Ticker

    Loading......

Ango Ya Rasu Kafin Amarya Ta Tare

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Mutun ya yi aure a ranar da aka kawo masa amaryar sai tafiya muhimmiya ta kama shi, a kan hanyar dawowa kuma sai ya yi hatsari ya rasu. Shi ne ake tambaya: Ko akwai gado da takaba a kan matar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce:

 وَٱلَّذِینَ یُتَوَفَّوۡنَ مِنكُمۡ وَیَذَرُونَ أَزۡوَ ٰ⁠جࣰا یَتَرَبَّصۡنَ بِأَنفُسِهِنَّ أَرۡبَعَةَ أَشۡهُرࣲ وَعَشۡرࣰاۖ

Kuma waɗanda suke rasuwa daga cikinku kuma suke barin matan aure, to matan sai (matan) su yi zaman jira da kawunansu har tsawon watanni huɗu da kwanaki goma. (Surah Al-Baƙarah: 234)

Malamai suka ce: Wannan ayar gamammen hukunci take ɗauke da shi, watau ta haɗe duk matar da mijinta ya rasu: Ko ya tare da ita ko bai tare da ita ba, ko ƙaramar yarinya ce ko babbar mace ce, haka kuma ko baiwa ce kuma ko ya ce.

Daga cikin dalilan da suke nuna har wacce ba a tare da ita ba ma ta shiga cikin wannan hukunci shi ne: Hadisin da Al-Imaam An-Nasaa’iy (3367) ya riwaito da isnadinsa har zuwa ga Alƙamah da Al-Aswad cewa:

An zo wa Abdullaah Bn Mas’ud (Radiyal Laahu Anhu) da tambaya a kan mutumin da ya auri wata mace amma bai yanka mata sadaki ba, sai kuma ya rasu alhali bai tare da ita ba. Sai Abdullaah ya ce: Ku bincika ko za ku samu wani hadisi a kan maganar. Suka ce: Baban Abdurrahman, ba mu samu wani hadisi a kan hakan ba. Sai ya ce: Zan bayar da amsa da fahimtata, idan na dace da daidai to daga Allaah ne. Idan kuma kuskure ne to daga gare ni ne, kuma daga sheɗan, babu ruwan Allaah da Manzonsa.

لَهَا كَمَهْرِ نِسَائِهَا لاَ وَكْسَ وَلاَ شَطَطَ وَلَهَا الْمِيرَاثُ وَعَلَيْهَا الْعِدَّةُ

Za a ba ta sadakinta cikakke, ba cuta ba cutarwa. Kuma wajibi ne ta yi masa idda, sannan kuma tana da gado.

Sai wani mutun daga Ashja’ ya miƙe ya ce: A cikin irin wannan masalar ce Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yanke hukunci game da wata mace a cikinmu wacce ake kira Birwau Bint Waashiƙ. Ta auri wani mutum sai ya rasu tun kafin ya tare da ita. Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi hukunci da cewa: Tana da misalin sadakin sa’o’inta, kuma za a ba ta gado, kuma za ta yi idda. Sai Abdullaah ya ɗaga hannuwansa ya yi kabbara. (Abu-Daawud (2118) da At-Tirmiziy (1176) da Ibn Maajah (1965) su ma duk sun riwaito hadisin, kuma Al-Albaaniy ya inganta shi a cikin Sahih Abi-Daawud (1839) da Al-Irwaa’u (1939)).

Don haka, wannan matar ita ma za ta yi wa mijin takaba, kuma za a raba gadon mijin da ita.

Amma ayar Suratul Ahzaab mai cewa:

یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوۤا۟ إِذَا نَكَحۡتُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَـٰتِ ثُمَّ طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمۡ عَلَیۡهِنَّ مِنۡ عِدَّةࣲ تَعۡتَدُّونَهَاۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحࣰا جَمِیلࣰا

Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan kuka auri mata muminai, sai kuma kuka sake su tun kafin ku tare da su, to ba ku da wata idda a kan su da za su yi ta. (Surah Al-Ahzaab: 49)

Tana magana a kan wadda aka saka ne, ba wadda mijinta ya rasu tun kafin tarewa da ita ba.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments