Ticker

Nazarin Rayuwar Malam Aliyu Ɗanbaba (Aliyu Sha'iri) Da Waƙoƙinsa

Kundin neman digiri na farko (b.a. Hausa) a ƙarƙashin sashen nazarin harsuna da al’adu, jimi’ar tarayya gusau, jihar zamfara, nigeria, 2023

Nazarin Rayuwar Malam Aliyu Ɗanbaba (Aliyu Sha'iri) Da Waƙoƙinsa

NA

SAMIR AMINU MUSA

08109474995

 

AMINCEWA

An amince da wannan kundin binciken na Samir Aminu Musa (1710104013) a kan cewa, ya cika duk ƙaidojin kammalawa da aka shimfiɗa dangane da neman takardar kammala digiri na farko (B.A. HAUSA) a sahen Nazarin Harsuna da Al‘adu, Jami‘ar Gwamnatin Tarayya Gusau.

SADAUKARWA

 Na sadaukar da wannan aiki zuwa ga kakata Malama Rahamatu Abdullahi, da kakana Malam Musa Langaye. Ina roƙon Allah jiƙan sa da rahma, ita kuma ya sa ta gama da duniya lafiya. Amin.

 TSAKURE

Wannan bincike da aka gabatar ya ƙunshi wani ƙwarya-ƙwaryar nazari kan rayuwar Malam Aliyu Ɗanbaba (Aliyu Sha'iri) da waƙoƙinsa tun daga haihuwarsa da tasowarsa da neman iliminsa da kuma rasuwarsa, shirya waƙoƙinsa, da kuma sharhin wasu daga cikin waƙoƙinsa.

GODIYA

 Haƙiƙa dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda bai haifa ba, kuma ba a haife sa ba. Tsira da aminci su ƙara tabbata zuwa ga mafificin halittu cika makin Annabawa Annabi Muhammad (S.A.W), da iyalan gidansa da Sahabbansa da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Ina miƙa godiya ta musamman ga jagoran wannan aiki Dr. Musa Fadama Gummi, bisa irin ƙoƙari da jajircewa da ya yi a kan ganin cewar wannan aiki ya sami kammaluwa. Ba kammaluwa kaɗai ba ya tsaya tsayin daka domin aikin ya sami inganci da ake buƙata. Allah saka masa da mafificin alkairi.

Bayan haka, ina miƙa godiya ta musamman ga ɗaukacin malaman jami'ar tarayya Gusau musamman waɗanda suke a sashen koyar da harsuna da al'adu. Ina jinjina da ban girma gare su bisa irin namijin ƙoƙari da suka yi na ganin mu ɗalibansu mun samu ilimi haɗe da tarbiyya wadda take sahihiya. Malaman sashen koyar da harsuna da al'adu waɗanda na zuƙo daga mashayar iliminsu su ne: Dr. Adamu Rabi'u Bakura wanda yake shi ne shugaban sashe, Dr. Musa Fadama Gummi, Malam Aliyu Rabi'u Ɗangulbi, Malam Isah S Fada, Malam Musa Abdullahi Zariya, Malam Bashir Abdullahi, Malam Abu-Ubaida Sani, Malama Halima Kurawa, Malam, Muhammad Arabi Umar. Allah saka masu da mafificin alkairi.

Haka kuma, ina miƙa godiya ga manyan jigajigan malamammu da suke ziyartar mu daga manyan jami'o'i waɗanda su ma suna da kaso mai yawa da alhaki a kan mu malaman su ne: Farfesa Aliyu Muhammad Bunza wanda yake shi ne shugaban sashe na biyu bayan shugaba na farko Farfesa Ahmed Haliru Amfani, Farfesa Ahmad Atiku Dumfawa, Farfesa Muhammed Abdulhameed Ɗantumɓushi, Farfesa Salisu Ahmed Yakasai, Dr. Nazir Abbas. Daga jami'ar Usumanu ɗan Fadiyo. Sai kuma malamammu daga jami'ar Ahmadu Bello Zariya su ne: Farfesa Magaji Tsoho Yakawada, Farfesa Muhammad Lawal Amin, Farfesa Balarabe Abdullahi, Dr.Muhammad Tahir, Allah saka masu da mafificin alkairi.

Ina kuma miƙa godiya ga mahaifana (Alhaji Aminu Musa Yasuf da Hajiya Faɗimatu Musa) bisa ɗawainiyoyinsu da suka yi a kai na tun daga haihuwata har zuwa yau. Ba su kasa ba wajen ba ni gudunmuwa da abin hannunsu da addu'o'i dare da rana ina roƙon Allah saka masu da mafificin alkairi.

Ina miƙa godiya zuwa ga kakannina Alhaji Musa, Hajiya A'ishatu Allah gafarta mata, da Hajiya Amina. Haka kuma ina miƙa godiya ga yayyena Mukhashinu Aminu Musa, Marwanatu Aminu Musa, ƙannena Samira Aminu Musa, Musa Aminu Musa, Abubakar Aminu Musa Hafizu Aminu Musa, Muhammad Aminu Musa A'isha Aminu Musa. Fauziyya Aminu Musa.

Ina miƙa godiya ga abokaina kamar Aminu Rabi'u, Sirajo Umar, Abdullahi Abdullahi (Ɗan Samu). Haka kuma ina godiya ga malamaina na gida Malam Umar Abbas, Malam, Malam Hamza Abubakar Dr. Sirajo Musa, Liman Saluhu Imam, Malam Jamilu Bello, da sauransu.

Har wa yau ina godiya ga abokanan karatuna da muka sha gwagwarmayar karatu tare irin su:

Alhaji Biliya Abubakar shugaban aji kuma mantor nawa, Sani Adamu (Dr.) Sabitu Sani (kwaleji) Babangida Ahmad Barau (Kagara), Ibrahim Muhammad (Gummi) Muhammad Yahaya (Darawa), Mustapha Ibrahim (Ɗan malam), Isma'il Aminu Adam (Abuja) Hajiya Ruƙayya Yusuf S Fada, Zainab (Maman Prof). Allah saka wa kowa da mafificin alkairi ya sa mana albarka amin.

KUNSIYA

Take -- --i

Amincewa-- ii

Godiya-- iii

Sadaukarwa-- --iv

Tsakure-- v

Kumshiya-- vi

Babi Na Ɗaya

Gabatarwa

1.0       Shimfiɗa -- 1

1.1 Manufar Bincike -- --1

1.2 Hasashen Bincike-- --2

1.3 Farfajiyar Bincike -- --2

1.4 Matsalolin Bincike-- --3

1.5 Muhimmacin Bincike-- -3

1.6 Hanyoyin Gudanar Da Bincike-- 4

1.7 Naɗewa-- 5

Babi Na Biyu

Bitar Ayyukan da Suka Gabata

2.0 Shimfiɗa-- 6

2.1 Bitar ayyukan da Suka Gabata-- 6

2.2 Hujjar Cigaba Da Bincike-- -10

2.3 Naɗewa-- 11

 Babi Na Uku

 Fashin Baƙi A kan Maanonin Da Suka Shafi Tubalan Bincike

3.0 Shimfiɗa-- 12

3.1 Ma’anar Waƙa-- --12

3.2 Ire-Iren Waƙa-- --13

3.3 Rubutacciyar Waƙa -- -14

3.4 Tsarin Rubutacciyar Waƙa -- 18

3.5.0 Hanyoyin Nazarin Rubutacciyar Waƙa ---25

3.5.1 Tarihin Marubuci: -- -25

3.5.2 Ma’aunin Waƙa -- --25

3.5.3 Mabuɗin Waƙa: -- --26

3.5.4 Jigo: -- -28

3.5.5 Warwarar Jigo: -- --30

3.5.6 Salo da Sarrafa -- --30

3.5.6 Zubi da Tsari: -- --30

3.5.7.1 Salon Karin Magana-- -33

3.5.7.2 Salon Hoto Cikin Bayani-- 34

3.5.7.3.1 Kamancen Fifiko-- -35

3.5.7.3.2 Kamancen Daidaito-- -35

3.5.7.3.3 Salon Kamance-- -35

3.5.7.3.4 Kamancen Kashi Ko Kasuwa----36

3.5.7.4 Salon Jinsantarwa-- 37

3.5.7.4.1 Mutuntawa -- --37

3.5.7.4.2 Dabbantarwa -- --37

3.5.7.4.3 Abuntarwa-- --38

3.5.7.5 Salon Kambamawa-- -39

3.6 Naɗewa-- 39

Babi Na Huɗu

 Nazarin Rayuwar Malam Aliyu (Ɗanbaba Aliyu Shairi) Da Waƙoƙinsa

4.01 Shimfiɗa-- 40

4.1 Taƙaitaccen Tarihin Malam Aliyu Ɗanbaba---40

4.1.1 Haihuwarsa-- -42

4.1.2 Ƙurciyarsa da Tasowarsa da Neman Iliminsa--42

4.1.3 Yaransa -- 43

4.1.4 Yawace-yawacensa-- 44

4.1.5 Shirya Waƙoƙinsa-- -44

4.1.6. Rasuwarsa-- --47

4.1.7 Matsayin Aliyu Ɗanbaba A Tsakanin Marubuta Waƙoƙin Da da na Yanzu-- --48

4.2.1 Koyon Waƙarsa -- --48

4.2.2 Nau’o’in Waƙoƙinsa -- -48

4.2.3 Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa-- 52

4.2.4 Zubi Da Tsarin Waƙoƙinsa-- 53

4.2.5 Jigon Waƙoƙinsa-- --58

4.2.6 Warwarar Jigon Waƙoƙinsa-- 58

4.2.7 Salon Sarrafa Harshe-- -61

4.3.1 Nazarin Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa ---62

4.3.2 Waƙar Yabon Islahuddini-- 63

4.3.3 Nazarin Waƙar Yabon Liman Aliyu---70

4.3.4 Nazarin Waƙar Bulaliya -- 74

4.3.5. Naɗewa-- 79

Babi Na Biyar

Sakamakon Bincike

5.0. Shimfiɗa -- --66

5.1 Sakamakon Bincike -- 66

5.2 Shawarwari -- --68

5.3.Naɗewa-- --69

Manazarta-- -71


Babi Na Ɗaya

Gabatarwa

2.0       Shimfiɗa

 Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Maɗaukakin sarki, wanda a cikin ikonsa ne da iyawarsa da baiwarsa ya halicci ɗan Adam har ya ba shi hankali, da harshe da hazaƙa. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga mafificin halitta da hikima Annabi Muhammad (S.A.W). A wannan babin za a kawo manufar bincike da hasashen bincike da matsalolinsa. Haka za a bayyana muhimmancinsa da hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da binciken daga ƙarshe a zo da naɗewa.

1.1 Manufar Bincike

 Manufar wannan bincike ita ce samar da wani kundi da zai ƙunshi nazari a kan rayuwar malam Aliyu Ɗanbaba (Aliyu sha’iri) da waƙoƙinsa tare da fito da jigogin waƙoƙin da salailansu domin a haɓaka adabin Hausa.

Nazari a kan marubuta waƙoƙin Hausa abu ne da aka daɗe ana yin sa ko kafin a yi wannan nazarin amma an ce “kowane bakin wuta da nasa hayaƙi kasancewar wannan marubuci ba a samu wani aiki da aka yi a kansa ba wannan ya ƙara ba mu ƙwarin guiwa wajen yin nazarin rayuwar malam Aliyu sha’iri da kuma waƙoƙinsa gwargwadon abin da Allah ya ba da ikon yi. Bayan haka tabbas manufar wannan bincike ita ce taimakawa wajen raya adabin Hausa, da kuma bar wa na baya tarihi da abin koyi da ƙara ƙarfafa su don su tashi tsaye tsayin daka domin ganin an ci gaba da raya wannan adabi na Hausa.

1.2 Hasashen Bincike

 An yi hasashen cewa, idan wannan aiki ya samu kammaluwa zai taimaka wajen raya harshen Hausa don haka ya sa muka zaɓi rubuta kundinmu game da nazarin malam Aliyu sha’iri da waƙoƙinsa. Domin waƙoƙin Hausa na da muhimmanci ƙwarai ga rayuwar Hausawa. Waƙa ta baka ko rubutatta, kamar yadda aka sani tun ba yau ba, ita ce hanya mafi sauƙi da ake bi wajen isar da saƙo ga jamaa.

 A ƙarshe, muna hasashen bincikenmu zai ba mu damar cika ƙaidojin da aka shimfiɗa na neman takardar shaidar digiri (B.A. Hausa) a sashen nazarin harsunan Najeriya a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau.

1.3 Farfajiyar Bincike

 Aikin binciken da za a gudanar ya shafi waƙoƙi rubutacci ne na Hausa. Saboda haka za a yi nazari ne a kan malam Aliyu Ɗanbaba (Aliyu shairi) da waƙoƙinsa daga farko har zuwa ƙarshen aikin.

Haka kuma, aikin zai tsaya a farfajiyar jigogi da salailai na waƙoƙinsa. Haka kuma binciken zai zaƙulo yanayin rayuwar malam Aliyu Sha’iri musamman yadda ya koyi waƙa da ire-iren waƙoƙinsa.

1.4 Matsalolin Bincike

 Kamar yadda aka sani cewa babu wani aiki da za a gudanar ba tare da an yi karo da matsaloli ba nan da can, musamman a kan aikin bincike. Malam Aliyu Sha’iri ya yi fice a kan kawo cigaban addini da kuma harshen Hausa ta fannin adabi rubutacce. Amma manazarta da masu bincike ko nazari a kan harshen Hausa ba su mayar da hankali ba wajen bincike ko nazari a kan malam Aliyu Sha’iri da waƙoƙinsa. Kuma koda an yi ba su yi yawa ba. Wannan ya sa na ci karo da matsaloli daban-daban a kan wannan binciken.

 Ganin irin matsalolin da na fuskanta wajen wannan bincike, ya ƙara ba ni ƙarfin guiwa ganin cewa manazarta ba su yi yawa ba a wannan fagen bincike. Don haka wannan aikin zai taimaka ma na tafe masu sha’awar nazari a akan malam Aliyu Sha’iri da waƙoƙinsa.

1.5 Muhimmacin Bincike

 Muhimmancin bincike shi ne bayyana matsayi da fasahar da ke akwai a cikin waƙoƙin malam Aliyu Shairi, dangane da haka, waƙoƙin malam Aliyu Shairi wani babban madubi ne na kallon rayuwar Hausawa ta fuskar addini da rayuwa, sannan kuma idan Allah ya so waɗannan waƙoƙi za su zama dalili na haɓakar adabin Hausa, da kuma taskace shi. Haka kuma muhimmancin wannan bincike ya haɗa da yin sharhi game da ma’ana a kan waƙoƙin malam Aliyu Sha’iri a ƙasar Hausa.

1.6 Hanyoyin Gudanar Da Bincike

 Hanyoyin da aka bi don gudanar da wannan bincike su ne:-

Ganawar da aka yi da iyalansa ido- da-ido kamar mai ɗakinsa malama Maimuna da ɗansa malam Lawwali a garin Talata Mafara 10- 02- 2023 a gidan shi marigayi malam Aliyu Sha’iri da ke garin Talata Mafara.

 Sannan kuma an gana da wasu abokanan karatunsa kamar Liman Sani a gidansa da ke garin Talata Mafara 22-02-2023. Alhaji Maidaga a gidansa da ke garin Talata Mafara 15-02-2023. Haka zalika an gana da malam Naziru a gidansa da ke garin Talata Mafara 15-3-2023. Da kuma malama Rabi'atu a gidan malam Ibrahim mai Li'irabi da ke garin Talata Mafara 21-3-2023

1.7 Naɗewa

 Wannnan babi wanda shi ne na farko a cikin tsarin wannan aiki an kawo abubuwa da dama wanda suke su ne muhimman bayanai na shimfiɗa. Da farko an kawo gabatarwa da shimfiɗa, Manufar Bincike, Hasashen Bincike, Farfajiyar Bincike, Matsalolin Bincike, Muhimmancin Bincike, Hanyoyin Gudanar da Bincike da kuma Naɗewa.

