In kin Karanta ki yi sharing please
"Bafa ma
ganin comment din ku anya kuwa?"
Ban iskar da aka samu kwana biyu ba tare da anyi ruwa ba ya sanya garin yin zafi, wannan ya sa da yawan mazan unguwar firfitowa kama daga matasa har dama maginta ko ina ka bi cikin unguwar maza za ka gani wasu bisa bencina wasu bisa tabarmi kowa da abin da yake, can gefen kwata bakin wani kanti bencin su Muktar ne shida abokan sa da suke zaune gefen teburin da Ibrahim ke saida kaza soyayyiya, kilishi, da dambun nama.
Nasir da ya ƙara so
wurin ɗauke da katuwar
baƙar
leda ne ya zauna ƙarshen bencin tare da faɗin
"wash! Allah yau na gaji da yawa" Salisu ne ya ɗan leƙo kai
"kai dai walllahi ka cika ragon ta in ba haka maine abin gajiya a wannan ‘yar
ledar da ka ɗauko?"
Hararar sa
Nasir ya yi "ai gwamma ni da baki kawai na ce na gaji kai na tabbatar sai dai
kama faɗi wanwar"
Muktar ne ya
sa dariya "kai dai Nasiru baka mutunci mai ka mai da Salisun ne?"
Nasir bai ba
shi amsa ba ya hau fito da atamfofi cikin leda yana faɗin " Haja ce na kawo muku dukan mu na san
kayan aure muke haɗawa"
Ibrahim da ke
gaban glass ɗin da
kayan sana'ar suke yana zubawa matashin saurayin da ya zo siyan dambun nama da
doya ne ya yi caraf ya ce inason jar can zatawa Fiddausi na kyau" ya faɗa yana ninke takardar da ya
zuba doya.
Salisu ne ya
zuro hannu zai ɗauka
Nasir ya yi caraf ya ce "koda ba shi ba ni baka, kuɗi hannu nake bawa marasa sana'a"
" Kut..
wai mai kuka mai da ni ne?" Salisu ya faɗa
a fusace.
Ibrahim da ya
komo ya zauna ne ya ɗauki
jar da ya ce yana so yana ƙara ɗaga
ta cikin hasken street light "anma atamfar nan ta yi kyau, bama zan sa a
lefe ba gobe zan kai mata, in haɗa
mata da kwanukan da tayo min cin cin" ɗan
juyowa ya yi ya kalli Salisu mutumina kabi shawarar Muntari ka kama sana'a
walllahi"
Banza Salisun
ya masa tare da ci gaba da ƙoƙarin kama tasha a radiyon sa.
Nasir ne ya taɓo Muktar da tun da aka fara
batun kayan baice komai kan su ba ya ce " ya mutumina ban ga kafa ɗauka ba?" Murmushi
Muktar ya yi abin ai na masu ‘yan mata ne.
Nasir ne ya ɗago wata golden ɗin atamfa ya ɗora kan cinyar Muktar
wannan ko fara ko baƙa za ta mata kyau ina faɗa
ma, kama daina wayancewa ni namiji ne na san duk nunƙufurcin mutun dole akwai
wadda yake ɗan
tayawa"
Kallon atamfar
da ke cinyar sa ya yi, bai ankara ba zuciyar sa ta fara zayyano masa Hafsa
cikin atamfar cikin sauri ya mayarwa da Nasir kan cinyar sa, " aiko kai
namijin ƙarya
ne tun da dai baka san da irin mu ba wanda sam soyayya ba ta gaban su"
Dariya Nasir
ya sa tare da mayar masa atamfar " ka rantse da Allah babu wadda kake
so"
Shiru Muktar
ya yi tare da shan kunu, Salisu ne ya zuro kai "ka rantse mana" ya faɗa yana tsare Muktar da
idanu.
Tsuke fuska
Muktar ya kumayi lokacin guda zuciyar sa na ayyano masa Hafsa yanzu da ya yi
tunani mai zurfi ya fahinci ba wai iya burgeshi yarinyar kawai take ba, har da ɓurɓushin so duda shiɗin baisan ya son yake ba.
" Sabida
mai zan rantse, abin da na sani shi ne dai kawai ba wanda nake so"
"Wai kana
nufin wannan tsuke fuskar zai sa in ƙyale ka," Salisu ya faɗa tamkar da shi aka fara
musun tun asali.
"To karma
ka kyale ni mana" Muktar ya faɗa,
nefa da yaran da ke ɗan
wasa tsakanin hanya suka faɗa
suna tsalle ya bawa Muktar damar miƙewa bayin Allah sai da safen ku dama zafi
ya fito dani"
Nasir ne ya yi
saurin miƙewa
ya danƙa
masa atamfar kaban kuɗin
ƙarshen
wata," numfashi ya furzar tare da kallon atamfar kamar zai maido masa da ita
sai kuma ya juya ya yi gida.
Wutar nefan da
aka kawo ta haske tsakar gidan su Inna na zaune tana kwaɓin fanke Juwairiyya na Feraye kabewa ya san ta
abincin safen gobe ce ya yin da Hajara ke rubutu ya yi sallama kusan dukkanin
su suka amsa.
Hajara ta ɗago ne ta ce "lah yaya
mai ka siyo?"
