Ko da so..... (Kashi na Goma Sha Uku - 13)

    In kin Karanta ki yi sharing please

    "Aifa dole kaya su dinga koɗewa, haba a ce sawa ɗaya sai an wanke kaya, su kaya ba wani na azo a gani ba" Inna da ta fito daga ɗaki riƙe da ɗan likidiri ta ce da Muktar wanda ke ta faman cuɗa kaya, ɗagowa ya yi yana murmushi daga sunkuyen wankin, "ai Inna kayan ne sam ba sa mun daɗi in nasu su da ɗauka ko yaya maiƙon jikina ya taɓa kayan na fiso kan in kuma sawa in wanke"

    Murmushi inna ta yi, "ai iyawa ne bakai ba, in ka dawo ka cire kayan sai ka baza su a inuwa su sha iska kafin ka mayar adaka"

    Murmushi ya yi ba tare da ya ce komai ba, inna tasan halin abin ta, tun da ya yi murmushin nan cewa bazai yi bane kawai ba zai ba anma bazai yi yadda ta ce É—in ba, kwafa ta yi "ai shike nan kayan ka" ta faÉ—a kafin ta yi zaure har ta kai ta tsaya ni na shiga gidan Harira in ka gama kan kaje in da za ka ka daure ka shigo ka duba Malam É—azu Fiddausi da ta shigo siyan taliya take cemun jinin nasa ya yi tsanani"

    "Tom shike nan a masa sannu kanin zo" Inna ba ta ce komai ba ta fice daga gidan tabarshi yana shanya.

    Sai da ya gama komai sannan ya fito, yana ƙoƙarin ɗaure ƙofar gidan da wayar kebir ya ji muryar juwairiyya na faɗin yaya kar ka kulle, sakin ƙofar ya yi tare da juyawa Juwairiyyar ya gani ɗauke da katuwar Kula tare da Hajara wadda ke sanye da uniform ɗauke itama da ƙatuwar kular kamar kullum in ta taso saga makaranta sai ta fara zuwa ta ɗauko kula inda Juwairiyya ko Ummi ke zama da abinci kafim ta tawo gida, bai ce musu komai ba ya tsallaka kwatar da ta raba tsakiyar layin nasu ya shiga gidan su Harira da sallamar sa.

     daga zaure suka haÉ—a ido da Bahayura wadda ke gefen tabarmar da su Inna ke kai tana gurza kuÉ“ewa murmushi ta sakar masa, lah yaya shigo mana ta faÉ—a lokacin da ta jawo turmi miÆ™o masa ta yi zauna daga bakin zauren ya zauna dan tsakar gidan ya tushe, a nutse ya gaida su ya musu ya mai jiki kafin Bahayura ta gai she da shi, "yaya ya aikin?, Jiya nazo ai baka nan"

    "Aiki Alhamdulillah, eh jiya naje lesson da nakewa yara da na dawo na biya ta majalisar mu sai dare na shiga gida"

    " Haba nifa in ce har gidan su Yaya Salisu naje bakanan"

    Murmushi ya yi " towo Allah ya sa ba ba shin ki naci na manta da shi ba" sai da kowa ya yi dariya kafin Umman su Bahayuran ta ce " ai ko ba shin ne ta ƙyaleka ka sarara.

    Aje kuɓewar ta yi kafin ta miƙe ta mika hannu saman kusa da jakun kunan su ke rataye daga ɗan inda rufi ya zubo, takardu ta ciro " ka gani Badawi ne ya kawo min tana nufin saurayin ta wai form ne na school of hygiene, ya sai mun to daga ni har shi muna tsoron mu cike ba dai dai ba" cike da annashuwa ya amsa " amma Badawi ba ƙaramin kyautawa ya yi ba gaskiya miko biro in cike miki yanzu in ya so ko gobe sai in miƙa miki in jiyo mai da me zakuyi."

    "Anma yaya da ka kyautamin walllahi don ni ya ce in kai da kaina gashi na kashe kuÉ—in motar da yaban."

    Tsaf ya cike mata kafin ya mike "bari in leƙa in gaida malam ɗin," sosai ya tausayawa yadda Malam ke jin jiki, a kasalance ya bar gidan kasancewar yau lahadi ranar da suke ɗaukan karatu ya sa da ya fito daga gidan littattafan sa ya ɗauka kafin ya wuce masallaci.