Babi Na Biyu

Bitar Ayyukan da Suka Gabata

2.0 Shimfiɗa

 Wannan babi wanda shi ne na biyu a cikin tsarin wannan aiki za mu kawo abubuwa waɗanda suke su ne muhimman bayanai kamar haka: shimfiɗa, bitar ayyukan da suka gabata, hujjar cigaba da bincike, da kuma naɗewa.

2.1 Bitar ayyukan da Suka Gabata

 Hausawa na cewa “waiwaye adon tafiya” duk aikin za a yi, ya kamata a yi bitar ayyukan masana da manazarta da suke da alaƙa da wannan aiki ko suka yi kama da shi, da nuna hanyar da suka bambanta da wannan aiki. An nazarci kundaye, da litattafai. Ayyukan da aka nazarta waɗanda ke da nasaba da wannan aiki su ne:

 Kabiru (1982), a cikin kundin digirinsa na farko, ya yi tsokaci ne a kan yadda ake nazarin rubutattun waƙoƙi, a inda ya fara da kawo tarihin marubucin waƙa, da yadda ake tsara waƙa har wa yau, ya ƙara da bayyana irin salon sarrafa harshe da ake amfani da shi.

 Kadage (1982), a cikin kundinsa na farko ya yi tsokaci ne a kan bambancin da ke tsakanin waƙar baka da rubutacciyar waƙa inda yake cewa Waƙar baka duk da yake waƙa duka waƙa ce, amma duk da haka akwai waɗansu hanyoyi da akan bi domin a gane wannan waƙa ta baka ce ko rubutacciya ce, waƙar baka ita ce waƙar da ake rerawa da baka, kuma ba a fuskar takarda take ba, ba a rubuce ba. Waƙar baka tsohuwa ce domin kuwa tattare take da daɗaɗɗen tarihi na halitta, wato ke nan tun da ɗan Adam ya fara furuci ya fara rera waƙa da baki, amma ita kuwa rubutacciyar waƙa ta kasance ita kanwa uwar gami a wajen waƙar baka. Saboda haka ɗan Adam ya daɗe yana tsara waƙa da ka, yana kuma rera ta da baki. Wannan tarihi ya nuna cewa rubutaciyyar waƙa a Hausa ba ta fi ƙarni biyu zuwa huɗu da samuwa ba.”

 Ikara (1983), a cikin kundin bincikensa ya bayyana tarihin waƙa da jigo da zubi da salon sarrafa harshe.

 Yakawada (1987), ya yi bayanin salon sarrafa harshe a waƙoƙin Aliyu Namangi, haka kuma ya yi amfani da salon saɓi zarce ko kuma ɗinkin baiti, wato shi ne zarcewar jumla daga wani layi ko ɗango zuwa mai bi masa, ba tare da katsewar tunani ba. Misali a waƙar Infiraji ya bayyana yadda yake ɗinkin baiti kamar haka:

“Na taho Manzon ina gaishe ka,

 Zaɓaɓɓen isasshe, 

Kar ka bar sheiɗan ya ɓasshe ni don

 Haka ko da yaushe,

Na tuna ka ba nai baƙin ciki ba.

Haka kuma ya kalli jigo da warwarar jigo da salon tsari da kuma salon sarrafa harshe tare da yin amfani da adabin baka kamar su: karin magana, kirari, sannan ya ƙara da adon harshe irinsu, mutuntawa, siffantawa, tamka, kwalliya da kuma ƙarangiya.

 Hauwa (2011) a kundin bincikenta na digiri na biyu ta yi aikinta ne a kan marubuta waƙoƙin mata amma a kan waazi da kuma irin gudunmuwar da mata suke bayarwa a rubutattun waƙoƙi.

 Suleiman (2011), a kundin bincikensa na digiri na biyu, ya kawo kwatancin rubutattun waƙoƙi ne guda biyu na waɗansu mashahuran malamai waɗanda suka yi rayuwa a lokuta mabambanta, malam Shi’itu Ɗan Abdurrauf ya yi rayuwarsa ne a ƙarni na sha tara (19 century) ya rubuta waƙa mai suna Ajizi Azimi a in da ya bayyana maanarta da cewa (Ƙwazon gajiyayye), saannan Aliyu Namangi wanda ya rayu a cikin ƙarni na Ashirin (20), ya kuma yi wata waƙa mai suna Kanzil Azimi wadda ya ba ma’ana da cewa (Babbar Taska). Wannan marubuci ya yi ƙoƙarin kwatanta waɗannan waƙoƙi guda biyu ta hanyar nuna, ko kuma fito da manufar kowanensu.

 A’isha (2016) a cikin kundin bincikenta na digiri na farko ta yi aikinta ne a kan shahararren marubucin waƙoƙin nan Malam Ahmad Maƙari Da Waƙoƙinsa, inda ta bayyana taƙaitaccen tarihinsa,

tun daga haihuwarsa har zuwa tsufansa, an bayyana yadda yake tsara waƙoƙinsa da jigogin waƙoƙinsa ta fuskar sarrafa harshe.

 Nura (2016) a kundin digirinsa na farko ya yi aikinsa ne a kan Malam Ibrahim Bin Ahmad Kabara (Natsugunne) Da Waƙoƙinsa, a nan ma an bayyana tarihin marubucin tun daga haihuwarsa har zuwa tsufansa, kuma an bayyana yadda yake tsara waƙoƙinsa da jigogin waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa ta fuskar sarrafa harshe daga ƙarshe aka yi nazarin wasu daga cikin waƙoƙinsa.

 Ibrahim (2019) a kundin bincikensa na digiri na farko ya yi nazari ne a kan Malam Nasiru Kabara Da Waƙoƙinsa, ya bayyana rayuwar Malam Nasiru Kabara tun daga haihuwarsa har zuwa tsufansa da kuma irin gwagwarmayarsa, tare da bayyana yadda tsarin waƙoƙinsa yake da kuma yin nazarin wasu daga cikin waƙoƙinsa ta fuskar jigogin waƙoƙin da salailansu.

 Hussaini (2021), a cikin kundin bincikensa na digiri na farko, ya yi aikin bincikensa ne a kan fasihin makaɗin nan ne Alhaji Ɗan Balade Morai. An bayyana tarihinsa tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa, da kuma yadda yake tsara waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa, a ƙarshe aka yi nazari a kan wasu daga cikin waƙoƙinsa.

 Yahya (2001) a cikin littafinsa mai suna “Salo Asirin Waƙa a ciki ya yi bayanin maanar salo a cikin waƙa. Sannan kuma ya bayyana muhimmancin salo, bayan wannan kuma ya yi bayani a kan sauran dabarun sarrafa harshe kamar jinsarwa, kamance, kinaya, zayyana da makamantansu.

 Bisa la’akari da ayyukan da suka gabata, na kundaye har zuwa litattafai, za a samu cewa ba wani aiki da ya yi daidai da nawa, saboda an yi wasu ayukka a akan wasu marubuta waƙoƙi daban-daban. Don haka a nan za a yi nazari ne a kan rayuwar Malam Aliyu Sha’iri da waƙoƙinsa.

 Daga ƙarshe an dubi waɗannan ayukka ne domin a ga yadda magabata suka gudanar da bincike, da kuma abin da bincike ya ƙunsa da irin hanyoyin da ya kamata mai bincike ya bi da kuma kariyar harshe daga salwanta.

2.2 Hujjar Cigaba Da Bincike

 Za a cigaba da wannan bincike ne sakamakon ba wani aiki da aka taɓa samu wanda aka aiwatar a kan wannan marubuci Malam Aliyu Sha’iri. Bayan bitar ayyukan da aka aiwatar masu alaƙa da irin wannan aiki nawa.

Saboda haka idan Allah ya so za a shiga cikin wannan aiki a aiwatar da shi gwargwardon abin da Allah ya sawwaƙe.

2.3 Naɗewa

 Wannan babi a cikinsa ne aka kawo bitar ayyukan da suka gabata, a inda aka fara shi da shimfiɗa aka yi tsokaci a kan wasu kundayen kammala karatu da litattafai na magabata, duk a cikinsa ne aka kawo hujjar cigaba da wannan bincike, da kuma naɗewa.

  Babi Na Uku

 Fashin Baƙi A kan Maanonin Da Suka Shafi Tubalan Bincike

3.0 Shimfiɗa

 A wannan babi za a kawo ma’anonin da suka shafi taken bincike, waƙoƙin da Malam Aliyu Shairi ya rubuta na Hausa dukkaninsu rubutattu ne, don haka wannan babin zai garzaya wajen masana don nemo maanar waƙa ire-irenta haka kuma a fito da tsarin rubutacciyar waƙa, da kuma hanyoyin da ake nazarin ta.

3.1 Ma’anar Waƙa

 Waƙa ɗaya ce daga cikin manyan rassan adabi, kuma fage ne da ya fi kowane fage farin jini a wajen masana da manazarta. Wannan ya sa masana da manazarta kowa yake ƙoƙarin tofa albarkacin bakinsa dangane da ma’anar waƙa. Maanar waƙa daga bakin masana da manazarta a iya rubuta manya-manyan litattafai masu tarin yawa ba tare da ƙure fagen ba, don haka za mu taƙaita daga bakin masana kamar su:

 A.B. Yahya {1991,sh.3} ya ce " Waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba, wadda ke ƙunshe da wani saƙo a cikin zaɓaɓɓun kalmomi waɗanda aka auna domin furucinsu ya yiwu ba tare da tuntuɓe ba."

 M.B Umar a cikin Muhammad {2019,sh.1) ya ce "Waƙa Bahaushiya ita ce, nau'in sarrafaffen harshe da ake gabatarwa da shi ta sigar gunduwoyin zantuka da ake kira baitoci ko ɗiyoyi waɗanda ake ginawa a kan kari ƙayyadadde, kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman."

 Ɗangambo {2008, sh.6} cewa ya yi “Waƙa wani saƙo ne da ake gina shi kan tsararriyar ƙaida ta baiti da ɗango da kari {bahari} da amsa-amo {ƙafiya} da sauran ƙaidojin da suka shafi daidaita kalmomi da zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle hakan suke a maganar baka ba.”

 Sa'id, {2016, sh.xi} ya ce "Waƙar Hausa wani fanni ne na hikimar tsara kalmomi masu rauji bisa ƙa'ida, wanda yake kuma baiwa ce daga Allah."

3.2 Ire-Iren Waƙa

 Dangane da ire-iren waƙa kuwa, masana sun kasa waƙa gida biyu wato waƙar baka, da kuma waƙa rubutacciya. Daga cikin masanan da suka karkasa ko kawo ire-iren waƙa akwai:-

 Ɗangambo,{2007, sh.5} ya ce "Ya kamata mu tuna cewa akwai waƙoƙi iri biyu wato: Rubutacciyar waƙa da waƙar baka wato waƙar makaɗa."

 Sa'id, {2016, sh.xi} ya ce "Waƙar Hausa iri biyu ce: akwai waƙar baka, akwai kuma waƙa rubutacciya. Waƙar baka ba a san ta da wasu tsayayyun ƙa'idoji ba, amma ita rubutacciyar waƙa ana tsara ta ne a bisa wasu shifiɗaɗɗun ƙa'idoji.

3.3 Rubutacciyar Waƙa

 Rubutacciyar waƙa ta Hausa ta samo asali ne sakamakon cuɗanya ko zuwan Larabawa ƙasar Hausa domin saye da sayarwa da kuma yaɗa addini. Dangane da ma’anar rubutacciyar waƙa kuwa, wasu daga cikin masana sun ba da maanoni da dama daga cikin su akwai:

 Mukhtar {2005,sh.2} ya ce "Rubutacciyar waƙa wata hanya ce ta gabatar da wani saƙo a cikin ƙayyadaddun kalmomi da aka zaɓa, waɗanda ake rerawa a kan kari da ƙafiya a cikin baitoci."

 Sarɓi {2008,sh.1}, ya bayyana ma’anar rubutacciyar waƙa da cewa Wani saƙo ne da aka gina shi cikin tsararriyar ƙaida na baiti da ɗango da kari da amsa-amo da sauran ƙaidojin da suka danganci daidaitattun kalmomi da zaɓarsu tare da yin amfani da su a rubuce sannan a rera su lokacin da ake buƙata.

 Hiskett {1975}, da Sa'id {1978} "Rubutacciyar waƙar Hausa ta samo tsari ne na kai-tsaye daga waƙoƙin Larabci, domin malaman Musulunci na Daular Usmaniyya su ne suka fara rubuta waƙoƙin Hausa a bisa tsarin waƙoƙin Larabci yadda za su ilmantar da al'umma addinin Musulunci cikin sauƙi, su kuma sami damar karkatar da nunaninsu daga sha'awar waƙoƙin hululu, su koma wa rera waƙoƙin addini da wa'azi da faɗakarwa. Da ma kuma Hausa harshe ne da za a iya auna kalmominsa a waƙe, kamar yadda ake auna waƙoƙin Larabci." Sa'id {2016, sh.xi}

 Rubutacciyar waƙa hanya ce ta isar da saƙo ga alumma wadda ake amfani da zaɓaɓɓun kalmomi tare da amsa-amo {ƙafiya} da kuma amfani da kari {bahari} don jan hankalin mai sauraro ko karantawa.

 Dangane da tarihin samuwar rubutacciyar waƙa a ƙasar Hausa kuwa, Ruƙayya {2008} ta ruwaito Saadatu {2005}, ta ce Tarihi ya nuna an fara samun rubutattun waƙoƙin Hausa tun a ƙarni na sha bakwai {17} A national archives Kaduna, an samu waɗansu waƙoƙi waɗanda ake kyautata zaton a wannan ƙarnin na sha bakwai {17} aka yi su cikin rubutun ajami, bayan zuwan Musulunci, daga cikin waƙoƙin da aka samu akwai: Shi’ir Hausa, Jumiyyah waɗanda Shaikh Ahmad Abdul Ƙadir Tofa ya yi su, sannan kuma akwai wata waƙa mai suna Sartse ta Malam Ali Abubakar Ƙutun Kura. Sannan kuma akwai wasu waƙoƙi guda uku waɗanda aka haɗe su aka ba su suna ɗaya waƙar Hausa.”

 A cikin wannan ƙarni na sha bakwai {17} ne aka samu wasu shahararrun malamai guda biyu waɗanda su ma sun rubuta waƙoƙi na Hausa a wannan ƙarni su ne: Wali Ɗan Marina, Wali Ɗan Masani daga cikin ayukkan da Wali Ɗan Marina ya yi akwai Daliyya’ da Nuriyya da waƙar Sharrin taba; haka kuma shi ma Wali Ɗan Masani ya rubuta Nafhatul-ambariyya da Sharhin Ishiriniyya alfazazi da sauransu.

 A cikin ƙarni na sha takwas {18} an sami cigaba da rubuta waƙoƙin Hausa domin a wannan ƙarni ne aka sami aikin su Malam Muhammad Alkatsinawi, da Malam Muhammad Birnin Gwari, da Malam Shi’itu Ɗan Abdurrauf, wanda waɗannan malamai sun rubuta waƙoƙin Hausa cikin ajami, shi ma Malam Shiitu ya rubuta waƙoƙin Hausa daga cikin waɗanda suka shahara misalin su shi ne: Wadar tuba, da waƙar Wawiyya, Jiddul azizu, da sauransu.

