Al'amuransa Ba Sa Tafiya Daidai

    TAMBAYA (49)

    Assalam alaikum warahmatullah wabarakatuh. Barka da Jumu’ah Malam Ya aiki, ya Iyali da hidima da jama’ah. Mal don Allah tambaya ce dani, Dan Uwanane, abubuwanshi basa tapia kamar na kowwah karatu wurin sau 4 daya fara sai abu yaƙi dadi dole ya dawo gida, kuma yana da ƙoƙari Alhamdulillah abun yana damunmu sosai sai nake tambayanshi mene ne Matsalan ya ce sam shima ya rasa dalili, amma yana ganin kamar idan ya yi addu’ah Allah baya kar6a, sai hakan ya tayar min da hankali na tambayeshi 6angaren addininsa duk da abinda ya bayyana garemu yana da riƙon addini kuma bamuga Chanji ba, sai na kuma tambayanshi ƙila akwai laipin da yike daga shi sai Allah yikeyinshi, ya tabbatarmun da Babu nace to ya yawaita Istighfari kafin na tambayi Malamai akan abin, tunda nasan tabbas Allah baya ƙin kar6an addu’ar Bawa ko dai bawan ya yi gaugawan ganin bata amsu ba, ko Allah ya chanja mishi da mafi alkhairi ko kuma Allah ya ijiye mishi ladan. Mal Inason sanin don Allah  mai ya kamata yayi. Nagode sosai. Allah ya ƙara lapia da imani

    AMSA

    Abinda ya kamata ya yi anan shi ne ya yawaita Istighafari domin kuwa idan Allah (Subhanahu wa ta'ala) yana fushi da shi to silar yawaita Istighfarin zai so shi kuma ya cire masa wannan damuwar, kamar yanda ayata 222 cikin Suratul Baƙara ta tabbatar da hakan;

    إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ )

    البقرة (222) Al-Baƙara

    Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakwa.

    Sannan kuma kada mu manta cewar dukkan abu mara kyau da ya samemu to kada mu jinginashi ga Allah (Subhanahu wa ta'ala) sai dai mu tuhumi kanmu domin kuwa Allah (Subhanahu wa ta'ala) ya ce;

    ( مَّا أَصَابَكَ مِنْ حَسَنَةٍ فَمِنَ اللَّهِ ۖ وَمَا أَصَابَكَ مِن سَيِّئَةٍ فَمِن نَّفْسِكَ

    النساء (79) An-Nisaa

    Abin da ya sãme ka daga alhri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya sãme ka daga sharri, to, daga kanka yake

    Sannan kuma a nusar da shi cewar mai yiwuwa matsalar da yake samu a karatunnasa shi ne alkhairi a gareshi domin kuwa wani abun muna son shi amman sharri ne a garemu haka kuma za kaga mun tsani abu amman kuma wannan abun shi ne alkhairi a garemu kamar yanda Allah (Subhanahu wa ta'ala) ya fada;

    ( كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِتَالُ وَهُوَ كُرْهٌ لَّكُمْ ۖ وَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ وَعَسَىٰ أَن تُحِبُّوا شَيْئًا وَهُوَ شَرٌّ لَّكُمْ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ )

     

    البقرة (216) Al-Baƙara

    An wajabta yãƙi a kanku, alhãli kuwa shi abin ƙi ne a gare ku, akwai fãtar cwa ku ƙi wani abu, alhãli shi ne mafi alhri a gare ku, kumaakwai fãtar cwa kuna son wani abu alhãli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma kũ ba ku sani ba

    Shawarar da zan bashi a takaice shi ne abunda na fada a farko wato ya gyara alaƙarsa da Allah (Subhanahu wa ta'ala), domin kuwa batunma babu wani laifin da yakewa Allah a fili ko a boye ma bai taso ba saboda ai daman shi ba zai iya fada miki laifin da yake a boye ba tunda ya tabbata a cikin sahihin hadisi wanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce kowanne dan Adam yana laifi sai dai wanda ya fi a wajen Allah shi ne mai yawan tuba, a sanarda shi cewar ya yawaita Istighfari, in sha Allahu silar hakan sai kiga Allah (Subhanahu wa ta'ala) ya kawar masa da damuwar ta sa

    Muna roƙon Allah (Subhanahu wa ta'ala) ya kawar mana da damuwarmu baki daya

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.