Ticker

Daurin Harafin ‘M’ A Karshen Gaba

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

157. Harafin ‘m’ idan baƙi ya ɗaure shi,

 A rubuta shi kar a yarda a canza shi,

 Kwai doka da an ka tsara ta a kan shi,

 Sautin ‘m’ a nan yana da muhallin shi,

  Ba tsakiyar gaɓa ba can gun ƙarewa.

 

158. Sautin ‘m’ idan ya zo ga misalin nan,

Wato ya taho da amsa-kama ke nan,

 Ɗaurin ‘m’ yana da gurbin a wurin nan,

 To kuwa dole ne a sa ‘m’ a wurin nan,

  Haka nan za a sa shi ba a juyawa.

 

159. Kalmomin da ke da ‘m’ ga su a jingim,

Ringim, can Kaduna sannan ga dinkim,

A misali muna da zungum! Ko tinjim,

Haka ma ba ka sauya ‘m’ kalmar birjim,

Ga kalmar rugum! da tsundum! ta shigewa.

 

160. Kalmomin da ad da ‘m’ ba a taɓa su,

 Ba a saka ‘n’ a ƙarshen bagirensu,

 Duba waɗannan ka gane dukkan tsarinsu,

Haka kalmar kwaram! Da jingim! Ga zubinsu,

Ko kalmar kurum idan ka ƙi muɗawa.

 

161. Duk ƙarshen gaɓa a nan ‘m’ aka sawa,

Kalmomin ga mun ga ‘m’ aka ɗaurewa,

Kar ka bari ka kama hanyar ruɗewa,

Sautin duk da yat taho ba canzawa,

  Ba a rubuta ‘n’ a nan ko farawa.

 

162. Sai a kula da kyau a nan masu rubutu,

 Ko da kun ji ‘n’ a sauti ta furtu,

 Sa natsuwa da kyau a loto na karatu,

 Kar ka murai ku sanya ‘n’ nan ga rubutu,

Don aikinka kar ya zam mai kwaɓewa.

 

163. Haka aka tabbatar hukuncin malammai,

 Ba sa sauya ƙa’ida, ba rage komai,

 A bi littattafai a koma a yi maimai,

 Ai nazarin ƙwaƙwaf a tambayi malammai,

  Ba makawa ga ɗalibai sai amsawa.

Post a Comment

0 Comments