Daurin Bakake Masu Kugiya

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa 

    188. Ɗaurin ƙugiya ko ba wanda ya korai,

     An kuma fid da ƙaida kuma ta aurai,

     Ba a hana shi ko kaɗan kuma ban sa rai,

     Harafi in da ƙugiyatai aka ɗaurai,

      Dole a bar ta liƙe nan ba a cirewa.

     

    189. Za ka ji ta fito cikin lafazi sosai,

     Haka nan za ka sa shi, sai ya fita sosai,

     Ba nashe shi, kana ba a kuma yassai,

     Furucin lanƙwasar tana nan  dai sosai,

    Kuma a rubuce ƙugiyar ba ta gushewa.

     

    190. Ɗaurin in ya kama ‘ƙ kai dai ƙyale,

     Ba a cire shi dole sai dai a yi lele,

     Kalmomin da sun ka zo nan ga misale,

     Ƙaton nan ƙafarsa duk ta ƙaƙƙalle,

      Kuma ya yunƙura shina tattakawa.

     

    191. To dai ga su yadda za ka rubutawa

     Raggo in an kirai yana ɓoɓɓoyewa,

     Ƙaƙƙarfan ƙanen ga nau bai ɓoyewa,

     Ɓaɓatun gyaɗa wuta ƙoƙƙonewa,

      Ga maciya a zaune sai ɓaɓɓarewa.

     

    192. Riga in ta tsufa sai ta ɓaɓɓarke,

     Damma ga su ɗaure yanzu a ɗaɗɗauke,

     Na ga buhuhuwan hatsi an ɗiɗɗinke,

     Wasu ɗaɗɗaure bakunan nasu a tsuke,

      Ga wata tashe yanzu sai ɗuɗɗurawa.

     

    193. In ka lura ƙugiya ba ta sauya ba,

     An jera su ka ga dai ba a canza ba,

     Ga misalin da yat taho in ka duba,

     Kowace ƙugiya a nan ba a karye ba,

    Kuma mai ƙugiya kawai aka ɗaurewa.

     

    194. Duk sautin da za ya ɗaure shi kalar shi,

     Ba a rubuta kowane dole a sa shi,

     Shi mai ƙugiya idan an ɗaure shi,

     Duk harafin da kas sani bai ɓoye shi,

      Sai mai ƙugiya kaɗai za ya biyowa.

     

    195. Je ka yi binciken abin ga ka tantance,

    Shiga littattafai ka nemo su nazarce,

    Kai nazari ka duba komi ka karance,

    In ka gan shi sai ka zana a rubuce

    Masana sun aminta mu ba mu musawa. 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.