Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
518. In ka kammala da zancen wani sosai,
Ka tabbata ka cika
ga zance nai sosai,
Zancen nan da yay yi in ya cika to sai,
Kai haka ” ka rufe
bayani duka sosai,
Za a saka ta don
alamar kullewa.
519. In an sa ta babu sauran ƙarawa,
Sai dai a yi can a
ƙara rubutawa,
Zance Ila ya cike,
babu ragewa,
Babu ka da lamuni
ka ƙara da daɗawa,
Ga jawabin da an ka nuno na gwadawa.
520. Malam ya yi zoru yac ce; “a kashe su”,
Kuma ya ce: “a
babbake su a ƙona su”,
Wani yac ce: “a
dakata kar a kashe su”,
Sai malam ya ce: “ a buɗe ɗaki a rufe su”,
Mun ka ga tausayin su mun ka ƙi zartawa.
521. Shi ko ɗaya sai faɗin; “Do Allah ƙyale mu”,
Daga nan mun ka
lura sun taushe haƙinmu,
Sun cuce mu sun
hana muna aikinmu,
Sai ɗaya makiri ya ce: “ga mu kashe mu”,
Shi kan mun ka lullusai had da karewa.
522. Lura da kyau, a dukkan
baitun nan,
Mun saka ‘yan
alamuna duk a saman nan,
Su ke tabbatar da
duk zantukkan nan,
Duk maganar da an ka sa wa alamar nan,
Mai ita ba ya nan riwaya aka yo wa.
523. Za a saka ta yadda duk yaf furta ta,
Ko da ya yi izgili
ba canza ta,
Ko ya ɓamɓaro ta, har ba a faɗinta,
Dole a sa ta ba a
ko inkarinta,
Yin gyara cikinta
shi ne ɓatawa.
524. Haka masana sun ka ce mun ko yarda,
Ba mu da ja, a
tilas muka yarda,
Ita ce ƙa’ida da kowa ya
shaida,
Babu ragi cikinta
ko da ga takarda,
Mai kaya ka cicciɓawa da azawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.