Zambo a Waƙar Alhaji Musa ƊanƘwairo

Zambo a Wakar Alhaji Musa Dankwairo

J/Waka:

Alhaji Musa na ci dariya,

Na kuma na yi mamaki,

Sannan kuma na ga tausan maza,

Siyasar ga wadda taz zarce,

Don ga wasu sun ci zaɓen ƙwarai,

Ga wasu kau ba su ci zaɓen ƙwarai ba,

Don wasu sun ci ƙubeji,

Wasu kau, ƙunƙu sun ka ci,

Don ba su da daɗin rai daji,

Kuma ba su da, daɗin rai birni,

Shi yaz zama hasken Balbela,

Balbela idan ta taso,

Sai ka ga jikinta zaf fari,

Amma cikin naman nan nata dub baƙi.


To, sai ka ga jikinta zaf fari,

Amma cikin naman nan nata dub baƙi.


Kai kan taka ta yi kyau Haji Shehu,

Su Ɗanbakaki ba a sha da daɗi ba.×2


Amshi:

Haji Shehu Ka Buwai Maza,

Baban Habibu Shugaban Kasa.


J/Waka:

Duy ya karya masu jayayya,

Ɗan Dottijo faɗi, sun kasa faɗi,

Sun san ya hi su gaskiya.×2


J/Waka:

Milkin Shehu yana da salsala,

Muhajiruna gidan Usumanu,

Tun hwarko ba a bas su baya ba.×2


Amshi:

Haji Shehu Ka Buwai Maza,

Baban Habibu Shugaban k'asa.


J/Waka: 

Maidaraja na Ishola Saraki,

Na Akwueme na Shehu ka biya.×2


Amshi:

Haji Shehu Ka Buwai Maza,

Baban Habibu Shugaban Kasa.


J/Waka:

Duk ka ɓadda masu hwaɗin Rai,

Kai na yi biɗa ni ban gane su ba,

Da ɗan Tunku da Kurut da ɗan Dila.


Alhaji Musa Dankwairo a faifansa da ya yi wa tsohon Shugaban Kasar Nijeriya Marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari.


Rubutawa: Umar S Ahmad
31-10-2019
Re-e
31/10/2023

Post a Comment

0 Comments