Jiki ba kwari Hafsa ta bi shi da kallo lokacin da ya bar ajin,idanunta ta mai da kan takardar da sunayen masu neman aikin ke kai Muktar ta kuma mai-maitamana, murmushi ta yi kafin ta ja biro jikin sunan nasa kamar yadda ta yiwa matashiyar matar ɗazu alamar ya ci interview ɗin.
Ahankali ta miƙe tana
duba agogo kafin ta miƙawa Malamin da suke interview ɗin
tare, wanda ke kusa da ita bari in je gun Abba, karɓa kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, ba ta
damu da rashin maganar tasa ba ta bar ofishin.
Har ta wuce ta
dawo, fuskar ta ɗauke
da murmushi "lah Anti ina kwana?" ta faɗa
cikin har shen turanci matar ma murmushi ta mayar mata, "kya ce ina kwana
mana, anya Hafsa? a ce tun da kukai candy ko a ɗan
leƙowa
a gaisa," matar ta mayar cikin turanci.
"Kai Anti
wallahi abububuwa sukai yawa, kuma gani na na yi in nazo ai duk kuna aji zan ɗauke muku hankali, anma ai
ina cewa Abba ya gaisar mun da ku."
"Eh fa ya
na faɗe wataran, bari
in je sauri nake Hafsa ta faɗa"
" nima
kin ga aji zan shiga" matar ta fada kafin ta yi gaba.
Abba na zaune
yana duba takardu Hafsa ta shigo da Sallamar ta, ɗagowa
ya yi yana kallon ta kafin ya ce "to sarkin rikici badai nufin ki anan
zaki zauna ba?," girgizar kai ta yi a'a tafiya ma zan yanzun nan naga an
mana fixing class 2-4 gwanda in je.
"Towo
class kuma gashi ni yanzu ina som mu tattaunawa da team ɗin da sukai interview ɗin, dan mu samu mu a turawa waɗan da suka samu nasara
sakon kar ta kwana zuwa gobe su fara zuwa, musanman wanda zai ɗauki Physics ɗin nan."
"Tom
shike nan kawai ba ni kuɗin
ɗan sahu da na ƙara
masa 200 a kan normal price zai kaini, dan innace sai driver ya zo kaini zan
makara."
Dubu Uku Abba
muƙo
mata "Allah ya bada sa'a," murmushi ta yi "Amin sunma yi yawa
ai, Allah ya saka da alkairi" ta faɗa
kafin ta wuce.
A nitse Muktar
yake tafiya tun da ya baro ɗakin
gwajin ya kasa tunanin hukuncin da mutanen za su yanke tsaf ya tsaya dan naƙaltar
su sai dai fuskokinsu ba su nuna sun yi maraba ko akasin haka da jawabin da ya
gudanar ba, duda cewa shi a ransa yana jin kwarin gwiwar ya yi abin da ya da ce
ko da bai samu Malamin senior ba to su ɗauke
shi a matsayin malamin primary.
Har ya wuce
mai lemon ya dawo soyayyar Umman sa da lemo mai ɓawo
ya san ya bazai iya ganin lemo ya wuce bai sai mata ba, Ɗari biyun sa ke nan,
"na ɗari za a
bani" ya faɗa a
takaice, Baba Yakubu ne ya yi miƙo masa bakar ledar kai dai Muntari kana
son siyan lemon ɗari
naga randa za ka sai na du ɗari
biyun.
Dariya Muktar
ya yi, " adai ci gaba da tayamu da addu'a wataran na dubu zan siya,"
Allah dai ya sa ai nima zan so haka.
A kishin giɗe Innan take tana jin
radiyo ganin shigowar Muktar ya sata gyara zama, yanayin fuskar ta ya nuna ɗoƙi da son jin labari mai
daɗi na an ɗauke shi aikin, ajiyar
zuciya ya yi kafin ya zauna kusa da ita ledar lemon ya miƙo mata
kafun ya ce "wanne shirin suke?"
"Kaji dai
shirin Muda likita nake son ji, ta yau ‘yan siyasa sun siye filin shi ne nake
saurara, ya aikin kuma fatan an dace.,?" Iska ya ɗan furzar "to gashi nan dai sunce zuwa
dare za su turo mana sako," ya faɗa
jiki ba kwari.
"To Ai
shike nan, ai mutun baya wuce ƙaddarar sa in ba a dace ba sai mu ci gaba
da jarrabawa" Umman ta faɗa
ga. Shiru kawai sukai kowa da abin da ke zarya a ransa ya yin da sautin Radio
ke ta shi a tsakar gidan.
*****
Sam Hafsa ta
gaji da ajin na farko ba son Physics take ba sabida ba ta ganewa, na biyu
malamin da ke koya musun yada ya wani haɗe
rai ya sa duk haushi ya cikata, ga kuma haushin kanta da take ji tun ɗazu da take tawowa idanun
ta sun gaza goge mata hoton mutumin ɗazun
ita a yanzu ba za ta iya faɗin
asalin mai take tunani akan sa ba.
Kamar jira
take Malamin ya fi ce zumbur ta miƙe, riko tan da ta ji an yi ya sa ta
juyowa Bilki su ce, tare sukai secondry school yanzu kuma suke aji guda a
Jami'a, "Hajiya ina zuwa haka cikin gaggawa Bilkisun ta tambaya tana
kallon ta.?"
Ɗan
wawwaigawa Hafsa ta yi taso mu tafi kar" yamma ta yi," dariya
Bilkisun ta yi "wato da a ce ban ruƙo ki ba kina nufin tafiya zakiyi ki barni
ko me.?"
Dariya Hafsa
ta yi "no da ba tafiya zan ba kawai zan ɗan
fita ne in shaƙi fresh iska,"
"ok jeki
ki shaƙa
bari in nuna ma Ummi wannan abun"
"ok"
kawai Hafsa ta ce har ta kusa bakin ƙofa ta ce "dan Allah karki barni ina
ta jira waya ta babu caji na san da Abba yaga biyar ta yi tun da na ce masa
four ne zai ta kira in bai same ni ba hankalin sa zai ta shi."
Tana tsaye
jikin karfen benen tana bin bishiyun gun da kallo tare da tsuntsayen da ke kai
kawo daga wannan bishiya zuwa waccan ji take tamkar kar ta bar gun wannan ya sa
ma ba ta kuma leƙawa ta dan cewa Bilkisun ta fito ba.
Kafaɗar ta Bilkisun ta taɓa "zo mu tafi"
kamar jela ta bi bayan bilkisun, sai da suka fara zuwa Masallaci sukai sallah
kafin su nufi wurin da za su shiga mota.
Har ƙofar
gida aka kai Hafsa in da ta sauka tana ɗagawa
Bilkisu hannu kafin ta fara kwankwasa kofar gidan su, minti kaɗan Baba mai gadi ya ta so
ya buɗe ganin ta ya
saki washe baki "a'a Hajiya karama a dawo?" dariya ta yi "eh
walllahi na dawo ya aiki?" ta tamtabaya.
"Aiki
Alhamdulillah ai tun ɗazu
da naga Alhaji ya dawo shi kaɗai
na ce araina yau ba ni da abokiyar hira sai kim kai yamma,"
" ka bari
kawai Baba ai Malaman nan ba sa kyautawa bamu san da aijin ba ɗazu aka sanya da na san da
shi ai da ban bi Abba ba duk na gaji."
"Assha
sannu, Allah dai ya sawa karatun albarka," "amin" ta ce kafin ta
yi gaba, gaban ta ne ya hau faɗuwa
lokacin da ta ɗora
idanun ta kan Momin su wadda ke saman bene tana faman watso mata harara, tasan
ba komai bane fa ce dan kawai ta ga tana magana da Baba, a hankali jiki ba
kwari ta nufi kofar da za ta datar da kai asalin falon gidan.
