Ana kira shekarar 1960 da suna 'Shekarar Afirka, saboda abubuwan da suka faru a cikin shekarar; wanda galibinsu na samun 'yancin kai ne na wasu daga cikin ƙasashe Afirka.
Tsakanin watan Janairu zuwa Disamba, ƙasashen Afirka goma sha
bakwai (17) ne ciki har da tsofaffin ƙasashen Faransa 14 suka samu 'yancin kai
daga Turawan mulkin mallaka. Daga cikin ƙasashen akwai:
1. Kamaru:- ta samu 'yancin kai daga ƙasar Faransa ranar 1 ga
watan Janairun 1960.
2. Jamhuriyar Togo:- ta bi sahun Kamaru wajen samu 'yancin
kai a ranar 27 ga watan Afrilun 1960 daga Faransa.
3. A ranar 26 ga watan Yunin 1960 Madagascar ta samu 'yancin
kanta daga Turawan mulkin mallaka na ƙasar Faransa.
4. Bayan tashin hankali da ɗauki-ba-daɗi da aka riƙa yi,
Congo ta tsira da 'yancin kai a ranar 30 ga watan Yunin 1960 daga hanun
Belgium.
5. Somalia:- ta samu nata 'yancin kan kamar sauran
takwarorinta a ranar 1 ga watan Yulin 1960 daga Burtaniya.
6. Jamhuriyar Benin:- tayi sa'ar samun 'yancin kanta a ranar
1 ga watan Agustan 1960 duk dai a hannun uwa Faransa.
7. Nijar:- ta bi sahun Jamhuriyar Benin wajen samun 'yancin
kai a ranar 3 ga watan Agustan 1960 daga Mama Faransa.
8. Burkina Faso:- al'ummar Burkina Faso sun yi sam barka da
samun 'yancin kai a ranar 5 ga watan Agustan 1960 daga wajen Faransa.
9. Ivory Coast:- ita ma ta bi sahun 'yan uwanta wajen karɓar nata 'yancin kan a ranar
7 ga watan Agustan 1960 a wajen Faransa.
10. Chadi:- Faransa ta 'yantata kamar sauran da 'yancin kai
a ranar 11 ga watan Agustan 1960.
11. A ranar 13 ga watan Agustan 1960 Faransa ta sake
sallamar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da 'yancin kai.
12. Jamhuriyar Congo:- ita kuwa ta samu nata 'yancin ne a
ranar 15 ga watan Agustan 1960 a hannun Belgium.
13. Gabon:- bayan magiya da roƙon da suka riƙa yi wa Faransa, a ƙarshe
dai haƙarsu
ta cimma ruwa; inda a ranar 17 ga watan Agustan 1960 aka ba su 'yancin kai.
14. Senegal: ta samu 'yancin kai daga Faransa a wani ɓangare na Tarayyar Mali a
ranar 4 ga watan Afrilun 1960, sannan ta zama ƙasa mai cin gashin kanta 'yan watanni kaɗan, wato a ranar 20 ga
watan Agustan 1960.
15. Mali:- bayan harara da kallon hadarin kaji da al'ummar ƙasar
suka riƙa
yi wa Faransa, a ƙarshe dai Faransa ta yanke shawarar ba su 'yancin kai a ranar
20 ga watan Yunin 1960.
16. Nijeriya:- Hajiya babba. Ƙasar Burtaniya ta girmama Hajiya babba
tare da ba ta nata 'yancin kan a ranar 1 ga watan Oktoban 1960.
17. Mauritania:- Faranta ta zaɓi
bai wa Mauritania 'yancin kai a ranar 28 ga watan Nuwamban 1960 saboda tsattsar
biyayyarta.
Daga:
Mohammed Bala Garba, Maiduguri.
02/10/2023.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.