 Ƙarni na sha tara {19} nan ne aka sami bunƙasar rubutattun waƙoƙi na Hausa, sakamakon aikin da masu jihadi suka yi, waƙoƙin sun sami tasiri da karɓuwa sosai a wannan lokaci, yawancin waƙoƙin masu jihadi ne suka yi su ƙarƙashin jagorancin Shehu Usman ɗan Fodiyo wannan ya sa ake kiran waƙoƙin wannan ƙarnin da waƙoƙin masu jihadi domin waƙoƙin da aka rubuta a wannan ƙarni an yi su ne a kan jigon addini saboda Musulunci a wannan lokaci ya yi ƙarfi shi ya sa ba a sami wata waƙa ba wadda jigonta ba na Musulunci ba, kuma duk waƙar da aka samu an rubuta wadda ba ta addini ba ana kiran ta da suna fululu wato waƙa maras amfani wannan ya sa waƙoƙin ƙarni na sha tara {19} duk suna da jigon addinin Musulunci ne, Yahya {1988, sh. 36-60}.

 

Muhammad {2019, sh.8-10} ya nuna cewar a ƙarni na sha tara {19} ne aka tabbatar da yawaitar samuwar rubuttun waƙoƙi a ƙasar Hausa. Bayan da Shehu Usumanu ɗanfodiyo shi da jama'arsa suka yi jahadi a ƙasar Hausa, a wannan lokaci an samu marubuta da suke rubuta waƙoƙi domin isar da saƙo da wa'azi daga cikin irin waɗannan marubuta akwai irinsu: Shehu ɗanfodiyo, da ƙanansa Abdullahin Gwandu, da 'ya'yansa kamar Isan Kware, da Nana Asma'u, da dai sauransu.

 Shehu Usmanu da mabiyansa duka waɗannan rubuce-rubuce da suka yi a cikin harshen Larabci, da ajamin Fulatanci da kuma ajamin Hausa suka yi su. Misalin waƙoƙin da aka rubuta, kamar waƙar Shehu Usumanu " Tabban Haƙiƙan" wadda 'yarsa Nana Asma'u ta fassara zuwa Hausa, ɗansa Isan Kware ya yi tahamisinta. Manufar waɗannan waƙoƙi na {Ƙ.19} shi ne yaɗa addinin Musulunci.

 A ƙarni na {Ƙ.20} an samu sauye-sauye domin kowane zamani yana nuna hoton mutanen wannan zamani ne. Shigowar baƙin al'adu, to a duk lokacin da wata al'ada ta kutso kai a cikin wata takan haifar da mutane su ma su canja ko kuma su rungumi wani sashe na baƙuwar al'dar da ta riske su. Wannan ya faru da Hausawa bayan shigowar Turawa a ƙasar Hausa. Wannan ya sa aka samu canji cikin rubuce-rubuce ta fuskar haruffan da ake rubutu a ƙarni na {19} duk rubuce-rubucen da aka yi a cikin harshen Larabci ne da Hausa ajami, amma a ƙarni {20} sai aka sauya saboda samun ilimin boko.

 Saboda haka an samu marubuta waƙoƙi a wannan ƙarni na {20} da suka haɗa da Sarkin Zazzau Aliyu ɗan Sidi, da Malam Aliyu Namangi Zariya, da Malam Sa'adu Zungur, da Alhaji Billo Giɗaɗawa Sakkwato, da Malam Garba Gwandu da Alhaji Sambo Wali Sakkwato, da Malam Nasiru Kabara, da Mudi Sipikin, da Na'ibi Sulaiman Wali da Alhaji Abubakar Ladan Zariya, da Malam Ɗahiru Musa Juhun, da Haruna Aliyu Ningi da sauransu. Haka zalika jigogin waɗannan waƙoƙi na ƙarni {20} sai ya cuɗanya ana samun jigon addini, sannan kuma ana sumun abin da ba addini ba kamar soyayya siyasar duniya da dai sauransu. An duba Sulaiman {2019, sh.9-10}.

3.4 Tsarin Rubutacciyar Waƙa

 Kamar yadda muka sani kowane abu yana da tsari ko siga, ko kuma matakin da ake bi wajen samar da wannan abu to ita ma waƙa rubutacciya tana da tsari wanda kuma shi ne ya bambanta ta da waƙar baka, idan muka ɗauki ma’anar da Sarɓi {2007, sh.1} ya bayar ta rubutacciyar waƙa da ya ce Wani saƙo ne da ka gina shi a kan tsararriyar ƙaida na baiti da ɗango da kari da amsa-amo da sauran ƙaidojin da suka danganci daidaitattun kalmomi da zaɓarsu tare da yin amfani da su a rubuce sannan a rera lokacin da ake baƙata.

Sarɓi {2007, sh. 50-66} ya kawo tsarin rubutacciyar waƙa kamar haka:

v  Mabuɗin Waƙa

v  Farawa da Bisimilla {sunan Allah}

v  Farawa da Godiya ga Allah ko Annabinsa

v  Farawa da yabo ko salati ga Annaabi {S. A. W}

v  Farawa da Addu'a

v  Jinkirta Mabuɗi

Bari a bayar da misalin abin da ake nufi da jinkirta mabuɗi saboda su biyar na sama akwai misalansu zuwa gaba a cikin Hanyoyin nazarin rubutacciyar waƙa da aka kawo. Misalin jinkirta Mabuɗi shi ne:

A waƙar Aƙilu Aliyu mai suna Saƙo a Hannun Mumini

 1. Saƙo a hannun mumini,

 Zai kai shi ba wani bimbini.

 2. Ni na kira sarki gwani,

 Wannan da ya samar da ni.

A nan an samu jinkirta mabuɗi maimakon a fara da baiti na biyu a matsayin na farko sai aka jinkirta shi zuwa baiti na biyu da marubucin ya ce " Ni na kira sarki gwani". Kamar yadda aka gani wannan shi ake kira jinkirta mabuɗi.

7- Rashin Mabuɗi

Misali A waƙar Aliyu ɗan Sidi ya fara da faɗar

Aboka zo nan mu bata,

Ka dubi ɗan ɗai ga wata,

Wada daban da batta,

Haske na rana da wata,

 Ba za su zamo daidai ba.

A nan idan an lura kai tsaye aka shiga waƙar babu mabuɗi kamar addu'a ko yabon Allah ko salati ga Annabi {S. W. A}, to irin wannan shi ake kira rashin mabuɗi a cikin waƙa rabutacciya.

8- Makullin waƙa

 Misali a waƙar Na'ibi Sulaiman Wali ta Gargaɗi Don Falkawa

 36. Na gode Allah nai yabo,

 A gare shi a nan zan dakata.

 37. Tsira da aminci rabbana,

 Ga rasulu da ya hana yin fuce.

 40. Tamat yau waƙa ta cika,

 Allah sa mu mu bar son yin fuce.

Wannan shi ake kira mukullin waƙa a yi yabo ga Allah, ko kuma a ce 'tamat' kamar yadda aka ga wannan marubucin waƙa ya yi.

9- Rashin Makullin Waƙa

Misali a waƙar Aƙilu Aliyu ta "Daddaɗan daɗi Saniya"

67. Jama'a daga nan zan dakata,

 In sanya alama in tsaya.

68. Ni naku Aƙilu Aliyu ne

 amsa a wajen mai tambaya.

10- Sunan Marubuci a Cikin Waƙa

 Misali a cikin waƙar Mu'azu Haɗeja ta "Yabon Ubangiji"

 79. Ni ne Mu'azu Haɗeja ni na yi wallafar

 Haza a ƙallu minal ƙalili yabon shi.

Wannan shi ne abin da wannan masani ya kawo dangane da tsari ko sigogin rubutacciyar waƙa.

 Bayan wannan akwai ilimin karin waƙa wanda ake iya rubuta waƙa da shi, wannan ma an aro shi daga harshen Larabci ne.

Bello {2013, sh.10-36} ya kawo karuruwan da ake da su tare da ƙafafun da suke samar da wannan karuruwan kamar haka:

1- Dawil.

2- Madid.

3- Basid.

4- Wafir.

5- Kamil.

6- Hajaz.

7- Rajaz.

8- Ramal.

9- Sari’i.

10- Munsari.

11- Hafif.

12- Mulari’i.

13- Muƙtalib.

14- Mujtas.

15- Mutaƙarab.

16- Mutadarak.

 Ya cigaba da cewa daga waɗannan karuruwa guda goma sha shida {16} da suka samo asali daga waƙoƙin Larabawa guda goma sha huɗu {14} ne aka samu a waƙoƙin Hausa a yanzu, kamar yadda ya jero su ya nuna cewa SARA’I ne da MULARI’I Hausawa ba su amfani da su, sai kuma ƙafafuwa da ake amfani da su wajen samar da karuruwan kamar haka:

 

Fa’ulun

Mafa’ilun

Mafa’alatun

Fa’ilatun

Fa’ilun

Mustaf’ilun

Fa’ilatun

Mutafa‘ilun

Maf’ulatun

Mustaf’ilun

 Dangane da yadda Hausawa suke tsara layukan waƙoƙinsu kuwa, nan ma abin lura ne, domin yana cikin tsarin rubutacciyar waƙa, ya zamana ana iya rarrabe adadin layuka da waƙa take ɗauke da shi, da kuma yadda tsarin layukan suke a cikin baitukan waƙa.

 Sa'id, {2016, sh.38-44} ya ce: "Bincike ya tabbatar da cewa, akwai ire-iren waƙar Hausa guda takwas. Don haka ana jin cewa rubutacciyar waƙar Hausa ba za ta fita daga da'irar waɗannan ire-iren ba. Amma kuma wani lokaci a bisa wasu dalilai, akan sami wasu mawaƙa su saɓa wa wannan tsarin." Ya kawo su kamar haka:

Gwauruwa.

Ƙwar Biyu.

Ƙwar Uku.

Ƙwar Huɗu.

Ƙwar Biyar.

Tarbi’i.

Tahmisi.

Tashɗiri

 Waɗannan su ne yadda tsarin rubutacciyar waƙa yake, kuma shi ne ya bambanta ta da duk wata waƙa wadda ba rubutacciya ba.

3.5.0 Hanyoyin Nazarin Rubutacciyar Waƙa

 Dangane da yadda ake nazarin rubutacciyar waƙa kuwa, masana sun fitar ko sun bayar da yadda mai nazari zai nazarci waƙa cikin sauƙi don fito da wani abu na ilimi a ciki.

Sarɓi {2007, sh.31-180} ya bayyana hanyoyi kamar haka:

3.5.1 Tarihin Marubuci: yana daga cikin abin da ake lura da shi wajen nazarin waƙa a san inda aka haifi mawaƙi, da lokacin da aka haife shi da kuma tarihin asalinsa da nasabarsa, bayan nan sai ƙurciyarsa da matakan karatunsa da kuma fito ko gano harsunan da yake ji da sunayensa ko cikakken sunansa, yana da kyau a san matansa nawa ne, da kuma adadin ‘ya’yansa, in ya rasu ya yi masa addu’a.

 A ƙarshe sai a bayyana tarihin fara rubuta waƙarsa, da abin da ya jawo raayinsa ya fara rubutawa da sunayen waƙoƙinsa.

3.5.2 Ma’aunin Waƙa: wannan fage ne da ake iya gane rubutacciyar waƙa masana sun tabbatar da cewa dole waƙa rubutacciya ta kasance tana da maauni da za a iya gane karinta da shi, da kuma nauin gaɓoɓinta da aka tsara waƙar da su, ta haka ne za a iya gane waƙar ta tsaru, ko kuma ba ta tsaru ba, kuma a iya fito da illolin da ke cikinta. Misali a waƙar Aƙilu Aliyu ta Kadaura Babbar Inuwa.

 Na gaida Manzo Alu su da abokai,

 Mata da 'ya'yaye nake tarawa.

 Na gai da man/ zo Alu su/ da abokai/

 Mata da 'ya/ 'yaye nake/Tarawa/.

 Idan aka lura ƙafa ta ɗaya da ta biyu a layi na ɗaya da na biyu, sun daidaita a kan gaɓoɓi hurhuɗu ko wacce. Amma ƙafa ta uku a layi na ɗaya ta saɓa wa ƙafa ta uku a layi na biyu, kamar haka:

 1 2 3 4 1 2 3 4 1 2 3 4

 Na gai da man/ zo Alu su | da abokai

 1 2 3 4 1 2 3 4 1 2 3

 Mata da 'ya | 'ya ye nake| tarawa|.

Wannan misalai ke nan na ma'aunin waƙa, idan aka yi la'akari da yawan gaɓoɓi, za a iya cewa, layi na ɗaya ya fi na biyu tsayi ko yawan gaɓoɓi.

3.5.3 Mabuɗin Waƙa: kasancewar rubutattun waƙoƙin da aka fara yi na addini ne da ya nuna fara yin komai da sunan Allah ko salati ga Annabi Muhammad {S. A. W} wannan ya jawo duk waƙar da za a rubuta sai an yi ɗayan abu huɗu kamar haka:

Basmala.

Godiya ga Allah {S.W.A}.

Salati ga Annabi Muhammad da Alayensa da Sahabbansa.

Addu’a. Misali

 Farawa da basmala

A waƙar Aƙilu Aliyu ta Kadaura Babbar Inuwa

 1. Bisimillahi da shi nake farawa,

 Kome nake niyyar nufin shiryawa.

 2. Na gaida manzo, Alu su da abokai,

 Mata da 'ya'yaye nake tarawa.

Farawa da godiya ga Allah

A waƙar Lalura ta Shehu Usuman ɗan fodiyo

 Gode Allah bisa ga samun bushara,

 Ahma ash shugabanmu mi ad da saura,

 Wanda an nashi nan da can shi ka tsira,

 Na fa gode ma wanda yab ban basira,

 Nasa addin saninsa dukkan lalura.

Farawa da yabo ko yin salati ga Annabi {S.A.W}

A waƙar Mu yi yaƙi da Jahilci

Ina yin nan salati zuwa

 ga manzon duk halittu.

Farawa da Addu'a

A waƙar Giya ta Maazu Haɗeje

 1. Allah na nemi buɗi gare ka,

 Zan waƙar mashaya giya.

 2. Allah ka daɗan basira gama

 Ko da ba ka ban ba zan godiya.

 Sannan idan an sami waƙa ba ta da mabuɗi, mai nazarin waƙa zai bayyana hakan yayin da yake nazarin.

3.5.4 Jigo: jigo na nufin gundarin saƙon da marubucin waƙa yake son isarwa ga alumma, dole ne mai nazari ya yi ƙoƙarin fito da jigon waƙar a fili tare da kafa ƙwararan hujjoji daga cikin waƙar sannan a nuna wasu baitukan da jigon ya fito ɓaro-ɓaro a ciki. Misali a cikin waƙar Usmanu Ɗanfodiyo "Tabban haƙiƙan wadda Nana Asma'u ta fassara zuwa Hausa kuma Isan Kware ya yi mata tahamisi, an fara da gabatar da furucin jigo har wurare huɗu, wato baiti na 34 da na 41, da na 45, da na 49 kamar haka:

 

 34 Wa'azu an yo shi 'yan'uwa don ku farka,

 Kui ta tsoron Ubangiji kui ta kuka,

 Kun jiya gaskiya fa babu shakka,

 Hakimai masu yin faɗa can ga zakka,

 Gobe a ta zakkace su tabban haƙiƙan.

 41. Wa'azu na anka yo daɗa don ku falka,

 Don ka shirya ma gobe can inda za ka,

 Bari zuwa yanzu-yanzu roƙo a ba ka,

 Mai fa roƙon da yaf faye gobe huska,

 Tai ana ƙarƙare ta tabban haƙiƙan.