    Ko da ya dawo dakyar ya samu bacci ya yi awon gaba da shi sabida tunane tunane haka kawai ya rasa mai ya sa da ya zauna sai Hafsa da ‘yar hirar rakin su mara tsayi ke dawo masa wani zubin takaicin kan sa ya kamashi wani zubun ya saki murmushi, bai san mai yake ji kan yarinyar ba kuma zai iya cewa maine ba ya san dai ba sabo bane ba kuma so bane cikin tunanin da son gano mai ne ya samu bacci ya yi gaba dashi.

    Washe gari da wur wuri kamar kulluum ya shirya bayan ya cika gidan da ruwa, fitowar da ya yi daga kama ruwa ya tarar an zuba masa abincin karin sa yau a langane har ya É—auka ba tare da dubawa sai kuma ya buÉ—e kosai da faanke ne, "an gama toya wainar nan kuwa?" ya tamaba.

    Umma ta ce "towo yau kai ke tambayar waina ina kafison fanke?" Murmushi ya yi abokin aikina ne rannan da kika zubamin ya ji daÉ—in ta shi ne nace bari yau in kai masa.

    "Hajara ɗibar masa a ta gidan Malam Hassan in ya so sai ki zuba musu wata" Inna ta faɗa da ɗan ƙarfi.

    "Ta É—ari biyu zaki zuba" shi ma ya faÉ—a

    Koda ta miƙo msa amsa ya yi ya sa a langar da ke hannun sa kafin ya zaro ɗari biyun ya miƙa mata, juyawa ta yi ta ce da Inna " kinga ya bada kuɗin"

    Da hanzari inna ta ce " wanne kuÉ—i ba shi abinsa kaji ka mene dan an baka ta É—ari biyu ka bawa wani?" "A'a inna abin fa siyarwa ne, sai na dawo" ya faÉ—a tare da saka kai ya fice ba tare da ya amshi kuÉ—in ba.

    **

    Yau tana tashi ta hau zuba kayan ta a ‘yar Æ™aramar akwatun ta, itakam wannan hutun semester É—in ba za ta iya yin sa guri guda ba takaicin first papar É—in su sai ya ishe ta sai da ta É—ebi duk abin da tasan za ta buÆ™ata kafim ta shiga wanka tsaf ta shirya kafin shida ta kammala komai ta fito riÆ™e da jakar ta sam batayi niyar faÉ—awa Momy za ta wani gurin ba, tafi so sai ta je ta bugo mata waya wannan ya sa take so kafin Mom É—im ta fito falo takai kayan cikin but É—in mota.

    Cak ta tsaya lokacin da ta ji Muryar Mum ɗin "ke Hafsa ina zaki da wannan fagon kayan?," Daurewa ta yi tare da tattara kwarin gwiwar ta guri guda kafin ta jiyo fuskar ta ɗauke da murmushin ƙarya " Momy yanzu nake son in kai kayan sai in zo in fada miki daga Flourish gidan Gwaggo zan dinga wucewa acan zan hutun"

    "Ba inda zaki da wannan damunar zaki tafi wannan gidan ga uban sauro da raɓa"

    "Allah Mum ba raɓa, sauron ma ni ba jin sa nake ba" Hafsa ta fada a shagwaɓe.

    "Nadai faÉ—a miki ba in da zaki, kin san ba iya aikin gidan nan zan ba ni kaÉ—ai in kin tafi"

    "Please Mum ki tallafa ki barni in tafi, walllahi ina missing É—in gwaggo"

    Harar ta Mum ta yi bayan ta zauna " ai kin san dai duk yadda kike missing din su ba kamar ni da suka haifa ba, ba inda zaki"

    Abba da ya fito ne ya ce "Hajiya Hansatu kai kayan ki mota" cike da murna ta fice sannan ya juyo kan Mum wai dan Allah Hadiza mai ke damun ki ne, kibar yara suyi zumunci mene ciki dan ta je ta yi sati biyu.

    Yatsina fuska Mum ta yi " ni karka min sharri Abban Farida ina ga satin da ya wuce ta je gidan, ni bance kar ta je ba kwana ne, uban sauron da ke gidan nan ta je zazzaɓi ya rufe ta kadai san dai Hafsa ba lafiya ta cika ba."

    Dariya Abba ya yi " kema dai kinsan duk yadda Gwaggo zatai ba za ta bari sauro ko wani abin ya cutar da Hafsa ba ki kyale ta taje" shiru kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.

