Ko da so... (Kashi na 19)

    Kukan da Khairi ke ta faman zabgawa Momy ta faman lallashin ta ya sa Usman da ke zaune yana faman duba takardun ɗaliban sa miƙewa, falon ya fito a nutse ya ɗauki yarinyar Momy ba ta ce komai ba zaton lallashin yarin yar zai yi ɗakin Hafsa ya nufa inda ya fito riƙe da hannun Khalil wanda ke ta wasa abinsa.

    Tsallen murna yaron yake ya biyo Usman ɗin a baya yana tsalle suka fice a baya ya sanya Khairin shi ma Khalil kusa da ita yaja ya zauna inda Usman ya hau mazaunin driver ya ja motar Khalil ya leƙo gaban motar "Uncle unguwa za mu?"

    "Gida zan mayar da ku" abin da kawai Usman ya ce ke nan Kalil ya koma lakwas rai ɓace, a dai dai ƙofae gidan yayar tasa ya faka motar ko ciki bai shiga ba ys buɗe ya fito tare da saɓo Khairin a faɗa Khalil ya biyo bayan sa bugu guda Mai gadi ya buɗe ganin Usman ya sa shi matsawa gefe alamar ya shigo sai da suka gaisa sannan ya yi cikin gidan.

    Farida na zaune tana kallo ya shigo da gudu Khalil ya ƙaraso ya rungume ta, ta cafe shi tana faɗin ɗan lele na " ɗazun nake cewa zani ganin ku ashe kun tafe" aje Khairi Usman ya yi, ta ko zunduma ihu ba za ta zauna na Usman ya miƙawa Farida ita, ta kuma maƙale shi, "kin gani ko kawai kik ɗauki yara kik kai wani wuri jibi tama manta da ke" ya faɗa lokacin da yake ƙokarin sauke Khairin.

    Hararar sa Faridan ta yi "gidan iyayen nawa ne wani wuri?"

    "Nidai koma mene yaran nan takuramin suke ko jiya inason in bacci Khalil ya zo ya takuramun sai dai muyi game, to ni ba Hafsa bane"

    "Eyye sannu issasshe kaine ma wa na, ka shigon gida ba ko gaisuwa ka hauni da faɗa,"

    Murmushi ya yi "ayi haƙuri Hajiya Aunty Farida, Ina wuni?"

    Harar sa ta yi ka ɗauki yaran nan ku koma, tumma kan Baban su ya dawo, dangwarar da khairin ya yi tare da yin waje da gudu, tsaki taja tare da ɗaukan wayar ta ta hau kiran Momy.

    Momy na zaune tana hutawa kiran Farida ya shigo da murmushi ta ɗaga " Momy kece kika sa Usman ya kawo su Khalil"

    Miƙewa Momy ta yi tamkar tana kallon Faridan " gida kuma nifa ɗaukan ta ya yi zai lalllashe ta bar in sa Hafsa ta zo ta tawo da su"

    "Yawwa Momy kisa ta zo yanzu, kafin Abban su ya dawo yama gansu"

    Katse wayar Mum ta yi tare da yin ɗakin Hafsa zaune ta same ta gefe guda takar du ne, ba tare da ta zauna ba ta ce "ince kodai baki faɗawa Hidaya kina da CO ba, jiya Sam mantawa na yi bamuyi Maganar ba, na ce karki faɗa mata"

    Fuskar Hafsa ta tuna ƙarara ba ta son batun CO ɗin murya aɗan dashe ta ce "ai bama maganar result da ita, nata ma gunki na ji" ajiyar zuciya Momy ta yi.

    "Yawwa kinga wai Usman ne ya ɗauki su Khalil ya mayar gida shi ne nake so ki je ki dawo da su,"

    "Towo shi ma dai yaya Usman, yaran da ba shi ke kula da su ba,"

    Kwafa Mum ta yi basshi zai zo ya samen maza jeki ki dawo dasu"

    Hafsa ba ta ce komai ba ta miƙe kasancewar ta kullum a kintse yasata maya fi kawai ta zara ta yo farfajiya inda suka ci karo da Abba." Yawwa Hajiya Hansatu ai gwanda ki cire damuwar haka ki yi walwalar ki, ina zaki haka"

    "Gidan yaya Farida zani wai yaya Usman ya mai da su Khalil shi ne ta ce azo a ɗauko su"

    Murmushi Abba ya yi irin nasu na manya "ho Usman sarkin rikici, ai ya kyau ta da mayar musu da yaran su, muje ciki ya faɗa"

    Binsa a baya Hafsa ta yi tana murmushi dan sam ba ta son zuwa gidan Aunty Farida a tsukun nan tasan damun ta za ta yi kan course din da ta fadi. Momy naganin sun shigo tare ta tsuke fuska, "ya kika dawo kuma?"

    "Abba ne ya ce ba inda za ta tun da an mai da su sai ki bari wani hutun in sun ra'ayi sa kawo miki, kayan su kuma in Usman din ya dawo ya kai musu" sin sin Hafsa ta shige ɗaki Mum ta hau faɗa Haba Abban Farida kana fa ji nace na ɗauko su ke nan" murmushi ya yi tun da dai ya riga ya mayar su shike nan bacin haka ke waye ya ɗauke miki naki yaran ki bar musu yaran su wurin su yadda za su shaƙu da abinsu.