Watau idan aka duba waɗannan wurare da aka nuna a sama za a ga duk ana ambaton wa'azi, wanda shi ne babban jigon waƙar.

3.5.5 Warwarar Jigo: a nan ana so ne mai nazarin ya kawo jigon waƙar tare da kawo ƙananan jigogin da marubucin ya yi amfani da su wajen ƙulla waƙarsa, don ganin saƙon ya fito yadda ake buƙata, sannan ya bi ta da sharhin baitukan da ya kawo don ƙarfafa hujjarsa.

3.5.6 Zubi da Tsari: wannan ɓangare ne da mai nazari zai kawo waƙar gaba ɗayanta ya kuma nuna yadda mawaƙi ya zuba tunaninsa a cikin waƙar, da yadda ya tsara ta, ana so ne ya dinga tattaro tunanin mawaƙin, misali ya ɗauka tun daga baiti na ɗaya {1} zuwa na biyar {1-5} mawaƙin ya fara ne da yabon ubangiji daga baiti na (5-15) a nan ya fito da jigon waƙarsa {15-30} sake bayyana manufarsa ya yi, tare da {30-39} sake bayyana manufarsa ya yi, {39- 45} ya faɗi sunansa da shekarar da ya rubuta waƙar, {45-53} ya yi addua ya kuma rufe waƙar tasa. Haka ake so a ga mai nazari ya fito da zubi da tsari waƙa wannan shi zai sa a san ya karanta waƙar sosai daga farko har ƙarshe.

 Amsa-amo: wannan wata gwaninta ce da mawaƙa ke yi a cikin waƙa, amsa amo {ƙafiya} yana zuwa ne a ƙarshen baitin waƙa, wani lokacin yana zuwa ne da wasali ko baƙi, wani lokacin kuma kalma. Dangane da ire-irenta masana sun raba ta biyu kamar haka:

 Amsa-amon ciki/ Ƙaramin amsa-amo,

 Amsa-amon waje/ Babban amsa-amo. Misali

 Ƙaramin amsa-amo: Kamar yadda Dumfawa a laccar aji {2022} ya ce mana "Ƙaramin amsa-amo shi ne gaɓar sautin da kowane layi da ke cikin baitin waƙa ke ƙarewa da ita. Ana samun ƙaramin amsa-amo a waƙoƙi 'yan ƙwar uku ko huɗu ko biyar. Ba a cika samun ƙaramin amsa-amo a waƙa ƙwar biyu ba face idan amsa amonta mai zaman kansa ne". Misalin ƙaramin amsa-amo:

Ya wanda sh ne tun azal,

 Kuma tun azal yake lam yazal,

 She ne Ganiyu bila misal,

 Shi yay yi komai ga shi fal

 Yai lahira yai duniya.

 Shi yai dare kuma yai wuni,

 Yai mai gani da marar gani,

 Yai jahili yai mai sani,

 Yai babba yai ɗan ƙanƙani,

 Kowansu yai masa kishiya.

A waɗannan baitoci an ga cewar kowane layi da ke cikin baitin waƙar na ƙarewa da irin sauti ɗaya, wannan shi ake kira ƙaramin amsa-amo.

Babban Amsa-Amo shi ma Dumfawa a laccar aji {2022} ya ce "Babban amsa-amo shi ne gaɓar sautin da kowane baiti na waƙa ke ƙarewa da ita. Misali:

Bisimillahi na nufi za ni waƙa,

 Bisa maƙiya Muhammadu Annasara.

Muna roƙo ga sarki mai sarauta,

 Mu sami fita mu bar jama'ar Nasara.

 Mutane sun ɗime wansu sun makafta,

 Yawanci sun zamo jama'an Nasara.

A nan wannan gaɓar sauti ta "Annasara" ita ce babban amsa-amo da ake bayani.

Waɗannan su ne nau’o’in amsa-amo {ƙafiya} da ake samu a rubutattun waƙoƙi na Hausa, kuma yana da kyau ga mai nazarin waƙa ya fito da irin amsa-amon da waƙar ke da shi.

3.5.7 Salo da Sarrafa Harshe: wannan ma wata dabara ce da mai nazari ake so ya lura da shi, yana da kyau ya fito da irin salon da marubucin ya yi amfani da shi sannan ya bayyana salon wane iri ne, wato salon miƙaƙƙe ne, ko rago ne, yana da armashi ko ba ya da shi.

 Sarrafa harshe kuma, ana so ne mai nazari ya yi bayani gaba ɗaya na yadda marubuci ya yi amfani da kalamansa wajen rubuta waƙa, kamar su adon harshe, wato {karin magana}, da hoto cikin bayani, da kamanci, da jinsantarwa, da abuntarwa, da dabbantarwa, da kambamawa, da sauransu, sannan mai nazari ya bayyana karin harhen mawaƙi Kananci ne, ko Sakkwatanci, ko Katsinanci, da sauransu. Bari a bayar da misalin irin waɗannan salalai da ake samu a cikin rubutattun waƙoƙin Hausa.

3.5.7.1 Salon Karin Magana

 Karin Magana gajeriyar jimla ce wadda ta ƙunshi ma'ana mai faɗi. Hikima ce da ta shafi fasahar dunƙule magana mai yawa wuri ɗaya.

 Aikin mai nazari shi ne ya gano baitin da aka yi amfani da karin magana watau haƙi ne ga mai nazari ya yi la'akari da irin yadda marubuci ya sarƙa karin magana a cikin waƙarsa. Misali a cikin waƙar yabon Sojojin Nijeriya ta Aƙilu Aliyu.

Baiti na 54 yana cewa:

 1. Duk abin da shukawarka,

 2. Za ka girbe kayanka.

 (Abin da ka shuka shi za ka girba)

 

3.5.7.2 Salon Hoto Cikin Bayani

 Hanya ce ta bayyana wani yanayi mai kama da na wasan kwaikwayo. Dabara ce ta jawo hankali ta hanyar saka wasu mutane ko dabbobi ko wasu abubuwa a wani hali ko bisa wani matsayi waɗanda idan an karanta ko an saurara, za a ga wato yanayin a zuci. Wato a ga kamar ga abin a fili yana faruwa. Misali a cikin waƙar Aliyu ɗan Sidi ta Tabarƙoƙo a baiti na

 

22 Ga wani wai shi ya iya

 Ya je ya jawo igiya

 Ta nannaɗe mai ga wuya

 Yana kira da waiwaya

 Ba za a ɗebe mai ba.

Idan aka lura da wannan misali a cikin wannan baiti za a ga cewa marubucin yana ba da hoton yanayi ko halin wanda yake magana a kansa.

 

 

 

3.5.7.3 Salon Kamance

Kamantawa hanya ce ta kwatanta abubuwa biyu don fayyace irin dangantakar da ke tsakaninsu. Kamance ya kasu kashi uku akwai na daidaito da na fifiko da kuma kasuwa ko kashi.

3.5.7.3.1 Kamancen Daidaito

 Kamancen daidaito shi ne inda marubucin waƙa kan kwatanta wani abu da wani ya ce daidai suke ba wanda ya fi wani. Yana yin wannan ta amfani da kalmomin daidai, ko sai ka ce, ko kamar ko tamkar. Misali

 Waƙar Karuwa ta Maazu Haɗeja

 Dube ta idan tana tafiya, sifarta kamar sifar gafiya.

A wannan misali an yi amafani da salon kamancen daidaito shi ne "kamar" watau marubucin yana so a dubi sifar karuwa kamar yadda aka san gafiya.

3.5.7.3.2 Kamancen Fifiko

Kamancen fifiko shi ne wajen da marubucin waƙa zai kwatanta abubuwa guda biyu amma ya nuna cewa ɗayan ya fi ɗayan. Ana yin wannan ne ta hanyar amfani da wasu kalmomi na nuna fifiko irin ya fi, ya ɗara, ya zarce. Misali a waƙar Aƙilu Aliyu ta Kadaura Babbar Inuwa ya ce:

 Ilimi ga mai shi ya fi babban rumbu,

 Domin hatsin rumbu suna ƙarewa.

A nan marubucin ya kwatanta abubuwa biyu, ilimi da kuma babban rumbu, amma ya nuna ilimi "ya fi" rumbun hatsi ba ma rumbu ba kawai babban rumbu gaba ɗaya.

3.5.7.3.3 Kamancen Kashi Ko Kasuwa

Kamancen Kasawa shi ne yadda marubucin waƙa zai kwatanta abubuwa biyu amma ya ce ɗayan bai kai kamar ɗayan ba. Ana amfani da kalmomi kamar su bai kai ba, wane, wa kaza, da sauransu. Misali waƙar ”Me zan faɗa ne”

 13. Zancen ɗabi'a ko a birnin Sakkwato,

 Aka reni 'ya halinta bai kai naki.

A wannan baitin marubuci ya yi amfani da salon kamancen kasawa ya nuna cewa mace ko a birin Sakkwato da aka sani can ne asalin cibiyar Musulmi to, ko a can aka reni 'ya halinta bai kai na wadda yake yabo watau ya kasar da wadda ba ta kai gare ta ba, ta hanyar amfani da kalmar "bai kai".

3.5.7.4 Salon Jinsantarwa

Salon jinsantarwa wani salo ne da marubuta waƙa ke amfani da shi ta hanyar saka wa wani abu musamman mutum halayya ta wani wanda ba mutum ba. Ana yin haka ne domin fito da wata kama wadda marubucin waƙar ke saka wa abin da yake magana game da shi. Salon jinsantarwa kashi uku ne mutuntawa da dabbantarwa da kuma abuntarwa.

3.5.7.4.1 Mutuntawa

Mutuntawa salo ne da marubuta waƙa ke amfani da shi ta hanyar saka wa dabba ko wani abu wata halayya ta mutum da nufin a dubi wannan dabba ko abun kamar mutum saboda irin halin da mutum da aka ce tana da shi. Misal a waƙar Aƙilu Aliyu ta Duniya Rawar 'Yammata ya ce:

 4. In shari a tai kira Je ka amsa ka jiya.

 A wannan baiti marubucin ya mutunta shari'a ya ba ta halayya irin ta mutum da aka sani da yin magana da ya ce "in shari'a tai kira."

3.5.7.4.2 Dabbantarwa

Dabbantarwa ita ma wani nau'i ne na jinsantarwa, wanda a nan ne marubucin waƙa ke saka wa mutum halayya ta dabba domin a dube shi kamar irin dabbar da aka saka masa halayyarta. Misali a waƙar "Son Maso wani Cuta ne"

 5. In na yo carar zakara,

 Kyarkyarata gun ki take.

A wannan misali marubucin waƙar ya dabbantar da kansa da ya ce "in ya yo carar zakara", mutum ba a san shi da yin cara ba zakara aka sani da wannan sifa haka da ya ce "kyarkyarata gun ki take" kaza aka sani da kyarkyara ba mutum ba wannan shi ake cewa dabbantarwa.

3.5.7.4.3 Abuntarwa

Abuntarwa shi ma wani nau'i ne na salon jinsantarwa. A wannan salo marubucin waƙa na ɗaukar wata halayya ta wani abu wanda ba mutum ba ba kuma dabba ba ya saka wa mutum ko dabba. Misali a waƙar Aliyu ɗan Sidi ta "Tabarƙoƙo" ya ce:

 Na ga shi duk ya kwaɓe,

 Ya yi taɓo ya taɓe,

 Ya yi baƙo ya raɓe,

 Neman jini ga babe,

 Ba za a sa mu nai ba.

A ɗangon farko na baitin, marubucin waƙar yana bayyana yadda ya ga wani mutum ya ce ya kwaɓe. Mutum ba ya kwaɓewa, tuwo ko wani abu mai kama da tuwo shi ke kwaɓewa, saboda haka cewa mutum ya kwaɓe to shi ake kira abuntarwa.

 

3.5.7.5 Salon Kambamawa

Kambamawa shi ne salon da marubucin waƙa zai ƙara gishiri wajen bayyana wani abu ga mai sauraro ko karatu ta hanyar bayyana abin fiye da yadda yake. Misali a waƙar "Allah da kansa ya ƙera 'yar nan Dije"

 23. Ke Dije ni fa ina da tarihinki,

 Mata na Hurul'aini ne asalinki.

A wannan misali a ɗango na biyu nan ne marubucin waƙar ya kambama masoyiyar tasa Dije ya faɗi abin da hankali bai ɗauka cewa Dije matan Hurul'aini ne asalinta. Irin wannan shi ake kira kambamar zulaƙe a cikin nazarin rubutacciyar waƙar Hausa.

Sarɓi {2007,sh.140-150}.

3.6 Naɗewa

 A cikin wannan babi mun fara gabatar da shi ne da taken fashin baƙi a kan maanonin da suka shafi taken bincike an ji raayoyin masana dangane da waƙa, sannan an kawo ire-irenta daga wajen masana, sannan kuma an kalli rubutacciyar waƙa a ƙeɓance, tare da yadda tsarinta yake da kuma yadda masana suke ganin za a bi wajen nazarin rubutacciyar waƙa. Wannan babi na uku abin da ya yi ƙoƙarin kawowa ke nan.


Babi Na Huɗu

 Nazarin Rayuwar Malam Aliyu (Ɗanbaba Aliyu Shairi) Da Waƙoƙinsa

4.01 Shimfiɗa

 A babi na huɗu kuma za a kawo bayanai game da gundarin taken bincike. Wato bayanai a kan malam Aliyu Shi’iri da waƙoƙinsa, a inda muka fara da shimfiɗa game da tarihin malam Aliyu Sha’iri wato haihuwarsa, ƙurciyarsa, da tasowarsa, da kuma neman iliminsa. Haka an zo da bayanai dangane da koyo da fara waƙoƙinsa, da yaransa, da kuma yawace-yawacensa, da yadda yake shirya waƙoƙinsa, da rasuwarsa, da matsayin malam Aliyu Sha’iri a tsakanin mawaƙan da da na yanzu, da nauoin waƙoƙinsa. Babin bai kammala ba sai da aka nazarci wasu daga cikin waƙoƙinsa, inda aka fayyace jigon waƙoƙin tare da warwarar jigo, haka kuma an bayyana salon sarrafa harshe a cikin waƙoƙinsa, sannan kuma aka yi bayanai game da zubi da tsarin waƙoƙinsa daga ƙarshe kuma aka zo da naɗewa.

4.1 Taƙaitaccen Tarihin Malam Aliyu Ɗanbaba

 An haifi Malam Aliyu Ɗanbaba wanda aka fi sani da Aliyu Shairi a garin Talata Mafara. Ya fara karatun allo a wajen mahaifinsa sannan ya wuce garin Gusau domin ci gaba da karatun allo a wajen malam Isa na malam Ango. Ya yi karatun litattafai a wajen malam Ibrahim Mai Li’irabi.

 Malam Aliyu Ɗanbaba mutum ne da aka shaide shi da son addini da kuma nuna ƙiyayya ga maƙiya addini. A wata fira da wasu daga cikin abokanansa na karatun ilimi kamar Liman Sani Talata Mafara ya bayyana mana cewa “shi malam Aliyu duk wanda ka ga yana hulɗa da shi, ko kuma yana kai masa ziyara to ka tabbata malami ne ko kuma almajiri. Kuma malam Aliyu ta ɓangaren ƙungiya yana tare da ƙungiyar Islahuddini kuma mabiyin ɗariƙar Tijjaniyya. Haka kuma malam Aliyu Shairi Allah ya azurta shi da yaya maza da mata da jikoki.