    Kalil ne ya fito yana sosa ido hango Abba da ya yi ne ya sa shi rugowa da gudu yana murna Abba ya rungume shi "a'a Khalilullahi an tashi?" GyaÉ—a kai ya yi " Good morning Abba, ta shi na yi da wuri Aunty Hafsa ta ce in ban tashi da kaina ba yau ba za ta ba ni cake ba"

    Dariya Abba ya yi "Morning my boy, wato kwadayi ya tashe ka kawai maza jeka ta shirya ka, kuyi sauri kar mu makara"

    Har Khalil ya ruga ya tsaya cikin daga murya irin ta yara ya ce "Good morny Mum" murmushi ta yi ganin ya yi gaba abin sa.

    Juyowa Abba ya yi ya kalle ta "wai yaushe zaki mayar musu da yaran su karfa yaron nan yacire kunya ya zo amsar su"

    "Mayar ya kuma? Ai na amso su ke nan ta faɗa tare da barin wurin" girgiza kai kawai Abba ya yi yana darya shikam bai taɓa ganin inda uwar mata ke iko da jikokin ta ba sai kan matar sa, shafa kansa ya yi "Hadiza ta akwai rikici"

    Dariya ta yi tare da juya idanu

    Tun da aka buga ƙararrawar fitowa break ya hanzar ta dan zuwa ganin Hafsan tun da ya shigo makarantar ya ji yana son ganin ta sai dai kasancewar ba dabi'ar sa ba ce zuwa aji gun malami ya sa ya daure zuwa a fito break ɗin.

    Annurin fuskar sa ne ya ɗauke hango wurin wayam ba kamar yadda ya saba daga nesa zai hango kanta alamun tana zaune a sanyaye ya karasa ya zauna lokacin lokaci yana duba agogo da hanya ko zai ganta tayo wajen sai dai babu alamar ta duk son sa da fanke yau kasa ci ya yi ji ya yi duk ya gundure shi, rufe langar ya yi tare da miƙewa sakamakon buga ƙararrawar da akai ta komawa aji har ya yi hanyar office da zummar aje langar sa sai kuma ya yi ajin da aka bawa Hafsan primary 2 ne teacher per class ne, gaban sa ke dukan uku uku dan bai san mai zai ce mata ba har ya ƙarasa bai iya tsaida abin da zai ce ba ya juyo muryarta na faɗin "lah Uncle ina kwana?"

    Juyowa ya yi fuskar sa ɗauke da murumushin da bai san ya iya irin sa ba ya ce " lafiya ƙalau, Aunty"

    "Kaga baka ganni ba ko?, Abubuwa suka sha min kai walllahi"

     

    Murmushi ya yi "aifa na ce yau wannan sarkin mallake kujera ko lafiya kinga na ma kawo miki waina baki fito ba ya miƙo mata" amsa ta yi tare da faɗaɗa murmushin ta kai amma Na gode walllahi kamar kasan ban karya ba shirya Kalil ke makarar dani.

    Murmushi ya yi bari inje kar mu shiga lokacin ɗalibai tom ta ce ya yi gaba cike da kwarin gwiwa sam bai za ta zai iya yin jarumtar nan ba ko da yake da ba ta leƙo ta ganshi ba har ta masa magana sai dai ya juya.

    Juyuwar da ya yi yaga ta koma ya sa shi sauke ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da tafiya.

    Tafe yake a nutse, lokacin da aka tashi zuwa titi mota ce ta tsaya gefen sa har ya yi gaba ya ji muryar ta na faÉ—in uncle ina kayi?"

    Juyowa ya yi " cikin gari na yi, kamar ba hanyar mu É—aya ba"

    Murmushi ta yi "yau ƙoƙi zani gidan kakan ni na sai mu saukeka a hanya shigo"

    Buɗe gidan gaba ya yi ya shiga suka gaisa da Malam Musa driver, sai dai ku saukeni a school of hygiene zan yi submitting form din ƙanwa ta," "tom" Hafsa ta ce, komai ta tina kuma ta ce " ina ne unguwar ku, form din kawai za ka miƙi?"

    " Dala ne, eh shi kawai zan bayar" ya faÉ—a a takaice

    "Ah tun da hanya ce Malam Musa sai mu jira shi ya bada ko?" Ta faÉ—a tana mai mayar da hankalin ta kan Malam musa, wanda ya gyaÉ—a kai tare da jan motar....

    Rubutawa

    Aeshakhabir

    Fadimafayau

    Soyayya
    Credit: LuckyTD

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.