Aikatau

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa  

    387.  Aiki na nufin abin da ka kaddarta,

     Za ka yi, ko ka yi shi nan har ka rubuta,

     Shi ne aikatau, ga hujjar manazarta,

    Aiki kowane iri za ka rubuta,

      Ka kiyaye da shi ga tsarin zanawa.

     

    388. Za a rubuta kowane aiki ware,

     MatuÆ™ar ya taho ga kalma jejjere,

     ‘Yanci ag garai rubuta shi a ware,

     Tabbata ka cire shi ka ware bare,

      Ba a raba shi tarsashinsa ga tsarawa.

     

    389. Yanka, yanke-yanke ko yayyankewa,

     Sara, sare-sare ko sassarewa,

     Datsa, datse-datse ko daddatsewa,

     ÆŠinki, É—inke-É—inke ko É—iÉ—É—inkewa,

     Girka, girke-gireke ko giggirkawa,

      Zanawa, karantawa da rubutawa.

     

    390. Jifa, jefe-jefe ga jejjefawa,

     Kamu, kame-kame ga kakkamawa,

     ÆŠauri, É—aure-É—aure ko É—aÉ—É—aurawa,

     Damu, dame-dame ga daddamawa,

      Dubi, dube-dube ga duddubawa.

     

     

    391. Darkake da daddaƙewa da dakewa,

     Ka ga niÆ™a da ninniÆ™awa da niÆ™ewa,

     To yage da yakucewa, yagewa,

     Mammatse da lanÆ™washewa, miÆ™ewa,

      Matsetseniya ka sa Æ™wai murjewa.

     

    392. Kalma kowace iri in aiki ce,

     A gajera ta zo a duba a rubuce,

     In ma doguwa a kalma ta kasance,

     Duk yada tat taho rubutu a taÆ™aice,

      HaÉ—e ake sa ta can ga dokar zanawa.

     

    393. Komi an ka aikata nan a rubuce,

     Ko kuma za a yo shi ba ko jinkirce,

     Za a yi, an yi shi wanga kwatance,

    Matuƙar an ka ce da kalma aiki ce,

      Ta zama aikatau ka lura da ganewa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.