‘ya’yansa maza su ne:

Malam Lawwali

Malam Rabu’u

Malam Jamilu

‘ya’yansa mata kuwa su ne

Malama Zabba’u

Malama Nana

Malama Suwaiba

Haka kuma malam Aliyu sha’iri ya auri mata uku su ne:

Malama Maimuna

Malama Zara’u

Malama A’ishatu

 Malam Aliyu a fagen sana’a manomi ne, kuma yana taɓa wa’azi musamman a ƙauyuka. Haka kuma shi kafinta ne, kuma ya taɓa aikin Bakalori daga shekara ta (1977-1979). A fannin waƙa ta rubutu Malam Aliyu ya shahara, ya yi waƙoƙi masu yawa waɗanda suka haɗa da:

Waƙar Bakalori, Waƙar Alfarma da dai sauransu.

4.1.1 Haihuwarsa

 An haifi malam Aliyu Sha’iri a garin Talata Mafara ƙaramar hukuma da ke cikin jahar Zamfara a cikin wata unguwa da ake kira Gwadara, a shekara ta alif da ɗari tara da arba’in da biyu (1942). An samu waɗannan bayanai daga shi kansa malam Aliyu kafin Allah ya yi masa cikawa a lokacin da ake ganawa da shi yayin da ake rubutun littafin Talata Mafara Jiya da Yau.

4.1.2 Ƙurciyarsa da Tasowarsa da Neman Iliminsa

 Kamar yadda muka yi fira da malam Lawwali wanda yake shi ne babban ɗa magaji a wajen malam Aliyu, ya bayyana mana cewa “kamar yadda al’adar Bahaushe take idan ya haifi ɗa idan ya tasa ya kai lokacin ƙuruciya babansa yana kai shi makarantar allo domin ya koyi ilimin Addinin Musulunci saboda haka, malam Aliyu Sha’iri ya fara karatun Alƙurani mai girma a hannun mahaifinsa mai suna malam Muhammad ana yi masa laƙabi da (Ɗanbaba). Bayan nan mahaifin nasa ya yanke shawarar ya kai malam Aliyu zuwa Gusau wajen malaminsa wanda shi kuma gare sa ya yi karatu, wannan malami shi ne malam Isa na malam Ango, a wajen sa ya sauke Alƙurani mai girma. Bayan ya sauka mahaifinsa ya ji cewa malam Ibrahim mai Liirabi zai wuce da yayansa zuwa Zariya sai ya haɗa shi da ɗansa watau malam Aliyu Sha’iri a can ne ya fara karatun ilimi.”

4.1.3 Yaransa

 Kamar yadda muka sami nusarwa daga malam Lawwali ɗanɗan malam Aliyu Sha’iri cewa akwai wata yayar malam Aliyu tana nan da ranta za mu iya samun wasu bayanai waɗanda shi ba shi da su, wannan datijiya ita ce malama Rabi wadda take mata ce ga malam Ibrahim mai Li’irabi malamin da malam Aliyu ya yi karatun ilimi a wajensa, mun samu ƙarin bayani daga wajen ta cewa malam Aliyu Shairi yana da yara da yake rera waƙa tare da su, suna yi masa amshi daga cikin yaran akwai: Yakubu, da Saluhu, waɗannan yara nasa suna taimaka masa yayin da yake rera waƙar tasa, suna yawace-yawace tare da shi a wasu lokuta har ana ba su sadaƙa.

4.1.4 Yawace-yawacensa

 Kamar yadda aka faɗa a can baya cewa malam Aliyu almajiri ne duka yawace-yawacensa ba su wuce a kan neman ilimi ne da karantar da ilimi ba. Malam Aliyu Sha’iri ya zauna a Bilbil har ma ana yi masa laƙabi ana ce da shi Nabilbil. Haka kuma ya yi yawace-yawace zuwa ƙauyuka domin yin waazi da faɗakarwa, sannan ya yi zuwa Ƙauran Namoda musamman a wajen abokanansa da suke tare a kan tafiya ɗaya da fahimta ɗaya a cikin Addini.

 Malam Aliyu Sha’iri ya yi yawon wa’azi a cikin wasu ƙauyuka da ke cikin Talata Mafara kamar irin Take-tsaba, Mirkidi da dai sauransu. Bugu da ƙari malam Aliyu bai koma ga Mahaliccinsa ba, sai da ya sami damar sauke farali na aikin hajji, saboda haka malam Aliyu Sha’iri ya je ƙasa mai tsalki domin gudanar da iba’dar aikin hajji.

4.1.5 Shirya Waƙoƙinsa

 Kamar yadda muka sani cewa mawaƙa suna da wani tsayayyen tsari na musamman da suke amfani da shi wajen rubuta waƙoƙinsu, to shi ma malam Aliyu Sha'iri yana amfani da irin wannan tsari wajen rubuta waƙoƙinsa misali

a) Mabuɗi (basmala): A nan ana dubawa ne a ga wane irin mabuɗi mawaƙi ya yi amfani da shi wajen buɗe waƙarsa, ko kuma ba a tsara waƙar da mabuɗi ba ma. Mafiya yawan waƙoƙin malam Aliyu suna da buɗi misali

Ya ku musulmi za ni yin fakarwa,

Ga ɗalibai almajirai duka kowa.

Bulaliya ce mai shirin tsalarku,

Ba ta bugawa zahiri na jikinku.

Cikin zukata ne take tsalarku ,

Tana horo don ku gyara halinku.

Dangane da marufi kuwa, waƙoƙin malam Aliyu wasu suna ƙarewa da marufi wasu kuma ba su ƙarewa da marufi.

b) Amsa-amo (ƙafiya): Dangane da amsa amo kuwa (ƙafiya), waƙoƙin malam Aliyu Sha'iri suna tafiya tare da kula da amsa-amo na ciki da na waje (babba da ƙarami).

c) Tsarin Baitocin Waƙoƙinsa: Malam Aliyu Sha'iri waƙoƙinsa mafiya yawa 'yan tagwai ne, amma ana samun mai ƙwar biyar misali

i) Ƙwar biyu ('yar tagwai)

 Duba na sakko babban jigo,

 Allah ya ƙara mai imani.

 Ina nufin haji Garba Ɗanɗa,

 Ya munfiƙu fi hazaddini.

 Ya yi ruwa kuma ya yi tsaka-tsiki,

 Ga taimakon Islahuddini.

 Ya Allah ka tsare muna wannan,

 Ga dukkanin sharrin shaiɗani.

 Misalin wata 'yar tagwai

 Liman Aliyu na ban sha'awa,

 Don bai guruf-guruf na siyasa.

 Bakin shi ba ka jin wata kalma,

 Mugunya da ba a so ta siyasa.

 Bai nuna wai ka zo ka yi fati,

 Da ya zan yana cikin ra'ayinsa.

ii)'Yar Ƙwar Biyar

 Na gode Rabbana mai baiwa,

 Sarkinmu jalla shi adda baiwa,

 Ya rarraba waɗansu da baiwa,

 Ya ba mu malami mai baiwa,

 Dalili na sayyadi mai asali.

 Malam Muhammadu Majtaba,

 Ibnu mu'allimu Isah,

 Allah jiƙan mu'allimu Isah,

 Domin rasulu manzon Isah,

 Don Ɗaha sayyadi mai asali.

Wannan shi ne mafi yawan tsarin da malam Aliyu yake bi wajen shirya waƙoƙinsa.

4.1.6. Rasuwarsa

 Kamar yadda bayanai suka gabata dangane da malam Aliyu Sha’iri, tun daga haihuwarsa har zuwa ƙurciyarsa da yadda ya gudanar da rayuwarsa. Abin da aka sani shi ne cewa kowace rayuwa za ta ɗanɗani mutuwa, haka malam Aliyu ya rasu ranar Alhamis (17) ga watan Rabi’ul Awwal wanda ya yi daidai da 13-10-2021. Kuma yana da shekara (79) a duniya, ya bar mata biyu da ‘ya’ya kamar malam Lawwali malam Jamilu.

4.1.7 Matsayin Aliyu Ɗanbaba A Tsakanin Marubuta Waƙoƙin Da da na Yanzu

 Kamar yadda aka yi bincike a ka cewar ko malam Aliyu Sha’iri yana da wasu abokanai da suke hulɗa da su kan rubuce-rubucen waƙoƙi, amma abin da aka samu na bayanai cewa malam Aliyu galibi a kan abin da ya shafi addini ne yake rubuce-rubucensa saboda haka, idan Allah ya sa ya rubuta wata waƙa yana aikawa zuwa ga abokanansa malamai da almajirai domin su karanta. Haka kuma malam Aliyu ba shi da wata alaƙa da marubuta waƙoƙin wannan zamani domin shi duka waƙoƙinsa a cikin Hausa ajami ya yi su.

4.2.1 Koyon Waƙarsa

 Kamar yadda aka tambayi Malama Rabi’atu matar malam Ibrahim mai Li’irabi malamin malam Aliyu, cewa shin ko malam Ibrahim ya koya wa malam Aliyu rubuta waƙa? Sai ta ce Aa ko alama baiwa ce kawai Allah ya ba shi, malam Ibrahim ya gan sa da baiwarsa ne kawai saboda haka, babu wanda ya zaunar da malam Aliyu ya koya masa rubuta waƙa.

4.2.2 Nau’o’in Waƙoƙinsa

 Kamar yadda bayanai suka gabata cewa malam Aliyu Sha’iri ya yi rubuce-rubucen waƙoƙi musamman a kan abin da ya shafi addini, haka kuma, ya yi a kan abin da ya shafi rayuwa daga cikin nau’ukan waƙoƙinsa akwai:-

Waƙar Yabon Ƙungiyar Islahuddini ya ce:

Duba na sakko babban jigo,

 Allah ƙara mai Imani.

Ina nufin haji Garba Ɗanɗa,

 Ya munfiƙu fi hazad dini.

Ya yi ruwa kuma ya yi tsaka tsaki,

 Ga taimakon Islahuddini.

Ya Allah ka tsare mana wannan,

 Ga dukkanin sharrin Shaiɗani.

Sai babban jigo a gare mu,

 Kun ji turakun ƙauye da birni.

Ai shugaban Islahu na Ƙaura,

 Bai kunyar maƙiyin addini.

Ka sha kabsawa da mutane,

 Kan salla rukunin addini.

Alhaji Sidi abansu Rumaisa,

 Mashin suke maras Imani.

Ka ba su nassi ka ba su shafi,

 Ya jikan kakansu Husaini.

Ya babansu Umar da Sumayya,

 Ya hadimi wurin jelani.

Sai Sufi mai tsoron Allah,

 Ya fitila hasken zamani.

 “Waƙar Yabo Ga Liman Ali ya ce:

Liman Aliyu na ban sha’awa,

 Don bai gurub gurub na siyasa.

Bakinshi ba ka jin wata kalma,

 Mugunya da ba a so ta siyasa.

Bai nuna wai ka zo ka yi fati,

 Da ya zan yana cikin ra’ayinsa.

Limamman ku zo ku kun yi,

 Da liman Aliyu ɗabi’a tasa.

Kowar riƙa shina nan nashi,

 Har wanda bai riƙa bai ƙin sa.

To ƙaddara hukuncin Allah,

 Shi ke izo ma bayi nasa.

Don ɗai ya zan yana jarabawa,

 Domin a gane mai tsoron sa.

Malamai waɗansu sun ƙarnanta,

 Karatunsu sun gama da siyasa.

Sai ɗai a ɗauki ayar Allah,

 Ana fassara ta nan ga siyasa.

 “Waƙar Taaziyyar Yanuwa ya ce:

Na gode Allah da Annabi manzo,

 Fiyayyan halitta mannzo ma’aiki.

Kafi da ya’i da su za ni roƙo,

 Du’a’in da zan yi wurin marigaya.

Allah jiƙan su Inna da baba,

 Da yannansu ƙannansu domin ma’aiki.

Malam Muhammadu Nasiru Bilbil,

 Allah jiƙan shi domin maaiki.

Malam Muhammadu Majimu ba shi,

 Allah jiƙan shi domin maaiki.

Malamai waɗanga an yi hasara,

 Allah jiƙan su domin maaiki.

Malam Musa Tullu Ɗanrini ke nan,

 Allah jiƙan shi domin maaiki.

4.2.3 Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa

 Kamar yadda bayanai suka cewa malam Aliyu sha’iri ya rubuta waƙoƙi da dama, daga cikin wasu waƙoƙin nasa akwai:-

1. Waƙar yan yau

2. Waƙar ɗalibai da malam sunna

3. Waƙar marsiyya ta malam Ibrahim

4. Waƙar sharuɗɗan salla

5. Waƙar sheɗan

 

4.2.4 Zubi Da Tsarin Waƙoƙinsa

 Dumfawa (2022) a laccar aji ya ce "Zubi da tsari shi ne wanda ake duba yadda mawaƙi ya zuba ya kuma tsara baitocin waƙarsa. Wannan shi ya sa wasu suke ce masa salon zubi da tsari. Salon zubi da tsari ya ƙunshi zubin baitoci kamar yawansu da yawan layuka a cikin baitoci da yadda cikon ma'ana ko kalmar wani layi ko baiti ke shiga cikin wani baiti da kuma amsa-amo."

Malam Aliyu yana zuba waƙoƙinsa ne wasu 'yan ƙwar biyu wasu biyar amma ya fi yin zubin 'yar tagwai wato (ƙwar biyu) misali

 Liman Aliyu na ban sha'awa,

 Don bai gurub-gurub na siyasa.

 Bakinshi ba ka jin wata kalma,

 Mugunya da ba a so ta siyasa.

Saɓi zarce

Wannan wani salo ne da cikon ma'anar layin waƙa kan kasa cika sai a cikin layi da ke biye. Kowane layin waƙa kamata ya yi ya zama cikakkar jumla, to idan jumla ba ta cika ba sai a cikin layi mai zuwa shi ake kira salon saɓi zarce a cikin rubutattar waƙa. Dumfawa, (2022)

Irin wannan salo malam Aliyu ya yi amfani da shi a cikin waƙarsa misali

 Bakinshi ba ka jin wata kalma,

 Mugunya da ba a so ta siyasa.

 Bai nuna wai ka zo ka yi fati,

 Da ya zan yana cikin ra'ayinsa.

Salon Ɗinkin Baiti ko Raɓa danni

 Ɗinkin baiti ko raɓa dannin baiti shi ne baitin da ma'anar da ke ƙunshe a cikinsa ba ta cika sai an tsallaka cikin baiti da ke bin sa. Dumfawa (2022).

Irin wannan salo malam Aliyu yana amfani da shi wani lokaci a cikin waƙoƙinsa misali

 32 A rijiyar zaki zan koma

 Akwai Mahir masanin Ƙur'ani.

 33. Ina nufin Shaikhu na musamman

 Bello abin faharin addini.

Babban amsa-amo

Shi ne gaɓar sautuka da kowane baitin waƙa ke ƙarewa da ita.

Malam Aliyu yakan tsara waƙarsa bisa tsari na amfani da babban amsa-amo a wani lokaci. Misali

 10. Tsarin Yahudu wagga siyasa,

 Mai hankali ka gane dasisa.

 11. Kana malami bafaden Allah,

 To mi za ya sa ka zaɓi siyasa.

 12. Wasu kam Yahudu sun halaka su,

 Ƙiyayyarsu yau tana ga siyasa.

Amsa-amo Mai Zaman Kansa

Amsa-amo mai zaman kansa shi ne amsa-amon da ya kasance kowane baitin waƙa yana da nasa amsa-amo na daban.

Malam Aliyu ya ɗora harsashin ginin waƙarsa a kan irin wannan tsari na amsa-amo. Misali

 Gida na malam ba a son a bas shi,

 Wurin karatu kawai ɗiyanai su yi shi.

 A zan ka sauraren karatu nasu,

 Ban da fa girman kai fa ko an fi su.

