Ko da So… (Kashi na Goma Sha Biyu - 12)

    In kin Karanta ki yi sharing please

    Tun da aka rubuta exam din farko hankalinta bai kwanta ba. Ganin yadda exam din ta yi mata ya saka ta hana idonta bacci ta dage da karatun sauran courses din. Sam ta cire wasa da ba ta lokaci a abubuwa marasa muhimmaci ta mai da hankalinta completely kan karatun. ba ta son failure a rayuwarta musamman ma ta fannin karatun.

    Pencil take fikewa wanda zatayi practicing zanen kifi da shi mummy ta shigo falon.

    “Hafsah dai ta ba ce bat. Wannan bamu san wacece ba.” Mumy din ta fada tana jawo kujerar kusa da Hafsahn ta zauna sannan ta dubi kan table din inda anan Hafsah take wuni.

    “Mummy sannu da dawowa.” Haka kawai ta ce sannan ta ci gaba da zanenta.

    Kallonta mummyn ta yi sannan ta yi murmushi. “Allah ya bada sa’a. Daman so nake kije gidan su Hidaya ki karbo min wani lace da na siya.”

    “Mummy dan Allah. Exam fa nake. Hidayan ta kawo miki mana.” Ta turo baki sannan ta juya.

    Sabanin yadda suka sabayi, mummyn ta ce, “Toh shike nan Allah ya bada sa’a. Da a ce komai na rayuwarki haka kika ba shi muhimmanci ai da ba haka ba. Ni na koma daki. Na dafa abinci ma in zaki zuba.”

    Yadda Mummy ta yi laushi ya sa Hafsah ta ji babu dadi ta kalle ta. “Mummy kinsan zan karbo miki ko?”

    Murmushi ta yi. “Bakomai. Good luck.” Da haka ta bar wurin.

    **

    Yau ma ta je makarantar don haka ta yi saurin zuwa kujerarta ta zauna. Tana ta duba takaardun hannunta, fuskarta cike da damuwa fal wadda ta mamaye fuskartata tun ran farko.

    A hankali ya tako, hangota da ya yi ya saka ya ji wani abu da ba zai kira shi da walwala ba. Kawai he felt something.

    Ko da ya karaso, Hafsah taso ta yi kamar ba ta ganshi ba don yau ba ta son yin magana amma sai ta kasa.

    “Hi.” ta ce sannan ta matsa mishi ya zauna. Murmushi ya yi ya ajiye flask din hannunsa a tsakanin su sannan ya zauna.

    “Hello.” Ya amsa mata sannan ya zauna. Sun jima ba su ce komai ba har sai da yaga ba zatayi magana ba sannan ya ce,

    “Bismillah: wainar gero.” Ta dago ta kalle shi da alamun tambaya ya yin da shi kuma yake kokarin buɗe flask din. Nan take kamshin geron ya cika mata hanci ta ji tana son ci. Sai a sannan ta tuna da rashin jin abincin safe da ta yi a ranar.

    Amma da yake ba ta taba ci ba sai kawai ta kalle shi har ya doni kulikuli ya kai bakinsa. Hankalinsa kwance yake taunawa.

    “Ban taba ci ba.” Ta amsa shi tana dora indanuwanta akan shi. Duk da tension din karatun da take ciki sai da ta ji wani abu ya amsa a zuciyarta. ba ta san da me za ta kwatanta shi ba. Kawai dai in an matsa mata za ta ce yana burgeta.

    Da mamaki ya kalle ta sannan ya yi murmushi wanda ba ta gani ba saboda dauke kanta da ta yi daga kan sa.

    “Yau zaki fara. Da dadi.”

    Ta kai hannu ta gutsuri kadan sannan ta doni kuli kulin. Sai da ta dan kalli piece din hannunta ta kalla taga baya kallonta sannan ta kai bakinta. Taunar farko, ta gaskata maganar sa sai gashi ba tare da ta ce komai ba ta kai hannu ta sake dauka. A haka suka cinye ba tare da kowa ya ce komai ba. Ruwa ya mika mata, ba musu ta karba da murmushinta ta sha. Daidai sannan aka kada kararrawa.

    “Thanks. Kuma da dadin sosai.”

    Ya murmusa. Wa ya gaya mata daman girkin Innarsa girkin wasa ne. “Inna ta ce take yi.” Ya fada cike da nuna jin dadin sa a fili.

    Ta gyada kai. “Five star.”

    Mikewa ya yi yana kallon yaran da suke guje gujen komawa class.

    “Thanks for lunch.” Ta sake maimaitawa wanda a daidai lokacin Mukhtar ya sake jin wani abu ya shiga zuciyarsa game da Hafsahn. Kalmar dai daya ce, ta burge shi.

    Ba tare da ya ce komai ba ya mata murmushi, ta mayar masa. A daidai wannan lokacin wata alaka ta shiga tsakaninsu. Alakar da babu wanda zai iya mata suna a cikinsu.

