Auren Jinsi (Lesbianism Da Homosexuality) Sun Zamo Ruwan Dare

    TAMBAYA (39)

    Dan Allah inaso a taimaka ayi write up mai dumi akan mata masu Neman yan uwasu mata wllh kazantar ta yi yawa takai har basajin kunyar bayyana kansu a cikin jamaa. Menene hukuncinsu (Daga: Abu Said BUK)

    AMSA

    Innalillahi wainna ilaihirrajiun

    Rashin kunyar bayyana kansu a cikin jama'a yanada nasaba da raguwar imaninsu, kuma daman ya tabbata a hadisin Abu Hurairah RA ya ce ma'aiki SAW ya ce mutumin da yake aikata zina ana a cire masa imaninsa ne, imanin zai dinga yawo a saman kansa kamar hadari, bayan ya gama zinar sai imaninnasa ya dawo jikinsa (Abu Dawud da al-Hakim suka rawaitoshi, Shaikh Albani ya ingantashi a cikin Silsila Ahadis-Assahiha mai lambata 509)

    Lesbianism ga mata wadda ake kira da madigo da hausa basada banbanci da Homosexuality ga maza wato Luwadi halayyar wasu daga cikin mutanen Annabi Lud AS, jinsi ne kawai ya banbantasu amman sun kasance daga cikin manyan alkaba'ir wadanda kan iya zama silar salwantar imanin mai aikatawa idan bai tuba ba, a karshe a tashi mutum cikin al'ummar Annabi Lud AS wadanda Allah ya hallakar

    A binciken da nayi kwanannan naga wasu Archeologist (masana tarihin ragowar kasa da abin da ta kunsa tun zamanin da) sun gano wani gunki mai suffar mace a garin da aka halakar da mutanen Annabi Lud AS (Ana kiran wajen da "Dead Sea" wanda yake a kasar Jordan) da sukayi bincike sai sukaga gunkin macen ya dace da abin da ya faru a yankin shekaru dubunnai da suka gabata (Wallahu a'alam)

    Allah SWT ya sanardamu irin zunubin da mutanen Annabi Lud AS suke aikatawa na neman jinsi a cikin Suratul A'araf ayata 80:

    "Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa: "Shin, kunã j wa alfãsha, bãbu kõwa da ya gabãce ku da ita daga halittu?"

    81) "Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã j wa maza da sha'awa, baicin mata; Ã'a, kũ mutãne ne maɓarnata."

    82) "Kuma bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa, fãce ɗai suka ce: "Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasumutãne ne mãsu da'awar tsarki!"

    83) "Sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyãlansa, fãce matarsa, ta kasance daga mãsu wanzuwa"

    84) "Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda ãƙibar mãsu laifi ta kasance!"

    Haka kuma bayanin hallakar da tsohuwar (wato matar Annabi Lud AS) da kuma mutanensa ya zo a cikin Suratu Ash-Shu'araa daga ayata 165 har zuwa ayata 175:

    165) "Shin kunã j wa maza daga cikin talikai?"

    (Yana nufin kuna luwadi ?)

    166) "Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarwa!"

    167) Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."

    (Ya zama tilas ga kowanne musulmi ya yi hani kuma ya qyamaci wannan ta'asa ta auren jinsi kamar yanda Annabi Lud AS ya qi sa)

    168) Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa."

    169) "Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa."

    170) Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya

    ( إِلَّا عَجُوزًا فِي الْغَابِرِينَ )

    171) Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa

    (Wannan tsohuwar ita ce matar Annabi Lud AS, wadda masu bincike suka gano gawarta a suffar dutse wanda ke daukeda sinadarin gishiri a kasar Jordan. Wallahu a'alam)

    172) Sa'an nan kuma Muka darkãke wasu

    173) Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana

    174) Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba

    (To ammanfa dukda haka idan sun tuba Allah mai Jin Kai Ne ga bayinSa kamar yanda ya rufe labarin da:)

     

    ( وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ )

    175) Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai

    Hakama a cikin addinin Judeo-Christian (Juda/Nasara) an haramta wannan babban laifi a cikin littafin Genesis Surah ta 19 ayata 4 zuwa 11, a cikin labarin Sodom da Gomorrah (mutanen Annabi Lud AS) sannan kuma Clement na Alexandria da Novatian ya kawo qwararan hujjojin haramcin madigo da luwadi inda ya ce yana cikin al'adun yahudawa qyamatar wasu dabbobi kamar irinsu zomo da weasel saboda nuna wasu sababbin dabi'u ya yin jima'insu (ma'ana suna auren jinsinsu) to indai yahudawa za su qyamaci dabba silar wannan mummunar dabi'a ta auren jinsi ai mu musulmai ne mukafi cancanta mu tsani wannan kazamar dabi'a (Karin bayani yana cikin littafin "World Of Homosexuality" ma'ana "Duniyar Yan Luwadi" babin "Addini da Luwadi" shafi na 39, wallafar shahararriyar Marubuciyar India, Shekuntala Devi)

    Zanso mutane su karanta daya littafin nata mai suna "World of Lesbianism" ma'ana "Duniyar Yan Madigo"

    Wasu sun mai da abin sana'a wadda da ita suke ci suke sha harma su dinka sutura. ya yin da wasu kuma shaidan ya qawata musu laifin a matsayin dabi'a, qwalamar son abin duniya da kuma rashin kiyaye al'aura ke sa shaidan ya qawata musu zunubin a matsayin dabi'a wadda yana wahala kaga mutum ya tuba, sai fa wanda Allah SWT ya tseratar. Haka kuma yawan kallace-kallacen fina-finai yana taka muhimmiyar rawa wajen fadawa tarkon zina, madugo da luwadi domin kuwa wasu abubuwan mostly anan ake koyonsu. Addu'ar da Ma'aiki SAW ya roqa ta kada Allah ya halakarda al'ummarsa kamar yanda ya halakar da na baya ita ce dalilin da ya sa har yanzu Allah bai sa an halakar damu ba dukda cewar laifuffukan da mukeyi ma sun shafe na al'ummar da suka gabacemu