Hajara ta
tambaya cewa ya yi "Idon matambayi," Juwairiyya tasa dariya inda
Hajara ta yi ƙas da kai tana zumɓura
baki. Gefen Inna ya aje ledar tare da faɗin
"Nasiru ke siyar wa na ɗaukan
miki wannan in kalar ba ta miki ba sai ince ya kawo ki zaɓa"
Da rawar jiki
Inna ta buɗe "kai
masha Allah, ai ta yi sosai gabaki ɗaya
suka faɗa, albarka
Inna ta hau sa masa tamkar ya siya mata duniyar nan ya yin da shi kuma yake ta
faman murumushi da faɗin
"Amin"
Ɗakinn
sa ya shige yana sauraron Addu'oin da Innar ke masa idanun sa bisa fanka da ke
kaɗawa baima san sa'adda
bacci ya yi gaba da shi ba.
***
Tunanin yadda
za ta iya koyan electricity and magnetism ɗinnan
ne duk ya cika mata rai, mafita ɗaya
ta faɗo mata shi ne
Uncle Muktar, inda tasan course ɗinnan
za ta faɗi ɗin da gaske, da tuni tun
suna hutu da take zuwa da zaman hira da suke lokacin break da tuni tasa ya fara
koya mata, sai dai yanzu babu dama tun da sun koma makaranta, next week za su fara
lectures gobe ko jibi take son siyi handing over da malamar da za ta rike ajin
da take.
Sam ta rasa
mai yake mata daɗi,
karatu da BUK ɗin duk
tabi ta tsane su, dama ba son Agric ɗin
nan take ba, tsaki taja ita dama art take tasan ba za a ba ta Agric ba.
Yunwa da ta
fara tambayar ta ya sa ta miƙewa ta kunna fitilar ɗakin ta dan tun da ta shigo
ta yi sallah take kan daddumar ba ta ko motsa ba tun bayan sakon da ta turawa
Aunty Halima, ranta sam babu daɗi
ta daure ta fito falon fatan ta kar ta haɗu
da kowa har zuwa gobe ta samu ta koma gidan Gwaggo.
Hango ta da
Khalil ya yi wanda yake ta fama wasa shida ƙanwar sa khairi ne ya rugo da gudu yana
tsalle yana faɗin
"Aunty Hafsa shi ne kika tafi kika barni ko, yau she kika dawo?"
Jin Khalil ya
anbaci Hafsan ya sa Abba juyowa " Hajiya Hansatu ashe kina gida?"
Daurewa Hafsan ta yi ta ƙaraso..
"Abba
sannu da gida" ta faɗa
kallon ta yi damuwar da ta bayyana a fuskar ta ya sa shi shi ma damuwa kafin ya
ce wani abu Momy ta fara faɗa.
"Eyye
sannu issasshiya, wato har kin yi girman da zaki shigo gidan nan ki kasa cemun
kin dawo, eh ba laifin ki bane laifin jami'a ne eh ai dole kiji kin isa tun da
kin shiga University"
Tun ɗazu da Hafsa ta gano result
ɗin ta take son yiin
kuka ta kasa sai yanzu faɗan
Momy duk yadda takai ga daurewa na kar kukan ya kwace mata sai da ya kufce
mata, aiko kamar ta tunzura Momy ta inda ta shiga ba tanan take fita ba.
Abba ne ya ce
"Dan Allah Hadiza ki kyale ta, jarrabawar su aka sa ta samu CO ba wai faɗan da kike mata ne ya sa ta
kukan ba" ganin da ya yi ta kuma tunzura kan Hafsan ta shagwabe daga ɗan faɗa ta hau kuka ya sa shu faɗin haka, zaton sa hakan zai
sa ta yi tausaya ta yi shiru bai san tunzura ta ya kuma yi ba.
Miƙewa ta
yi tana faɗa tana faɗin " retake fa kace,
ke yanzu ahaka da kike cewa zakiyi medicine din, ai Allah ya taimake ni da can
kike da kunya ta ishe ni, ki na dai kallon Sajida ita ce best student a faculty
ɗin su"
Takaici ne ya
kuma kama Hafsa ta tsani a dinga haɗata
da wasu a rayuwar ta, bacin haka ai kowa da irin tasa kwakwalwar.
Abba ne ya ce
"dan Allah Hadiza ki kyale ta, bacin ma haka ai GP din ta mai kyau ne in
ta dage next semester ta samu GP irin wannan CGPA ɗin ta zai kyau kafin su shiga lvl two din zan
wa Malamin da yake koyawa yaran mu Physics magana ya dinga zuwa gida lahadi
yana koya mata har na second semester ɗin
da zasuyi"
Ba wai baƙin
cikin samun CO ɗin ne
ya bar ta ba, a'a sai dai anbatar Muktar zai dunga zuwa gida koya mata ne ya
kwantar mata da hankali, farin ciki ya ɗan
samu a zuciyar ta, murmushi ta yi na gode Abba ta faɗa tare komawa wurin da ake aje abinci ta ɗiba Inda Khalil yabi bayan
ta cike da murna Khairi tasa kuka Abba ya ɗauke
ta ya yi ɗakin Hafsan.
Momi ta ja
tsaki sam lamarin Hafsa takaici yake bata, ko wata ba aiba Hajiya Sa'adatu
mahaifiyar Hidaya ta gama cika mata baki Hidayan ba ta samu matsala ba, itama
jira kawai take a kafewa su Hafsan ta take ta je ta zayyana mata, komai ta tuna
oho ta kuma jan wani dogon tsakin tare da faɗin
aikin banza...
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.