    Kallon bayansa ta yi har ya ba ce mata da gani sannan ta mayar da hankalinta kan takardun ta tana sake jinjina dadin wainar gero din. ta yi mata dadi kuma za ta fadawa mummy don ta koya mata.

    **

    Bayan kwana biyu an yi exam fiye da rabi, Hafsah tana zaune tana kallo mummy ta shigo falon. Sannu ta yi mata sannan suka ci gaba da kallon su. Karan kiran da ya shigo wayar mummy ne ya ratsa shirun da sukayi. Mummy ta dauka tana dariya ita kada

    “Ke dan Allah? Kai kai kai amma nayi murna wallahi.” Iya abun da Hafsah ta iya jiyowa ke nan kafin mummyn ta tashi ta bar falon. Ko kadan ba ta ci gaba da tunanin ba ta ci gaba da kallon fim din indiyan da ake haskawa a tashar. ta yi nisa gun kallon sai ga mummyn ta dawo.

    “Kin san Hajiya Deenah wadda muke sarar laces a wajen ta da na gaya maki rannan?”

    Hafsah ta kalle ta, “Matar nan ta Abuja?”

    Mummy ta murmusa. “Dadi na da ke baki da mantuwa. Ita ce ta zo Kano in fada miki wallahi. Gobe za ta zo mu gaisa. Toh kin san dai bai kamata na ji kunya ba. Maza maza ki je drawer ta ki nemo leshin da zaki kai a rage miki…” Hafsah tana jin haka ta juya tana kunkuni.

    “Yau dai daya ba zan saurareki ba. Wannan umarni ne.” Mummy ta sha kunu wanda ya sa Hafsah ta yi saurin mikewa don ita barin wajen ma zatayi kafin mummy ta tuno wani abun ta sake saka ta dole. Har ta taka mummy ta dakatar da ita.

    “Sannan ki kira Hidaya tazo. Ko kuma bar shi ma zan kira mamanta. A nan za ta kwana. Zaku je shopping ne ku siyo kayan girke girken da za a mata gobe. A nan za ta yi lunch.” Ita dai Hafsah ba ta tanka ta ba. Sai da mummy ta sake daga murya cike da fada.

    “Baki ji ni bane!”

    “Na ji mummy.” Da sauri ta bar falon tana jin wani haushi yana cika ta. Ita sam ba ta son kalar rayuwar nan kuma ba ta san me ya sa Abba baya hana mummy ba bayan su kullum a cikin yi musu nasiha yake kan kar su dauki rayuwa da zafi.

    Mummy kuwa a take ta kira Farida ta sanar mata da kawarta za ta zo daga Abuja. “Mummy ki aro chef din Hajiya Maryam mana ta taya su.” Ta bada shawara wadda ta saka mummyn nishadi. Nan da nan ta ajiye wayar ta kira Hajiya Maryam wata business partner dinta ta yi sa’a kuma chef din is available. Bayan nan ta kira gidan su Hidaya sannan ta aika driver a dauko ta.

    Account balance dinta ta duba taga ba ta da matsala ko da kuwa nawa za ta kashe ba tare da ta taba jarinta ba. Wannan opportunity ne babba a wajen ta. Ta dade tana son kawance da manyan mata ko dan connections da kuma business. Duk kawayen ta kaman ita suke bab wata babbar hajiya da duniya ta san da ita. Cike da zumudi ta tashi ta tafi dakinta tana binciko kayan da ya fi ko wanne tsada a kayanta wanda beifi sau daya ta taba sakawa ba.

    Drawer gwal dinta ta buɗe ta ciro wanda daman saboda irin wannan ranar ta tanade shi.

    Ranta fari tas ta fara shirye shirye da goge gogen gidan.

    **

    Kamshi ne yake ta faman tashi a kitchen din inda chef Roy ta dage wajen nuna bajintar ta ta iya girki sannan kuma tana nunawa Hafsah da Hidaya wasu dabarun girkin.

    “Duk sanda kike bukatar wani dandano na musamman a tattare da girkin ki musamman ma nama, marinate it first. Taste din na daban ne. Ki masa hadi sannan ki diga mai sai ki rufe shi na wasu awanni. The resulting aroma is fantastic.” Ta fada musu tana saka marinated minced meat din a fridge don ya fi tsimuwa.

    Hafsah ta tabe baki ta ce, “girki akwai wahala wallahi.”

    Chef Roy ta yi murmushi. “Amma akwai faranta ran jama’a musamman ma masoyan ka. Ai girki yana da tasiri sosai akan mutane. In fact hanya mafi sauki wajen janyo hankalin mutane gareka shi ne ta hanyar abinci me dadi. My advice? Ki daure ki koya.”

    “Gaya mata dai.” Hidaya ta mara mata wadda tasa Hafsah ta yi shiru don ta gaskata maganar su. Abinci me dadi yana shiga zuciya ya yi abubuwa da dama. ba ta manta wainar geron da taci ba, ba ta manta dadinta ba, ba kuma tajin za ta taba manta wanda ya ba ta din.

    Da haka suka ci gaba da girke girken main dishes sannan suka fara rolling sheets na samosa.

    “Zan iya zuwa koyan girki wajen ki?” Hafsah ta tambaya ba tare da ta dago ba.

    “Of course, ko yaushe.” Chef ta amsa.

    Hidaya ta kurawa Hafsah ido alamun tambaya sai dai ba ta samu damar cewa komai ba mummy ta shigo.

    “Dan Allah kuyi sauri. By now ya kamata a ce kun fara jera abuncin nan a table. Chef kar ki biye wa yaran nan.”

    “Yes ma’am.” Ta russuna sannan mummy ta fice directly zuwa dakinta inda za ta shirya. Su kuma suka ci gaba da sarrafa snacks din cikin sauri.

    ***

    “She’s amazing gaskiya.” Hafsah ta fada tana gutsirar samosa tana sake yabawa girkin chef din wadda har ta gama gyara wurin da suka ba ta ta tafi.

    Su Hafsah ma sunyi wanka ke nan sunyi kyau sosai sannan suka zauna ciye ciye.

    “Ku zo ku gaishe ta. Kuma dan Allah Hafsah kija ajinki.”

    “Toh mummy.” Ta amsa don ta gaji da wannan warnings tun jiya. Jikinta ma duk ya yi sanyi saboda ta rasa me zatayi don ta burge mummy. Ita she’s not a good actress akan irin abubuwan nan. Da sai ya fi ma in mummyn ba ta nuna tana nan ba.

    A hankali suka fito daga dakin Hidaya ta rike mata hannu kamar tana guiding dinta. Sai da suka isa falon, fuskarsu a sake sannan Hidaya ta radawa Hafsah.

    “Banda dariya, jin kunya and too much talks.” Saura kiris Hafsahn ta yi tsaki.

    Cike da nutsuwa suka karasa sannan suka durkusa suka gaida Hajiya Deena.

    “Ma sha Allah. Ya kuke?”

    Hafsah za ta amsa, Hidaya ta rike hannunta a boye sannan ta amsa in a classy way don ita gwana ce.

    “Ya sunan ku.”

    “Ni Hidaya and ?”

    “Hafsah. Sannu da zuwa aunt.” Hafsah ta fada cike da murmushin da ya sa kumatun ta ya fara ciwo. A haka ta saci kallon mummy taga fuskarta. And it showed ba ta kwafsa ba.

    “Wannan ita ce Asma, diya ta ce amma ba ta gani.”

    “Ohhh.. I’m so sorry.” Su dukka suka furta a tare suna nuna rashin jin dadinsu a fuskarsu sannan suka kalle ta. A take Hafsah ta ji tausayin yarinyar ya cika ta har sai da ta yi kwalla. Da kyar ta kalle ta again tace. “Hi.”

    Suna kallo Hajiya Deena ta kama hannun yarta. “Go with them habibty.” Da haka suka kama hannunta suka fita daga falon jikinsu ya yi sanyi sosai. Har suka isa daki ba wanda ya sake magana inda suke ta tunanin ta inda za su soma yi mata hira.

    “Hi, sunana Asma AbdoulJalal. I was born blind. Ban san meye kala ba. And I’m happy.” Hafsah ba ta san sanda ta rungume ta ba sannan ta runtse nata idanuwan. Duhun da ya mamayeta ya saka ta fara hawaye. She couldn’t imagine life a makance. ba ta san ta inda za ta soma ba.

    “Kowa sai ya dinga jin tausayi na, saboda ban san kalar komai ba. Not even Mamma.” Ta fada sadly amma da murmushi a fuskarta.

    Duk sai suka zama bebaye suka kasa magana.

    “Amma all the same, the world ia equally beautiful. Komai sai dai nayi imagining. The only thing i am missing is colors. Duhu kawai na sani so komai a duhu nake ganinsa. A duhu nake tunanin sa. Ance I’m beautiful haka ne?”

    Da ido suke ta binta tana ba su mamaki. Yadda take ta surutu freely. Su kuwa sai faman goge hawayen su suke. Cike da karfin hali Hafsah ta amsa mata.

    “Kina da kyau. Ba kadan ba. Kina da mugun kyau. I don’t know how to describe it for you.”

    Shiru Asma ta yi wanda ya bawa Hafsah daman tashi ta tafi bandaki tana kukan rashin godewa Allah akan dukkan ni’imomin da ya mata. Rashin kula cewa idon ta da ya bar mata ma wata babbar kyauta ce da rahama sa a gareta….

    Rubutawa

    Aeshakhabir

    Fadimafayau

    Soyayya
    Credit: LuckyTD

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.