Ko da So..... (Kashi na 3)

    In kin karanta ki yi sharing

    "Wai dan Allah Hafsa ke wacce irin mutun ce?, kin kira mutun kince ya zo ya taimaka ya koya mana, kuma ya zo kin ce yunwa kike ji" Bilkisu ta faɗa a fusace cikin faɗa fada.

    Juyowa Hafsa ta yi cikin halin ko in kula "Please Hajiya dena mun ihu, kina ji fa ya ce zai je gun abokin sa ɗan level five ya jira mu ai ko addini ya bawa yunwa haƙƙin ta, in coke village ɗinne ba zaki ba ki je gun sa ku fara" ta faɗa gami da yin gaba ba tare da jiran amsar Bilkisu ba.

    Ƙwafa kawai Bilkisu ta yi tare da bin bayan Hafsa rai ɓace.

    Sai da suka sai lemo da cake sannan suka wuce gun ma su gurasa, Hafsa na son gurasar sosai tun randa ta fara ci shike nan kullum sai ta siya ada ƙyankyamin ta ma take anma tana jin ɗanɗanon ta ƙyankyamin ya bar ta. Suka wuce faculty of engineering ɗin dan can sukai za su haɗu bilayi suka hau yi har Hafsa ta ɗauki wayar ta tana neman Number ɗin sata jiuryar sa na musu magana.

    Shi kuwa zaune yake suna hira da Umar abokin sa lokaci-lokaci yana duba agogo sam baya son jira kawai dai dan yaran sun takura masa ne, kullum ya tuna yaddda suka haɗu sai ya yi dariya, yana zaune yana koyawa Umar Mechanics da yake carrying suka ji muryar ta, ta musu sallama," Ina wunin ku?" ta ce suka amsa da" lafiya ƙalau," ta ɗan sa hannu ta ɗauki takardar gaban su, mintina kaɗan da dubawa ta juya " lah Bilki zo kiga ya iya Physics wallahi" wadda aka kira da Bilkin ta matso "Allah Hafsa ki fita ido na bana son Bilkin nan"

    Dariya Hafsa ta yi " sorry Bilkisu"

    Kallon takardar Bilkisun ta yi "lah walllahi ya iya kuwa"

    Ba tare da wani tunani ba, Hafsa ta ce " kawo wayar ka in sa ma Number ɗin mu dan Allah za ka dinga koya mana walllahi bamu iya ba," kasa magana ya yi ya miƙo mata wayar ta rubuta ta ce " na yi saving Suna Hafsa ita kuma Bilkisu me zan sa, dariya ya sa "Ba shir zaki sa but ni bance zan koya muku ba gaskiya."

    "Dan Allah ka taimaka" ta ce

    "Oktom ba yanzu ba kumin message ɗim sanda kuke da free time zan duba tamu time table in"

    "To mun gode"kawai Hafsa ta ce taja Bilkisu sukai gaba suka bar Umar da Ba shir da mamaki.

    Umar ne ya taɓo Ba shir wanda ke ta murmushi bayan tuna yadda suka haɗu "waɗancan ba yaran da kake jira bane?'" ta taga Ba shir ya leƙo kun gann nan wayar ya Hafsa ta mayar suka haura saman.

    Zaune suke yana faman bayani ya yin da Bilki ta mai da hankali sosai har tambaya take jefawa ya yin da Hafsa ta mai da hankalin ta ga gurasar ta da lemon ta, Ba shir ne ya kalle ta ya girgiza kai kafin ya ce ya ce, “ai sam electricity and magnetism ɗin nan ba shi da wuya amma Hafsah tafi mai da hankali kan gurasar.” Bilkisu ce ta fara dariya " hmm ai in kaga ta mayar da hankali to ta cinye" Bilkisu ta faɗa, amma duda haka ko a jikin Hafsah sai ma kafaɗa da ta ɗage musu, tare da zuƙar lemon da ke hannunta tana kallon yadda yake ci gaba da rubutun yana bayani.

    Kusan awa guda ya yi yana koya musu, ba laifi ta dan tsinci wani abun daga ciki. Ita dai burinta bai wuce ta yi passing ba. ba ta damu sai makin da ta samu ya yi yawa sosai ba tun da shi kadai ne course ɗin da ba ta ganewa ko Organic da 1301 da mutane ke tsoro ba sa razana ta. Sam ba ta so ma ta gayawa Abba cewa ba ta iya ba, yanzu zai ɗaga hankalinsa akan sai ya nemo me nuna mata ita kuma ba ta so ya nemo. Kusan ɓata lokaci za ayi don sam ba ta ƙaunar course din balle ta fahimce shi.