    Kwafa ta yi tare da miƙewa tabar wurin, shi Usman ɗin zaizo ya samen ne"

    Da ɗan ɗaga Murya Abba ya ce "haba rabin ran ko kin manta da ɗan tsohon naki ne ya mayar miki da su ba, abin cin nawa fa"

    Juyawa ta yi zuwa dining area ta haɗo abincin ta aje masa ta juya za ta tafi, Haba masoyiwa ki zauna abincin zaifi daɗi badai Usman bane zan miki maganin sa"

    Murmushi ta yi ta dawo ta zauna tare da ɗora motar ta, ya yi murmushi ya hau cin abincin sa.

    ***

    Tun da sukai batun koyawa Hafsan ya kasa tsaida shawara gashi gobe lahadi, sam baya son tunanin da zuciyar sa take kan yarinyar, yana son kuɗin da za a biya shi yana son koyawa Hafsan sai dai take taken zuciyar sa ya sa yake tsoron tusa kansa kusa da ita yana tsoron kamuwa da son ta, a hankali ya fito tsakar gidan su ajiyar zuciya ya yi, ya sani yarinyar talaka ma ba lallai ta so shi ba, bare irin su Hafsa, yanzu sa a ce tana son ka, kai za ka iya riƙe ta? Tambayar da zuciyar sa ta masa ke nan.

    Fitowar da ya yi a ƙofar gida ya zauna yau sam baya son zuwa wurin su Salisu baya son damun sa da suke batun budurwa, Juwairiyya da ya hanga ɗauke da kula ne ya sa shi miƙewa ya ƙarasa inda take "kawo ya ce"

    "Akwai wata can yau Hajara kanta ke ciwo nace ta bari in kawo sai in zo in ɗauki ɗayar ta jirani"

    "Ok kar ki bar gidan ba kowa bari in ƙarasa gangaren"

    "tom" kawai ta ce ta yi gida shi kuma ya ƙarasa daga ɗan nesa ya hangi Hajara sanye da Uniform zaune kan tebur gaban ta kuma kula ce, take zuciyar sa ta ce mai kake jira dubu ashirin fa ba wasa ba ce, kana buƙatar samun kuɗi da yawa ko dan ƙannen ka su daina zuwa cikin maza haka suna yini.

    Jiki a saluɓe ya ƙarasa wurin, Garba ne ya riga shi ƙarasowa tare da ɗaukan kular ta shi muje ya ce ta miƙe dakyar sai dai ganin Muktar ɗin ya sa taja ta tsaya fuskar ta cike da tsoro cikin rawar murya ta ce "wallahi yaya ba ni na kira shi, kawai ganin sa nayi"

    Muktar bai ce komai ba ya ƙarasa tare da sa hannu ya amshi kular, ya kan naki ya ce a nutse lokacin da ya ɗan kalli gefen da take. A hankali ta ce a Alhamdulillah har suka zo gida ba wanda ya yi magana a tsakar gida ya dire kular ya zari buta dan yin alwalar magariba.

    Ana idar da Salla fanadol ya soya gun Mahadi chemist, Garba na hango shi ya fito dags chemist ɗin ya ƙaraso da sauri, ganin sa ya sa Muktar tsayawa.

    Ɗan rissinawa Muktar ya yi kan ya gaishe shi, shiru sukai ns sakanni kafin Muktar ya ce "ka tsaidani?"

    Sosa kai Garba ya yi kan ya ce "dama rokon alfarma zan yi, dan Allah karka yima Hajara faɗa walllahi ba ita ta kirani ba"

    Murmushi Muktar ya yi "Karka damu da zan mata da tuni nayi, shike nan"

    A'a sai kuma roƙon dan Allah ko sau ɗaya a wata ne yaya ka taimaka , kabari ina zuwa taɗi, walllahi zan jira har sa'adda za ta gama karatun kuma bazan hana ta ci gaba da karatun ba, ni kaina bana jin daɗin yadda sai dai in dinga binta hanya"

    Tsai Muktar ya yi da idanun sa kan Garba na sakanni numfashi ya furzar, zan kiraka" ya fada a takaice kafin ya ƙarasa cikin gida, ajiyar zuciya mai nauyi Garba ya furzar Allah ya sani yana masifar shakkar Muktar din duda in zai girmeshi baifi da shekaru kaɗan ba.

    Maganin da ya siyo ya bawa Hajara tare da kara yi mata sannu, ya shige ɗakin sa wayar sa ya ɗauka ya rubutawa Alhaji Ba shir saƙon accepting offer din kafin ya ɗauki wasu Physics test book ɗin sa ya hau dubawa duda ya manta maine akeyi a electricity and magnetism na lvl one, anma ya san dole akwai da yawa cikin littatafan da yake dubawa.....

    Rubutawa

    Aeshakhabir

    Fadimafayau

    Soyayya
    Credit: LuckyTD

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.