Da sauri ta yi
ƙoƙarin
shigewa ɗaki dan karma
Momin ta sassko ta mata faɗa,
sai dai saurin nata bai idda ita ga shiga ɗakin
ba ta ji Muryar Momin, "sannu issasshiya wato zaki iya cewa wancan mutumin
kin dawo ni ban isa ki zo ki ce mun kin dawo ba?."
Ajiyar zuciya
ta yi a hankali kafin ta jiyo, "No momy kawai ina san aje jakata ne sai in
hauro saman," taɓe
baki Momin ta yi, yanzu fisabilillahi Kalle ki, kin kyautawa mahaifin ki ke
nan?" kallon kanta Hafsa ta hau yi, tana son gano aibun ta gaza gano hakan
ya sa ta cewa Momy "mai nayi?"
"Eh kya
ce mai kikai zaku je makaranta inda mahaifin ki keda alfarma a ce duk kayan ki
ki rasa wanda za ka sa sai wannan jemammiyar rigar..?"
Dariya Hafsa
ta yi "kai Momy wannan fa sabuwa ce last week na saya 17k fa" tsaki
Momin ta ja, "ai walllahi lefin Abban naku ne ni ai bazan ta fi da ke a
haka ba," dariya kawai Hafsa ta ce "shike nan Mum karki damu in za mu
fita tare sai abin da kika zaɓar
min zan sa but banda takalmi mai tudu."
"Ni in
tafiya da ke a'a kawai ki je ki bada ni cikin manyan mutane," dariya Hafsa
ta yi "mai aka dafa? yunwa na ke ji" ta faɗa tana shiga ciki.
"in sai
na faɗa miki zaki ci
ki kwana da yunwa," Momin ta faɗa
tana ƙokarin
zama, Hafsan ba ta dena dariya ba ta nufi in da kwanunakan abin cin suke.
***
Muktar na
zaune cikin abokan sa kamar kullum bayan sun yi mangariba zuwa isha kafin ya
wuce gida wayar sa ta yi ƙara alamar saƙo ya shigo, tun ɗazu yake duba wayar shiru ba kira ba saƙo
wannan ya sa har ya banzatar da wayar sai kuma ya ɗauko ya duba _"muna ta ya ka murnan samun
aiki na koyar da Physics bisa gwajin da ka zo ɗazu,
za ka iya fara zuwa aiki daga gobe, gaza zuwa cikin wannan satin na nufin baka
amshi aikin ba, Mun gode Hukumar Makaranta" _
Zumbur ya miƙe
bayan kammala karatun saƙon Umman sa kawai ya tuna ita ya dace ta fara jin labarin nan,
"ina za ka ne?, ai 8:30 batai ba" ɗaya
cikin abokan sa ya faɗa
cikin ɗaga murya.
Shi ma cikin ɗaga murya ya ce "mu haɗu gobe kawai, zan ma
bayani," gudu gudu sauri- sauri yake har ya ƙarasa gida sallamar ma tare da kiran Umma
ya haɗa ta, cikin
sauri ta fito "kiran da yake mata ya sa ta kasa amsa sallamar lafiya dai
kake mun wannan kira?"
Wayar sa ya
hau nuna mata kallon sa ta yi " yo banda abin Muntari ni me zan gane a
waya mai ya faru?' sun ɗauke
ni aikin ya faɗa cike
da murna ɗo.
"Kai
Alhamdulillah, Allah ya ƙarawa annabi daraja ya sa a fara asa'a, ayiriri!" ta sa
buɗa, daɗi ya kuma rufe Muktar a
duniya yana son ganin farin cikin Innan sa, "yau she kuma zaku fara zuwa
ta tambaye shi?."
"Go be in
sha Allah" ya ce
"Allah ya
sa muna da rai" ta faɗa
"amin Inna, bari in amso Omo gun Musa in zo in wanke kayan da zan sa gobe, gwanda in fara zuwa a mutunce," dariya ta yi "tom sai ka shigo" ya fice...
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
Credit: LuckyTD
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.