 A zan nufin Allah da Manzon Allah,

 A samu yarda nan ta sarki Allah.

 

Mabuɗi

A tsarin waƙoƙin malam Aliyu Sha'iri wasu suna farawa da mabuɗi, wasu kuma ba su ba su farawa da shi. Misalin waƙarsa da ya fara ta da mabuɗi kamar waƙar yabon Islahuddini da ya ce

 1. Bisimillahi da sunan Allah

 Sarki jalla gwani mai baiwa.

A wannan baitin ya buɗe ne da basmala, amma kuma a wata waƙar sai ya buɗe da godiya ga Allah da Annabi misali

 1. Na gode Allah da Annabi,

 Fiyayyen halitta Manzo ma'aiki.

 2. Kafi da ya'i da su za ni roƙo,

 Du'a'in da zan yi wurin marigyaya.

 

Marar Mabuɗi misali

 1. Liman Aliyu na ban sha'awa,

 Don bai gurub-gurub na siyasa.

 2. Bakinshi ba ka jin wata kalma.

 Mugunya da ba a so ta siyasa.

Marufi

Wasu waƙoƙinsa suna da marufi wasu kuma ba su da marufi. Misalin mai marufi

 70. Don Islahu ta haɗa kowa,

 Dukkan mai kishin addini.

 Tamat bihadillahi wa husni aunihi.

 Maras Marufi misali

 13. Dut wanda ba ya fati nasu,

 Kamar kafiri suke hangensa.

 30. Sai wanda ya zan nakasa ta kama,

 Ba shi da mai ɗaukan lalura taima.

 31. Shi zan bara nai ban da yin ƙarya ko,

 Shi na ta yi nai ban da cin zarafi ko.

Wannan shi ne misalin yadda malam Aliyu yake zuba ko tsara waƙoƙinsa a taƙaice.

 

4.2.5 Jigon Waƙoƙinsa

Jigo shi ne saƙo ko manufar da marubuci yake son isarwa ga mai karatu ko nazarinsa.

A nan za a duba jigogin waƙoƙin malam Aliyu Sha'iri. Kamar yadda aka gani bayan nazarin wasu daga cikin waƙoƙinsa an ga cewa waƙoƙin duka jigoginsu suna da alaƙa da addini ne kaitsaye ko a fakaice. Misali kamar waƙar yabon ƙungiyar Islahuddini an ga yadda wannan marubuci ya ɗauki manufarsa ta waƙe wasu manyan mutane da suka bayar da gudunmuwa ga wannan ƙungiya ta Islahuddini.

Haka kuma idan aka ɗauki waƙar yabo da ya yi wa Liman Aliyu, za a ga jigonta na yabo ne kan wasu nagartattun halaye nasa. Haka kuma, idan aka ɗauki waƙar Bulaliya da aka kawo za a ga tana ɗauke da jigon faɗakarwa ko gargaɗi musamman ga ɗalibai da almajirai kan su guji wasu munanen halaye, sannan su yi riƙo da wasu kyawawan halaye. Saboda haka waƙoƙin malam Aliyu Sha'iri galibi suna ɗauke da jigogi ne da suka shafi addini kaitsaye ko a fakaice.

4.2.6 Warwarar Jigon Waƙoƙinsa

 Kamar yadda aka gani waƙar da aka fara nazari an yi warwarar jigonta ita da sauran waƙoƙin da aka kawo. Kamar dai yadda aka faɗa mafi yawan jigogin waƙoƙin malam Aliyu Sha'iri sun shafi addini ne.

Waƙar yabon ƙungiyar Islahuddini tana ɗauke da jigon yabo ne kuma wanda ke da alaƙa da addini. Haka zalika, waƙar yabon Liman Aliyu ita ma waƙar yabo ce, domin ya nuna yabawa ga wasu nagartattun halaye na Liman Aliyu misali da ya ce

 

 Liman Aliyu na ban sha'awa,

 Don bai gurub-gurub na siyasa.

 Bakinshi ba ka jin wata kalma,

 Mugunya da ba a so ta siyasa.

 Bai nuna wai ka zo ka yi fati,

 Da ya zan yana cikin ra'ayinsa.

Kamar haka dai ya ci gaba da yabon sa da kyakkyawan harshe.

Sai kuma waƙar da ke ɗauke da jigon faɗakarwa ko gargaɗi watau waƙar Bulaliya. Wannan waƙa ya yi ta ne domin ya faɗakar da masu neman ilimi wasu halaye maras kyau da ya kamata su guje su, da kuma kyawawan halaye da ya dace su yi riƙo da su. Misali

1. Ya ku musulmi za ni yin faɗakarwa,

 Ga ɗalibai almajirai duka kowa.

2. Bulaliya ce mai shirin tsalarku,

 Ba ta bugawa zahiri na jikin ku.

 3. Cikin zukata ne take tsalar ku,

 Tana horo don ku gyara halinku.

4. Dut wanda almajiri ga su malam,

 Shi daina jayayya da 'ya'yan malam.

5. In malamin nan naku ya yi wafati,

 Sai ku riƙe kulan dubu na salati.

Haka dai marubucin ya ci gaba da nusar da ɗalibai da almajirai har ya kai ga cewa

 13. A zan ka sauraren karatu nasu,

 Ban da girman kai fa ko an fi su.

 14. A zan nufin Allah da Manzan Allah,

 A samu yarda nan ta sarki Allah.

To duka idan aka lura jigogin waɗannan waƙoƙi ke nan da suke ɗauke da darasi da abin a yi koyi.

 

4.2.7 Salon Sarrafa Harshe

 Salo yana nufin dabara ko hikima da aka yi amfani da ita domin isar da saƙo.

Dumfawa (2022) a laccar aji ya ce "Salon kwalliya ko sarrafa harshe a cikin rubutacciyar waƙa shi ne amfani da wasu zaɓaɓɓun kalmomi masu ratsa zuciya da marubucin waƙa ke amfani da su cikin hikima da basira domin saka wa mai sauraron sa ko karatunsa ko nazari raha tare da jawo hankalinsa ta yadda zai fahimci saƙon waƙar ba tare da ƙosawa ba."

Masu nazarin waƙa sun saka wa waɗannan salailai sunaye domin bambance kowane nau'i na salo daga wani. Daga cikin fitattun nau'o'in akwai salon kinaya, da kamance, da jinsantarwa, da alamtarwa, da kambamawa, da hira, da dai sauransu.

 Idan aka dubi waƙoƙin malam Aliyu Sha'iri suna ɗauke da wasu daga cikin waɗannan nau'o'in na salo misali

 

Salon Kambamawa

 Salon kambamawa shi ne a faɗi abin da hankali bai iya ɗauka, marubuta waƙa suna yin hakan ne domin su nuna gwarzantawa ga wanda suke yi wa waƙa.

A cikin waƙar yabon Islahuddini malam Aliyu ya yi amfani da irin wannan salo na kambamawa da ya ce:

 24 Ya baharun fi kulli fununi,

 Ya ƙa'ilun riauli irfani.

 25. Ina nufin Shaikhu Bilalu Kano

 Ma'adinun lifumiddini.

 37. Ya kogin ilimi tarbiyya,

 Anta Mudarrisus sibiyani.

 Kamancen Daidaito

 12. Dut wanda ba ya fati nasu.

 Kamar kafiri suke hangen sa.

4.3.1 Nazarin Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa

 Wannan nazari na waƙoƙin malam Aliyu Shairi zai kasance ƙwarya-ƙwaryar nazari ne na jigo da zubi da tsari da salon sarrafa harshe, a cikin waƙoƙin malam Aliyu za a nazarci waƙoƙin ne kamar yadda masana suka bayyana a babi na uku. Da farko za a yi nazari a kan waƙar malam Aliyu da ya yi ta Yabon Islahuddini.

 

4.3.2 Waƙar Yabon Islahuddini

 Kamar yadda bayani ya gabata a cikin bayanin tarihin malam Aliyu Sha’iri

cewa shi mabiyi ne ga wannan ƙungiya ta Islahuddini. Marubucin ya rubuta wannan waƙa ne domin yabo ga ƙungiyar da kuma manyan jagororinta. Haka zalika domin ya nuna manufar wannan ƙungiyar da ci gaban da take kawo ga addinin Musulunci.

1. Zubi Da Tsarin Waƙar: an tsara wannan waƙa ne a cikin baitoci masu layuka biyu -biyu wato yar tagwai ko ƙwar biyu. Haka kuma waƙar tana da baitoci {70}, dangane da ɗangwaye kuwa tana ɗauke da ɗangwaye {140}. Haka kuma, waƙar tana ɗauke da babban amsa-amo na “ni”. Haka zalika, waƙar tana da mabuɗi ta fara da basmala da yabon Ubangiji da godiya ga Allah, da neman daɗin tsira ga Annabi Muhammad {S.A.W}. Misali

 1. Bisimillahi da sunan Allah,

 Sarki jalla gwani Rahamani.

 2. Sai shukarammu ga sarki Allah

 Ya ƙara samu ruƙon addini.

 3. Allah ka yi tsira da aminci,

 Ala Muhammadu ɗan Adinani.

 2. Jigon Waƙar: Dangane da jigon wannan waƙa za a iya cewa wannan waƙa tana ɗauke da jigon “Yabon ƙungiyar Islahuddini da jagororinta.

Marubucin ya bayyana hakan tun a baiti na 4 inda ya ce:

 

 4. Na yi nufin in tsara ƙasida,

 Ta yin yabon Islahuddini.

3. Warwarar jigo: Marubucin bayan ya bayyana manufarsa tun farko sai ya ci gaba da yabon malamai jagororin wannan tafiya ta Islahuddini kamar daga baiti na 10- da ya ce:

 10. Shaikhu Yusufu Ibnu Yahuza,

 Ka yi gadon kishin addini.

 11. Sai jarumi mai halin girma,

 Jagoran Islahuddini.

 12. Zaki ja da ƙarfin Allah,

 Kar ka ji tsoron bawa fani.

Bayan marubucin ya cika abin da ya amabata a matsayin manufa da ya gina waƙarsa a kansa watau yabo ga jagororin ƙungiyar Islahu da ya ce a baiti na 53

 53. Bayan yabo ga malammaina

 Zan yi nasiha gun ikhwanni.

A baiti na 65-66 sai marubucin ya nemar wa wannan ƙungiya tsari daga sharrin shaiɗan da ya ce:

 65. Ya Allah domi Shurafa’u,

 Don kakan su Hassan da Husaini.

 66. Ya Allah ka tsare Islahu,

 Ga dukkanin sharrin Shaiɗani.

A ƙarshe sai marubucin ya kammale da nuna cewa ƙungiyar Islahu ta haɗa kowa idan har mutum mai kishin addini ne yana cikin ta. Ya ce:

 68. In an ce ma wayyi ƙasida

 La tabahal a’ada’addini.

 69. Ce Ibrahim ɗan Abbdullahi,

 Ce mariƙin wuridin Tijjani.

 70. Don Islahu ta haɗa kowa,

 Dukkan mai kishin addini.

4 Salon Waƙar: Salo dabara ce da marubuta waƙoƙi suke amfani da ita domin su jawo hankalin mai karatu ko mai nazarin waƙoƙinsu. Marubucin ya yi amfani da miƙaƙƙen salo, domin an fahimce saƙon da waƙar take ɗauke da shi babu kwan-gaba-kwan-baya a ciki. Bugu da ƙari ya yi amfani da salo mai armashi kuma sassauƙa. Haka kuma, an yi amfani da salailai na jawo hankalin mai sauraro ko mai nazari ga su kamar haka:

5. Salon aron kalmomi: wannan wata dabara ce da marubuta waƙoƙin Hausa ke amfani da ita, ta hanyar tsalma wasu kalmomi da aka aro daga wani harshe misali harshen Larabci ko Ingilishi. kalmomin aro da aka yi amfani da su

Larabci

v  Bisimillahi Da sunan Allah

v  Allah Ubangiji

v  Shukur Godiya

v  Ƙasida Abin da aka rubuta a waƙe

v  Hizbu Runduna

v  WujubanAbin da yake tilas

v  Addini Hanyar bauta

v  Shaikh Dattijo ko babban malami

v  ZamanWani lokaci

v  Ƙur’an Littafin Allah mai tsalki

11 Baharun Teku

 12 Funun Ilmoma

 13 ƘailunMai abin cewa

 14 Lisanun Harshe

 15 KulliGaba ɗaya

 16 MaƙalAbun magana

 17 MakanBigire

 18 Amana Yarjejeniya

 19 Faharun Ƙware

 20 IslahGyara

 21 Jaza’u  Sakamako

 22 Ihsan  Kyautatawa

 23 Da’awa Kira zuwa ga Ubangiji

 24 IlimiSani

 25 AntaKai

 26 Mudarris Mai koyarwa

 27 SibiyanYara

 28 MunfiƙuMai ciyarwa

 29 Fi Ciki

 30 Haza Wannan

 31 Sharri Mugun abu

 32 Ikhwan‘Yan uwa

 33 Majanun  Marar hankali

 34 Alƙadir Mai iko

 35 La tabahal Kar ka yi rowa

 36 A’ada’a Maƙiyi

 37 Fani Mai ƙarewa

Kalmomin Ingilishi da aka yi amfani da su

 1 Sakatare Maga takarda

 2 Fi’ar’o Mai sanarwa

 

6. Salon Siffantawa Gajeruwa

Marubucin ya yi amfani da salon siffantawa gajeruwa a baiti na 12-13 inda ya ce:

v  Zaki ja da da ƙarfin Allah

 Kar ka ji tsoron bawa fani.

v  Malam Abdul Basir Ishaƙa

 Ya Allah ya daɗa maka auni.

7. Salon Kambamawa

Marubucin ya yi amfani da salon kambamawa domin gwarzantawa da kaiwa maƙura wajen yabon jagororin ƙungiyar Islahuddini. Misali da ya ce:

 24 Ya baharun fi kulli fununi

 Ya ƙailun riauli irfani.

 25 Ina nufin Shaikhu Bilalu Kano

 Ma’adinun lifumiddini.

Haka kuma, marubucin ya sake yin amfani da wannan salo na kambamawa misali a baiti na

 30 Ya lisanun fi kulli maƙali

 Ya faɗinun fi kulli makan.

 37 Ya kogin ilimi tarbiyya,

 Anta mudarrisussibiyani.

4.3.3 Nazarin Waƙar Yabon Liman Aliyu

 Wannan waƙa malam Aliyu ya yi ta ne domin ya nuna hali na dattako da ke ga Liman Aliyu, saboda rashin shigar sa cikin lamarin siyasa.

1. Zubi Da Tsarin Waƙar

 Dangane da yadda marubucin ya zuba waƙar tasa, wannan waƙa tana ɗauke da baitoci (13), ɗangwaye (26). Haka kuma, tana ɗauke da babban amsa amo na “sa.” Haka kuma a tsarin waƙar ba ta da mabuɗi ba ta da marufi.

2. Jigon Waƙar

Wannan waƙa jigonta shi ne yabo ne zuwa ga Liman Aliyu

3. Warwarar Jigon Waƙar

 Tun a baiti na 1-3 marubucin ya bayyana manufarsa inda ya ce:

v  Liman Aliyu na ban sha’awa

 Don bai gurub-gurub na siyasa.

v  Bakin shi ba ka jin wata kalma,

 Mugunya da ba a so ta siyasa.

v  Bai nuna wai ka zo ka yi fati,

 Da ya zan yana cikin ra’ayinsa.

