𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
ina da mata
biyu, ɗiyar talaka
da ɗiyar mai kuɗi, shin ya halatta na
yiwa ɗiyar talaka
tufafi masu araha, ita kuma ɗiyar
mai kuɗi na yi mata
masu tsada?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Akwai hujjoji
daga Alƙurani mai
girma da Hadisai ingantattu da magan-ganun malamai akan wajabcin Miji yaciyar
da Matansa, wannan kuma ya biyo bayan gwar-gwado dama da ikon da yake da ita.
Kuma ba ya yiwuwa ya bar ta ta ciyar da kanta ko da kuwa mawadaciya ce, sai dai
idan da yardarta akan za ta ciyar da kanta.
Kuma wannan
ciyarwar da za'a yiwa mace daga ciki akwai tufatar da ita, lokacin sanyi da
zafi, bawai sai kowacce shekara ba, da kowane biki ba, a'a zai yishi ne ko da
kuwa tana da tufafin, ba maganar sai ya ga tufafinta sun lalace, sannan ya yi
mata ɗinki, A'a
tufatarwa na kasancewa ne gwar-gwadon bukatar matarsa ga tufafin kuma
gwargwadon karfi/ikonsa, ba tare da kuma ya yi fifita wata akan wata ba, 'yar
Masu kuɗi da 'yar
talaka, lura da Alƙur'ani
mai girma cewa hakan zai kasance ne da kyautatawa kuma gwar-gwadon Wadatarsa:
ۚ وَعَلَى
الْمَوْلُودِ لَهُ رِزْقُهُنَّ وَكِسْوَتُهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۚ لَا تُكَلَّفُ
نَفْسٌ إِلَّا وُسْعَهَا ۚ
"Wajibine
akan wanda ake yiwa haihuwa (miji) ciyarda Matansa da tufatar dasu bisa
kyautatawa, Bamu kallafawa rai sai abin da za ta iya" (Suratul Baƙara:233.)
Ibn Kaseer
Allah ya yi masa rahma ya ce: "Ana nufin ciyar dasu irin abinda al'adar
mutanen gari take cewa shi ne Abunda ake ciyar damata da shi gwar-gwadon
arzikinsa garinsu ke tafiya akan shi, ba tare da bannatar da dukiya ko noketa, gwar-gwadon dai samunsa da
wadatarsa" Tafseer Ibn Kaseer (1/634)
Anan abinda ya
fi zama maslaha shi ne ko wace ya siya mata irin abin da ya siyawa ɗayar gwar-gwadon
arzikinsa.
Domin Adalci
Allah ya ce Ayi, matsayinsu ɗaya
awajanka kowacce matarka ce, kasonsu ɗaya
acikin gadon dukiyarka koda kuwa Ubantane ya fi kowa wadata aduniya, inka mutu
da ita da wacce Ubanta ya fi kowa talauci aduniya ɗaya suke wajan Allah saboda haka nema yaraba
gadonsu dai-dai babu ban-banci idan ka mutu.
Bai halatta kayi wannan Shaiɗanci tsakanin Matankaba,
kuma lallai kasani yin hakan kunna wata gobarar dajice agidanka wanda bakasan
iyakacin ɓarnar
dazatai acikin gidanka da zurriyarka baki ɗaya
ba.
Maganace
Mummuna kuma Koda kaji koka karanta awani waje cewa hakan yahalatta, katabbar
kuskurece, ta saɓawa
Ayoyin Alƙur'ani da
hadisan Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam da tunani mai kyau.
Wajibine
katsayar da adalci tsakanin matanka, haramun ne kafifita wata akan wata, wajan
tufafi ko kayan kwalliya ko yanayin irin Abuncin dakake ciyar dasu.
Wajibine
kadunga yi musu tufafi masu kima ɗaya
daraja ɗaya, haka
abunci haka wajan kwanciya haka gida dole kabaiwa kowacce dai-dai da ɗayar.
Inka saya wa ɗiyar masu kuɗi tufafin dubu biyar,
wajibine ɗiyar
talakama kasai mata tufafi mai darajar datakai dubu biyar, balalle su zama kala
ɗaya ba, amma
darajarsu da tsadarsu dole ne suzamto dai-dai.
Waccan in
kullum kana saimata lemuka da nama da dukkan wani Nau'in Abunci mai kyau kona
Sha, ɗayar ma
wajibin kane kadunga sai mata irin wannan abunci mai daraja iri ɗaya dakuma karin kuzari
da inganta jiki irin wacce kasaiwa ɗiyar
masu kuɗin da ka
auro.
Haka in ka baiwa ɗaya
gida mai dakuna uku da firji da setlight da kayan kawa, itama ɗayar dole ne kasai mata
gida irin na ɗayar
maicike da kayan kawa da more rayuwa
irin na ɗayar babu
ban-banci.
Wannan shi ne
zai tseratar dakai agaban Allah rannar Alkiyama daka shiga wuta.
Bayan haka
yana daga abinda ya fi zama maslaha yayin da mutum zai yi aure ya duba
MUKAFA'AH wato dai-daito tsakanin miji da mata, domin duk lokacin da ya zamto
miji daba ya iya hidimawa matarsa wajen kiyaye mata abincinta, muhallinta
uwa-uba bashi da karfin siya mata mai wanda zai gyara mata fatar jikinta kamar
yadda take a gidan iyayenta, to dole ne a samu matsala. Don haka yana da kyau
idan son samu ne ya auro dai-dai da shi ko kuma wacce ya fita.
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.