san komai ba. “She didn’t say a word.”
Da mamaki ya
kalli Bilkisu. “Babu komai kawai wayar ce kwana biyu bana taba ta. We’re good.
Na zuba ma lemo?” Ta tambaya fuskarta cike da murmushin gaske. Har mamaki take
yadda ma ta sake da shi har haka ta ji haushin nasa yana ba cewa.
Ya kalli lemon.
“Kuma ba poison a ciki?”
Hafsah ta yi
dariya. “In ma akwai sai dai poison din love ta saka ma.” Ya kalli Hafsah sai
kuma ya dauke kai da sauri yana kallon Bilkisu.
Ta zuba masa
lemon ta mika shi kuma ya kalli zobon da aka ajiye ya ce shi zai sha. Ta zuba
masa tana kallonsa. Da kyar ya sha duk da dadin da ya masa.
“Wallahi babu
wani abu tsakanina da Iftee.” Ya fada. Hafsah ta yi wani boyayyen murmushi.
Bilkisu ta
girgiza kai. “Yayata ce fa. Me ya kawo zancen ta? Nace ma wani abu ne?”
Ya jijjiga
kai. Hafsah ta saci kallonsa taga duk ya rasa yadda zai yi sai ta mike ta ce,
“Dama fita za
muyi. Na baku aron minti biyar..” da haka ta bar wajen sannan ta koma cikin
gidan ta nemo wayarta.
Ko da ta dauko
tunowa ta yi ashe ba ta da number din uncle Mukhtar. A lokacin ji ta yi kamar
ta kira Abba ta tambaye shi ya bata.
Zama kawai ta
yi tana tuno yadda yake kallonta. Lokaci yana cika ta koma ta hango su suna
dariya. Har ranta ta ji dadin yadda suka dinke. Hakan ya sa ta sulale ta bar
gidan cike da farin cikin ganin Bilkisu a farin ciki.
Sai bayan
sallahr isha Bilkisu ta kira ta mata godiya. Cike da jin dadi ta mata fatan
alheri. Har ta kwanta bacci ta tuna da assignment dinta duk da ta yi.
Daukowa ta yi
ta sake dubawa ta gani ko ya yi. Ta mayar ta koma ta kwanta amma ta ji kewa ta
cikata. Ko baccin ma ya gudu.
Tashi ta yi ta
fita tsakar gida inda suka zauna. Ta zauna a wurin ta daga kanta sama tana
kallon taurari tana murmushi.
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.