A baiti na ɗaya marubucin ya nuna cewa Liman Aliyu yana ba sa sha’awa domin ya tsare ƙimarsa da mutuncinsa bai shigar da kansa cikin siyasa ba saboda kasancewar sa jagora na addini. A baiti na biyu kuma sai marubucin ya sake yabon Liman Aliyu amma sai ya nuna ba siyasar ce Liman Ali ba ya yi ba a’a ba ya yin wani zance na Allah waddai a kan siyasa.

Sai kuma a baiti na uku sai ya marubucin ya sake nuna wasu halayen Liman Aliyu ko da yana yin siyasa a matsayin sa na jagoran addini bai nuna wa mutane ga inda yake muradin a zaɓa. Wannan marubuci yana so ya nuna ko da malami yana yin siyasa to bai kamata ya nuna a zahiri ba.

Sai kuma marubucin bayan ya yabi Liman Ali sai ya waiwaya domin ya bayyana waɗansu malamai da ba su yi koyi da irin halin Liman Ali ba, domin su sun gwama karatunsu da siyasa. Sannan kuma marubucin ya nuna abin da ya fi wannan muni shi ne yadda suke ɗaukar ayar Ƙurani suna ba ta warin zama a cikin siyasa domin son zuciya da neman abin duniya.

 8. Malamai waɗansu sun ƙarnanta,

 Karatunsu sun gama da siyasa.

 9. Sai ɗai a ɗauki ayar Allah,

 Ana fassara ta nan ga siyasa.

4. Salon Waƙar

Wannan waƙa tana ɗauke da salo mai armashi kuma ba ta ɗauke da kalmomi masu wuyar fahimta, kaitsaye ana fahimtar saƙon da ke ciki. Akwai wasu nauukan salailai da aka yi amfani da su domin jawo hankalin mai karatu ko nazari, daga cikinsu akwai:

5. Salon Aron Kalmomi: Wannan wata dabara ce da marubuta waƙoƙin Hausa ke amfani da ita ta hanyar cusa wasu kalmomi waɗanda ba na harshen da aka rubuta waƙar a kansa ba. Misali harshen Larabci ko ingilishi. A cikin wannan waƙa mawaƙin ya tsalma kalmomin Larabci da Ingilishi misali

 Larabci

1.Ƙarnantawa Haɗawa ko Gwamawa

2. Allah  Ubangiji

3. Aya Alama

4. Yahud Masu biyar addinin Yahudanci

5. Imam Liman ko Jagora

6. Ɗabia Abin da aka saba

7. Kalimat Kalma

8. KufurKafirci

Kalmomin Turanci

v  Gurub Taro ko Ƙungiya

v  Fati Jam’iyya

6. Salon Habaici: Magana ce za a yi ta gugar zana, domin yin hannun ka mai sanda ga wani mutum ko wasu ɗaiɗaikun mutane. Malam Aliyu ya yi amfani da irin wannan salo misali da ya ce

 8. Malamai waɗansu sun ƙarnanta

 Karatunsu sun haɗa da siyasa.

Mawaƙin yana yin habaici ne ko zuzar zana ga wasu malamai da suka gwama karatunsu da siyasa. Amma wannan ba wai don ya tozarta su ba, ya yi haka ne domin ya isar da saƙo ga irin malaman da ke yin irin wannan domin su gyara.

Salon kamancen daidaito: marubucin ya yi amfani da salon kamance amma na daidaito da ya ce:

12 Dut wanda ba ya fati nasu,

 Kamar kafiri suke hangensa.

Salon amfani da karin harshe: mawaƙin ya yi amfani da karin harshen Sakkwatanci a cikin waƙar a baiti na 10 da ya ce

 10 Tsarin Yahudu wagga siyasa,

 Mai hankali ka gane dasisa.

Kalmar wagga Sakkwatanci ne. Daidaitacciyar Hausa kuwa (wannan).

 2 Bakinshi ba ka jin wata kalma,

Shi ma wannan “bakinshi” Sakkwatanci ne. Daidaitacciyar Hausa kuwa shi ne (bakinsa)

4.3.4 Nazarin Waƙar Bulaliya

 Wannan waƙa ta bulaliya ya yi ta ne domin yin faɗakarwa da gargaɗi ga ɗaliban ilimi da almajirai domin su guje wa ɗabi’u waɗanda suke abin zargi, haka kuma su yi riƙo da ɗabi’u masu nagarta.

1. Zubi Da Tsarin Waƙar: marubucin ya zuba baitoci (31) dangane da yawan ɗangwaye kuwa, wannan waƙa tana ɗauke da ɗango (62). Tsarin waƙar ba ta da mabuɗi, haka kuma ba ta da marufi. Dangane da amsa-amo wannan waƙar tana da amsa-amo wanda ya kasance kowane baitin waƙa yana da nasa na daban.

2. Jigon Waƙar

Wannan waƙa tana ɗauke da jigon faɗakarwa ko gargarɗi.

 

3. Warwarar Jigon Waƙar

Marubucin ya bayyana manufarsa tun a baiti na ɗaya da ya ce:

1.      Ya ku musulmi za ni yin faɗakarwa,

 Ga ɗalibai almajirai duka kowa.

Wato mawaƙin yana so ne ya faɗakar da masu neman ilimi kan wasu ɗabi’u da bai kamata a ce suna aikatawa ba, sannan kuma da nusar da su kan abin ya dace su yi.

Daga cikin faɗakarwar da ya ce zai yi ga ɗalibai da almajirai shi ne, su bar jayayya da ‘ya’yan malamansu. Inda ya ce

4 Dut wanda almajiri ga malam,

 Shi daina jayayya da ‘ya’yan malam.

Bayan mawaƙin ya faɗakar da almajirai da ɗalibai kan wannan ɗabi’a marar kyau. Sai kuma ya ci gaba da faɗakarwarsa ya ce

v  A zan ka saurarin karatu nasu,

 Ban da girman kai fa ko an fi su.

Malam Aliyu da ya ke ya san halin waɗanda yake gargaɗi sai ya nuna su guji yin girman kai ga ‘ya’yan malamansu ko da kuwa sun fi su domin su sami albarkar ilimi.

A baiti na 18-19 sai mawaƙin ya nuna dalilin da ya sa ya faɗakar da ɗalibai da almajirai a fakaice da ya ce

 18 Waɗansu manyan ɗalibai na zaure,

 Da babu malam yanzu dut sun ware.

 19 Sun yi ta jayayya karatu nashi,

 Sun yi nufin gade gida nashi.

Marubucin yana bayar da labari ne kan waɗansu ɗalibai da irin wannan abin da yake faɗakarwa a kansa, ya faru da su, saboda Hausawa sun ce “Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.

4. Salon Waƙar

 Salo wata dabara ce ta ko hikima ta isar da saƙo da marubuta waƙoƙin Hausa ke amfani da ita domin su jawo hankalin mai karatu ko mai nazarin waƙoƙinsu. Wannan waƙa tana ɗauke da salo mai armashi kuma wanda yake sassauƙa sannan marubucin ya yi amfani da wasu salailai domin jawo hankalin mai nazari ko karatu, daga cikin salailan da ya yi amfani da su akwai:

5. Salon aron kalmomi: a cikin wannan waƙa mawaƙin ya yi amfani da salon aron kalmomi misali

Larabci

1.Muslim Musulmi

2. Zahir. Abin da yake a fili

3. Hali yanayi

4. Salati Ambaton Ubangiji

5. Wafati Rasuwa

6. Aibi. Mummuna

7. Ɗalibi. Mai neman ilimi

8. Halifa. Mai maye gurbi

9. Ilimi. Sani

10. Kulli. Baki ɗaya

11. Fanni. Wani yanki

12. Waliyi. Masoyin Ubangiji

13. Allah. Ubangiji

14. Wa'azi. Faɗakarwa

15. Waƙati. Lokaci

16. Maktubi Sanannen lokaci

6. Salon kinaya: Marubucin ya yi amfani da irin wannan salo a baiti na ɗaya da ya ce

 1. Ya ku musulmi za ni yin faɗakarwa,

 Ga ɗalibai almajirai duka kowa.

Marubucin ya ambaci ɗalibai yana nufin ɗalibai 'yan matsakaita. Haka kuma, da ya ce almajirai yana nufin waɗanda ana iya kiran su malamai.

7. Salon Mutuntawa

Mawaƙin ya yi amfani da salon mutuntawa inda ya yi ƙoƙarin mutuntar da Bulaliya da ya ce

 2. Balaliya ce mai shirin tsalar ku,

 Ba ta bugawa zahiri na jikinku.

 3. Cikin zukata ne take tsalar ku,

 Tana horo don ku gyara halinku.

 

6. Salon Amfani da Karin Harshe

Marubucin ya yi amfani da karin harshen sakkwatanci a cikin waƙarsa da ya ce

 31 Shi zan bara nai ban da cin zarafi ko,

 Shina ta yi nai ban da cin zarafi ko.

Sakkwatanci Daidaitacciyar Hausa

Shi zan Ya zan

Bara nai Baransa

Shina ta yi nai Yana ta yin sa

4.3.5. Naɗewa

 A cikin wannan babi an fara da gabatar da shi ne, inda aka kawo bayanai game da gundarin taken bincike. Wato fashin baƙi a kan malam Aliyu Sha'iri da waƙoƙinsa, a inda aka fara da Shimfiɗa, sai kuma Tarihin Malam Aliyu Sha'ir i, Haihuwarsa, Ƙuruciyarsa, da Tasowarsa, da Neman Iliminsa, Koyon waƙoƙinsa, Yaransa, Yawace-Yawacensa, Shirya Waƙoƙinsa, Rasuwarsa, Matsayin malam Aliyu Sha'iri a Tsakanin Mawaƙan Da da na Yanzu, sannan sai Zubi da Tsarin Waƙoƙinsa, Jigon Waƙoƙinsa, Warwarar Jigon waƙoƙinsa, Salon Sarrafa Harshe, daga ƙarshe sai Nazarin Wasu daga cikin Waƙoƙinsa da Naɗewa.


 

Babi Na Biyar

Sakamakon Bincike

5.0. Shimfiɗa

 Kamar yadda za a gani a cikin wannan babi na biyar sh ne babin ƙarshe a cikin wannan bincike da aka gabatar. A cikin wannan babin za a gabatar da Shimfiɗa, Sakamakon Bincike Shawarwari, Naɗewa, da kuma Manazarta.

5.1. Sakamakon Bincike

 Sakamakon wannan bincike ya dace da hasashen wannan bincike da aka yi tun farko cewa wannan zai taimaka wajen raya harshen Hausa.

Bayan kammala wannan nazari, binciken ya gano wasu abubuwa musamman ta la'akari da jigogi da salailai da ke cikin waƙoƙin malam Aliyu Sha'iri. Daga cikin abubuwan da wannan bincike ya gano su ne kamar haka:

1) Wannan bincike ya gano cewa waƙoƙin malam Aliyu idan da a ce al'ummar musulmi za su riƙa komawa cikinsu suna nazari to ana sa ran samun gyaruwar halaye da ɗabi'un al'ummar musulmi tun daga mu'amalar mutum tsakaninsa da mahaliccinsa, da kuma mu'amala tsakanin Shugabanni da talakawansu, da malamai da almajiransu.

2) Haka kuma wannan bincike ya gano cewa malam Aliyu Sha'iri yana da ƙungiya domin shi mabiyi ne ga ƙungiyar Islahuddini waɗanda ake cewa ('yan sai mun gani). Har wa yau kuma shi malam Aliyu ɗan ɗariƙar Tijjaniyya ne kamar yadda ya nuna a cikin rubuce-rubucensa.

3) Har wa yau wannan bincike ya sake la'akari da cewa, malam Aliyu duk da cewa malami ne kuma Sha'iri amma wannan bai hana sa neman na kansa bai miƙe ƙafafuwa yana bara ba. Wannan ne ya sa a cikin waƙoƙinsa yake yi wa wasu malamai zuzar zana da suka mayar da wa'azi hanya ta samun abin duniya. Watau a taƙaice an gano cewa malam Aliyu mutum ne mai tsantseni da gudun duniya.

4) Bugu da ƙari wannan bincike ya gano cewa ashe malam Aliyu har a cikin abin da ya shafi harkokin duniya, ba addini kaɗai ba yana ƙoƙari wajen baza hajar baiwar da Allah ya yi masa. Malam Aliyu ya nuna ƙyamar abin da waɗansu limamai da malamai ke yi kan sha'anin siyasa, su daina nuna inda suke so ko kuma tallata 'yan siyasa a kan mumbari domin wannan aikinsu ba ne. Idan aka lura wannan abun yana faruwa har yau a wannan ƙasa ta mu Najeriya.

5) Har wa yau an gano cewa waƙoƙin malam Aliyu Sha'iri cike suke da hanyoyin warware matsaloli da suka shafi al'ummar musulmi amma saboda ba a sami yin nazari a kan rayuwarsa da waƙoƙinsa ba shi ya sa ba a ci gajiyar wannan baiwa Allah ya yi masa ba.

Wannan abu kuwa ana iya cewa ya faru ne saboda dalilai kamar haka:

i) Kasancewar malam Aliyu yana rubutunsa ne da Hausa ajami, ga shi kuma yanzu an sami ilimin boko Turawa sun zo da wasu haruffa saɓanin Larabci wannan ya sa rubutun ajami ya yi ƙoƙarin ɓacewa baki ɗaya zamani ya kau da shi.

ii) Aka yi rashin sa'a malam Aliyu bai sami wasu magadansa da za su ci gaba daga inda ya tsaya ba musamman su da suka shiga wannan zamani suka yi karatun boko ƙyila da an samu da waƙoƙinsa sun yaɗu sosai ga al'ummar Hausawa.

5.2 Shawarwari

 A ƙarƙashin 5.1 an bayyana sakamakon wannan bincike. An zayyano sakamakon da aka tattara. A wannan bagire kuma 5.2 za a mayar da hankali wajen ba da shawarwari, dangane da abin da ya kamata a yi kan wannan marubuci da kuma waƙoƙinsa. Daga cikin abin da ya kamata a yi shi ne:

1) Ya kamata a sake samun wani mai nazari da bincike ya yi nazari a kan wasu daga cikin waƙoƙin wannan bawan Allah domin akwai alfanu a cikin yin hakan daga cikin amfanin sake yin nazarin wasu daga cikin waƙoƙinsa sh ne:

i) Domin ƙara raya adabin Hausa da kuma taskace shi.

ii) Domin ƙara fito da wani ilimi wanda ba a gano ba a karon farko.

iii) Domin samun abubuwan da za a iya yin nazari nan gaba idan an sami taskace su.

2) Ya kamata a riƙa binciko irin waɗannan marubuta da ba su bayyana ba sosai, ana yin nazari a kan rubuce-rubucensu domin hakan zai taimaka wajen ƙara raya harshen Hausa.

3) Ko yanzu ƙofa a buɗe ta ke ana iya samun wani mai bincike ya sake faɗaɗa wasu abubuwa da suka tsuke a cikin wannan bincike.

4) Ya kamata marubuta waƙoƙin Hausa su daina mayar da hankali ko da yaushe kan abin da ya shafi duniya kawai a cikin waƙoƙinsu, maimakon haka su riƙa gwamawa da jigogi na tauhidi da wa'azi, gargaɗi, sallah, kamar yadda malam Aliyu yake yi.

5.3.Naɗewa

 Kamar yadda sunan wannan aiki ya gabata watau "Nazarin rayuwar malam Aliyu sha'iri da waƙoƙinsa." Wannan babin shi ne babin da aka kawo magaryar taƙewa na wannan bincike watau wannan shi ne babin ƙarshe na wannan bincike da aka gabatar.A cikin wannan babin an zayyana wasu abubuwa da wannan bincike ya yi ƙoƙarin ganowa a matsayin sakamakon bincike. Har wa yau an kuma bayar da shawarwari a kan abin da zai ƙara taimakawa wajen raya wannan harshe na Hausa da kuma ci gaban al'umma.