    Sai da me tutorial din ya ba su assignment suka masa godiya tare da ba shi lemo da cake ɗin da suka siyo yaƙi amsa Hafsa ta ajewa Umar gaban sa, sannan suka taso suka tafi.

    “Hnmm wallahi gwara ayi test dinnan mu huta. Duk nabi na gaji da mafarkin course dinnan.” Bilkisu ta fada suna saukowa daga bene.

    “Ke nima.” Hafsah ta ba ta amsa tana hamma. Da alamu ta gaji sosai. Wajen kujeru suke samu suka zauna jiran direban Hafsah.

    Ba su wani jima ba ya zo ya dauke su.

    **

    Tun da Inna Kulu ta ji labarin ya samu aikin nan wani irin farinciki ya lullube ta tana gyara kayan miya tana waƙe waƙen farin ciki, Harira da ta shogo ne ta ce towo ka ce yau za mu yini da yunwa har yanzu ba akai markaɗe ba, kinga Malam ya aikon in siya masa Taliya da wake sai dai ke nan a zuba masa da mai.

    Ɗagowa Inna ta yi tana Murmushi "a'a wannan na gobe ne yanzu nake shirin Hajara ta zo su ɗauki na kaiwa Bakin kasuwar nan kafin rana ta kwalle"

    "Haba koda na ji to na dari biyu za a ban taliyar sai waken hamsin ya ce karasa salak" Harira ta faɗa

    Amsar kwanon da kuɗin Inna ta yi tana ci gaba da ‘yan waƙe waƙen ta, " wai Inna kulu albishir ɗin Hajji aka miki ne?, Tun da na shigo na gane kina cikin farin ciki"

    Dariya Inna ta yi " Bari kawai Harira, yaron nan ne yasamu ailki a sa masa albarka"

    Buɗa Harira tasa oh danma ba ni da hanci ai da har gidan mu sai anji, Allah ya dafa ya sa duk mu anfana"

    "Amin kedai Harira Inna ta fada dedai lokacin da take miƙo mata kwanon taliyar"

    Yamma ce lis iska na ƙaɗawa a hankali, Wanke wanke sukeyi ita da Saratu bayan sun kammala.

    Saratu ce ta dubi Inna lokacin da ta miƙe dan ɗaukan kwadon kwanunakan “Inna kuma wai Yaya barin gida zai naga Hotoro da Nisa?”

    Shiru Innar ta danyi kan ta amsa. “To ya za ayi shi canjin rayuwa haka yake ai. Zuwa daga nan zuwa inda makarantar take ay ya yi masa nisa.”

    “Toh wurin wa zashi?”

    “Wannan saindai ki jira zuwansa ki tambaye shi.” Nan suka ci gaba da wanke wanken wanda ba yadda basuyi da Innar ba akan ta dena taki sam. ta ce rashin aikin zai saka ta tsufa da wuri. Girki daman ba wahala yake ba ta ba balle a ce ya ishe ta a matsayin aiki.

    Shiru sukayi na dan lokaci akan tabarma, iska na kadawa. Suna zaune ne aka kira sallah duk suka tashi sukayi alwala da tunani barkatai a cikin kawunnan su sam yanzu da sukai maganar barin sa gida sai Inna ta ji ba daɗi ba ta shirya rabuwa da Muktar ba. Ko wannen su yana hasashen yadda rayuwa za ta ci gaba da zuwar musu bayan Mukhtar din ya bar gidan da zama da haka sukai Sallah. Shi din jarumi ne kuma uba ne a gare su. Shi ne katangar gidan shi ya sa suke ganin tamkar idan ya bar to wani gata ko lullubi da zai kare su daga sanyin gari ya bar su. Mutanen unguwar ba kaɗan ba suka sa musu ido ba musanman yadda shi kaɗai ne namiji da yadda suke ciniki sosai. Zagi babu kalar wanda ba a musu. Girman da Mukhtar ya yi ne ya sa ya danyi sauki. Da zarar ya daina kwana kullum a gidan sun san abun zai dawo.

    Su din ana musu kallo da dama. Inna ba irin sunan da ba a kiranta da shi saboda kawai ba ta ƙara aure ba bayan rasuwar mijinta. Kuma sana’ar ta ma ta sayar da abinci da takeyi ance abu take zubawa a ciki shi ya sa magidanta da yawa suke mata ciniki sosai. Yaran gidan kuma ko wacce sai a ce yar mace ce ba wata tarbiyya suka samu ba. Suna tafe ana nuna su a unguwa. Dukka wannan sunyi sauki saboda Mukhtar din da yake da kwarjini da rashin daukar raini daga jama’a.

    **

    Tsaye take gaban mudubi a cikin ɗakin ta wanda yake madaidaici ne tana kwalliya. Ɗakin anyi masa fenti purple da fari, daga gefen gado kuma sticker din bismillah ce da frame din ayatul kursiyy. Dayan bangon kuma stickers din motoci ne wanda suke bala’in burge Hafsah. Dakin bai cika tarkace ba, daga madaidaicin gado sai drawer sa da mudubin kwalliya. Daga gefe kuma wata kujera ce ta ado sai dai Hafsah ta cika ta da kaya. Daga kan takalma ne zuwa hijabai da kayan da ta cire, duk ta loda su a kai. Har jakarta ma da handouts ma anan suke samun masauki shi ya sa suke saurin yagewa. Da zarar ta shigo dakin abun da ta fara cirewa akan kujerar za ta wurga shi.

    Bayan wannan, dakin tsaf yake. ta yi shara kamar ko yaushe haka ma gadonta ta gyara shi tsaf. Daga kasan gadon kwanon abincin da taci ne bayan ta shigo.

    Fitowarta ke nan daga wanka bayan ta tashi daga baccin gajiyar da ta kwaso.

    Tana kokarin zana ‘yar siririyar jagira aka buɗo ɗakin. Ta mudubi ta hango Mummy tana yatsina fuska. Doguwar mace ce, fara mai tsananin kyau wadda a gunta Hafsah ta ɗauko kysu. Sanye take da atamfa gold wadda aka mata dinkin bubu da shi an bi zanen adon da duwatsu masu sheƙi. Hannunta na dama ta ƙawata shi da bangle din gold guda biyu ga zobunan gold biyu a yatsunta. Hannun hagun ta dauke yake da agogo da kuma zoben azurfa. Kamar ko yaushe a cikin kamshi take don tafi bawa kamshin muhimmanci akan kwalliyar fuska. Fuskar ta fayau, sai kyalli da shekin hutu take yi duk da ko hoda babu.

    “Mummy…” Hafsahn ta yi saurin fada tana juyowa kafin mummyn ta fara mita.

    “Hnmm jibi ɗakin mutum kamar ɗakin mahaukata. You should be ashamed of yourself!” Ta faɗa tana sake kallon dakin da har ji take kamar yana karnin datti. Ita macece mai tsafta sosai.

    “Mummy dawowa ta ke nan fa.”

    “Hnmm two hours ago. Toh mutum dai tun da kazanta ya sa a gaba sai ya yi ta yi ai. Ni na fita zan leka boutique naga cinikin yau da aka yi zuwa Magariba.”

    Shiru Hafsahn ta yi.

    “Na san yanzu zaki fara mita. In kina so kya iya zuwa gidan su Hidaya sai na dauke ki can idan na gama. Baban ki sai jibi zai dawo.” Da haka ta fice. Jin an ambaci Hidaya ya sa Hafsahn jin daɗi sosai. Hidaya cousin dinta ce, yar yayar mummy wadda suke sa’anni. Dama sun dade ba su hadu ba. Tun dazu kwalliyar da take yi don ta je ta siyo ice cream ne ta dawo gida ta sha sannan ta duba assignment dinnan taga ko za ta iya. Amma yanzu da Hidaya za su je.

    A gurguje ta gama shiryawa ta saka atamfa ta kashe dauri. Da sauri ta fito ta gaida driver suka fita zuwa unguwar su Hidayan.

    Suna zuwa ta kira ta a waya. Da gudu itama Hidayar ta fito zuwa compound din. Suna tsalle n murna da ihu suka rungume junan su.

    “Longest time, besty!” Ta fada with a strong accent. Hafsah ta tabe baki.

    “Iyayi dai Hidaya. Muje na gaida Ammi.” Da haka suke shige ciki suna hira.

    Rubutawa

    Aeshakhabir

    Fadimafayau

    Soyayya
    Credit: LuckyTD

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.