Ticker

    Loading......

Daurin Harafin ‘n’ Cikin Mallaka

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Ɗaurin Harafin ‘n’ Cikin Mallaka

147. Babu rikirkiɗa kamar ‘n’ ga rubutu,

 Ta taka rawa ga mallaka nan ga rubutu,

 Gun nasaba akwai ta kun jiya masu karatu,

 Haka jinsi akwai ta, komi ya saitu,

Sa natsuwa da kyau ka zan bambantawa.

 

148. In ta shigo a mallaka gun kalma ɗai,

 Ita ko mallaka iri biyu ce daɗ ɗai,

 Ga mu da doguwa, gajera su ne ɗai,

 To ita ‘n’ ga mallaka, kuma kalma ɗai,

  Ga harafi kusanta ɗan leɓancewa.

 

149. Harafin duk da zai biyo bai canza ta,

 Ba a rubuta ‘m’ fa, ‘n’ za a rubuta,

 Masana sun ka ce a nan ba a taɓa ta,

 Ta kuma samu kariya gun ‘yancinta,

  Ta shiga mallaka a nan sai ƙyalewa.

 

150. Ko harafin da ke biyan ta baleɓe ne,

 Ko da ‘b’ da, ‘f’, da ‘ɓ’ kai ko ‘m’ ne,

 Ba a rubuta ko guda malam gane,

 Ita ‘yanci gareta tsarin doka ne,

  Ba ta rikirkiɗa ta zan mai sauyawa.

 

151.  Lura da ‘n’ da za ta zo ga misalinmu,

 ‘Yan yaranmu, ‘Yan’uwanmu, ka kishinmu,

 Duba Garinmu, yai fice nan lardinmu,

 Ga gonanmu ga abinmu abin sonmu,

Wasanninmu, harsunanmu na zantawa.

 

152.  Jimlolin da sun ka zo ga misalanmu,

 Duba su da kyau akwai baleɓen sautinmu,

 Bai kuma nashe ‘n’ ba dama ta samu,

 Shinkafinmu, Cefanenmu na jarinmu,

Gonakkinmu, karkaranmu ta nomawa.

 

153. Ita dai mallaka da ta zo a rubuce,

 In ‘n’ ta taho ga kalma a misalce,

 To a saka ta babu laifi hujja ce,

 Matuƙar mallaka gajera ta kasance,

  Harafin ‘n’ cikinta ba ya sauyawa.

154.  Ko harafin da ke biyarsa baleɓe ne,

 Doka za a bi a kyale ko me ne,

 Sai a saka ta ko’ina ko ka gane?

 Kai ko ma wane haraf yaz zam gane,

  Ba a kula da shi a nan ba saɓawa.

 

155. Duba nan ƙasa ka gane bayaninmu,

 Ba a rubuta, cefanemmu, da jarimmu,

 Gonakkimmu, karkarammu, abincimmu,

 Ba a rubuta rigunammu na ɗakimmu,

Ko babammu mai gidammu na ganawa.

 

156. Laifi ne hakan ga tsarin harshenmu,

 Ba ka sauya ‘n’ da ‘m’ a rubutunmu,

 Sai dai rigunanmu koko ɗikinmu,

 Sanya gidanmu ko ka zana danginmu,

Ko babanmu mai gidanmu na gadawa.

Post a Comment

0 Comments