    Gashi mun tsinci kanmu a wani zamani na hauhawar farashin komai da komai, to wannan jarabawace kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin Suratul Mulk ayata 2, kuma idan mutum ya ci test din ya kiyaye hannunsa daga sata silar talauci, ya kiyaye abin da ke tsakanin cinyoyinsa (farjinsa kamar yanda Allah ya fada a cikin Suratul Mu'uminun ayata 5) dakuma abin da ke tsakanin lebbansa (wato harshensa, Mu'uminun ayata 3) to Allah yana masa albishir da Aljannah (Mu'uminun ayata 10 zuwa 11) idan kuma masu kuɗi sukai amfanida kudinsu wajen lalata mata da maza ta hanyar sakasu a wadancan kazaman hanyoyi to saidai muce "Inna rabbaka labir mirsad" maana "Allah yananan a madakata" yana jiran kowa. Zabi ya rage namu

    Rashin ambaton Allah shi ne dalilin dayasa muketa kidimewa, yanzu dai ka duba kaga mutane duk sun daga hankali akan tashin farashin petrol, to idan Dajjal ya bayyana wanne halin rikici za a kasance ke nan, kaga ai sai wanda Allah ya tserar kawai. Kuma daga cikin yawan wadanda za su bi Dajjal a karon farko sune yahudawa 70,000 sannan kuma sai mata dayawa da kuma yayan da aka haifa ta hanyar zina wanda kuma ya tabbata a cikin hadisin Abi Umamah Al-Bahili RA ya ce: Ma'aiki SAW ya ce: "An nunamin a cikin mafarki na ana yiwa wasu maza da mata azaba a cikin wani kwatami mai tsananin doyi, da na tambaya sai aka cemin ai wannan mazinata ne" (Ibn Khuzaima lambata 1986 da Ibn Hibban da wasunsu sannan Nasiruddin Albani ya ingantashi a cikin Sahihut Targhib lambata 991)

    A kula: Wannan fa makomar mazinata ke nan wadanda ba su tuba ba, ina kuma ga makomar masu luwadi da madigo ?

    A shawarce ina son nayi amfanida wannan damar wajen janyo hankalin iyayenmu da kuma malamai akan su daina amfanida littafin "Queen Primer" Part II wajen koyar da yayansu na Nursery da Primary domin kuwa manufar mawallafan wannan littafin (Nelson Publishers Limited) shi ne su koyawa yayanmu musulmai aqidar auren jinsi (Homosexuality, Lesbianism da ake kirada LGBTQ). A shafi na 5 cikin littafin sun rubuta "Let us be gay. Let us run" ma'ana "Mu zamo gay. Mu gudu". Sai kuma shafi na 22 inda suka rubuta "Is this the way. Yes, let us be gay" ma'ana "Wannan ce hanyar. Eh, mu zamo gay" (Wal'iyazubillah). Silar hakan tuni gwamnatin jihar kano ta umarci malaman Nursery da Primary da su gaggauta dakatarda amfani da irin wannan littafin da makamantanshi wajen koyarda yayanmu yaren English

    Hakama a hanasu kallace-kallacen Tom & Jerry domin kuwa akwai bincike mai zaman kansa da nayi wanda babu lokacin fayya ceshi anan. Sannan kuma a hana yara amfanida Games irinsu Subway Surfers wadda itama a hankali a hankali sun fara bayyana manufarsu ta auren jinsi ta hanyar updating game din da wata sabuwar fuska mai suna "Rain" yar jihar New York da ke Amurka mai sanye da kaya launukan bakan gizo (Rainbow) wanda daman shi ne alamar masu aqidar auren jinsi (LGBTQ). Na bibiyi posting dinsu inda sukace "Subway Surfers da hadin gwiwar LGBTQ da kungiyar taimakon marayu na muku maraba da sabon tsarinsu". Sun saka kungiyar taimakon marayune saboda yawancin marayu sunada naqasu da kuma neman taimako na gaggawa musamman idan akwai qarancin fahimtar addini a taredasu. Kumadai munsan yanda wannan Game ta Subway Surfers ta samu karbuwa sosai. Saidai muce Allah ya tsare mana imaninmu baki daya

    A karshe ina mai bawa kaina shawara da kuma masu karanta wannan sako da ma sauran musulmi baki daya, da mu yawaita istighfari, sannan mu yawaita halartar karatuttukan addini ko don samun bonanzan taka fuka-fukan mala'ikun rahama, zanso mu nemi littafin "Adabul Mufrad" wallafar Imam Al-Bukhari, mu karanta littafin "Talbis Iblis" wallafar Ibn Al-Qayyim dalibin Ibn Taimiyya kuma mahaifi a wajen Ibn Khathir, a littafin zakagane yanda Iblis yake danawa musulmai tarko, kai har malamai ma bai barsu a bayaba

    Sannan mu karanta littafin "Zaadul Ma'ad" wato "Guzurin Alqiyama" na Ibn Al-Qayyim" domin kuwa ko sanda aka sakani makarantar boarding saida aka hadani da Provision (Guzuri) ballantana kuma zuwa Lahira, tabbas ita yakamata a hadawa guzuri tun da zuwanta ya zama dole

    Ku tayamu yada wannan saqo, Allah kadai ya san adadin mutanen da za ka zama silar shiriyarsu

    Amsawa

    Usman Danliti Mato, (Usmannoor_As-salafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.