 A babi na ɗaya a cikin wannan bincike an kawo abubuwa muhimmai kamar haka farko an kawo Gabatarwa, Shimfiɗa, Manufar Bincike Hasashen Bincike, Farfajiyar Bincike, Matsalolin Bincike, Hanyoyin Gudanar da Bincike da kuma Naɗewa.

 Babi na biyu kuwa, wanda shi ne na biyu a cikin tsarin wannan bincike an kawo abubuwa muhimmai kamar haka: Shimfiɗa Bitar Ayykan da Suka Gabata, Hujjar Ci gaba da Bincike, da kuma Naɗewa.

 A babi na uku kuwa, shi ne babi wanda ya ƙunshi fashin baƙi a kan ma'anonin suka shafi taken bincike a inda aka fara da Shimfiɗa, Ma'anar Waƙa, Ire-iren Waƙa, Rubutacciyar Waƙa, Tsarin Rubutacciyar Waƙa, Hanyar Nazarin Rubutacciyar Waƙa sai kuma Naɗewa.

 Babi na huɗu kuwa, wanda shi ne ƙashin baya ko kuma ruhin wannan bincike, kamar yadda aka gani wannan babi shi ne babin da ya ƙunshi fashin baƙi a kan Rayuwar malam Aliyu Sha'iri da Waƙoƙinsa. Inda aka fara da Shimfiɗa, Taƙaitaccen tarihin malam Aliyu Sha'iri har zuwa ƙarshen wannan babin.

 A ƙarshen wannan bincike kuwa, watau babi na biyar ya ƙunshi Shimfiɗa, da bayani a kan Sakamakon Bincike, sai kuma Shawarwari. Sai kuma Naɗewa da kuma Manazarta.


 

Manazarta

Adam, S.N. (2016). "Malam Ibrahim Bin Ahmad Kabara da Waƙoƙinsa." Kundin digiri na farko Wanda aka gabatar a Sashen harsuna da a'adun Afrika. Jami'ar Ahmadu Bello Zariya.

A'isha, A.S. (2016). "Malam Ahmad Maƙari Sa'id da Waƙoƙinsa." Kundin digiri wanda aka gabatar A Sashen harsuna da al'adun Afrika. Jami'ar Ahmadu Bello Zariya.

Bello, A. da Sheshe, I. N. (2013). Arulin Hausa A Sauƙaƙe. Kano: S M Graphics Printers & Publishers.

 S M Graphics Printers & Publishers Kano.

C.B.T.T.M. (2008). Talata Mafara Jiya Da Yau.

Dumfawa, A. A. (2022). A ajin ALH 407 Contemporary Poetry in Hausa.

Ɗangambo, A. (2008). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Zariya: Amana Publishers.

Husaini, Y. (2O21) “Ɗanbalade Morai Da Waƙoƙinsa. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Nazarin harsuna da Aladu Jamiar tarayya Gusau.

Ibrahim, (2019) "Malam Nasiru Kabara Da Waƙoƙinsa." Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen harsuna da al'adun Afrika Jami'ar Ahmadu Bello Zariya.

Mukhtar, I. (2OO5) Bayanin Rubutacciyar Waƙar Hausa. Abuja:

Countryside Publishers.

Muhammad, S. S. (2019) Matakan Nazarin Rubutacciyar Waƙar Hausa.

Zariya: Jami’ar A B U.

Sarɓi, S. A. (2007). Nazarin Waƙen Hausa. Kano: Samarib Publishers

Sa’id, B. (2016) Rubutacciyar Waƙa Hausa Ma’auninta da Amsa-amonta da ire-irenta. Kano: Jami’ar B U K.

Yahaya, A. B. (2001). Salo Asirin Waƙa. Sokoto: Guaranty Printers Sokoto.

Yahaya, I. Y. (2002). Hausa A Rubuce. Zariya: NNPC.

 

 


 

 Waɗanda Aka Yi Fira da Su

 

Suna Tsokaci

 Malam Lawwali Babban ɗan Malam Aliyu Sha'iri

 Malam Naziru Aminin Malam Aliyu Sha'iri

 Alhaji Maidaga Aminin Malam Aliyu Sha'iri

 Liman Sani Abokin Karatun Malam Aliyu Sha'iri

 Malama Maimuna Matar Malam Aliyu

 Malama Rabai'atu Yayar Malam Aliyu

 


 

Rataye

Waƙar Yabon Islahuddini da jogororinta.

1. Bisimillahi da sunan Allah,

 Sarki jalla gwani Rahmani.

2. Sai shukurammu ga sarki Allah,

 Ya ƙara sa mu ruƙon addini.

3. Allah ka yi tsira da aminci,

 Ala Muhammadi ɗan adinani.

4. Na yi nufin in tsara ƙasida,

 Ta yin yabon Islahuddini.

5. Ba ƙafiya babu aruli,

 Sai ƙaunar hizbur Rahmani.

6. Ya Allahu ka ƙarfafa tsarin,

 Ɗan baiwarka mutum mai rauni.

7. Yin jinjina a gare ka wujuban,

 Ga dukkanin mai son addini.

8. Ya Allah ka tsare Shaikh Yasuf,

 Da ya riƙa muna wannan tsani

9. Ya ce ban shakkar sa ku taka,

 Allah tare da ikhwani.

10. Shaikhu Yasufu ibnu Yahuza,

 Ka yi gadon kishin addini.

11. Sai jarumi mai halin girma,

 Jagoran Islahuddini.

12. Zaki ja da ƙarfin Allah,

 Kar ka ji tsoron bawa fani.

13. Malam Abdul Basir Ishaƙa,

 Ya Allah ya daɗa maka auni.

14. Dole na sa babansu Husaina,

 Sarkin tsauri na bin addini.

15. Allah ɗai da ya yo shi ya san shi,

 Sakataren Islahuddini.

16. Bai tsoro kuma ba ya rauni.

 Wurin karo da mutan zamani.

17. In sun yi gungu don su tare shi,

 A hankali yaka sa masu rauni.

18. A ba shi hujja ko ko ya ba da,

 Kun ji nufin rayat addini.

19. Ina nufin Shaikh Nasiru nawa,

 Mai kanwa ne ismus sani.

20. Naku ma'auni bayan namu.

 Fira da kwaɗɗi ya ikhwani.

21. Ina nufin malam na marere,

 Sufina mai yin Tijjani.

22. Masu kira a bi hanyar Allah,

 Da damana bazararsu da rani.

23. Ya shiga ƙauye lugu-lugu,

 Don tabbatar da biyar Ƙur'ani.

24. Ya baharun fi kulli fununi,

 Ya ƙa'ilun ri'auli irfani.

25. Ina nufin Shaikhu Bilalu Kano,

 Ma'adinun lifumiddini.

26. Wallahi malam sai Allah saka,

 Ya yi rawa ta ƙane ikhwani.

27. Sai Alhaji Mukhtaru Balarabe,

 Allah ya ƙara ma imani.

28. Su sa jikinsu su sa kuɗinsu,

 Kun ji mujahiddan addini.

29. Sai ma'ajin wannan jam'iyya.

 Ina nufin malam Zayyani.

30. Ya lisanun fi kulli maƙali,

 Ya faɗinun fi kulli makani.

31. Halin ƙwarai a wurin Zayyanu,

 Riƙon amana ba nuƙusani.

32. A rijiyar sarki zan koma,

 Akwai Mahir masanin Ƙur'ani.

33. Ina nufin Shaikhu na musamman,

 Bello abin faharin addini.

34. Akwai fi'ar'o gun Islahu,

 Mai himma mai son addini.

35. Malam Hasan Allah ya biya

 Jaza'ul Ihsani Ihsani.

36. Sai malamin da'awa Ya'aƙubu,

 Tunatarwa yaka yi ba rauni.

37. Ya kogin ilimi tarbiyya,

 Anta mudarrisussibiyani.

38. Dole na sakko babban jigo,

 Allah ya ƙara mai imani.

39. Ina nufin haji Garba Ɗanɗa,

 Ya munfiƙun fi hazad dini.

40. Ya yi ruwa kuma ya yi tsaki-tsiki,

 Ga taimakon Islahuddini.

41. Ya Allah ka tsare muna wannan,

 Ga dukkanin sharrin shaiɗani.

42. Sai babban jigo a gare mu,

 Kun ji turakun ƙauye da birni.

43. Ai shugaban Islahu na Ƙaura,

 Bai kunyar maƙiyin addini.

44. Ka sha kabsawa da mutane,

 Kan salla rukunin addini.

45. Alhaji Sidi aban su Rumaisa,

 Mashin soke maras imani.

46. Ka ba nassi ka ba su shafi,

 Ya jikan kakansu Husaini.

47. Ya baban su Umar da Sumayya,

 Ya hadimi wurin Jelani.

48. Sai Sufi mai tsoron Allah,

 Ya fitila hasken zamani.

 49. A nan manufata Shaihu Yahaya,

 Manyan gwagwarmayar addini.

50. Baban Abdullahi da Aliyu,

 Baban Zainab mai imani.

51. Ya sha kakaniyar munkirai,

 Masu musun hanyar addini.

52. Ya Allah ka daɗa ma baiwa,

 Ta lafiya da yawan imani.

53. Bayan yabo ga malammaina,

 Zan yi nasiha ya ikhwani.

54. Mui biɗar ilimin Isalamu,

 Don shi ne tushen addini.

55. Mai gaskiya bai jan fitina don

 Kar gaskiyarsa ta zan baɗalani.

56. Mu kauda zargi cikin tafiyarmu,

 Da jita-jita cikin addini.

57. Mugun zato kuma ba shi da kyawo,

 Domin kay ya saka muna rauni.

58. An yi kira an ce muna gyara,

 Dole mu amsa ya ikhwani.

59. Mun tafi mun shiga don mu ga gyaran,

 In ko an gyara ikhwani.

60. Ba mu da zaɓi kan manufarmu,

 Sai bin addinir Rahmani.

61. Amma kau in anka ƙi gyaran,

 Ba a hana mu biyar addini.

62. A kan bakarmu ga wannan hanya,

 Ba ma bin dukkanin majanuni.

63. Ga wanga ƙarni babu jununa

 Kamar hana mu biyar Ƙur'ani.

64. Ya Allahu gwani mai ƙarfi,

 Ya Ƙadirun fi kulli zamani.

65. Ya Allah domin Shurafa'u,

 Don kakan su Hasan da Husaini.

66. Ya Allah ka tsare Islahu,

 Dukkanin sharrin Shaiɗani.

67. Dubun tsira Allah da aminci,

 Ga Musɗafa sirrir rahmani.

68. In an ce ma wayyi ƙasida,

 La tabahal a'a da addini.

69. Ce Ibrahim ɗan Abdullahi,

 Ce mariƙin wuridin Tijjani.

70. Don Islahu ta haɗa kowa,

 Dukkan mai kishin addini.

 Tamat bi hamdillhi wa husni aunihi.

 Waƙar Bulaliya

1. Ya ku musulmi za ni yin faɗakarwa,

 Ga ɗalibai almajirai duka kowa,

2. Bulaliya ce mai shirin tsalar ku,

Ba ta bugawa zahiri na jikin ku.

3. Cikin zukata ne take tsalar ku,

 Tana horo don ku gyara halinku.

4 Dut wanda almajiri ga malam,

 Shi daina jayayya da 'ya'yan malam.

5. In malamin nan naku ya yi wafati,

Sai ku ruƙe kulan dubu na salati.

6. Fi kulli yaumi waƙati maktubi,

 Riƙe hakanga sai ka tsalke aibi.

7. In malamin nan naku ba shi da manya,

 Cikin ɗiya sai ƙanƙana ba manya.

8. To ɗalibai nan za ku taru shawara,

 Ku zaɓi daidai wanda zai jagora.

9. Dut mai kwaɗai mai son a sa shi gare ta,

 Ku bas shi wawa bai iya ma gabata.

10. Ku zaɓi mai ƙi wanda bai da kwaɗaita.

 Da sannu shi ne zai zama da nagarta.

11. In ko manya suna da ilimi

 A ɗauki babban su halifa ilimi.

12. Gida na malam ba a son a bas shi,

 Wurin karatu kawai ɗiyansa su yi shi.

13. A zan ka saurarin karatu nasu,

 Ban da girman kai fa ko an fi su.

14. A zan nufin Allah da Manzon Allah,

 A sumu yarda nan ta sarki Allah.

15. Ka bar ganin kai ka hi 'ya'yan malam,

 Wurin karatu yanzu kai ma malam.

 16. Ba ka buƙatar 'yan ɗiyan malam.

 Ganin kakai kai ka ɗara su fahimta,

 17. Ka ɗauki kanka ka ɗara su fahimta.

 Ka zaɓi kanka yanzu kai ka gabata.

 18. Waɗansu manyan ɗalibai na zaure,

 Da babu malam yanzu dut sun ware,

19. Sun yi ta jayayya karatu nashi,

 Sun yi nufin gade gidan nashi.

20. Ga kau ɗayan nan nashi sun san fannin

 Iri karatu nashi sun kuma gane.

21. Komi kake yi zan ki kyauta ɗabi'a,

 Halin ƙwarai zaƙe ka zan yin ɗa'a.

22. Mai wa'azi don kar ka sanya kwaɗanka,

 Wurin mutane kodayaushe su ba ka.

23. Da nuna kai dai ga buƙata taka,

 A zan biya ma tun da ga wa'azinka.

24. Ba ka da koyar wada Manzon Allah,

 Da kau waliyyai masu yi don Allah,

25. Shi wa'azi in ka yi domin Allah,

 Shina biyan dut kanin buƙatu Allah,

26. Shi wa'azi yau an kasa shi ga hanya,

 Da kasuwanni don ababan duniya.

27. A ba ka sadaka ya halatta ka amsa,

 Ka daina roƙo koda yaushe ka amsa.

28. Kana ta amsa babu kau an bar ka,

 An ɗebe kwarjini ga fuska taka.

29. Ka ɗebe kwarjini cikin iliminka,

 Saboda roƙo koda yaushe a ba ka.

30. Sai wanda ya zan nakasa ta kama,

 Ba shi da mai ɗaukan lalura taima.

31. Shi zan bara nai ban da yin ƙarya ko,

 Shina ta yi nai ban da cin zarafi ko.

 Waƙar Yabo ga Liman Aliyu.

1. Liman Aliyu na ban sha'awa,

 Don bai gurub-gurub na siyasa.

2. Bakinshi ba ka jin wata kalma,

 Mugunya da ba so ta siyasa.

3. Bai nuna wai ka zo ka yi fati,

 Da ya zan yana cikin ra'ayinsa.

4. Limamman ku zo ku zo ku yi kun yi,

 Da Liman Aliyu Ɗabi'a tasa.

5. Kowarriƙa shina nan nashi,

 Har wanda bai riƙa bai ƙin sa.

6. To ƙaddara hukuncin Allah,

 Shi ke izo ma bayi nasa.

7. Don ɗai ya zan yana jarabawa,

 Domin a gane mai tsoronsa.

8. Malamai waɗansu sun ƙarnanta,

 Karatunsu sun gama da siyasa.

9. Sai ɗai a ɗauki ayar Allah,

 Ana fassara ta nan ga siyasa.

10. Tsarin Yahudu wagga siyasa,

 Mai hankali ka gane dasisa.

11. Kana malami bafaden Allah,

 To mi ka sa ka zaɓi siyasa?

12. Wasu kam Yahudu sun halaka su,

 Ƙiyayyarsu yau tana ga siyasa.

13. Dut wanda ba ya fati nasu,

 Kamar kafiri suke hangensa.

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments